Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Uku

0
6

Sai bayan la’asar suka dawo tare kamar yanda suka fita, a lokacin yara suna islamiyya. Don haka cikin walwala ya ƙarasa ciki don ya san Khadeeja ta kular masa da yaran. Sai da ya leƙa parlor ɗinta ya gaya mata ya dawo sannan ya wuce ɗakinsa. Yara suna dawowa daga islamiyya suka wuce parlor ɗin Naja inda suka jiyo su ita da Abbansu.

Kafin wani ya yi magana Shukra ta faɗa jikin Naja tace ‘Yauwa Anti kin dafa mana abinci ko? Wallahi yau gari muka sha mu da Anti, tace idan kin dawo za ki dafa mana abinci. Ta kalli Mustapha sanna ta sake kallon Shukran, kafin tace wani abu Mustaphan ya janyo Shukra jikinsa yace ‘Gari kuka ci Shukra?’

Ta ɗaga masa kai. Nan take ragowar yara suka tabbatar masa da haka aka yi. Ya kalli Afaf wadda shigowarta kenan tana ƙoƙarin zama yace ‘Ke ba sai ki dafa muku ko indomie ba ce? Ta zumɓura baki ta kawar da kai ba tare da tace komai ba. Ya yi gajeren tsaki sannan ya dubi Nasreen yace ‘Ina Hafsa? Ita ba sai ta dafa muku ba?’

‘Ita ma garin ta ci ai, Anti ba ta ce ta dafa komai ba haka tace mu jira Anti Naja ta dawo ita ce da girki. Ya kalli Najan wadda take ta faman cika tana batsewa, ya miƙe a fusace ya fice daga parlor ɗin. Tana zaune a parlor ɗinta tana shan kunun alkama ya same ta.

Kafin ta gama amsa sallamarsa ya fara magana a fusace ‘Khadeeja wane irin raini da wulaƙanci ne zai saka ki ba wa yara gari, ke ba za ki girka musu abinci ba kuma ba za ki saka yarinyarki ta girka musu ba. Ta ajiye kofin kununta ta kalle shi tana jijjiga kai sannan cikin halin ko in kula tace ‘To ai mai girkin ba ta bar musu abinci ba kuma ba ta barwa yarinyar tawa wani abu tace ta dafa musu ba, shi yasa da aka ji yunwa na haɗa mana gari duka muka sha. Ina laifi?’

Ya fesar da iska mai zafi saboda yanda takaici ya kama shi, ba ya son yanda idan Khadeeja za ta yi masa fitina take zama da nutsuwarta shi kuma tana saka shi yana yin spark. ‘Khadeeja, don Allah me kike so ne kike min wannan wulaƙancin? ‘Ba wulaƙanci nake maka ba. Abu ɗaya kawai nake so shi ne ka yi adalci.

Yanda nake buƙatar hutu daga kwana saboda jego haka nake buƙatar hutu daga hidimar gida da ta yara, don dama wallahi dagewa nake yi. Idan kuka gama arba’in ɗin muka fara rabon kwana sai na dinga haɗawa ina karɓa. Ya ja dogon tsaki ya yarfar da hannu, har ya buɗe baki zai yi magana kuma sai ya fasa. Ya juya ya fice daga parlor ɗin.……..

Duk yanda yake tunanin Khadeeja za ta saurara masa hakan bai samu ba. Yana so ya mayar mata da kwananta da ya karɓa ya ba wa Naja amma kuma yana son ƙarin lokaci don ya ƙara sabawa da Najan. Haka dole ya haƙura ya zuba musu ido; sai dai duk wani jin daɗi da yake sa ran zai samu daga wajen Najan ba ya samuwa saboda yanda take wuni a gajiye saboda hidima.

Suna kwanciya bacci yake kwashe ta; ga shi kullum cikin yi masa mita take a kan ita ya mayar da hidimar yara wajen Khadeeja. Duk da kusan Khadeejan ta sallama musu Hafsa tana taya ta. Ita kuwa Khadeeja gaba ɗaya haushinta yake ji don gaba ɗaya ya daina kula ta, a yanda yake ji yanzu ma ba ya jin zai kula ta koda ta yi arba’in ɗin idan dai ba itace ta kawo kanta ta ba shi haƙuri ba.

Duk yanda Naja ta za ta kula da yaran nan zai yi mata sauƙi abun ba haka ba ne, domin da ƙyar take kai wa yamma saboda gajiya. Ga shi Khadeeja ta sallama musu Hafsa kullum cikin taimaka mata take; abu ɗaya da Khadeeja ta hana Hafsa yi mata shi ne girki. Ta so ƙwarai a ce ta dinga bar wa Hafsa tana yi musu girki idan ta fita, amma Khadeeja ta ƙi bari.

Don haka kullum kafin ta fita aiki sai ta dafa musu abincin rana kuma idan ta dawo sai ta yi na dare. Ga shi duk da suna shiri da Afaf ta gane Afaf ta fita son jiki, don duk yanda take jin za su taya ta aiki hakan ma bai samu ba.

Yau satinta biyu da tarewa; yana zaune a parlor ɗinta shi da yaransa kamar yanda suka saba suna kallon TV bayan sallar isha’i. Ita kaɗai ce a tsaye tana ƙoƙarin jera abincin dare a dining. Tana jerawa tana mita a ranta yanda yaran ba sa taya ta aiki, ko da za ta ce su taya ta to fa idan dai yana nan ba za su taya ta ba; sai dai ta yi aikinta ita kaɗai.

Gashi kuma ba ya son Hafsa ta dinga yi masa girki. Bayan ta gama jera abincin suka taso gaba ɗayansu suka zauna har da ita suna cin abinci. Jollof sphagetti ce da kifi; ana cikin cin abincin Shukra ta ɗaga kifin da yake kwanonta tace ‘Abba a cire min ƙaya. Har ta buɗe baki za ta ce Afaf ta cire mata ya yi sauri yace ‘Ki miƙowa Antinki ta cire miki.’

Haka Afaf wadda take zaune a tsakanin Najan da Shukran ta ɗauki plate ɗin da yake gaban Shukran ta miƙawa Naja. Ba tare da ta ce komai ba ta sa hannu ta ɓara kifin gida biyu ta cire ƙayar sannan ta miƙawa Afaf wadda ta sake miƙawa Shukra. Haka har suka gama cin abincinsu babu wanda Naja ta sake yi wa magana.

Tana zaune a gefen gado tana shirin kwantawa bacci ya tura ƙofar ya shigo da sallama, da ƙyar ta amsa sallamarsa saboda yanda take jin haushinsa. Gani take kamar da gayya ya bari matarsa ta sallama mata yaran sannan kuma sun kai su kula da kansu amma komai sai yace sai ta yi musu.

Ya ƙarasa ya hau gadon ta bayanta ya kwanta, tana kwanciya ya janyo ta jikinsa. Ta ɗan ture shi tana cewa ‘Bacci fa nake ji Habibi, wallahi na gaji. Kuma ka ga gobe yara za su makaranta kuma zan je aiki. Ya ƙara ƙanƙame ta yana laluba jikinta yana cewa ‘Sannu, bari na yi miki massage yanzu gajiya za ta sauka.’Ta dage ta janye jikinta ta zauna a kan gadon, hakan ya sa shi ma ya tashi ya zauna a kusa da ita yana kallon fuskarta kamar mai neman amsa a fuskar tata.

Kafin ya yi magana ta langaɓe kai tace ‘Habibi ni dai don Allah ka mayarwa da maman Hammad kwananta, in ya so mu cigaba da yi kwana bibbiyu yanda tsarin yake. Da mamaki ya kalle ta suka haɗa ido sannan yace ‘Kin gaji da ni kenan Baby. Ta miƙa hannu ta shafi gefen fuskarsa tana murmushin yaƙe sannan tace ‘Ya za a yi na gaji da kai, ni kam ai ban ƙi ba a ce ni kaɗai ce matarka kullum muna tare.

Amma ka ga aiki yana yi min yawa sosai, yi wa yara abinci kaɗai ya ishe ni da shirya su makaranta. Kullum a gajiye nake kai kanka ba ka samun yanda kake so a wajena. Amma ka ga idan zan dinga samun kwana biyu a tsakani na huta ai ina ga hakan zai fi mana sauƙi ko?

Tunda nace a ɗaukar min mai aiki ka ce Hafsa ta ishe mu; ita kuma wannan yarinyar wallahi ƙarin aiki ce saboda ta fi su wasa da son jiki. Ni ban ma san yanda aka yi Khadeejan take zama da ita ba. Kawai dai kace ta karɓi kwananta. Har ta gama maganar yana bin ta da kallo ba tare da yace komai ba, sai da ta gama ta numfasa sannan yace ‘Um haka ne, amma dai ai kin ga kula da yaran yanzu fa ba wani aiki ba ne tunda gaba ɗayansu kowa ya iya kula da kansa.

Kusan za a iya cewa abinci ne kawai sai an dafa musu. Ta kalle shi suka haɗa ido. Har ta buɗe baki za ta yi magana kuma sai ta fasa; ta kula ba so yake ya karɓi uzurinta ba. Yaran da hatta kula da kan nasu ma da yake cewa sun iya idan dai ba ta tsaya a kansu ba babu wanda zai yi, idan kuma aka bar su haka yace zai yi wa mutane fada.

Ta ja numfashi sannan tace ‘To ka dai mayar mata da kwananta don Allah, a fara rabon haka tunda ka ga yanzu saura kusan sati uku ta cika arba’in ɗin. Ya numfasa ya zame sannan ya janyo ta jikinsa ta gyara mata kwanciya yana shafa bayanta sanna yace ‘Kada ki damu, in sha Allahu da safe zan yi mata magana. Ai na san kina ƙoƙari wajen kula da yaran nan kuma suma za ki ga suna jin daɗin zama a wajenki, nagode sosai da kike kula min da su.’

A haka dai ya samu ya lallaɓata suka kwanta. Ya san wulaƙancin Khadeeja, tabbas idan ya je yace mata za a fara rabon kwana yanzu ba lallai ta saurare shi ba. Baya jin ma zai iya tunkararta da wannan maganar idan dai ba so yake ta yi masa dariya ba. Haka ya cigaba da lallaɓar Naja don ba ya ma son ya tayar da maganar mayarwa da Khadeeja kwananta da ya ƙwace.

Tunda ta kwana ashirin da bakwai da haihuwa ta yada wankan jego, kuma da yake ita ɗin mace ce wadda ta damu ta fatarta sai ta mayar da hankali wajen gyaran fata da gashin kanta waɗanda ruwan zafi ya ɓata. A zaman da suke yi da Mustapha ta san yana jin haushinta saboda ta ƙi ta cigaba da kula da yara shi da amarya su yi amarci, ta san ba lallai ya ba ta wasu kuɗi ba.

Don haka ‘yan kuɗaɗenta da ta samu a barkan Hammad su ta fito da su ta nemi Baffanta ya ƙara mata dubu goma sannan ta haɗo kayan gyaran fata. Nan da nan cikin sati guda haske da santsin fatarta ya fara dawowa. Kamar yanda ya saba kullum da safe zai leƙa su gaisa kafin ya fita. Yau ɗin ma haka ya shigo parlor ɗin da sallama.

Suna zaune a parlor ɗin ita da Habib suna cin abinci; ita tana zaune ta miƙe ƙafa da Hammad a kan cinyarta yayin da shi kuma Habib yake zaune daga gefenta yana cin nasa abincin. Funkaso ne ta soya da zafinsa tare da parpesun kaza suke karyawa da shi; don kanta ta dafa farfesunta amma ta riga ta saba shi Habib idan dai tana nan ba ya cin abinci a wajen Naja.

Don haka idan dai ya shigo ba ta hana shi, domin wani lokacin ma ajiyewa take yi don ta san zai zo nema. Ya ƙarasa ya zana a kan kujera daga kusa da Khadeejan, bayan ya amsa gaisuwarsu yace ‘Nan kuka ƙule kuna cin daɗi ashe shi yasa na ji shiru. Ta yi dariya kawai ba tare da tace komai ba, Habib ne yace ‘To ai Abba Anti Naja tuwo ta dafa jiya na san ɗumame za a ci shi yasa na gudo.’

Suka yi dariya gaba ɗaya. Ta san so yake yace zai ci domin yana son funkaso, ita kuma ba ta so yace zai ci saboda dafawa ta yi har abincin rana tunda so take ta fita idan ta dawo kawai sai ta ci abunta. Ya dube ta tana cinye funkason ƙarshen yace ‘Idan akwai funkason ki zuba min na ɗan ci, duk da dai na yi breakfast amma ya ba ni sha’awa.’

Ji ta yi kamar tace masa babu, amma Allah ya sa ba ta iya rowar abinci ba, musamman ga mutumin da shi ya kawo cefanen. Don haka bayan ta cinye nata ta miƙe ta kwashi kwanukan ta shige kitchen bayan ta miƙawa Mustaphan Hammad; Habib shi ma ya kwashi nashi kwanukan ya bi bayanta.

Jimawa kaɗan suka fito tare, ta kawo tray ɗin da ta riƙo ta ajiye a gaban Mustaphan sanna ta sa hannu ta karɓi Hammad; shi kuma Habib ya fice daga parlor ɗin.Ya sauka ƙasa ya fara cin abincin sannan ya dube ta yace ‘Shi ne kin yi funkaso ko ki kirawo ni. Ta yi ‘yar dariya tace ‘Ai na san ka riga ka ci better ka cika cikinka shi yasa na sa yarona a gaba muna ci mu kaɗai.

Ya yi dariya ya mayar da hankali wajen cin abincinsa. Jimawa kaɗan ta tashi ta shige ɗaki, ba ta daɗe ba ta fito tana riƙe da takarda a hannunta. Sai da ta zauna sannan ta miƙa hannu ta ajiye takardar a gafensa tana cewa ‘Ga posting letter ɗina, jiya na karɓo. An yi posting ɗina gidan talabijin na ARTV.’

Nan da nan ya ɓata rai, bai ce mata komai ba sai da ya ƙarasa cinye abincin sanna ya dube ta yace ‘Kin san dai ba na son aikin jaridar nan ko, sai da nace ki saka a yi posting ɗinki makaranta amma shi ne kika je kika saka aka kai ki gidan talabijin don ki dinga fitowa a TV.’

Ta kawar da kai tana mamakin Mustapha. Tana karatunta na aikin jarida ya ganta ya auro ta amma tunda ya ga ta kusa gamawa yake ta faman gaya mata aiki ɗaya zai bari ta yi shi ne koyarwa. Wataƙila ma da a ce bai ƙara aure ba da ta haƙura ta yi koyarwar amma yanzu kam babu yanda za a yi ya auro amaryarsa tana aikin office duk da dai ba na TV ba ne; sannan ita yace koyarwa za ta yi.

Tace ‘Ni ba ni nace su kai ni can ba, sun duba abinda na karanta ne kawai. Kuma idan nace a kaini makaranta na je na koyar da su me? Ni da na karanci aikin jarida.’Cikin halin ko in kula yace ‘Ko Hausa ba sai ki koyar ba ko English, amma kin san babu yanda za a yi na barki kina fitowa a gidan TV duk duniya suna kallonki kina iyayi ko?’

‘To yanzu ya kake so a yi? Ki je kawai su canza miki, idan kuma ba haka ba ni zan je a canza amma ba za ki yi aikin TV ba matuƙar da aurena a kanki ba na so. Ta ɗan gyara zama tace ‘To ai ko na je gidan ARTV ɗin ma ba lallai na dinga fitowa a TV ba tunda aiyukan suna da yawa kuma ba duk ma’aikatan ne suke fitowa a TV ba.’

Ni dai ba na son ki je wajen kwata-kwata tunda idan dai kana wajen wata rana za a saka ki a wani shirin kuma babu yanda za ka yi. Kawai ki je su mayar da ke makaranta ko kuma ki ba ni takardun ni na je.’ Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Ba ta ce komai ba yace ‘Ni na tafi gidan Hajia.’

‘A dawo lafiya, ka gaishe min da su.’ Ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba, kuma da yake shi ma ba kallon nata yake yi ba bai ma san yanayin da take ciki ba. Ta bi bayansa da kallo bayan da ya fice daga parlor ɗin; ta ma rasa me za ta ce masa. Koyon aikin jarida ya ganta tana yi ya auro ta, kuma sau da dama ta sha gaya masa cewa babu abinda take so take buri kamar a ce yau ga ta a gidan talabijin tana karanta labarai ko kuma gabatar da wani shiri.

Sai da ta kusan gama karatun sannan yake sanar da ita shi ba ya son matarsa ta dinga fitowa a TV, kuma duk lokacin da ya gaya mata ana gaya masa cewa ita kuma burinta ɗaya kenan a duniya. Daga baya ne ma ta fahimci cewa da ba don ya auro Naja a ma’aikaciya ba to da tabbas ba zai bar ta ta yi aiki ba ma gaba ɗaya.

Yanzu kam ma sai ta ga kamar yana dai so ya takura ta ne saboda ba ta yi masa yanda yake so ba, amma za ta san yanda za ta ɓullo wa lamarin. Sai da ta bari dare ya yi lokacin ta san Baffa yana zaune a gida sannan ta kirawo shi, bayan sun gaisa ta sanar da shi abinda Mustapha ɗin yace game da inda aka kai ta bautar ƙasa.

Bayan a saurari bayaninta yace ‘To ke ki je makarantar mana, ai ba shi ne aikinki ba tunda bautar ƙasa shekara ɗaya ne kawai. Tace ‘To ai Baffa idan na je ina fatan ne su riƙe ni su ba ni permanent aiki, kuma ka ga Baffa gaskiya ba zan iya aikin koyarwa ba don za a dinga samun matsala da ni.’

‘Um haka ne, to bari mu gani. To ko gidan rediyo za ki je a mayar da ke? In ya so sai na yi wa Mustaphan bayani. Baffa ni dai da ka yi masa magana ya bar ni na je gidan TV ɗin. Yace ‘A a, ki yi haƙuri ki yi a gidan rediyo tunda dai yace ba ya son a dinga nuna matarsa a TV kin ga kuma hakan ya nuna yana kishinki. Ki je ki yi a gidan rediyo ta yanda ko da an saka ki a wani shiri to muryarki kawai za a ji ba za a ganki ba.’

Ta so ƙwarai a ce Baffa ya goya mata baya ta tafi gidan TV domin shi ya san tun tana yarinya burinta kenan, amma ta san tunda yace haka ba zai goya mata baya ba; sai dai idan ta matsa ranta ya ɓaci. Don haka sai kawai ta haƙura. Suka yi sallama da Baffa suka ajiye wayar.

Sati yana zagayowa ta fara bautar ƙasa a gidan radio na Freedom Radio bayan da Baffa ya kirawo Mustaphan ya yi masa bayani sannan ya ba shi haƙuri a kan ya bar ta ta yi a nan ɗin. Haka ya bari ba don ya so ba.

Tunda ta fara zuwa aiki kuma sai aikin gida da na yara suka ƙara taruwa suka yi wa Naja yawa. Domin sai ya zama kullum idan Khadeeja za ta fita da Hafsa take fita saboda riƙe mata Hammad a wajen aiki. Ganin haka ya sa Naja ta saka Mustapha a gaba sai da ya bari ta ɗauki mai aiki wadda take zuwa kullum tana tafiya da yamma; tunda ya ce ba za ta raba wa su Afaf wanke-wanke da gyaran gidan su dinga yi idan sun dawo daga makaranta ba.

Babu yanda ba ta yi da shi ya mayar wa da Khadeeja kwananta ba amma ya ƙi; saboda ƙi-faɗi. Duk da shi ɗin ma yanzu zai so a ce sun fara kwana bibbiyun tunda yanzu yana son shiga harkar Khadeejan; amma dai ya san Khadeeja ba za ta karɓi kwanakin nan da ta bayar ba tare da son ranta ba sai ta saka masa ciwon kai. Ita kuma ta so ta yi wa Khadeejan magana amma ba za ta yi ba.

Saboda kusan tunda ta zo gidan ba wata magana da take haɗasu da Khadeejan bayan gaisuwa; da yake ma Khadeejan ba mai son fitowa ba ce sai ya zama idan dai ba aiki za ta je ba to za su iya kwana biyu ma ba su haɗu ba. Haka suka cigaba da rayuwarsu.

Ranar Juma’a ce ta kama ranar da Khadeeja ta cika arba’in. Duk wani shiri ta gama yinsa, ta gama gyaran jikinta kamar yanda duk wata maijego take yi. Sai dai ba ta sa rai zai ba ta kwanan ba kuma ta ci alwashin ba za ta taɓa kai masa kanta ba sai dai shi ya kawo kansa. Bayan ta idar da sallar asuba sai ta sake bin gado ta kwanta tunda ta san Hammad ba zai taɓa wuce ƙarfe takwas yana bacci ba zai tashe ta.

Ba ta san iya tsawon lokacin da ta ɗauka tana bacci ba bugun ƙofar da ake mata ne ya tashe ta, a tare suka farka da Hammad wanda ya sa kuka. Ta lalubo wayarta ta duba lokaci inda ta ga 8:30am; nan da nan ta mutssike ido don ya kamata a ce kafin ƙarfe tara ta fita ta tafi gidan rediyo. Sai da ta ɗauki Hammad sannan ta miƙe ta buɗe ƙofar. Hafsa ta gani a tsaye; bayan ta gaishe ta tace ‘Anti na gama aikin gaba ɗaya na ga ba ki fito ba kuma jiya kin ce min na shirya da wuri za mu fita.’

‘Hmm! Bacci ne ya kwashe ni. Zauna ki jira ni na shirya Hammad na miƙo miki shi ni ma na shirya mu tafi. Nan da nan ta shirya Hammad ta miƙa shi wajen Hafsa suka zauna a parlor sannan ta koma ɗakin ta shiga wanka. A gurguje ta yi wankan ta fito ɗaure da ƙaramin farin tawul ɗinta, tana riƙe da wani tawul ɗin tana goge jiki. Mustapha ta hango yana zaune a gefen gadonta ya miƙe kafa yana kallo a waya.

Ba ƙaramin mamaki ta yi ba domin gaba ɗaya ta kasa tuna me yake jira. Ba wai ba ya shiga ɗakin ba ne amma dai tunda Naja ta tare bai zauna a ɗakin ba sai dai ya shiga ya gaya mata abinda zai gaya mata yana daga tsaye ya fice. Ta ɗan tsaya kaɗan ta kalle shi sannan tace ‘Ina kwana. Ya ajiye wayar ya amsa gaisuwar tata da fara’a. Ta ƙarasa gaban mudubi tana goge jiki yayin da shi kuma Mustaphan ya miƙe tsaye ya nufo ta.

Ya ƙarasa ya tsaya a bayanta ya rungumo ta ta baya, ta kalle shi ta cikin mudubin suka haɗa ido tace ‘Fita fa zan yi ka ga ma na makara. Ya yi murmushi ya saka bakinsa a kan kunnenta yace ‘Ni ma fita zan yi, amma dai kin san yau kin yi arba’in ko? Ta ɗan motsa saboda yanda yake ƙara shigewa jikinta tace ‘Um. ‘Ok, ki karɓi kwananki yau sai ki ajiye min dinner.’

Murya ƙasa-ƙasa tace ‘Toh. Ya sumbaci gefen wuyanta sannan ya sake ta ya juya. Har ya kusa zuwa bakin ƙofa kuma sai ya juya ya dawo, kafin ya ƙarasa inda take ita ma ta juyo don haka ya tsaya a gabanta. Cike da damuwa ya kirawo sunanta, bayan ta amsa yace ‘Bana jin daɗin yanda kuke zama da Naja kamar kuna gaba, please ki dinga ɗan zama a parlor ɗin kasa saboda ku saba.

Ta dan yi murmushi tace ‘Ba wata gaba da muke yi tunda muna gaisawa, kuma duk abinda ya kama na magana ai muna yi. Ya kalleta suka haɗa ido sannan ya riƙe ƙwayar idonta yana cewa ‘Duk da haka dai ki dinga dan zama a can kuna hira. Kin ga idan kina nan ba za ta shigo ba ita ma sai ta yi ta zama a parlor ɗinta inda ke ba kya shiga.’

Ba ta son ta ja zancen saboda ba ta son ta makara, don haka tace ‘To shikenan. Ya sake tsattsare ta da ido sannan yace ‘Please! Ta yi gajeren murmushi ta ɗaga kai. Ya fice bayan tayi masa a dawo lafiya. Ta ja tsaki bayan da ya fice; ba ta jin za ta iya raɓar Naja, ta tsaneta.

Wataƙila hakan yana da alaƙa da yanda Mustaphan ya ɓata mata rai a kan Najan tun kafin aurensu da kuma maganganun da ta gani a wayar Afaf da suna chatting da Naja. Gaskiya ba za ta iya hira da wata Naja ba, gashi kuma ba ta iya munafurci ba balle ta je ta yi na ƙarya. Shi dai da ya ga Naja yana so ya auro ta suje can su ƙarata. Cikin sauri ta karasa shiryawa suka fice ita da yaranta.

Tun kafin Magriba ta gama abincin dare, don haka Habib yana shigowa daga masallaci sallar magriba ta tura shi ya kirawo ƙannensa a wajen Naja. Nan suka zauna a parlor ɗinta suka ci abinci inda ta dafa macaroni da miyar hanta da salad. Suna gama cin abinci Afaf wadda dama bayan sallama ba ta ce mata komai ba ta tashi ta fice daga parlor ɗin. Sauran yaran kuma suka zauna a nan aka cigaba da hira ana kallon TV.

Wajen 8:30pm duk suka fara jin bacci don haka da kanta ta tashi ta raka su ɗakinsu, ta shirya shukra sannan ta tsaya Nasreen ma ta shirya suka yi brush suka kwanta sanna ta koma nata ɗakin. Shi ma Habib ya yi mata sai da safe sannan ya wuce nashi ɗakin. Har zuwa lokacin Mustapha bai dawo ba, sai dai ya yi mata waya ya sanar da ita sun fita da Alhaji don haka sai ta gan shi.

Don haka bayan ta yi wanka ta yi shirinta na bacci sai ta koma ta jera masa abincinsa a table ɗin parlor ɗinta sannan ta wuce ɗakinta ta kwanta. Sai wajen 9:30pm sannan ya shiga gidan. Kai tsaye bayan ya kulle gidan parlor ɗin Naja ya shige tunda ita ce a ƙasa. Tana zaune a kan kujera tana shan cornflakes ranta a ɓace. Ya ƙarasa bayan ta amsa sallamarsa ya sumbaci kumatunta sanna ya zauna a kusa da ita yana cewa ‘Cornflakes kike sha a daren nan?’

‘Um. To me gidan ce da girki kuma ba ta ba ni nawa abincin ba shi ne na haɗa cornfakes nake sha tunda ban saba zama da yunwa ba.’ Ta faɗa tana ƙara shan kunu. Ya ɗan shiga duhu, yace ‘Umm, Khadeeja ba ta yi abinci ba ne? Ta yi, amma nan ta turo aka kirawo yara suka je samanta suka ci abinci. Da suka gama cin abincin ma a can suka yi zamansu Afaf ce kawai ta sauko ta taya ni hira.’

‘Um! To ai na zata kowaccenku dama girkinta za ta dinga yi ko? Ta harare shi sannan tace ‘A ina ake haka? Tunda wadda take da girki ita ce za ta dinga kula da yara ai girkin ma gaba ɗaya za ta dinga yi. Shi yasa ni ma idan na yi abinci nake fito wa da shi nan parlor ɗin inda kowa zai iya ɗiba, ita ce ba ta fitowa ta ɗiba saboda ba ta son ganina.’

‘Wa ya gaya miki? Ba haka ba ne. Bari zan yi mata magana in ya so sai ta dinga yi da ke, ke ma ranar naki girkin sai ki dinga yi da ita kun ma ragewa kanku aiki. Ta zumɓura baki ‘Ah to don ni dai haka na san duk masu mace sama da ɗaya suna yi. Ya yi mata sallama ya wuce sama. Bata taɓa sanin idan Khadeeja ta karɓi kwana abun zai sosa mata rai ba sai a wannan lokacin.

Gaba ɗaya zucuyarta ta yi ƙunci, haka ta bi bayansa da kallo har ya fice daga parlor ɗin ya rufe mata ƙofa. Nan take hawaye ya wanke mata fuska; ta ajiye kofin da yake hannunta a kan tebur ta haɗa kai da gwiwa ta sa kukan da ta kasa gane me ya kawo shi. Haushin Khadeeja ta karɓi kwana ko kuwa haushin an barta da yunwa?

Yana ƙarasa shiga parlor ɗinsa ya kalli dining table, bai ga alamar abinci ba. Kamar ma ko taɓa wajen ba a yi ba tunda ya fita da safe. To me Khadeeja take nufi? Duk wannan ɗokin da yake na zuwa wajenta ita ashe ba ta gama fushin ba kuma ba ta gaya masa ba? Cikin sanyin jiki ya ƙarasa ya shiga ɗakinsa. Ga mamakinsa ɗakin ma ba a gyara ba.

Yanda Naja ta fita ta bar shi da safe yana nan a haka, babu ma alamar da take nuna mutum ya shiga ɗakin bayan fitarsa. Khadeejan ma da yake sa ran zai gani a ɗakin ba ta ciki. To ina take? Me take nufi bayan ya sanar da ita yau ita ce da kwana?

Gaba ɗaya  ranshi ya gama baci; ba ya son fitinar Khadeeja don ita rigima da ita ba ta ƙarewa, musamman a yanzu da yake da buƙatarta. Har ya juya zai fita kuma ya fasa, ya tsaya ya canza kaya ya shirya sannan ya ɗauki wayarsa ya fito ya nufi ɗakin Khadeejan.

Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Ɗaya

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceWasu Kayan Aikin Ƙira
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.