Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Huɗu

0
108

Yana shiga parlor ɗinta ya kai hankalinsa kan dining table, yanda ya ga wajen a jere da kwanuka ya tabbatar abincin ne ta dafa ta ajiye masa. To me yasa ta yi hakan? Ya ƙarasa kan tanle ɗin ya buɗe kwanukan ya ga abinda ta dafa, sannan ya taɓa flask ɗin ruwan zafi ya ji shi a cike; tabbas ya san shayi ta dafa masa.

Ya gyaɗa kai ya juya ya nufi ɗakinta. Duk da ita ba mace ce mai son mu’amala ta turaren wuta da humra ba amma dai tana son ƙamshi, tana da haɗaɗɗun turarkanta na jiki da na kaya waɗanda idan dai ta zauna a waje sai ka ji ƙamshinsu. Yana tura ƙofar ɗakin nata ƙamshin turarenta ya yi wa hancinsa maraba.

Fitilar ɗakin a kashe take sai dai dim-light wadda take ajiye a kan durowar gefen gado ita ce a kunne; ga alama bacci ne ya kwashe ta ba tare da ta kashe fitilar ba. Ya ƙarasa kan gadon inda take kwance, ya leƙa fuskarta; bacci take yi hankalinta a kwance ga shi yanayin baccin ya yi wa fuskarta kyau. Kamar ya ƙyale ta sai kuma ya canza tunani, ya zauna a hankali a gefen gadon daidai inda ƙafafunta suke, ya ɗaga abinda ta rufa da shi ya sosa mata tafin ƙafa a hankali.

Ta janye ƙafarta da sauri sannan ta buɗe ido a hankali hankalinta gaba ɗaya yana kan Hammad wanda yake kwance a cikin gadonsa na baby a gefen gadon nata. Ya yi dariya a daidai lokacin da ta gan shi, ya lakace mata hanci yana cewa ‘Yanzu mutum ɗaya ne a rayuwarki wato Hammad ko? Ke na taɓa amma ba abinda ya taɓa ki kike nema ba yaronki kike nema kada a taɓa miki shi.’

Ta yi murmushi ta mutssike idonta tana gyara zama sannan tace ‘To ina laifi, ni ce gatansa ka ga kuwa dole na kula da amanar Allah. ‘Haka ne. To a taso a ba ni abincina yunwa nake ji sosai. Ta zubo ƙafafunta daga kan gadon ta miƙe tana cewa ‘Bari na wanko baki. Ta wuce ta gaban shi ta nufi banɗaki.

Ya bi bayanta da kallo yana yaba yanda jego ya karɓe ta. Ya daɗe bai ganta a haka sanye da rigar bacci kamar wannan ta jikinta ba sai yau kuma ta yi matuƙar burge shi. Yana nan zaune yana lissafi ta fito daga banɗakin suka fito parlor ɗin. Sai da ya zauna a table ɗin sannan ta zuba masa abincin ta ajiye a gabansa, ta koma ta haɗa masa shayi kamar yanda yake so shi ma ta ajiye masa ta koma ta zauna a kujerar kusa da shi.

Tun kafin ta zauna ya fara cin abincin saboda da gaske yunwar yake ji; bayan ya cinye lomar bakinsa ya dube ta yace ‘Ke kin ci abincin ne? Tace ‘Um, mun ci ni da yara mun ƙoshi tun ɗazu. Suka yi shiru na ɗan lokaci, jimawa kaɗan yana cin abincinsa yace ‘Wai me yasa ba ki saka abincin a parlor na ba kika kawo shi nan?’

Ba tare da wata damuwa ba tace ‘Ba komai, kawai dai nan ɗin ya fi min kusa da kitchen saboda sauƙin aiki ko? Um haka ne. Ki dinga sakawa a parlor ɗin kawai kin ji can ɗin zai fi yanda duk wanda yake son ya ci zai iya ɗiba. ‘Ok, next time in sha Allah. Suka sake yin shiru na ɗan lokaci, jimawa kaɗan ya ajiye cokalinsa ya fara shan shayin.

Bayan ya kurɓa ya ajiye kofin sannan yace ‘Kuma na ga ba ki gyara mana ɗakin ba, yanzu za ki gyara kenan ko a haka kike so mu kwana? Ta kalle shi da mamaki tana ɗan zare ido ‘Duk gyaran da na yi kuwa? Ko dai ba ka kalli ɗakin ba? Koda yake ba ka kunna fitila shi yasa ba za ka ga ɗakin sosai ba amma na gyara sosai fa.’

Ya kula da tana maganar hankalinta yana kan ƙofar ɗakinta kamar dai ta za ta ɗakinta yake nufi ba ta gyara ba, yace ‘Ba fa ɗakinki nake nufi ba, ɗakina nake nufi tunda ai a nan za mu kwana. ‘Oh,..’ sai kuma ta ɗan sunkuyar da kai kamar dai ta kasa faɗin abinda take son faɗa ne. Ya kurɓi shayi ya bi ta da kallo yana jira ta ƙarasa faɗin abinda ta fara faɗa.

‘Gaskiya mu kwana a dakina, in ya so duk ranar kwana kai sai ka dinga zuwa ɗakina muna kwana. Da mamaki yake kallonta yana dariyar yaƙe ‘Khadeeja a ina kika taɓa jin miji ya bi matarsa ɗakinta kawai saboda su biyu ne? shikenan yanzu duk wacce take da kwana ni ne zan je ɗakinta kenan? Ta ɗan ɓata rai ‘Ni fa ba haka nace ba, ita idan tana so ta dinga zuwa ɗakinka ba ni da matsala da hakan amma ni dai sai ka dinga zuwa ɗakina.’

Dariya ma maganarta ta ta so ta ba shi; tunda yake bai taɓa jin inda maigida yake bin ɗakin matansa ba sai dai a inda ba shi da ɗakin saboda ƙanƙantar gidan ko kuma a gidan haya. Amma ya za a yi yana da gida kamar wannan ga ɗakinsa da parlor ɗinsa amma a ce shi ne zai dinga bin mace ɗakinta? Allah ma dai yasa Khadeeja wasa kawai take yi.

‘Tunda kike don Allah kin taɓa jin inda aka ce maigida kamar wannan yana bin matansa ɗaki saboda kwana madadin su su je ɗakinsa?’ Ya tambaye ta yana nuna gidan, sannan ya cigaba ‘Kuma ma a wanne karatun aka biya miki haka bayan ga yanda kika taso kika ga ana yi? Ta kalle shi ta marairaice da fuska tana cewa ‘Don Allah ka bari mana, na ga ɗakin nawa ma duk gidanka ne ai meye don ka kwana a ciki.

Ita ma Najan idan tana buƙatar hakan ba sai ka je ɗakinta ka kwana ba? ‘Oh, ni ne ma zan dinga bin ku ina kai muku kwanan kenan? ‘To meye a ciki, abu ne fa wanda ya zo a tarihi ma. Ya ɗan zaro ido yana kallonta ‘Wanne tarihin Khadeeja? In ce ko dai tarihin tsumburbura ne? Ta kula dai so yake ya raina mata hankali, kuma idan ba ta yi da gaske ba so yake ta dinga zuwa ɗakinsa kwana.

Ita kuma gaskiya ba ta jin za ta iya kwanciya gadon da ya kwanta da wata matar ko da kuwa ba Naja ɗin ba ce. Gara kawai ya dinga zuwa ɗakinta. Ta ƙara ɓata fuska tace ‘To a islamiyya dai tunda ake biya mana sirah sai dai a ce Annabi SAW ya je ɗakin Aisha, ko ya je ɗakin Hafsa da sauransu, duk bayanan da aka yi mana sun nuna shi yake zuwa ɗakin kowacce.

Kuma tunda dai auren nan shi ake kwaikwayo SAW ai ba zai zama matsala ba idan an kwaikwayi wannan ɗin ma. Buɗe baki ya yi kawai yana kallonta; ya rasa yanda aka yi Khadeeja take lale shi haka har take samun damar gaya masa duk maganar da ta ga dama. Ya jijjiga kai yace ‘To idan nace ba zan zo ba fa sai dai ke ki zo ɗakin nawa?’

Ta yi murmushinta wanda yake ƙara ba shi mamaki; kana cikin magana da ita fuska murtuke sai kuma ta koma murmushi har ka ga kamar da zuciyarta take murmushin, haka ma kuma idan tana walwala lokaci guda za ta sha kunu ka zata kamar ba ta taɓa murmushi ba.

Muryarta ce ta katse masa tunanin tana cewa ‘Na san ma ba za ka ce hakan ba, kai da gidanka. Abinda ko a parlor ka kwana babu wanda zai nuna maka yatsa balle don ka kwana a ɗakin matarka? Bin ta kawai yake da kallo yana jijjiga kai, yace ‘Toh tsara ni Khadeeja. Ta yi dariya tana miƙewa tsaye tana cewa ‘To ina laifi, yaushe rabon da a tsara ka.

Kasa magana ya yi kawai ya dinga bin ta da kallo har ta gama kwashe kwanukan. Buƙatar ta yake yi saboda shi kansa ya san ya yi kewarta, don haka ma ba ya son ya ja rigima a wannan daren da yake son ya huce gajiyarsa. Gashi sai kai wa da kawo wa take yi tana kwashe kwanuka tana juya jikinta kamar da gayya, ya ma rasa me zai ce mata.

Bayan ta gama kwashe kwanukan ta dafa kafaɗarsa tace ‘Sai ka shigo. Ba ta ko saurari amsar shi ba ta wuce ɗakinta ta bar shi a nan. Sai yau ya tabbatar Khadeeja ta raina shi; tunda yake bai taɓa ganin matar da idan ta yi niyyar abu sai ta yi shi ba ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai Khadeeja.

Anya kuwa ba wani abu Khadeeja ta yi masa ba; idan ta ga dama ta gwada masa taurin kai da fitina idan kuma ta ga dama ta mayar da shi kamar wani sakarai ta yi masa wayo? Amma dai gaskiya ba zai juri bin ta ɗakinta ba dole ta haƙura ta yi yanda aka saba wato duk mai kwana ta bi miji ɗakinsa.

Babu yanda ya iya da yake shi ne yake da buƙatarta dole ya tashi ya bi ta ɗakinta; kafin ya je ma bacci ya riga ya kwashe ta. Don haka sai da ya tashe ta ta sake lallaɓa ta sannan ya sami biyan buƙatarsa.

Washegari ya kama ranar Asabar ce don haka yara ba su da makaranta; ko da ya dawo daga masallaci a kan dadduma ya sami Khadeeja a ɗakinta tana azkar, bayan ta idar ta gaishe shi sannan tace ‘Mantawa fa na yi jiya ban gaya maka yau ne bikin su Fatin Baba Sani wanda na nuna maka invitation ɗin last week ba. ’Ya gyara pillow ya kashingiɗe a kan gadon yana cewa ‘Ok, Allah ya sanya alkhairi.

Ai insha Allahu ni ma za ni ɗaurin aure don Baffa da kansa ya turo min kati. ‘Ok. Ni sai wajen azahar zan tafi don ka ga ban je yawon arba’in ba sai na haɗa gaba ɗaya, idan na kwana biyu a gidan Mommy ranar Litinin sai na dawo. Ya ɗan ɓata fuska ‘Kuma shi ne har kwana biyu? Ai na zata a gidan bikin za ki ga duk wani wanda ya kamata ki je masa yawon.’

Ta yi ‘yar dariya sanna tace ‘Kada fa ka manta bikin na dangin Baffa ne, ‘yan uwan Mommy su kuma ai sai dai na je musu gida yawon arba’n ɗin ko? Hajiya Nana dama ban kai mata baby ba ga su Anti Halima da Baba Usman. Ka ga yau a gidan biki zan wuni, gobe kuma tun safe za mu fara da Nabila; dama za mu kai musu katin bikinta tunda ka ga an fara rabo duk da dai bikin saura sati uku.’

‘Uhm, sai kun dawo. ‘Mun dawo kuma? Ni kaɗai fa zan tafi, Hafsa kawai zan ɗauka saboda Hammad. Ya tashi zaune yana fuskantarta ‘Na zata ke da yara za ki tafi kamar yanda kuka saba. Ta jijjiga kai tana dariya ‘Haba dai, yawon arba’in ɗin na kwashi yara har huɗu? Dama saboda babu mai kula da su ne yanzu kuma ka ga Antinsu tana nan. Ni kaɗai zan tafi.’

Duk yanda ya so ta tafi da yaran nan haka ya haƙura ya ƙyale ta domin ta ci alwashin ba za ta sake tafiya da su danginta ba tunda yanzu suna da uwar ɗakin da za su dinga kawowa gulma. A kan lokaci ta gama abincin safe, sai dai da yake yana nan babu yanda ta iya haka ta jera a dining table ɗin parlor ɗinsa. Dankalin bature ta soya da ragowar sauce ɗin jiya da aka ci abincin dare sannan kuma da soyayyen ƙwai.

Kowa a plate ɗinsa ta zuba masa har shi Mustaphan ta saka sauce a gefe da kuma soyayyen ƙwai. Nashi ta fara ajiye masa tare da na Shukra sannan ta juya ta koma kitchen ɗin. Tana shigewa kitchen ɗin ya dubi Afaf yace ‘Je ki ƙasa ki kirawo Antinki ta zo mu yi breakfast.’

Nan da na ta miƙe ta fice, ya dubi Habib ya miƙe yana shirin ya bi Khadeeja kitchen ya karɓo nashi abincin yace ‘Shiga parlor ɗin Anti ka ɗauko kujerar dining guda ɗaya a ƙara. Don haka ya bi bayan Khadeejan. A hanya ta haɗu da shi ta riƙo plate biyu, tana ƙoƙarin miƙa masa yace ‘Abba ne yace na ɗaukowa Anti Naja kujera tare za a yi breakfast ɗin da ita.

Kafin ta gama fahimtar abinda ya faɗa ya wuce ta ya nufi dining; tana ƙarasowa ta ajiye farantan hannunta ɗaya a gaban Nasreen ta zagayo da ɗayan za ta ajiye a kujerar da take kusa da Mustaphan a daidai lokacin da Afaf ta shigo tare da Naja suna tafe suna hira. Kafin ta yi magana ta zauna a kujerar da take kusa da Mustapha daga damansa a daidai lokacin da Khadeejan take shirin ajiye nata abincin a wajen.

Ta yi cak ta ɗauke farantin da take niyyar ajiyewa ta dubi Habib tace ‘Yaya ka je kitchen ka ɗauko naka abincin ke kuma Afaf ungo wannan ni sai na ɗauko wani. Cike da fara’a Naja tace ‘Ina kwana Umman Hammad. Ita ma nan da nan ta saki fara’a ‘Lafiya ƙalau amarya ba kya laifi, ya gajiya? ‘Alhamdulillah. Sannu da aiki. ‘Yauwa.’

Har cikin ransa ya ji daɗin yanda suka gaisa, haka yake son iyalansa ko da dai idan ba ya nan ba za su haɗu su yi hira ba to idan yana nan a zauna duka kamar haka a ci abinci tare; ya dubi Khadeeja yace ‘Yauwa ita ma ki taho mata da abincin ko? ‘Ok.’ Ta amsa a gajarce sanna ta juya ta nufi kitchen ɗinta. Kafin ta ƙarasa kitchen ɗin zuciyarta ta gama tunzura; Mustapha so yake ya yi mata dole kenan?

Ta gaya masa ba za ta yi abinci da matarsa ba amma shi ne zai saka a kirawo ta har da zama a kujerarta. Lokacin da ita Najan take girki ai bai taɓa kiran Khadeejan yace ta zo su ci abinci ba shi ne sai yanzu don ya tabbatar mata Naja ita ce matar da yake ƙauna shi ne zai ce ta ba ta abinci. Nan take ta juye ragowar dankalin wanda dama ba yawa ne da shi ba ta ajiye ne saboda Shukra, ta haɗa da wanda da ta zuba wa Afaf ta zuba sauce da ƙwai.

Ta haɗa shayinta mai kauri ta ɗauka ta wuce ɗakinta ta bar Hafsa a kitchen tana cin nata abincin. Shiru Khadeeja ba ta fito ba, kowa yana ta cin abinci yayin da Naja take shan shayinta wanda ta haɗa. Shirun ya yi yawa ya dubi Habib yace ‘Je ka dubo ko Antinka dankalin ta tsaya soyawa? Bai daɗe da shiga ba ya dawo yace ‘Abba ba ta kitchen ɗin, tana ɗakinta kuma ta kulle ƙofar.

Ya zauna ya cigaba da cin abincinsa ba tare da wata damuwa ba. Ajiye fork ɗin da ke hannunsa ya yi, ya yi shiru saboda takaici; mantawa ma ya yi ya ba wa Khadeeja mukullin ɗakinta saboda a da ya yi alƙawarin ba zai sake ba ta mukullin ɗakinta ba saboda yanda take kulle kanta a ciki ta yi burus da kowa. Ya ture kwanonsa ya miƙe, ita ma Naja ta miƙe a lokacin.

Ya kalli plate ɗinsa; ya riga ya ci da yawa sannan kuma sauran duk ya dame da sauce. Cike da damuwa ya cewa Naja ‘Ko wannan za ki ci naje na dubo. ‘No, kada ka damu. Ku ci abincinku akwai bread a ƙasa zan je na ci.’ Ta juya ta fice daga parlor ɗin ba tare da ta surare shi ba. A fusace ya nufi ɗakin Khadija, tun kafin ya fara buga ƙofar ya kirawo sunanta.

Ba tare da ɓata lokacin ba ta amsa sannan ta taso ta buɗe masa ƙofar, ko a fuska ba ta nuna masa ta san ta yi laifi ba. Ya shige cikin ɗaki ya kalli abincin da take ci a gefen dadduma yace ‘Ya za ki taho nan ki kama cin abinci ki bar mutane? Kuma kina ji nace ki ba ta abincin ita ma. Duk yanda ta so ta bi maganar a hankali bai samu ba, domin yanda ya yi mata wannan tambayar da isa da gadara take ta ji duk wata kara da za ta iya yi masa ta bushe.

Ta kalle shi ta kawar da kai sanna ta wuce shi ta koma ta zauna a gaban abincinta inda ta taso sannan tace ‘Gani na yi kun cike table ɗin, abincin kuma babu tunda ni ban soya dankali da ita ba. Me kake so na ba ta? ‘Ai tun jiya nace ki dinga saka abincin a can don kowa ya ci kuma kika amsa ko? Me yasa ne kike so ki dinga raina ni a gaban mutane? Saboda me nace ki ba ta abinci ba za ki ba ta ba zaki shigo nan ki bar mutane?’

Ta kula dai duk wani zille-zille ba zai yi mata ba, ta kalle shi suka haɗa ido ta yi murmushin yaƙe mai ɗauke da takaici sannan tace ‘Kwana kusan talatin ta yi a gidan nan tana girki ba ta taɓa ba ni ba, kuma tare kuke cin abinci kai da ita da yara ba ka taɓa cewa a kirawo ni na ci abinci ba; ko da yake ko ka kirawo ni ma ba ci zan yi ba tunda ni ma na iya girkawa.

Ka yi haƙuri ba zan haɗa girki da matarka ba ita ma kar ta haɗa da ni, duk wanda ya girka yaci shi da maigida da yara kawai. Ta miƙa hannunta ta ɗauki fork a kan plate ɗin da yake gabanta ta fara wasa da shi tana ƙoƙarin tokare takaicin da yake taso mata yana neman ya saka ta kuka.

‘Wai ke me yasa ban isa na gaya miki magana ki ji ba ne Khadija? Ko.. ‘Ita da ka gaya mata ai ta ji har ta ba ni abincin, ko da yake ita ka ɗauka mutum shi yasa kake nema mata abinda za ta ci. Ni da babu wanda ya damu da rayuwata ina nan kake fita ka siyo muku abinci ka saka ta a gaba ita da yaranka ku cinye ba tare da ko rabona an ba ni ba. Ban yi magana ba, shi ne kuma yanzu za a ce ni zan ba ta abinci; to ta cigaba da jira na ta ga idan za ta ci abinci.

Ta gyara zama ta jingina da bango ta kawar da kai. Ya rasa abinda zai gaya mata saboda tabbas ya san duk abinda ta faɗa gaskiya ne, sai dai a wancan lokacin ai laifi ta yi masa na ƙin amincewa ta kula da yara don haka bai ga dalilin da zai sa ya ba ta abincin da ya siyo ba bayan ta ƙi ta girka. Ba tare ya ce mata komai ba ya fice daga ɗakin don a yanda ya san Khadija da taurin kai sai dai ya datse igiyar auren nan amma ba za ta yi abinda yake so ba.

Sai dai tabbas idan ta cigaba da gwada masa taurin kai irin wannan zai datse igiyar auren ya huta, ta je can gidansu ta cigaba da taurin kan. Haka ya ƙarasa shiryawa zuciyarsa babu daɗi, don ko ɗakin Najan ma bai shiga ba suka fice tare da Habib suka tafi ɗaurin aure. Yana ficewa ita ma ta gama shiryawa, ta kulle ɗakinta da parlor ɗinta gaba ɗaya.

Ta haɗa mukullanta da wanda ta cire daga jikin nashi keys ɗin duka ta jefa a jaka don ba ta so ko shi ya buɗe mata waje idan ba ta nan. Ta goya Hammad ta tasa Hafsa a gaba, suna saukowa ƙasa ta shiga parlor ɗin Naja inda ta jiyo hayaniyar yaran, ta dube ta da fara’a tace ‘To Anti ni na fita, zan je gidanmu ne in sha Allahu zan kwana biyu. Sai ranar Litnin zan dawo.’

Ta juyo ta yi mata wani kallo na raini sanna tace ‘A dawo lafiya. Shukra ta tashi da gudu ta kama hannunta tace ‘Anti gidan Mommy za ki je? Ta shafa kanta ‘Can zan je Shukra, sai ranar Monday zan dawo. Ta langaɓe kai tana cewa ‘Kai Anti ina son zuwa fa, kwana biyu ban je wajen Anti Nabila ba fa.’

‘Ai kin ga Monday akwai school ko? Shi yasa ba zan tafi da ke ba. Amma idan zan koma ranar da babu makaranta zan tafi da ke kin ji. Haka ta tsaya ta lallaɓa ta sannan ta wuce.

Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Uku

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMakaman Da Hausawa Ke Amfani Da Su Wajen Faɗa Ko Yaƙi
Labarin na GabaMijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Biyar
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.