Haka rayuwarsu ta cigaba; duk yanda ya so Khadeeja ta dinga bin shi ɗakinsa gaba ɗaya ta ƙi. Don haka ba shi da zaɓi duk daren da yake buƙatarta sai dai ya bi ta ɗakinta su kwana, idan bai je ba sai dai kawai ta leƙa ɗakin nasa tace masa sai da safe. Sau da dama ya sha ƙyale ta ya ga ko za ta biyo shi amma da zarar ta shiga ɗakin tace masa sai da safe sai ta yi ficewarta.
Da farko duk ranar kwananta idan bai ya buƙatarta ya yi kwanciyarsa a ɗakinsa haka yake kwana shi kaɗai, amma tunda Naja ta gane sai ta dinga bibiya; idan ta same shi shi kaɗai sai ta yi kwanciyarta a nan da uzirin laulayi. A zatonsu Khadeeja ba ta sani ba; sai dai ita ɗin ta zaɓi ta yi shiru ne tunda ta san yana yin hakan ne don ta hakura ta koma kwana ɗakinsa.
Ita kuma har ga Allah gani take yi babu yanda za a yi kowa take aure ta kwana gadon da yake kwana da wata matar; musamman Naja wadda ba ta taɓa tsanar wata mace kamar ita ba. Tunda Khadeeja ta dawo daga gida kuma sai laulayi ya saka Naja a gaba. Haka za ta wuni jikinta babu ƙwari, abinci kuwa to idan dai ita ce ta dafa ba za ta iya ci ba dole sai dai ya siyo mata wanda zata ci.
Yau Khadeeja take fita daga girki don haka a wajenta shi da yara suka ci abincin rana. Ragowar abincin ranan shi ta ɗiba ta zuba a flask ta ajiye musu ita da Hafsa saboda ta huta shiga kitchen da daddare. Tana zaune a parlor tana ba wa Hammad nono ya shigo parlor ɗin, bayan ta amsa sallamarsa ya zauna kusa da ita.
Sai da ya gama kame-kamensa yace ‘Da-Allah ki yi abincin dare gaba ɗaya saboda Naja ba ta da lafiya, kin san na gaya miki ciki ne da ita kuma yana ba ta wahala. Ko da dai ba ta zata abinda ya zo faɗa kenan ba amma tana jiran wannan ɗin ma domin tun tuni yara suka gaya mata Najan ba ta da lafiya kuma ta fahimci menene ciwon.
Ta cire Hammad daga nono ta saka shi a kafaɗa tana cewa ‘Ai kuwa ka ga yau ba girki zan yi ba ga ragowar abincin rana can shi na ajiye za mu ci da daddare. Allah ya ba ta lafiya. Ya sake ɓata rai ‘Khadeeja, da-Allah ki bari. Yarinyar nan ba ta da lafiya ko abincin ma ita ba ta iya ci, kuma ba ita nace ki yi wa girki ba. Ni da yara za ki girkawa, idan ta sami lafiya za ta karɓi girkinta.’
Ta kwantar da Hammad a gefenta sannan ta fuskance shi gaba ɗaya don ba ta cikin yanayi na son zance, tace ‘To ai cikin ba wani abu ba ne, ko ka manta ne? Haka na dinga haɗawa da cikin da komai duka da ƙarancin shekaruna ga rashin mataimaki. Ita kuwa yanzu ka ga tana ma da mai aiki; ai babu wani abu da zai gagare ta. Idan dai kwana ya zagayo kaina insha Allahu zan yi kamar yanda muka saba.’
A fusace ya kalle ta na ɗan lokaci sannan yace ‘Yanzu kenan ke babu halin a ce ki yi wani abu sai ki tuno abinda ya faru shekarun da suka wuce? Kuna zaune tare a gidan kina kallon ba ta da lafiya nace ki yi girkinta amma kina nema ki ce ba za ki yi ba? Wai ke me kike son zama ne? Babu wanda ya isa ya tanƙwara ki kenan saboda zaman kanki kike yi ko me?
Ta sunkuyar da kai murya ƙasa-ƙasa tace ‘Ba haka ba ne, kawai dai ni ma mutum ce, yanda aka yi min na zata haka ake yi wa mutanen da ake so shi yasa nake so ko yaya ne a yi adalci. Ba ta saurari abinda zai faɗa ba ta miƙe ta ɗauki Hammad a hankali saboda ba ta son ta tashe shi ya fara bacci, ta wuce ɗakinta ta bar shi a nan.
Yanda ta yi wannan tafiyar ya tabbatar ko me zai yi ba zata saurare shi ba; wanda hakan yake nufin shi da yaransa za su shiga halin rashin samun kulawa na tsawon wata takwas har Naja ta haihu, sai dai su sami kulawa kwana biyu kwana biyu kuma a bar su a gantale. Babu yanda za a yi a ce ya ɗauki wannan kuma a halin yana da mata biyu.
A yanda cikin nan yake wahalar da Naja kuma dole Khadeeja ce za ta ɗauki wannan hidimar har zuwa lokacin da za ta haihu. Sai da ya gama lissafinsa sannan ya miƙe ya fice, kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya ɗauki mukullan motarsa. Bai zame ko ina ba sai gidansu Khadeeja; ba ya son kai ƙara don ya kula ita ko ya kai ƙararta ma goya mata baya za su yi, sai dai yanzu ba shi da wani zaɓi da ya wuce hakan.
Ya ci sa a yana shiga gidan Baffa yana shirin fita, a nan bakin gate ya tsaya ya yi masa bayanin halin da ake ciki. Cike da kulawa Baffa ya jijjiga kai yace ‘Subhanallahi, to Allah ya ba ta lafiya. Yanzu ka ga fita zan yi amma in sha Allahu idan na gama abinda nake zan zo har gidan na sami Khadeejan. Kada ma kace mata zan zo, ka ƙyale ni da ita zan zo na same ta ka ji.
Ai ɗaya daga cikin amfanin ƙarin auren kenan ɗaya ta taimakawa ɗaya a irin wannan yanayin. Suka yi sallama kowa ya nufi inda zai je. Ba shi da tabbacin abinda Baffa zai yi a kan wannan matsalar amma dai yana saka ran Baffan zai fahimce shi ya saka Khadeeja ta dinga taimakawa Naja, a ƙalla a lokutan da ba ta da lafiya; idan ba haka ba menene ribar mata biyun ga namiji.
Ba ta samu ta yi sallar isha’i a kan lokaci ba don haka har wajen 8:30pm tana zaune a kan dadduma, Hammad yana wajen Habib wanda yake zaune a parlor ɗinta yana kallon TV. Ta so ta jiyo muryar Baffanta suna gaisawa da Mustapha a tsakar gida, amma da yake bata sa rai da zuwan Baffan ba sai kawai ta zata kunnenta ne ya jiye mata ba daidai ba.
Tana nan zaune Mustapha ya turo ƙofar ɗakin ya shigo da sallama, bayan ta amsa sallamarsa yace ‘Baffan Mommy ne yazo, ga shi nan a parlor na. Da mamaki ta kalli Mustaphan da alamomin tambaya a fuskarta, tace ‘Baffana? Ya yi ‘yar dariya saboda yanda ta tambaya sannan yace ‘Baffan Nabeela dai. Ita ma sai ta ɗan yi dariya tare da miƙewa tsaye; kwata-kwata ba ta yi zaton ƙararta Mustapha ya kai wajen Baffa ba.
Ta yi zaton zuwa ya yi ya ga sabon gidansu kamar yanda take ta faman roƙonsa tunda suka tare ya zo ya ga gidan. Nan da nan ta tashi ta fice don zuwa ta taryi Baffan nata. Sai da ta shiga kitchen ta jera ruwa da lemo a faranti sanna ta fito, ta dubi Habib wanda yake zaune a parlor ɗin yana riƙe da Hammad tace ‘Yaya ku taso ku gaida Baffa ga shi nan a parlor ɗin Abbanku.’
Tana shiga parlor ɗin ta same shi da Shukra da Nasreen yayin da Abban nasu yake zaune daga gefe a kan kafet; yanayin zaman da Mustaphan ya yi kawai ta kalla ta sha jinin jikinta. Ko da bai kai ƙararta gida ba to tabbas ta san a wannan ɗan zaman da Baffan ya yi ya gaya masa laifinta. Ta ƙarasa ta ajiye ruwan a gaban Baffa a daidai lokacin da Naja wadda ita ma ta shigo ta gaishe shi take ficewa daga parlor ɗin.
Ta zauna daga gefen ƙafarsa sannan ta gaishe shi ya amsa cike da girmamawa. Sai da ya gama raha da yaran sannan ya zaro sababbin kuɗi a aljihunsa ya ba wa kowa naira dubu sannan ya sallame su suka wuce suka bar su daga shi sai Khadeejan da Mustapha. Ya dubi Khadeeja ya yi gyaran murya sannan yace ‘Deeje, garin yaya kika ce ba za ki taimaka ki karɓarwa abokiyar zamanki hidimar gida ba bayan ba ta da lafiya?
Haba Khadeeja, hakan ai shi ne zaman tare tunda dai Allah ya haɗa ku. Ta yi shiru ta sunkuyar da kai tana tunanin ta inda za ta fara, ina ma da Baffa ya zo da Mommy. To ta ina za ta fara gaya wa Baffa yanda Mustapha ya yi mata lokacin tana nata laulayin? Kuma ya za a yi ta gaya wa Baffa cewa ita ba ta bin Mustapha ɗakinsa kuma duk ranar da ba ta bi shi ɗakinsa ba Naje yake kira ta taya shi kwana?
To ai Baffa ma sai dai ya sake yi mata faɗan ƙin zuwa ɗakin miji domin tabbas abu ne da haka aka saba; kuma ta sani mata biyu ne da kakanta mahaifin baffa. Wanda da wayonta kafin dukansu su rasu ta san matan ne suke zuwa ɗakinsa. Wannan kam ai sai dai ta ƙara kai ƙarar kanta.
Muryar Baffa ce ta katse ta yana cewa ‘Deeje me yasa ba za ki taimakawa abokiyar zamanki ba? Ta ɗan yi firgigit kamar wadda aka tasa daga bacci sannan tace ‘Uhm Baffa wallahi ni ma daurewa nake ina yin hidimar ranar girkina, tunda ga jego ina yi sannan kuma ina zuwa aiki. ‘Eh, ai wannan ba zai gagare ki ba tunda kin ga da a ce ke kaɗai ce a gidan ai duka za ki haɗa ko?’
Suka yi shiru na ɗan lokaci sannan daga baya tace ‘Baffa ni ma fa haka nake haɗa nawa laulayin da aikin gidan babu wwanda yake taya ni. Kuma ka ga Baffa akwai mai aiki fa wadda za ta iya yi mata duk abinda take so idan ta yi mata bayani. Baffa ya ɗan yi murmushi sannan yace ‘Na fahimce ki Khadeeja, amma dai ki yi haƙuri ki karɓar mata aikin.
Tunda kin ga yanzu ke ma idan kika kuma samun wani cikin ai za ta karɓar miki ko? Ki yi haƙuri Deeje, ba na son taurin kai da yawa. Allah zai ba ki lada har kashi biyu, ladan biyayya wa miji da kuma ladan taimakon ‘yar uwarki musulma wadda take neman taimakon naki. Ki yi haƙuri kin ji, tunda ga yarinyarki nan tana taimaka miki ki zauna lafiya tunda dama yara duka naki ne tun kafin ma a auro ta.’
Haka Baffa ya ɗauki lokaci yana ba ta haƙuri, daga ƙarshe kuma ya ba ta umarnin lallai ta taimaka wa Naja ta karɓi hidimar gidan. Bayan ya miƙe duka suka miƙe gaba ɗaya, a nan ya yi sallama da Khadeeja yace ta koma ciki. Suka fice shi da Mustapha wanda ya yi masa rakiya har wajen motarsa sannan ya yi masa sallama ya tafi.
Ya san ko da ya koma wajenta a yanzu ba za ta saurare shi ba sai dai ma ta gaya masa maganganun da ba ya son ji, don haka ya wuce wajen Naja tunda dama kwananta ne. Har turiri take ji yana taso mata a ƙirjinta saboda tsabar yanda zuciyarta take tafasa; sai da ta yi da gaske sannan ta kai kanta ɗakinta ba tare da ta rushe da kuka ba. Ya za a yi a ce ta karɓarwa Naja girki saboda kawai tana da ciki?
Bayan ita a lokacin da tana da nata cikin haka ya dinga barinta da duk wata hidima yana hana yaranshi su taya ta. Sannan kuma idan ta yi magana ya dinga nuna mata cewa laulayi ba komai ba ne kamar ma dai ita ce take son nuna raki. Yanzu kenan haka za ta kwashe wata takwas ko tara tana kula da yara yayin da Naja take kwana da miji tunda laulayin bai hana idan ta same shi shi kaɗai a ɗakin ta kai masa kanta ba?
Tana shiga ta murza mukulli ta rufe ƙofar, sai da ta ƙarasa kan daddumar da ta tashi sannan ta zube da gwiwoyinta ta rushe da kuka. Shikenan ita ta zama baiwar Mustapha ne? Ya iya nunawa kowa ƙauna da tausayi a duniya amma banda ita? Anya za ta iya wannan rayuwar a gidan Mustapha kuwa? Amma ta san dole ne ta bi umarnin Baffanta, musamman da yake a gaban Mustapha ya ba ta umarnin. Ta kifa goshinta a ƙasa ta sake rushewa da kuka.
Ya so ƙwarai kamar yanda ya saba leƙawa da daddare ya yi wa wadda ba ta da kwana sai da safe ya leƙa wajen Khadeeja, amma da yake bai shirya rigimarta ba sai kawai ya ƙyale ta suka shige ɗaki shi da Naja suka yi kwanciyarsu. Ba ƙaramin daɗi ya ji ba da ya dawo daga masallaci sallar asuba ya jiyo motsinta a kitchen, tabbas ya san ta ji maganar Baffanta.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta shirya su sannan ya fito ya kai su makarantar. Kafin ya dawo daga kai su makaranta ta gama nata shirin, a zaune ya same ta a parlor ɗinta tana karyawa. Babu yabo babu fallasa suka gaisa, sai dai daga gaisuwar ba ta sake ko da kallon inda yake ba. Jimawa kaɗan ya miƙe zai fice, tace ‘Idan na tsahi daga aiki zan je gidan Mommy.’
Ya ɗan tsaya yana kallonta yana ƙoƙarin su haɗa ido ko zai karanto wani abu a fuskarta, sai dai ba ta ba shi damar ba. Daga tsayen yace ‘Ki gaishe min da mutanen gidan. Ya fice ita kuma ta cigaba da cin abincinta ba tare da ko da ta kalli inda ya wuce ba; gaba ɗaya ma a halin yanzu ko kallonsa ba ta son yi.
Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Huɗu
Edita@rumasau-kallamu







