Mijin Marigayiya Babi Na Ashirin

0
13

Ranar ɗaurin aure tun da sassafe baƙi suka fara zuwa gidan, zuwan nasu ma sai ya fi mata sauƙi tunda ya ba ta dama ta baro Mustapha a sama ta taho wajen baƙin. Ba za ta iya tsayawa a inda yake ba yana ta faman walwala yana kai wa da kawowa yana kwalliya, sai ta ga kamar yana yi ne don ya ba ta haushi.

Don haka ta ji daɗi sosai da aka ce mata Yaya Jidda ta zo da mutane. Nan ta sauko suka gaisa, ta buɗe musu ɗakin baki tunda dama a ɗaya parlor din suka sauka wanda ba na amarya ba. Sosai Yaya Jiddan ta so su hau sama amma sam Khadeeja ta ƙi ba da fuska, don haka suka haƙura suka baje zugarsu a nan ƙasan.

Duk wani abu da suke buƙata na cefanensu sun taho da shi da manyan tukwanensu, shi kansa Mustaphan bai san a nan za su yi girkin ba da ya biya an girka musu don ba ya son a ɓata gidan nan. Amma haka yana ji yana gani kafin ma ya sauko an sauke kayan aiki an hau ƙoƙarin hura wuta; a cewar Yaya Jidda sun bayar a yi musu tuwon shinkafa da masa da shinkafa amma masu yi miyarsu ba ta daɗi don haka su za su girka tasu miyar.

Nan da nan ya ja motarsa ya fice daga gidan suka tafi ɗaurin aure. Tunda Mustapha ya fita ta ɗauki Hammad ta haye sama, suka zauna da Nabila wadda dama ba ta sauko ba ma balle ta ga kalarsu. Hafsa mai aikinta dai ita dole ta zauna ana komai da ita, sannan ga su Afaf waɗanda tuni suka shiga cikin dangi ana ta rawar kai.

Can kusan la’asar su Yaya Mama suka zo ita da cousins ɗinsu mutum biyu da kuma ƙannen Mommy su biyu. Bayan sun gaisa da Yaya Jidda a parlor ɗin ƙasa kai tsaye suka haye sama. Ba su daɗe da hayewa ba kuma Hajia mahaifiyar Mustaphan ta iso da tata zugar, nan da nan gida ya cika ana ta kai wa da kawowa.

Bayan an gaggaisa Hajia ta dubi Yaya Jidda tace ‘Ina Khadeejan ne? Ban ganta ba. Inna Ramla ta yi sauri ta amsa kafin Yaya Jidan tace wani abu ‘A a suna saman benen nan fa ita da ‘yanuwanta, benen da ‘yan gidan ma ban ga suna hawansa ba tunda duk ga su nan tare da mu.’

Ta sake duban Yaya Jidda tace ‘Ban gane tana sama ba. Ta taɓe baki ‘Toh haka muka gani, tana saman ita da ‘yan uwanta. Kafin tace wani abu Khadeejan ta sauko parlor ɗin da sallama; Shukra ce ta hau ta gaya mata zuwan Hajia shi ne ta yi sauri ta sauko saboda kada ta yi laifi.

Ta ratsa mutanen har gaban Hajia ta tsuguna ta gaishe ta cikin girmamawa sannan ta yi mata Allah ya sanya alkhairi. Ta dubi mutanen duk suka gaggaisa tana kama sunan waɗanda ta sani. Har ta miƙe Hajia tace ‘Ina Mommyn naki, ba ta zo ba? Tace ‘Eh, ba ta zo ba, su Yaya Mama ne kawai suka zo.’

‘To madalla.’Ta miƙe ta fice tsakar gidan suka gaggaisa da mutanen da ke zazzaune, ta kalli wajen da su Yaya Jidda suka yi aikinsu yanda ya yi kace-kace ta ɗauke kai. Har ta juya za ta koma ciki Habib ya turo gate ya shiga, daga inda yake ya kirawo sunanta ‘Anti.’ Ta tsaya ta juyo ‘Yaya Habib, ina ka shiga ne tun ɗazu Shukra take nemanka.’

‘Ina nan Anti, wajen abokina na je. Yanzu ma wallahi yunwa nake ji, abinci za ki ba mu. Tace ‘To ai Anti Jidda za ka yi wa magana ga abinci nan an dafa. Ya shafa kai yana cewa ‘Anti ai na gaya mata, tuwo ne fa da masa Anti don Allah ni dai ki ba ni abinci. Ta yi dariya don ta san tabbas Habib ba ya cin tuwo da masa da ma abincin gargajiya da yawa, tace ‘Kaje sama wajen Anti Nabeela ta zuba maka.’

Har ya wuce yace ‘Ni da abokaina Anti? ‘Eh, ka gaya mata ko ku nawa ne. Bai jima da hayewa ba ita ma ta bi bayansa, kafin ta je ya ɗauko flask Nabeela ta zuba masa shinkafa da kaza ga coleslaw da sauce ɗin dankalin bature wanda duk a nan saman suka dafa shi tunda ba su da yawa. Ya ɗauko kwanukan ya sauko ya fice.

Haka aka yi ta hada-hada ana kai wa da kawowa. Sai dai zuwan Hajia ya sa babu yanda Khadeeja za ta yi dole ta zauna a ƙasa a yi da ita, don haka Yaya Mama da kuma Anti Innani suka sauko suka gaida Hajia suma suka zauna don taya ta zama. Bin mutane kawai take yi da kallo zuciyarta tana ƙuna; ji take a ranta kamar da za a buɗe zuciyarta to da za a tarar tana turiri saboda zafin da take ji.

Fuskokinsu take kallo ɗaya bayan ɗaya, musamman Hajia wadda ake ta yi mata Allah ya sanya alkhairi ana barka da arziƙi tana amsawa kamar wadda aka yi wa bushara da kujerar Makka. Haka tacigaba da zama a cikinsu tana jin kamar ta ruga da gudu; sai dai lokaci zuwa lokaci ta kan tashi kamar mai duba wani abu ta haye sama, idan ta ja numfashi ta share ƙwalla sai ta dawo.

Haka suka yi ta yi har gefin magriba; abokan ango suka zo da motaci suka ɗebi yan ɗauko amarya sannan suka tafi ɗauko amarya. Har ta yi sallar magriba zuciyarta tana dukan uku-uku; ta rasa ma abinda yake ɓata mata ran. Tabbas tana kishi to amma ta fi tsoron rashin adalcin da take ji a jikinta Mustapha zai shimfiɗa; amma tana addu’a kuma ba za ta fasa ba don ta san tabbas Allah ne gatanta.

Wajen 8:30pm aka shigo da amarya, nan da nan gida ya ɗau guda mata na ta shewa. A lokaci guda kuma bugun zuciyar Khadeeja ya ƙara gudu. Tana zaune a kan kafet kusa da Hajia; duk su Yaya Jidda suka miƙe suna tarbar amaya, aka buɗawa waɗanda suka riƙo amarya suka ƙarasa gaban Hajia wadda take hakimce a kan 3-seater. Aka zaunar da amarya a gaban Hajia, mata suka cigaba da zabga guɗa.

Sai da hayaniya ta lafa sannan aka gaisa da masu kawo amarya, suka miƙa ta hannun Hajia. Hajia tace ‘Masha Allah, Allah ya sa wannan aure har aljannah. Wannan ai ‘yar uwarta za a ba wa ita ba ni ba, ina Khadeejan ne da fa tana nan zaune kusa da ni. Wadda take zaune kusa da Khadeejan tace ‘Gata nan fa.’

Mutane ne suka zauna a gabanta suka kare ta da aka shigo da amaryar; nan da nan aka buɗa. Hajiya ta miƙa hannu yayin da Khadeejan ta matso tana cewa ‘Zo Khadeeja ga ƙanwarki an kawo miki. Ta sunkuyar da kanta tana duban cinyarta domin tana tsoron kada idanuwanta su ba da ita ta hanyar tunkuɗa hawaye a daidai wannan lokacin.

Hajia ta kama hannunta sanna ta kamo hannun Naja ta ɗora ta haɗa ta riƙe tana kallon Khadeejan tana cewa ‘Ga amanar ƙanwarki nan, ki riƙe ta amana ku zauna lafiya ku samarwa da mijinku nutsuwa. Allah ya haɗa kayuwanku. Mata suka kaure da amshi ‘Amin. Amin.’

Wata cikin iyayen amaryar ta karɓe ta cigaba ‘Eh gata nan amana, a yi haƙuri uwargida sarautar mata ku zauna cikin amincin Allah domin kayan Allah na annabi ne. Aka sake kaurewa da guda. So take ta zare hannunta amma Hajia ba ta ba su dama ba; bugun zucuyarta ƙara sauri yake yayin da take jin hanunta kamar ta riƙe wuta.

ƘoƘari take ta dafe bakinta saboda kada abinda yake zuciyarta ya fito; Amana! Ita za a ba wa amanar matar Mustapha? Ina ruwanta da ita? Ko sun yi mantuwa ne? Shi da ya ga zai iya da amanar ai ya yi gammo ya ɗauko. Don me za su ce ita aka ba wa amana? Tabbas wanna amana ce da ba ta karɓa ba kuma ba za ta taɓa iya karɓa ba.

Sai da aka gama addu’oi sannan Hajia ta saki hannuwansu, cikin dabara Khadeeja ta faki ido ta goge ƙwallar da ta taru a kwarmin idonta. Ba daɗewa kuma aka fara miƙewa aka kama hannun amarya aka nufi ɗakinta, a haka ne Khadeeja ta samu ta sulale ta haye sama, yayin da su kuma matan suka bi bayan amarya.

Haka ta koma cikin su Yaya Mama ta cigaba da dagewa, su kuma suna ta ba ta baki da nasiha. Wajen 9pm gayya ta fara watsewa, aka kirawo ta ta yi sallama da Hajia, ba daɗewa kuma su Yaya Mama suma suka yi mata sallama suka bar ta ita da Nabeela. Tana zaune a gefen gadonta tana jiyo yara wajen 11pm suka hawo saman, gaba ɗayansu sai da suka leƙa ɗakinta suka yi mata sai da safe amma banda Afaf, suka wuce ɗakinsu inda suke kwana tare da Hafsa.

Ba su daɗe ba kuma Nabila ta fito daga ɗakin baƙin da yake saman ta turo ƙofar ɗakin a hankali ta shiga, ta wuce Khadeejan a gefen gadon ta zagaya ta kwantar da Hammad a gafe ta lullube shi. Ta zagayo ta zauna a kusa da Khadeejan, ba ta motsa ba kamar ma ba ta san an zauna a kusa da ita ba. Ta mika hannu ta dafa nata hannun da yake kan cinyarta tana kallon fuskarta tana cewa ‘Yaya Khadeeja ga Hammad fa na kwantar miki da shi.’

Ta kalle ta suka haɗa ido, ba tare da tace komai ba ta sake kawar da idonta saboda ta tokare hawayen da suke neman ƙwace mata. Nabila ta ɗan matsa hannunta tana cewa ‘Ya Khadeeja. Kafin tace wani abu hawayen ya fara bin idonta, gaba ɗaya ta sake su saboda yanda take faman riƙe su tana jin kamar an ɗora mata dakon wani kaya mai nauyi.

Gaba ɗaya ta faɗa jikin Nabeela wadda ta rungume ta gaba ɗaya suka sa kuka. Ita Nabeela auren ma gaba ɗaya ya ƙara ba ta tsoro, kuma ta tabbatar ko da wanne lokaci za a iya ɗaura nata auren; tunda da ba don Ahmad ya tafi UK ƙaro karatu ba da tuni ta shekara a ɗaki. Ita kuma Khadeeja gaba ɗaya komai ma ya tsaya mata; tana dai fatan Allah ya sa Mustapha ya zama mai adalci.

A hankali suka fara lafawa, Khadeeja ta zare jikinta ta kalli Nabeela. Suna haɗa ido suka tuntsire da dariya duk da hawayen da suke fuskokinsu. Suka riƙe hannun juna suna murmushi. Khadeeja ta dube ta tace ‘Sorry. Itama murmushin tayi mata tana cewa ‘Its’s ok, you will be fine in sha allah. Komai zai wuce kamar ba ayi ba.’

Murmushi ta sake mayar mata sanna tace ‘Ki je ki kwanta, na san yanzu Abbansu zai shigo. Ta sake rungume ta sannan ta yi mata sallama ta fice ta rufe mata ƙofa. Ba tare da ɓata lokaci ba ta miƙe ta shiga banɗaki inda ta yiwo wanka sannan ta fito da alwala, ta shirya ta sa kayan baccinta sannan ta kabbara sallar isha’i.

A nan ya shigo ya same ta tana zaune a kan dadduma tana gyangyaɗi; kallo ɗaya ta yi masa ta ji zuciyarta ta sake komawa cikin damuwa wadda ta fi ta da. Sai wani faman yage baki yake yana muzurai a lokaci guda; a sanin da ta yi masa ta san murna ce da ɗoki yake yi na amarya kuma yana ƙoƙarin tabbatarwa ita ɗin ba ta kawo masa cikas ba.

Nan da nan ta danne duk wata damuwa da take ranta ta ƙaƙalo murmushi ta yi masa sannu da zuwa. A tsaye ya amsa ya yi mata bangajiyar biki sannan yace ‘Um ni bari na je, na ga ke ma bacci kike ji. In ya so da safe na shigo da ƙanwar taki ku gaisa. ‘To Allah ya kai mu. Ya juya ya fice ya rufo mata ƙofa.

Ta ji daɗi sosai da ya sanar da ita ba zai shigo da matarsa a wannan daren ba, domin gaba ɗaya a gajiye take. Ba jikinta ba har ruhinta ma ji take ya gaji, fatanta kawai waɗannan kwanakin su wuce ko kuma ma ta farka ta ga mafarki take yi.

Ta ga rayuwarsu ta dawo kamar yanda take a farkon aurensu; ko da yake a farkon auren ma babu wani abun kirki da za ta ɗorar; kamar dai gara ma tace rayuwarsu ta dawo yanda ake kafin aure. Sai da bacci ya fara ɗibanta sannan ta tashi ta kwanta a kan ganto ta kashe fitila.

Edita@rumasau-kallamu

Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Tara

 

labarin da ya wuceMijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Tara
Labarin na GabaMatsayar Ɗanbala
Sakina Muhammad Yazid
Ni ma'abociyar son rubuce-rubuce ce, malama kuma mai gudanar da sana'o'i. Ina ƙarfafawa matasa gwuiwa ta hanyar jagorantarsu da koyar da su. Ina rubuta labarai masu jan hankali kuma masu ƙunshe da tsari da al'adun Bahaushe.