Menene Wasan Ƙunshi?

0
60

Wasan ƙunshi, yana daga cikin nau’o’in wasannin gargajiya wanda samari da ‘yan mata suke aiwatarwa shekara-shekara. Sannan yana ɗaya daga cikin wasanni na al’ada da ake aiwatar a watan cika ciki.

Mafi tsufa daga cikin mutanen da aka gana da su sun bayyana cewa wannan wasan haka suka tashi suka ga ana gudanar da shi ba za su iya tabatar da lokacin da aka fara shi ba. Sun bayyana mana sunayen iyaye da kakanninsu da suka yi wannan wasa irin su: Uba maiwake da Hamza Kashi da Tokare da sauransu. (Hira da Shehu Maroɗo).

Wasan ƙunshi wasa ne na Hausawa na gargajiya a ƙasar Gaya ya nuna al’ada ce daɗaɗɗiya “wasa ne da ake gudanar da shi domin nuna farin ciki musamman a cikin watan azumi.”(Hira da Ɗahiru Roka). “Wasa ne na gargajiya wanda ake haɗuwa samari da ‘yan mata da yara wajen nuna farin ciki da sanya nishaɗi.” (Hira da Rabi’u).

Don haka,a taƙaice wasan ƙunshi wasa ne wadda ake gudanar da shi a tsakanin ‘yan mata da samari domin sanya nishaɗi tare da motsa jiki bisa tsarin gargajiya.

Ranar Wasan Ƙunshi

Babu wata rana da ake sanyawa domin a tsayar da lokaci ko wuri wajen aiwatar da wasan. Wannan ya samo tun asali tun farko farko samar da wasan, saboda haka kowa ya san watan da kuma ranar aiwatar da shi.

Amma a wannan lokaci ko kuma a yanzu saboda tasirin zamani ana yin la’akari da ranakun da ba a yin aikin gwamnati, misalin Asabar ko Lahadi, domin ranaku ne da ba a zuwa makarantun boko, suna yin haka, saboda wasu daga cikin ‘yan matan da ake shirya wasan tare da su, suna a makarantun kwana.

Hanyoyin Sanarwa da Sadarwa

Kafin samun kafofin sadarwa na zamani da kuma hanyoyin isar da saƙo na karta kwana, babu wata hanya da ake amfani da ita wajen sanar da wasan sai ta hanyar gargajiya, ita ce wannan ya faɗawa wannan da dai sauran hanyoyin isar da saƙo na gargajiya.

Amma a sakamakon juyawar zamani ana amfani da waɗancan kafafen yaɗa labarai da kuma wayoyin tafi da gidanka wajen faɗakar da al’umma, musamman samari da ‘yan mata.

Masu Aiwatar da Wasan Ƙunshi

Bisa al’ada yawancin wasannin gargajiya a ƙasar Hausawa, ya fi ta’alaƙa ga samari da ‘yan mata musamman wajen aiwatar da shi, domin su ne matasa manyan gobe. Haka abin yake a wasan ƙunshi, masu aiwatar da wannan wasa su ne samari da ‘yan mata sai kuma ƙananan yara waɗanda suke taimakawa wajen gudanar da shi, duk da kasancewar iyaye mata ba abar su a baya ba, domin suna bayar da gagarumar gudummawa tare da ruwa da tsaki wajen aiwatar da wasan.

Lokacin Gudanar da Wasan Ƙunshi

Wasan ƙunshi, wasa ne da ake gudanarwa shekara-shekara, ana gudanar da shi a cikin watan azumi (Ramadan). Watau ana fara wa daga ranar ashirin da shida (26) ga watan, zuwa ashirin da takwas (28) ga wannan wata, wato kwanaki uku (3) ake yi ana gudanar da shi

Tanade-Tanaden Wasan

Iyaye mata sukan tanadi wasu abubuwa waɗanda za su taimakawa ‘ya’yansu wajen alkinta kafin lokacin aiwatar da wasan, a wasu lokutan akan tanadi kayayyakin amfanin gona da aka samu daga roro ko kale ko ja-gindi ko tsinka da sauransu, wacce yarinyar ta samo domin adanawa sai lokacin ya zo, wadda da irin wannan ne ake sayarwa domin a yi mata sabon ɗinki da takalmi da a warwaro da sauran kayan ƙawa.

Haka nan, Budurwa takan kai ziyar gidajen ‘yan uwa da abokan arzuƙa, da sauran dangi, bayan sun gaisa akan ba ta wasu abubuwa da suka haɗa da; sabulai da turare da kayayyakin abinci kamar hatsi da wake da gyaɗa da sauran nau’o’in kayan amfanin gona. Wasu kuma sukan bayar da kuɗi, dukkaninsu suna daga cikin tanade-tanaden gudanar da wasan ƙunshi.

Sannan samari da ‘yammata sukan tanadi kuɗaɗe, idan ranar wasan ta kusanto sukan je kasuwa su sayo kayayyakin da suke da buƙata. ‘Yammata ne suke ɗaukar nauyin saye-sayen kayayyakin da ake da buƙata, domin samarinsu da iyayensu na samar masu da kuɗaɗen, domin su sami damar sayen kayayyakin da suke buƙata.

Amma a yau abubuwa wasu sun sauya saboda sauyin zamani inda samarin da ‘yanmatan su ne suke tanadar waɗannan abubuwa da kansu da suka haɗa da; kayayyakin ciye-ciye wadda suka haɗar da; biredi da cincin da biskin da doya da kwai da arnaki da biri-biri. Sai kuma kayayyakin shaye-shaye, waɗanda suka haɗa da; kyayyakin tsotse-tsotse, misalin; alawar madara, da sauran alawoyi, iri daban-daban.

Ana amfani da kayayyakin shaye-shaye na zamani, irin su lemukan roba da bobo da yagot da lemon kwalaba kamar fanta da kokakola da diyu da kuma lemukan gwangwani kamar maltina da fefsi da lakasera da mirinda da sifirayit, da lemukan kwali, misalin fayif alayif da kuma ruwa iri daban-daban.

Daga cikin samari da ‘yan mata masu aiwatar da wannan wasa akan samu wasu daga cikinsu sukan ɗinka sababbin tufafi domin yin amfani da su, a lokacin wasan. Amma yin ɗunkuna ba wajibi ba ne. Saboda haka, ana samun wasu daga cikin samari da ‘yan mata waɗanda ba su yi sabon ɗinki ba a lokacin wasan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga maƙala mai taken Nazarin Wasan Ƙunshi Jiya Da Yau A Ƙasar Gaya wadda Magaji Ahmad Gaya Ph.D Sashen koyar da Hausa Jami’ar Northwest, Kano ya wallafa.

Emai: magaya@nwu.edu.ng 08066009039

Karanta Waiwaye A Kan Al’adun Gargajiya

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMijin Marigayiya Babi Na Ashirin Da Bakwai
Labarin na GabaYadda ake Gudanar da Wasan Ƙunshi
Dr. Magaji Ahmad Gaya
Dr. Magaji Ahmad Gaya shahararren malami ne a fannin harshen Hausa. Ya yi digiri na uku (PhD) a ɓangaren nazarin al’adu a jami’ar Umaru Musa “Yar Adua da ke Katsina. Haka kuma ya yi aikin koyarwa a wasu makarantun firamare da sakandare da kuma Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso. A halin yanzu yana koyarwa a Jami’ar Northwest, Kano Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya.