Larurar Sarƙiwar Numfashi Da Ake Kira (Asthma)

0
114

Cutar asthma wannan wata larura ce da itama tafi shahara lokacin sanyi ko hazo. Asthma larura ce dake shafar huhu wato sashin numfashi ko ace sashi na musayar iska ajika,wanda kananun kafofin shigar iska domin numfashi ke motsewa su doɗe ta yadda saidai iskar data rage cikin huhu ta fita amma wata bazata shaƙuma zuwa ciki ba.

Kunga kenan kamar mu da bamu da larurar babban misalin da zamu fahimci yadda masu cutar keji shine mu gwada daina shekar iska koda na minti 1 zuwa 2 ne, ya zamto saidai mu rika fitar da ita ta hanci batare da muna shaƙa ba….
Tsaya ku gwada yin abunda nace kafin cigaba da karatu don Allah

Okay! Nasan kun jaraba kamar yadda na rokeku zuwa yanzu ya kukaji? Shin abune mai sauki ko kuwa? Shi yafi komi sauki a mutu,toh wannan tasa nan da nan komi karfin mutum in asthma taso masa sai ya galabaita,saboda jini da kake ganinsa ako’ina ajikin mutum in anhuda ba jinin bane kadai hade yake da iska… hasali ita ke taimaka masa yana zagayawa ko ina ajikinsa,idan babu iska shyasa yanzu zaka zube aga mutum jikinsa ya fara canzawa zuwa kalar blue.

Shin Mee Kee Faruwaaruwa A Cikinikin uhunHuhun Nasuasu Har arAsthmasthma Din inTaa Tashiashi

Kamar yadda nace cikin ƙafofin numfashin mu dake huhu,a cikinsu musayar iska ke faruwa haka kuma ade cikin huhun anan ake samar da majina wacce za muga wadda ta lalace ta daiaina amfani muna fitar da ita ta hanci ko yayin mura.

Domin karanta Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Daukar Ciki Danna nan

Amma ainishin majina abace mai amfani ita ke hanamu jin zafi yayin da ƙirjin mu ko huhun mu ke tasawa da komawa in muna numfashi,tare da hanamu jin zafi yayin hadiyar abinci ko ruwa zuwa cikin mu ta maƙogoro tare da sanya koya abu ya nemi shiga maƙoshin mu zamuji ta ankarar damu munyi tari don fitar dashi,sannan majinar ita ke ƙƙara taimaka mana iska na ratsawa cikin huhun mu yadda ya kamata…

Ita wannan majina dai ha ila yau duk shafe take da kafofin numfashin mu,toh amma ko a maƙoshin mu, ko hancin in majina ta kakare mana ya mukeji? zakaji ba dadi da har tana shaƙeka ko tana to shi ma hanci baka iya shaƙar iska saika shafa robb da sauransu…

Toh abunda ke faruwa a asthma kenan wato majinar tai yawan da ta toshe kafar iskar baki daya, sakamakon samar da ita da yawa fiye da yadda ya dace da ƙƙwayoyin asthmar suka haddasa ayayin da mutum ya shigi ko yai ta’ammali da abunda ke sasu sakin majinar (triggers) wanda
insun saki majinar ne sai muji ana asthma ta tashi.

Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan

Toh kamar yadda nace sakamakon ƙwayoyin halittun cutar asthma din da mutum ya gado sai ya zamto sun rika sakin wasu ƙwayoyi masu illata kafofin iskar ta hanyar haddasa raunuka jikinsu,wanda hakan kesa su motse sa saki majina da yawanta ke ruɓɓanya ta toshe kafofin iskar ta yadda iska bazata iya shiga ciki ba,koda sunyi yunkuri kuma sai akejin numfashin na ƙara wato wheezing yayin da insuka karfafa sai su fadi kasa.

Hakan yasa a lokacin da ciwon ya motsa,ƙofofin shigar iskar numfashi tun daga maƙƙogaron dan aadam kan rufe ta yadda za’a samu nauyi ko sarkewar numfashih,huhu zai samu karancin iskar da ta dace ya shaka.

Tsananin Larurar

Matsalar asthma tana cikin matsalolin da kan hana mai fama da ita rayuwarsa ta yau da kullum, kamar zuwa aiki a office , ko gona,ko anguwa ziyara,ko kuma makaranta idan dalibi ne.

Asthma har ila yau kan hana iyali samun isashshen barci da daddare,kuma lokaci da dama iyaye kan rasa yin aiki da rana saboda cutar asmar ‘ya’yan su,takan kuma iya haddasa jinkirin samun haihuwa ga masu dauke da ita.

Me Ke Haddasa Cutar Asthma

Kaso 70% cikin dari na asthma gadonta akeyi walau daga mahaifa ko wasu kakannin na mutum da ko a tarihi ma mutum bai san labarinsu ba. Yayin da kaso 30% ke samunta sakamakon alaka ko ta’ammali da taba sigari,dattin masana’antun hada ceiling,asbestos, kamfanin takin zamani,yankan katako, da sauran sana’oi dake sa shakara abubuwa masu illah na tsawon shekara da shekaru.

Wannan cuta na iya bayyana a babba da yaro, har sabuwar haihuwa akoda yaushe,saide mahimmin abu duk da haka shine: wanda ya gado wannan cutar zai iya zama lafiya lau na tsawon wani lokaci duk da yana da ita kafin ta bayyana ko agane,domin konkana da ita inbaka haikewa abubuwan dake tada ita.

Haka inma ba’a dalilin gado bane, wato kenan takan iya faruwa kusan ga kowa daga kowane mataki na shekaru har zuwa karshen rayuwarsu.

Suwa Kan Kamu Da Cutar Asthma?

Kamar yadda nace asthma tana shafar kowanne jinsi na mutane mata da maza, fararen fata da bakaken fata kuma a kowane mataki na shekaru cikin kowacce kabila.

Suwa Ke Cikin Hatsarin Kamuwa Da Ciwan

Galibi wadanda keda tarihin cutar cikin yan uwa na jini ko mahaifa sune kan gaba.

Mutane masu kiba ko nauyin da ya wuce kima.

Mutane masu shan taba sigari, ko masu zama a inda ake shanta.

Masu aiki a masana’antun harhada chemicals na noma, ceiling, kamfanonin ƙere-ƙere

Talauci; anyi amannar cewa mutane matalauta su suka fi yawa wajen fama da wannan matsala.kila hakan nada alaka da cewa galibi su sukafi irin wadancan ayyuka masu wahala a kamfanoni irin wadanca

Shin Wani Na Iya Daukar Cutar Daga Wani?

Amsa: A’ah. cutar asthma bata yaduwa daga wani zuwa wani walau ta hanyar barci a daki daya da mai cutar,ko cin abinci a kwano daya ko amfani da cokali daya, bandaki guda, sumbatarsu abaki, rungumar mai cutar kamar majinyacin marar lafiyar,ko abokin auratayya me dauke da ciwon.

Shin Ko Ana Gagon Cutar?

Kwarai kucutkamar yadda na fada abaya, bincike ya nuna cewa akwai yiwuwar gadon cutar tsakanin iyalai madanganta kamar daga kakanni ko iyaye ko yayyen uwa ko na uba, ko daga yaya

Alamomin Asthma

Alamomin asthma ba’a ɓoye suke ba kuma sun haɗa da:

Nauyin numfashi wato ariƙa yinsa sama-sama,hade da jin wata irin kara yayin numfashin kamarta usur musamman ayara.

Jin zafi ko ciwon zafi

Matsanancin tari yayin tashinta.

Ƙaruwar fitar ruwa ta hanci, ba lalle ne aga majina ba.

Tsukewa ko ɗaurewar kirji da rashin jin walwala a qirjin.

Abubuwan Dake Tada Ciwon Asthma

Kamar yadda nace asthma aƙwance ta ke, tashi take jefi-jefi.

Anyi amannar waɗannan abubuwan dazan lissafa suna cikin muhimman abubuwan dake tayar da ciwon,saboda haka yana da kyau adauki matakin kariya daga su,sannan kowanne mai asthma ya kamata yasan me yake tayar masa da asthma dinsa,domin abunda ke saurin tayarwa da wani ita kila a wani ba wannan bane,don sanin abunda ke tayar maka/ki zaisa akiyaye shi,domin kowa da nashi abun dake tayar masa da ciwon:-

Gashin mage (idan yabi iska aka shaƙeshi) shi yasa ba’ason ajeta agidan da masu larurar suke musamman in asthma din na yawan tashi akai-akai

Shakar iska mai tsananin sanyi. Kunga da wannan zamu fahimci me yasa lokacin sanyi tafi tashi.

Shan taba sigari ko shakar hayakinta.

Tashin hankali; walau fushi,ɓacin rai ko samun mummunan labari.

Amfani da kayan rini, saboda karfin chemical din

Shaƙar iska mai ƙura,ko hazo,ko garin alli,ko shaƙar hayaƙi kamar na wutar itace,kara ko hayakin injin janareto.

Shakar kamshin turare

Shin Ana Gwajin Cutar Asthma

Mafi yawan lokuta likitoci kan gane ciwon asthma ne ta hanyar tambayoyi da sauraron karar numfashi a huhun mai matsalar,don haka basai likitoci sun jira gwaje-gwaje ba kafin suce akwai asthma ko babu.

Saide awasu lokutan akan buƙaci wadannan gwaje-gwajen domin tantance ƙarfin matsalar da nemo wasu matsalolin na daban

Yanda dakyau ku karanta Abubuwa Da Ya Kamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada

Akwai gwajin numfashi da ake kira [spirometry] inda akan bin ciken yawan iskar dake shiga da fita a huhu.

Hoton kirji na x-ray

Gwajin kajin majina wato [sputum].

Awon kwayoyin iska acikin jini.

Yadda Za’a Rage Ko Kawar Da Cutar

Cutar asthma bata da magani, kuma ta kansa arasa rai idan ba’a dauki matakin da ya dace ba idan ta tashi,yana da kyau iyali su lura cewa maƙasudin maganin cutar asthma shine:

Domin kawar da dukkan alamominta.
Domin dawo da numfashi dai-dai
Yana da kyau asan magungunan dake lafar da cutar
Shan magani kamar yadda likita ya bayyana.
Asan abubuwan dake haddasa cutar kamar yadda na zayyana asama, sannan a kawar dasu ko a ragesu a muhalli.

Abubuwan Da Ya Kamata Ayi Lokacin Da Ciwon Ya Tashi

1 Abu na farko shine mutum yai ƙoƙari ya nutsu,kada ya tayar da hankalinsa sanda yaji ta tashi,domin tada hankali zaisa buƙatar iska ya ƙaru ajika alhalin kuma babu ita.
2 Mutum ya daure yayi ta numfashi sannu-sannu lokacin da ciwon ya tashi kada yasa karfi
3 A dauki maganin da aka tanada asha ko ashaƙa cikin gaggawa kamar yadda likita yai umarni.
4 Mafi yawan lokuta maganin na shaƙa ne wato (inhaler),saboda tafi saurin bude ƙafofin iska tunda kai tsaye a hanyar numfashin ake fesawa ya shiga.
Don haka mutum ya tabbatar ya koyi yadda ake shaƙawa,haka yan uwansa ma ko mahaifa ya zamto sun koya saboda kada ayi aikin wuce gona da iri.
5 Idan magungunan basu sa matsalar ta lafa ba sanda ta tashi,maza agarzaya asibiti mafi kusa.

Ire-Iren Magungunanta

Akwai magunguna shahararru masu ƙwantar da ciwon nan take da masu kiyaye tashin ciwon wanda idan mutum yaje asibiti ana rubuta masa su na ƙwayoyi.

Kamar yadda nace akwai wadanda ake shaƙa ko kuma zuƙa ta baki (Aerosol inhalers) wadanda ke aiki cikin gaggawa,suma ana iya rubutawa mutum ya saya. suma iri biyu ne;

  • Akwai mai ƙwantar da ciwon inya tashi
  • Akwai kuma mai kiyaye tashin ciwon
    Likita zai rubuta duk wadanda suka dace.

Ya Ake Amfani Dana Zuƙar Wato Inhaler

Idan ta tashi kamar yadda nace ka nutsu, ka zauna kada ka ranƙwafa ko duƙawa

Kana zaune bayan kadau inhaler din saika girgizata,sannan kasa abakinki ka rufe bakin inhaler din da laɓɓanka ya zamto bawata kafa da zata zurare.saika danna inhaler din sau 1,sannan ka cigaba da matsawa duk sekons 30 zuwa minti 1

Bayan ka matsa inhaler din akalla sau 10 amma batare da jin sassauci ba sai karuwar ciwon toh ai maza ataho asibiti,

Kar adaina matsa inhaler din sanda ake kan hanyar asibitin, akalla duk minti 15 amatsa.

A Ƙarshe

Kar a manta ba’a yiwa Inhaler nisan ɓoyo, galibi wasu na galabaita su fadi sakamakon mance inda suka ajeta, asaba mata da gurin ajiya guda daya kuma afili kuma akusa, inma za a fita asata ajaka, saboda sau tari wasu ana samun gawarsu suna kokarin cimma inhaler din sun kasa saboda sun ajeta nesa gata suna hange amma basu da karfin karasawa su dauka, gashi ba kowa agida.

Domin karanta Bayani Mai Mahimmanci Zuwa Ga Mata Akan {Ovulation} Danna nan 

labarin da ya wuceIna Son Ɗa Namiji,Sadai Iyalina Mata Take Ta Haifarmun,Shin Meke Faruwa,A Kimiyance Laifin Waye
Labarin na GabaSamiha-Borin Jini {Hives,Urticaria,Neetle Rash}