Galibi mutane suna ɗaukar annobar cututtuka da masifun rashin zaman lafiya su ne kaɗai masifu; ana mantawa da wasi abubuwa da ke yaƙar mu kuma suke yin galaba sau tari ba tare da mai da hankalinmu a kansu ba.
Musulunci da ya zo ƙasar Hausa ya tarar da Hausawan wancan lokacin a kan ɗabi’u kala-kala, sai ya tsame na gari bai yi hani a kansu ba amma waɗanda suka danganci baɗala, tsafi ko kafirci nan take ya taka musu birki. Alhamduluillahi; Al’ummar Hausawa suka kasance masu ɗa’a da yakana da amana da taimakekeniya da rufin asirin junansu, a ƙolololuwa kuma masu tsoron Allah da gaske, ga shi wasu ba su da tarin ilimin addinin musulunci irin na wannan zamanin.
An sannu sannu Malam Bahaushe ya yi watsi da waɗannan gwalagwalan ɗabi’u na gari wanda ya sa ko a da a kudancin Najeriya iidan za a yi alƙalanci tsakanin mutane, Bahaushe ake nema kokuma ana son a ba da ajiya ko amana shi ma Bahaushe ake nema. Na san mutanen kudu da dama waɗanda a wancan lokacin manyan abokanensu Hausawa ne har ma su suka kasance musu manyan abokai lokacin aurensu a can ƙasashen nasu na kudu.
Zuwan Turawa da kuma mutanenmu da suke yawan zuwa Turai sun zo da ɗabi’un Nasara amma a wancan lokacin ƙyamatarsu ake yi, yanzu kuwa rungumarsu ake yi. A sannu-sannu yanzu Yahudanci da Nasaranci ya ratsa Hausawa har wasu na ganin abin kunya ne a ce ‘ya’yansu sun fi iya Hausa a kan Turanci. Bature ya yi tasiri wajen yaɗa manufofinsa da muradansa ta hanyar mutanenmu saboda haka har yanzu wannan igiyar ta “Indirect Rule” ba ta tsinke ba.
Jama’a ina so ku yi nazari cikin hankali da nutsuwa wajen tantance abubuwan Nasara da suke amfanar mu da waɗanda suke cutar da mu. Da yawa wasu suna ganin in suka ƙyale ‘ya’yansu suna yin abin da suke so shi ne wayewa, ci gaba da kuma zaman lafiyarsu. A da talaka ya tsaya a matsayinsa amma a yau haɗa kansa yake da kowa, wannan shi ne musabbabin jefa al’ummar Hausawa cikin yanayin da suke, kowa ya bar matsayinsa yana kokawar komawa na wani.
Daga ƙarshe ina so in jawo hankalin iyaye, yayye da duk wanda tarbiyya take hannunsa da ya duba irin barnar da kafofin sadarwa suke yi mana sannan babbar masifar iPhone da take yaɗuwa kamar wutar daji a tsakanin ‘ya’yanmu musamman mata. Kashi sama da casa’in na ‘ya’yan marasa ƙarfi da suka mallaki iPhone sun mallake su ne ba ta hanya mai kyau ba.
Babu abin da ba a yi da ‘ya’yan Hausawa don kawai a ba su iPhone a nan Kano da kuma wajen Kano. Zina, luwaɗi, maɗigo, shaye-shaye, tsafi, guduwa daga gida da dai sauransu, yin su ake a ‘kulli yaumin’ amma mun yi biris ko kuma mun yi kunnen-uwar-shegu, ba ta wannan muke ba.
To wallahi wutar dajin nan ta kusa ƙone mu ƙurmus, sai dai tokar mu idan ba mu tashi haiƙan wajen kashe ta ba. Wayar iPhone ba ƙaramar masifa ba ce, kuma ta saka yara da dama yi wa iyayensu maza rashin kunya da rshin yi musu biyayya da tsanar su da kallon su a matsayin waɗanda suka gaza don kawai ba su mallaka musu iPhone ba, duk sun manta da ɗawainiyar da iyayen suka yi da su da iyayensu mata har zuwa girmansu da yanzu suke jin sun kawo ƙarfin su mallaki iPhone.
Wayar iphone ta kasance hanya da take kangarar da yara take iskantar da yara take sa yara yin shirka da dai sauransu. Ya kamata gwamnati da jama’a su yi wani babban motsi wajen ganin wannan masifa ba ta ƙara gaba ba.
Ɗan uwanku Taufiq Aminu Yahya, Jami’ar Bayero Ta Kano
08035972272 taufiqyahya29@gmail.com
Karanta Zikiri Yayin Shiga Gida
Edita@rumasau-kallamu