Hanyoyin Zamantakewar Hausawa

0
9

Al’ummar Hausawa ba haka nan suke zaune kara-zube ba, wato zama irin na ba-kai-ba-gindi, suna da tsararriyar ingantacciyar hanya wadda ta shafi yadda suke tafiyar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum.

A gaskiya ma ko da addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa ya tarar da Hausawa suna tafiyar da harkokin rayuwarsu bisa ingantaccen tsarin da ya shafi harkokin aure da haihuwa da mutuwa da sauran ma’amalolin rayuwa. Wannan ne ya sa ba a sami wata matsala ba a lokacin da Hausawa suka karɓi addinin Musulunci wajen tafiyar da rayuwarsu kamar yadda shari’ar addinin Musulunci ta tsara wa mabiya addinin.

Dangane da haka tsarin zaman Hausawa na yau da kullum an tsara shi daga kafuwar iyali. Daga iyali ne al’umma ko jama’a suke faruwa har su zama babban gida (gidan-gandu) daga nan sai ‘yar unguwa. Ire-iren waɗannan unguwanni ne suke haɗuwa su kafa ƙauyuka, ta haka ne kuma aka sami garuruwa da birane waɗanda sarakuna suke mulki (Smith, 1957:241- 42).

Domin tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum cikin sauƙi, al’ummar Hausawa suna tafiyar da rayuwarsu bisa tafarkin cuɗan-in-cuɗe-ka, watau taimakon-kai-da-kai. Ta wannan fuska idan abin arziki ya sami wani mutum a wannan unguwa ko ƙauye ko gari, misali aure ko haihuwa, sai ‘yan’uwa da abokan arziki su taru don taya shi murna. Kuma kowa kan kawo irin tasa gudummuwa wadda wasu kan kawo hatsi ko abinci ko kuɗi ko sutura da sauran abubuwan arziki.

Dalilin yin haka shi ne don a taimaka wa wannan ɗan’uwa da abin da zai yi wannan hidima ba tare da ya fuskanci wata matsala ba. Irin wannan halayya ce ta haifar da ƙungiyoyin taimakon kai-da-kai domin a ƙara taimaka wa juna. Za a tarar ‘ya’yan waɗannan ƙungiyoyi akwai maza da mata da ma waɗanda ba Hausawa ba a cikinsu, kuma ana yi wa kowane ɗan ƙungiya dukkan abin da ya dace a yi wa wani ba tare da la’akari da jinsi ko ƙabila ba.

Haka kuma idan abin baƙin ciki ya sami wani mutum misali, rashin lafiya ko mutuwa ko wata masifa ‘yan uwa da abokan arziki na kusa da na nesa suna zuwa wurinsa don su yi masa jaje da taya shi jimamin wannan hali da ya shiga ko wani nasa ya shiga. Idan rashin lafiya ya kama mutum, a nan ma za a tarar cikin masu zuwa don jajantawa akwai maza da mata da ma waɗanda ba Hausawa ba, duk suna zuwa ne saboda zaman lafiya da mutuntaka da take tsakaninsu da Hausawa a wuraren da suke zaune.

Bayan wannan al’ummar Hausawa suna tafiyar da ayyukan gayya don taimaka wa kansu-da-kansu. Ana yin ayyukan gayya a gidaje inda ake yin sababbin ɗakuna da gyara tsofaffi da yin darnin gida ko na garka da ɗora ɗan bisan ɗaki da na rumbu da sauransu. Su kuma mata suna yin ayyukan gayya don yin daɓen ɗaki da shafen jangargari da na farar ƙasa da sauransu.

Ana kuma yin ayyukan gayya a gonaki inda ake yin sassabe da huɗa da shuka da noma da girbi da ɗaurin amfanin gona da kawo shi gida. Haka kuma a cikin ƙauyuka da garuruwa ana yin ayyukan gayya wajen gyara masallatai da maƙabartu da magudanun ruwa da mashayar ruwa da gyaran hanyoyin da ake bi don kawo amfanin gona gida da kasuwa.

A wannan zamani ire-iren waɗannan ayyukan gayya da Hausawa suke yi sun yi rauni saboda tasirin zamananci a kan wannan al’umma. A yanzu mafi yawancin mutane suna zaune a bisa tafarkin kowa-tasa-ta-fisshe-shi, amma duk da haka ana samun ɗaiɗaikun al’ummomi a wasu wurare cikin ƙasar Hausa da suke aiwatar da ayyukan gayya a garuruwansu.

Tsarin Shugabanci a Tsakanin Hausawa

Shugabanci na nufin yi wa mutane jagora a halin zamantakewarsu na yau da kullum. A nan duk wanda aka ba ragamar tafiyar da mulkin al’umma, nauyi ya hau kansa na tsare lafiyarsu da dukiyarsu da mutuncinsu. Su kuma waɗanda ake shugabanta haƙƙinsu ne su ba mai mulkinsu haɗin kai, su kuma riƙa bin umurninsa don ya sami sauƙin tafiyar da mulkinsu cikin kwanciyar hankali.

A ƙasar Hausa shugabanci yana farawa daga gida ne, don kuwa a kowane gida wanda yake ƙunshe da mutanen da suka kai biyu ko waɗanda suka wuce haka, akwai maigida wanda nauyin dukkan mutanen wannan gida ya rataya a wuyansa. Shi yake jagorancin wannan gida a dukkan wasu harkokin rayuwar yau da kullum.

Dukkan mutanen gidan waɗanda suka haɗa da matansa da ‘ya’yansa da matan ‘ya’yansa da ƙannensa da matansu da ‘ya’yansu da jikokinsa da barorinsa da ‘yan cin arziki da dai sauran duk wanda yake ƙarƙashinsa na bin ummurninsa. Shi yake yi masu kome wanda ya shafi sutura da abinci da tsaro da kare mutuncinsu da nema masu magani idan sun kamu da wata rashin lafiya.

Idan ire-iren waɗannan gidaje suka yi yawa sai su kafa unguwa. Daga cikin masu gidajen sai a sami wani mai kwarjini daga cikin su wanda ya iya tafiyar da harkokin al’ummarsa, a ba shi mai unguwa. Mutanen wannan unguwa ne tare da amincewar dagacinsu suke zaɓar sa, daga nan shi kuma nauyi ya hau wuyansa na mulkin al’ummar wannan unguwa. Shi kuma ne zai riƙa wakiltar su a duk wasu hidimomi da kuma yin sasanci a tsakanin talakawansa (Usman, 1972:176).

Samuwar unguwanni da yawa yake samar da dagaci wanda dukkan masu unguwanni suke ƙarƙashinsa. Dukkan abubuwan da suke faruwa a waɗannan unguwanni sai an sanar da shi, kuma duk wani sasanci da ya gagari mai unguwa wurin sa ake zuwa don ya yi sasanci. Dagaci yake wakiltar al’ummominsa da suke unguwanni a wasu ma’amalolin rayuwa.

Garuruwan dagatai da yawa suke samar da ƙasar Hakimi wanda shi yake shugabancin dukkan garuruwan dagatai da suke ƙarƙashinsa. Dukkan abubuwan da suke faruwa a garuruwan dagatai sai an sanar da shi, kuma shi yake wakiltar su a duk wata hidima. Idan dagatai sun gaza wajen yin wani sasanci, sai su miƙa maganar gare shi, don ya yi tasa hikimar ya sasanta saɓanin.

Waɗannan garuruwa na hakimai ne suke taruwa su yi ƙasar sarki. Sarki shi ne wuƙa da nama a duk harkokin da suke faruwa a wannan masarauta. Dukkan mutanen wannan ƙasa suna ƙarƙashin mulkinsa, kuma hakimai na sanar da shi dukkan abubuwan da suke faruwa a ƙasashensu. Idan hakimai sun gaza wajen yin sasanci a tsakanin talakawansu, sai su kai ga sarki wanda ta hanyar shawartar ‘yan majalisarsa zai yanke hukunci ko da daɗi ka ba daɗi. Wanda hukuncin bai yi wa daɗi ba dole sai ya yi haƙuri, wannan ne ya sa ake yi masu laƙabi da ‘wuƙar yanka’ (Usman: 1972:176).

A kowace masarauta akwai ‘yan majalisar wannan sarki, su ne suke taimaka wa wannan sarki da shawarwarin da za su taimaka a aiwatar da mulkin wannan ƙasa cikin nasara da adalci. Waɗannan ‘yan majalisa sun haɗa da Waziri wanda shi ne babban mai ba sarki shawara kuma shi yake wakiltar sarki a lokacin da ya fita daga masarautarsa. Bayansa akwai Alƙali da Magatakarda da Shamaki da Shantali da Ma’aji ko Ajiya da Sarkin Fada da Galadima da Sarkin Gida da dai sauransu da dama.

Bayan waɗannan sarautu akwai kuma sarautun da ake ba masu sana’o’in gargajiya. Kowace sana’a akwai wanda ake ba jagorancin mutanen da suke gudanar da irin wannan sana’a don ya yi sasanci a tsakanin ma’abota sana’ar da kuma tafiyar da ita bisa ingantaccen tsari. Ire – iren waɗannan sarautu sun haɗa da sarkin noma ga masu yin noma da sarkin maƙera ga masu yin ƙira da sarkin aska ga masu yin sana’ar wanzanci da sarkin makaɗa ga masu yin sana’ar kiɗa da sanƙira ko sarkin roƙo ga masu yin sana’ar roƙo da sarkin fawa ga masu yin sana’ar fawa da sauransu da dama (Adamu, 1978:5).

Dukkan waɗannan sarautu da aka yi bayani a kansu tun daga mai unguwa zuwa ga sarki da ‘yan majalisar sarki da masu riƙe da sarautun sana’o’in gargajiya, an tsara su ne bisa tafarkin gado. Wato idan wanda yake riƙe da sarautar ya mutu ko ya yi murabus ko aka tuɓe shi, a mafi yawancin lokaci ana zaɓar wani daga cikin ‘ya’yansa don ya gaje shi, wani lokaci kuma ana ba ƙanensa ko wani ɗan uwansa don ya gaje shi.

Wannan na faruwa ne saboda irin ƙima da mutunci da martaba da muhibbar kowane daga cikin ‘ya’yan sarkin ko danginsa. Hanyar da ake bi wajen zaɓar sarki a ƙasar Hausa kafin jihadin Shehu Ɗanfodiyo ba tsari ne na bai ɗaya ba. Akwai bambanci a tsakanin wannan masarauta da waccan. Daga kafuwar Daular Usmaniyya zuwa mulkin mallakar Turawa an sami canji dangane da yadda ake tafiyar da wannan tsari.

Don kuwa dukkan sarkin da aka zaɓa, a fadar Mai Martaba Sarkin Musulmi ne za a yi naɗinsa, kuma Sarkin Musulmi ne yake amincewa da zaɓensa kafin a naɗa shi, saɓanin tsarin da suke bi kafin wannan lokaci. Kafuwar mulkin mallaka kuma, sai ya ƙara sauya tsarin don kuwa dukkan sarkin da za a zaɓa sai Gwamna ya amince kafin a naɗa shi ya hau gadon sarauta.

Kafin jihadin Shehu Ɗanfodiyo a shekarun 1804 zuwa 1809 dukkan ƙasar Hausa tana rarrabe ne masarauta-masarauta. Kowane sarki na mulkin iyakar garuruwan da suke ƙarƙashin ikonsa. A babban birnin wannan masarauta ne ake gudanar da harkokin mulki da na tattalin arziki. Wannan dalili ne ya sa ba a sami dunƙulalliyar ƙasar Hausa wadda take ƙarƙashin mulkin sarki ɗaya ba. Sai bayan da aka yi jihadi kuma aka kafa Daular Usmaniyya, sannan ne aka haɗe su a ƙarƙashin daula ɗaya mai cibiyar mulki a Sakkwato. A wancan zamani tsakanin su sai dai yaƙe-yaƙe da kai hari don kamen bayi.

Tun daga mulkin Hausawa har zuwa mulkin Fulani a ƙarƙashin Daular Sakkwato zuwa mulkin mallaka na Turawa, tsarin sarautar ƙasar Hausa bai sauya ba. To, amma ayyukan da sarakunan suke yi ya sauya, kuma a wajen mulki ba su da izinin aiwatar da wasu hukunce-hukunce kamar yadda suke yi a da can. A yanzu an ɗauke su iyayen ƙasa kawai, ba su da cikakken iko da ƙasa da talakawa, duk sun koma ƙarƙashin gwamnati.

Idan ma za su yi wani abu, sai sun nemi izini daga gwamnatin ƙaramar hukumar da suke ko jiha ko gwamnatin tarayya idan abin mai ƙarfi ne sosai. A wannan zamani sarautun gargajiya an mayar da su ƙarƙashin ikon ma’aikata mai kula da ƙananan hukumomi da masarautun gargajiya ta kowace jiha a faɗin Tarayyar Nijeriya. A Jamhuriyar Nijar ma suna da tsari irin nasu wanda shi ma dai sarautun gargajiya na wannan ƙasa suke ƙarƙashin irin wannan ma’aikata wadda take kula da yadda suke tafiyar da harkokinsu.

Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

Edita@rumasau-kallamu

 

labarin da ya wuceFassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya 1st August 2025
Labarin na GabaAddinin Mutanen Ƙasar Hausa
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.