Gudunmawar Ali Gumzak Wajen Samarwa Da Kuma Haɓaka Finafinan Hausa

0
32

Muhammad Sahal Aliyu

NAZARIN WASU DAGA CIKIN FINAFINANSA

DAGA
FATIMA ADAM ISAH
adamisahfatima@gmail.com
07015974659
DA
MUHAMMAD SAHAL ALIYU
Sahalaliyu@gmail.com
07065994177
ƊALIBA A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA DA KIMIYYAR HARSHE,
JAMI’AR JIHAR KADUNA, KADUNA

Maƙalar Da Aka Gabatar A Taron ƙara Wa Juna Sani Na ƙasa Da ƙasa Karo Na Biyar Mai Taken ‘Hausa Playwrights And Dramatists As Agents Of National Integration And Development’ In Commemoration Of Late Playwright, Alhaji Yusuf Ladan, Ɗan Iyan Zazzau, 2th-4th Dec 2021. Wanda Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Harshe Jami’ar Jihar Kaduna Ta Shirya.

DECEMBER, 2021.

Tsakure
Tun samuwar fina-finan Hausa a shekarun baya, harkar ta sami bunƙasa da haɓaka sosai wanda hakan ba ya rasa nasaba da yadda matasa da ‘yan kasuwa suka shigo cikin harkar shirya finafinai. Waɗannan fina-finai na Hausa idan aka masu fyaɗar kaɗanya, za a ga yawancin saƙonnin da ke ƙunshe a cikinsu ba ya wuce soyayya da matsalolin zamantakewar aure.

Don haka ne ma wannan muƙalar za ta mayar da hankali a kan ɗaya daga cikin jigogi a harkar shirya fina-finan Hausa da ba da umurni wato Ali Gumzak tare da nazarin gudummuwarsa wurin samar da kuma haɓaka fina-finan Hausa. Daga ƙarshe, za a yi nazarin gundarin soƙonni da ke ƙunshe a wasu fina-finansa guda uku wato Burin Fatima da Izzatu da kuma Ƙawaye.

Gabatarwa

Ko shakka babu, finafinan Hausa ɓangare ne na adabi kuma fasaha ce ta al’umma da ke nuni da yanayi da tsarin rayuwar al’umma. Ta hanyar fina-finan Hausa za a iya ganin hoton rayuwar wata al’ummar da ta gabata, haka kuma za a iya fahimtar tsarin rayuwar waɗannan mutane da ɗabi’unsu da tattalin arziki da zamantakewarsu.

Za a iya ganin hoton abin da ke faruwa a cikin al’umma, har ma wani lokaci a iya kirdaden abin da zai iya faruwa a cikin al’umma. Finafinan Hausa hanya ce ta bayyana tunanin mai shirya fim ɗin, ko marubuci, ko kuma irin falsafarsa game da rayuwa.

Taƙaittaccen Tarihin Samuwar Fina-finan Hausa

Fim abu ne mai gajeran tarihi idan aka kwatanta shi da sauran ɓangarori na adabin zamani. Misali waƙa da rubutun zube waɗanda tuni suka ci gaba ta fuskar nazari da aikace-aikacen masana da manazarta masu rubuta kundayen bincike don neman digiri na farko zuwa na uku.

A wajen Hausawa wasan kwaikwayo shi ne tushen samuwar fina-finan bidiyo domin shi aka fara aiwatarwa a dandali kafin a samu na’urar ɗaukar hoto ta majigi wadda daga baya kuma aka sami gidajen talabijin da na’urar bidiyo da ake amfani da ita a yanzun.
Dangane da wasannin kwaikwayon majigi, sun fara samuwa ne a wajen 1950 lokacin da ma’aikatar yada labarai ta Arewa (Ministry of Information Northern Nigeria) take ƙoƙarin wayar da kan ‘yan Arewa dangane da harkokin noma da wayar da kan su al’amuran da suka danganci rayuwar yau da kullum.

To sai ma’aikatar ta zaɓi ta yi amfani da wasan kwaikwayon majigi domin shi ne hanya mafi sauƙi da za a jawo hankalin ‘yan Arewa a kan su noma abubuwan da gwamnati take buƙatar da su a kan yadda da wannan noma ta hanyar amfani da hanyoyin zamani. To gwamnatin wannan lokacin ta yi amfani da wasan kwaikwayon majigi domin gudanar ta hanyar amfani da mota wadda take ɗauke da na’urorin nuna majigi wato “Projector”.

Ana amfani da wannan mota ne ta bin birane da ƙauyuka domin nuna wasannin domin ilimantar da su a wannan ɓangare na noma da kuma ɗebe masu ƙewa. Dangane da fim wanda aka fara aiwatarwa a harshen Hausa kuwa shi ne Baban Larai Mai Auduga a cewar Abdulkadir (1998:24) wanda aka aiwatar a shekarar 1948.

Daga nan sai Ɗan Arewa a London, sai kuma fim ɗin Shaihu Umar a shekarar 1976 da sauran ɗimbin fina-finan da aka samar a wannan lokacin, sai dai akwai fina-finan masu yawa da wasu mutane ko jihohi suka shirya, to amma ba su zo ga jama’a ba saboda wasu dalilai.

Akwai kuma fina-finan da tashoshin gidajen talabijin na ƙasa da suke jihohin Arewa suka gudanar don nuna wa jama’a. Misali Golobo daga Sakkwato da Karkuzu na Bodara daga Kano. Dukkan waɗannan shirye-shirye na NTA da suke a waɗannan jahohi. Har ila yau, kuma akwai Bakan-Gizo da Hadarin Kasa sa Hankaka na CTV 67 Kano (Gidan Dabino da Wani), a cikin Adamu da wasu, (2004:342).

Fim na farko da ma’aikatar yaɗa labarai ta Arewa ta fara nuna wa jama’a sun haɗa da fim ɗin Baban Larai da Dan Arewa a London da Shaihu Umar da Kulɓa na Ɓarna da sauransu. Nuna fim babu ko shakka hanya ce mafi inganci ta yada al’ada. Ta wannan hanya ce al’adun ƙasar Indiya da Sin da Amurka su ka zo Nijeriya har ma wasunsu suka samu karɓuwa, aka kwaikwaiye su.

Binciken da aka gudanar a 1970, a Arewa akwai gidajen silima ɗari huɗu(400) wato a cikin birnin Kano kawai, akwai guda shida (6) kuma kowannen su za su iya ɗaukar mutane fiye da dubu biyu(2000) a lokaci ɗaya. Sa’anan kuma akwai gidajen silima da dama a sauran ƙasashen Arewa, amma duk cikin su babu na ‘yan ƙasa, ƙwarori ne (Lebanese) ke da su. Saboda haka mutanen Arewa, ba su da zaɓin fim ɗin da za a nuna masu.

Dangane da wannan dalilin, shi ya sa mutane suka shaƙu da kallon fina-finan Indiya, ga kaɗe-kaɗe da raye-raye. Ba abin mamaki ba ne a ƙasar Hausa ka ga wani magidanci na rera waƙar Indiya lokacin da yake nishaɗi ko kuma lokacin da yake gudanar da wani aiki. Su ma mata ba a bar su a baya ba, lokacin Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna a 1974, lokacin da fito da wani fili na kaɗe-kaɗen Indiya da ake sawa, ba mamaki ka ji ana kiran mace Bahaushiya da sunan Hema ko Rani da dai sauran sunayen taurarin da suka yi fice a fina-finan Indiya.

Kaunar da Hausawa ke wa labaran soyayya, shi yasa CTV 67 ke nuna wasu wasanni guda biyu wato Bakan Gizo da Hadarin Sama waɗanda suka sami nasara. An gina labaran ne kan soyayya irin ta Indiya (Salihu,2002).

Bunƙasar Fina-Finan Hausa

Sun fara samuwa ne tun kafin ‘yancin Nijeriya musamman bayan kammala yaƙin duniya na biyu. A wannan lokaci tattalin arziƙin Turai ya yi rauni ƙwarai tun ma ba na Ingila ba. Saboda haka ne Turawan mulkin mallaka suka taru don tattauna hanyoyi da za su fitar da ƙasashensu daga wannan ƙangi, inda suka shirya cewa a samu kaya da suka sarrafa a kasuwa.

Nan take aka yanke shawarar cewa ƙasshen da ake wa mulkin mallaka ne za a iya matsawa su noma abubuwa da za a kawo nan ƙasar Ingila irin su gyaɗa da auduga maimakon kayan abinci, sa’annan kuma a yi wa jama’a farfaganda domin su yi amfani da kayayyakin da aka ƙera a ƙasashen wajen. Ta irin wannan hanyar ce sai su jama’a suka kashe kuɗaɗen da suka samu ta sayan kayayyaki daga waje.

Me ya kamata a yi don a tura wa mutane wannan hanyar kashe kuɗi? Sai aka yanke shawarar yin fina-finai da Hausa domin ‘yan Arewa. Nan ne aka fi samun manoma sai aka shirya fim ɗin Baban Larai. Wanda aka nuna wani hamshaƙin manomi ne da ya bunƙasa wajen noman gyaɗa da auduga.

Bayan samun ‘yancin kai an yi fina-finai don nuna muhimmancin haɗa kan ƙasa, da samun ‘yancin kai, da yadda ake gudanar da zaɓe. Haka kuma an yi fina-finai irin na Sir Ahmadu Bello da sauran mashahuran mutane da Jam’iyyar NEPU da NCNC mafi yawan waɗannan fina-finan Hukumar Talabijin ta Amurka ce ta yi su, inda aka yi fim mai suna Ɗan Arewa a Landon inda aka nuna Dr. Ibrahim Tahir a matsayin tauraro. An nuna yadda ɗan Arewa ya kamata ya gudanar da rayuwarsa a Landon.

An fara yin fina-finan Hausa a 1960 lokacin da Adamu Halilu ya shirya fim ɗin Shehu Umar wanda aka gina kan littafin nan na Shehu Umar na Abubakar Tafawa Ɓalewa. Fim ɗin ya sami gagarumar nasara saboda abu biyu. Na ɗaya, ita ce a lokacin babu fim na Hausa tsantsa sai shi, na biyu kuma shi ne jigon labarin mai tsuma jiki ne wato soyayyar uwa zuwa ga ɗanta.

A lokacin da aka nuna fim ɗin a silima ta ‘Plaza’ a Kano a 1976, duk wanda yake ganin ya shahara wajen zuwa silima ya je kallo. Bayan waɗannan fina-finai an yi waɗansu fina-finan da suke magana kan al’adun gargajiya na Hausawa waɗanda suka haɗa da “Auren Hausawa” da “Kano Heritage” da “Hawan Sallah” dukkansu na Alhaji Yahaya Imam.

Dangane da bunƙasar fina-finan Hausa kuwa (Salihu, 2011) ya ce za a iya cewa sun yi tashin gwauron zabi ta yadda suka kai ga wani matsayi da za a iya kwatantawa da matsayin sana’ar kwatantawa da matsayin sana’ar acaɓa a ƙasar Hausa.

Daga shekarar 1990 lokacin da aka fara gudanar da fim ɗin bidiyo na sayarwa zuwa yanzu an sami kamfanoni fiye da 121 da suka yi rijista da ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Jihar Kano, ban da waɗanda kuma suke gudanar da harkokinsu a ɓoye, sannan daga wannan lokaci zuwa yanzu an samar da fina-finan Hausa sama da guda dubu (1000).

Muhimmancin Fina-Finan Hausa

Fina-finan Hausa abubuwa ne masu matuƙar muhimmancin gaske ga al’ummar Hausawa, musamman domin ilmantarwa da faɗakarwa da ke tattare da irin waɗannan fina-finan. Maƙasudin shirya fim shi ne domin wayar da kai ko kuma maganin wata matsala da take tattare ga al’umma, wato ta yi wa al’umma dabaibayi. Ta harkar fim ake nuna wa jama’a wata matsala mai wuyar warkewa kuma a warwareta domin nuna wa jama’a ta yadda za su kuɓuta duk lokacin da suka ci karo da irin wannan matsala.

Kuma ana shirya fim a kan kowace matsala ta rayuwa domin warware ta ko maganinta.
Fim hanya ce ta faɗakar da al’umma, wato ana amfani da fim don ilimantar da mutane a kan wani abu da ya shige musu duhu ko kuma wani abu da ake so su yi ko su ɗauka.

Misali, idan gwamnati tana so ta faɗakar da jama’a bisa ga muhimmancin ilimi za ta sa a shirya fim wanda wani ya shiga makaranta har ya gama ya samu aiki ya zama wani a al’umma ta yadda mutane za su kwaikwayi wannan mutum. Akwai fina-finan da aka shirya domin ilimantarwa waɗanda suka haɗa da Jahilci Ya Fi Hauka da Wuyar Magani Zato wanda yake ilimantarwa a kan yawan zage-zage da ke faruwa a ƙauyuka musamman a kan maganar maita da sauransu.

TAKAITACCEN TARIHIN ALI GUMZAK

An haifi Ali Gumzak a shekarar alif ɗari tara da saba’in da tara (1979), a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano. Asalin sunansa Aliyu Ibrahim Khalil. Ya yi karatun firamare a makarantar Makama Primary School, sannan ya yi karatun sakandire a wata makaranta da ake kira “Gwale Secondary School, sannan daga bisani ya tafi School of Management Studies, inda ya karanci Financial.

A hirar da aka yi da shi, ya bayyana cewa abun da ya jawo shi shiga harkar fim shi ne sha’awa da kuma sana’a. Ya fara harkar fina-finai a shekarar dubu biyu da sha ɗaya inda ya shirya fim ɗinsa na farko mai suna Salma Hayat. Fim ne da ya ja hankalin mutane sosai saboda saƙon da yake cikin sa.

Salma Hayat fim ne da aka yi shi domin jan kunne ko gargaɗi ga ‘yan mata masu wulaƙanta samari. Ali Gumzak ya ce ba zai iya tuna adadin fina-finan sa ba sai dai a ƙalla za su kai hamsin (50) ko fiye da hakan a halin yanzun’. Misalan wasu daga cikin wannan fina-finan sun haɗa da:

1.Salma Hayat
2.Baban Sadiq
3.Manyan Gobe
4.Sultan
5.Zango
6.Dawo Dawo
7.Burin Fatima
8.Jaruma
9.Ka yi na yi
10.Aliya
11.Wata Ruga

12.Ruma
13.Meera
14.Wasiya
15.Haidar
16.Maƙota
17.Ƙawaye
18.Sai da ke zan rayu
19.Manyan Mata
20.Ga Duhu Ga Haske
21.Rumfar Shehu
22.Karangiya

DALILIN SAMUWAR SUNAN GUMZAK

Ya samu wannan suna na Gumzak ne sanadiyar wani aiki da ya yi a ƙarkashin kamfanin wani mutum mai suna Hamza, Hamza ya haɗa sunan garin Mahaifinsa wato (Gumel) da kuma sunan garin Mahaifiyarsa (Zakirai) shi ne ya samar da Gumzak. Sanadiyar ficen da ya yi a wannan kamfanin ne ya sa ake kiran shi da wannan sunan.

Ali Gumzak ya kara da cewa ba shi da wata gaɓa da ya fi karkata a kai, yana taɓa kowane sashe walau na barkwanci ne ko na soyayya da dai sauran irin nau’in fina-finai. Duk wanda ya kalli fim ɗin Rumfar Shehu ya san fim ne na barkwanci, fim din Dawo-Dawo fim ne na soyayya, fim ɗin Salma Hayat fim ne na jan hankali. Ya shirya fim ɗin da ya shafi addinin muslinci wato Ga Duhu ga Haske.

ƘALUBALEN DA YA FUSKANTA A RAYUWARSA

Kamar yadda muka sani duk wata ɗaukaka ta rayuwa sai an sami ƙalubale. Daga cikin ƙalubalen da ya fuskanta su ne; Ba ya manta lokacin Gwamna Shekarau a Kano, shi da abokin sa Aminu Saira sai da suka bar garin Kano suka dawo garin Kaduna, a lokacin ko kuɗin da za su kama ɗaki ba su da shi. Sai daga baya suka samu wani ɗaki da ake biya a Arewa House.

Ya ƙara da cewa wannan babban ƙalubale ne mutum ya tafi ya bar mahaifansa. Bayan haka ya ce kallon da mutane ke musu da cewa suna ba da gudunmawa wajen ƙara taɓarɓarewar tarbiyan yara, ya ce wannan ma wani babban ƙalubale ne’. Sannan yace satar fasaha ma ƙalubane ne, domin sai sun gama wahala ba su mai da kuɗinsu ba sai zauna gari su kwafe don su saida.

NASARORIN DA YA SAMU A HARKAR FIM

Yace nasarorin da ya samu sun fi kalubalen yawa, sanin da mutane suka mai a duniya yana ganin babban nasara ce a rayuwar shi. Da kuma tarin masoya da ya samu ya ce matuƙa wannan abun yana burge shi. Daga cikin nasarorin ya samu gidan zama na shin a kan shi sannan ya sai abun hawa, har ila yau ya yi aure duk ta sanadiyar wannan harka ta fim. Inda yace yanzun kam Alhamdulillah yaran sa biyu sannan yana da mata ɗaya kuma yana zama a garin kano .

YADDA ALI GUMZAK YAKE KALLON HARKAR FIM

Ya ce a ganinsa harkar fim hanya ce da ke gyara tarbiya, sai dai kowa akwai irin kallon da ya ke ma harkar. Yadda mutum ya ɗauke ta, haka zai amfana da ita, sai dai su suna yi ne don gyara da jan hankali da kuma gargaɗi ga masu irin halin walau mai kyau ko akasin hakan. Ko kuma ya za a yi a nuna ma al’umma dai dai da kuma akasin hakan. Ya ƙara da cewa jigon fim shi ne mutum ya gani ya yi koyi da mai kyau ko ya watsar da na banza.

NAZARIN FIM ƊIN BURIN FATIMA

Yan Wasa
1.Adam.A.Zango
2.Aisha Aliyu Tsamiya
3.Maryam Booth
4.Ummah Shehu
5.Jamila Gwaska
6.Jamilu Kochila
7.Haj. Aisha Mahuta
8.Tasiri Kaduna
9.Asma’u Nass

Shiryawa; Abubakar Bashir Maishadda
Mataimakin mai shiryawa; Aisha Aliyu Tsamiya
Umarni; Ali Gumzak
Mataimakin mai shiryawa; Murtala Balala
Shirin kamfanin Maishadda Investment Nig.Llimited
Shekarar: 2017

Da farko dai an nuna Fatima da ƙawayenata su biyu a cikin makaranta, suna Magana a kan auren da Fatima ta yi, suna ba ta shawarar cewa ya kamata ta yi irin tsarin nan na ma’aurata domin idan ta haihu hakan zai shafi karatun ta. Bayan Fatima ta ba wa mijin ta wannan shawarar sai ya yi fushi ya nuna mata baya so. Sannan ya faɗa mata cewa haihuwa ba ya hana karatu, ya kuma kawo mata misali da wata da ta zama Farfesa, kuma ta yi aure ne bayan ta kamala karatun sakandare.

An nuna Fatima ta samu juna biyu bayan wani ɗan lokaci, Umar ya yi matuƙar murna da wannan labarin sai dai bayan ta je makaranta ne ƙawayenta su ka ga tana amai sai suka fara ba ta shawarar cire cikin, har suna ba ta misali da cewa cikin mai laulayi ne ga shi karon farko har ta rasa jarabawa na gwaji na makaranta.

A haka Fatima ta biye wa shawarar ƙawayen ta aka zubar da wannan cikin, ta cewa mijin ta ta yi ɓari. Bayan kammala makarantar Fatima da ɗan wani lokaci ne sai ta fara son haihuwa, amma sai Umar mijin ta ya ce mata “haihuwa na Allah ne, in lokacin ya yi zai ba su”. Duk da haka Umar bai daina neman mata magani ba a duk inda ya samu labarin wani likita ko mai maganin gargjiya.

Ana haka ne kwatsam Umar ya samu labarin wani ƙwararren likita sai ya ɗauki Fatima, ya kai ta wajen shi. Bayan gwaje- gwaje sai ya gano wannan zubar da cikin da tayi ne a baya ya haifar mata da wanann matsalan, bayan komawar su gida ne sai Umar ya yi fushi da Fatima har ta kai ga ya ƙarba shawarar da mahaifiyarsa ta daɗe tana ba shi a kan ya ƙara aure.

Bayan Umar ya ƙara aure ne da ɗan wani lokaci sai wannan matar ta samu ciki, murna a wajan Umar da mahaifiyar sa ba kama hannun yaro, lokacin ne koma Fatima ta ci gaba da ganin bambamci a cikin gidan, wanda amaryan ta haihu a hakan ba abun da ba ta gani. Umar bai da lokacin Fatima sai daga ƙarshe da ta nuna za ta bar gidan sai ya ce mata ya yafe mata kuma zai cigaba da neman man mata magani har Allah ya sa a dace.

JIGON FIM ƊIN BURIN FATIMA

Kamar yadda muka sani jigo na nufin ginshiƙin abin da fim ya ƙunsa. Wato dalilin yin fim ɗin. Akwai masana da dama da suka yi magana a kan jigo. Sun haɗa da, Sarbi,(2007;71) in da ya ce jigo a fagen adabi na nufin manufar marubuci, wanda dukan bayanai suka dogara da ita.

Jigon cikin wannan fim ɗin shi ne “Gargaɗi ko jan hankali ga masu bin shawarar ƙawaye”. Idan muka yi duba yadda mijin Fatima wato Umar ya nuna mata soyayya sannan ya nuna mata yana son haihuwa, amma ƙawayen ta suka zuga ta da cewa idan ta bari ta haihu za ta kasa karatunta na jami’a, tattaunawarsu da ƙawarta a cikin cikin makaranta ɗaya ga cikin ƙawayen ta ta ke ce mata:

“Ni fa na san ba a iya haɗa aure da karatu, domin da zarar kin samu ciki za ki fara samun carryover, daga nan kuma sai spillover, daga nan kuma sai tafiya, ba ki ga Karima ba sai da aka kore ta.” Har ila yau, za mu ga tun daga nan ta fara haska mata irin matsaloli da za ta fuskanta idan har ta yadda ta ɗauki ciki, da kuma abin da zai biyo baya na samun cikas a a harkar karatu, tare da buga mata misali kan makomar ɗaya daga cikin ƙawayensu mai suna (Karima) ta shiga, suna dai ganin rashin cikin shi ne alheri a shawarar su.

An kara nuna su tare, inda suke zuga Fatima domin ta zubar da cikin da ta samu, duk da cewa ta nuna musu tana jin tsoro amma a hakan suka dage suka cusa mata wannan ra’ayin a zuciyar ta har ta amince da wannan shawarar: “Fatima kin ga tun daga yanzun daga samun cikin, kin fara samun matsala ba ki da test ɗin da malam ya yi jiya, sannan ya ce ba zai yi ma kowa makeup ba, kin ga abun da muke guje miki ke nan tun farko, don haka ki zo mu je asibiti a markaɗe cikin.”

Sai Fatima ta ce:To me zan ce wa Umar? Ba ku ga yadda yake son cikin nan ba.”
Sai ƙawarta ta ce mata: “To ki faɗa mai za ki yi kin zubar da cikin, zuwa kawai za ki yi mu je wajen wani doctor na cikin sauƙi zai miki komai, shi dai kawai ya san kin fito makaranta idan an gama ki koma gida ki kira shi a waya ki sa kuka yana zuwa ya tambaye ki ki ce cikinki, kin yi ɓari, shi ke nan”

Bayan Fatima ta amince ne sai suka je aka cire cikin kuma ta yi duk yadda suka tsara mata. Idan muka duba wannan maganan da ƙawar Fatima ta yi za mu ga cewa ta ɗora ta a kan turbar ƙin yi wa mijinta biyayya wanda hakan ne ya haifar mata da duk wata matsala da ta shiga ciki na rashin haihuwa. Fim ɗin Burin Fatima ya nuna mana ƙin aminta da ƙawayen banza da kuma ɗaukar shawararsu wacce idan mutum ya bi tabbas zai faɗa halaka.

NAZARIN FIM ƊIN IZZATU

Jaruman cikin shirin sun haɗa da:
Ali Nuhu
Abdul.M.Shareef
Hadiza Muhammad
Fatima Muhammad(Fandi)
Abdussalam Imam
Ladidi Fagge

Shiryawa; Yakubu Inuwa qyari
Umarni; Ali Gumzak Sak
Kamafanin; Gumzak investment Nigeria Limited
Shekarar; 2019

An nuna yadda wata budurwa mai suna Izzatu da wani ɗan uwanta wanda yake tamkar aboki a gare ta duk inda za ta suna tare haka ma aikin gida ko saƙo duk tare suke yi. Har iyayen su suke tunanin haɗa su aure domin ana ganin soyayya suke yi, kwatsam Izzatu ta kawo mijin aure gida aka sa lokacin aure ana ta shirye-shiryen buki, kwanaki na ƙara ja har lokacin bukin nan ya zo.

Suna cikin shagalin buki ne a dandali da daddare sai ga wani tsoho ya zo yana musu magana a kan su daina dare ya yi, sai Izzatu ta yi masa rashin kunya ta ce bai isa ya hana su yin rawar gaban hantsi ba, har tana cewa ji tsohon nan. Bayan ta koma gida ta kwanta bacci ne sai wasu irin ƙuraje suka fito mata a jiki, aka dinga neman magani amma ba a dace ba, kwatsam sai aka samu labarin wani mai magani.

Bayan sun je wajen shi sai ya ce wannan mutumin aljani ne, sannan za a samu magani amma sai wani na jikin ta wato mahaifin ta ko ɗan uwan ta ko dai mijin ta su ne kaɗai za su iya zuwa wajan maganin. Babanta makaho ne ba zai iya zuwa ba, don haka sai aka ce mijin da ta aura shi ya ce. Kwatsam sai wannan mijin ya kawo mata takardan saki.

Don haka wannan ɗan uwan nata shi ya tafi wajan samun maganin, dama kuma da sharaɗin wanda ya je sai ya dawo shi ma da wata kalar cutan. Cikin nasara ya samu mata magani ta samu lafiya sai dai ya samu irin ƙurajen a jikinshi da kuma ƙusinbi.
Iyayen Izzatu sun yi tunanin haɗa Izzatu da wannan abokin nata aure amma ta yi butulci ta ƙi yarda.

Mahaifiyarta ta yi Alawadai da halin ta har ta kai ga gudu ta bar gida. Garin guduwan ne sai mota ta bige ta har aka yanke mata ƙafa. Bayan dai wannan abun da faru da ita sai suka so haɗa ta aure da ɗansu, sai suka gano asalinta su ma suka yi tir da ita suka mai da ta gidan su, da ƙyar suka yafe mata dai a ƙarshe.

JIGON FIM ƊIN IZZATU

Kamar yadda aka ba da ma’anar jigo a baya, shi ne ginshiki na gina fim ɗin. Wannan fim na Izzatu jigon shi, shi ne Butulci. Butulci na nufin (yankakkiyar rashin godiyar Allah). Rashin nuna godiya ga wani mutum. Inda butulci ya fito a wannan fim din shi ne inda Izzatu ta ƙi ta aure wannan ɗan uwan nan ta har ta gudu ta bar gidan su sanadiyar hakan.

Sannan butulci a karo na biyu shi ne inda mijin ya sake ta a lokacin da ta ke buƙatar shi, lokacin da ya kamata a ce ya tafi wajan neman mata magani, amma sai ya mata sakayya da takardan saki duk da irin soyayyan da aka nuna sun yi. Butulcin da Izzatu ta ma wannan ɗan uwan na ta har ta nuna tana ƙyamar shi sannan kamar ma ba ta san shi ba.

Wannan shi ne abun da ya faru a cikin shirin izzatu, an yi ƙoƙarin jan hankalin ‘yan mata masu ma tsofaffi rashin kunya da rashin ladabi ga na gaba da su, sannan an ja kunne ga kyautata wa wanda ya kyautata maka a rayuwa.

NAZARIN FIM ƊIN ƘAWAYE

Jaruman cikin fim ɗin
Ali Nuhu
Sani Danja
Hafsat Ɓarauniya
Aisha Humaira
Hajara Usman
Rahama Hassan
Da sauran su

An nuna ƙawaye guda biyu Ruma da kuma Fatima a makaranta saboda tsabar ƙawancen su a ɗaki ɗaya suke kwana a makarantar babu abin da ɗaya za ta yi ɗaya ba ta sani ba. Sai dai halinsu ya sha bamban kamar yadda ma su iya Magana kan ce ”Sai hali ya zo ɗaya ake abota” Su kuma wajan su ba haka ba ne. Don ita Fatima tana da natsuwa akasin ƙawarta Ruma.

Hakannan matsalar ɗaya ta ɗaya ce, haka kuma kowa da yake a makarantar ya san su tare don haka komai na su ɗaya su ke yi. Suna cikin hakan ne ita Ruma ta samu matsala da saurayin ta sanadiyyar halinta na bin maza. Bayan kodayaushe ƙawar tana nuna mata gaskiya da cewa iyayen su fa karatu suka turo su ba wasa ba, amma ta ƙi ji. Saurayin da ya gane sai ya dai na zuwa wajan ta ya kuma dai na kiran ta.

Sanadiyar hakan Ruma ta ne ma ƙawarta ta raka ta Abuja wajen shi, amma sai ta umarci ƙawarta da tace mai ta zo biki ne, hakan kuma suka yi sai ya kama mata ɗaki ya kuma ba ta kuɗi bayan ta faɗa ma Ruma ne sai ta ce ai soyayya su ke yi ba ta yarda ba, cikin hakan ne ta kira mahaifiyarta a waya tace mata ga fa ƙawarta ta tafi Abuja bayan kuma ta hana ta tafiya, maman ta yi fushi ta kira ta a waya ta tambaye ta inda ta ke sai ta ce tana gidan yayarta.

A haka dai har ta samu ta kira yayar ta mata bayani shi koma saurayin Ruman ya biya mata kuɗin jirgi don ta yi saurin dawowa. An nuna lokacin da za ta shiga otel ɗin da ya kama mata, mijin da za ta aura ya ganta daga nan ya je ya yi mata mummunan zato sannan ya fasa auren ta, ya aika gidan iyayen ta aka kwaso masa kayan auren shi.
Haka ita ma Ruma saboda halinta wannan saurayin nata ya fasa auren ta, ya dawo ya aure wannan ƙawar tata wato Fatima mai natsuwa da kuma hankali.

JIGON FIM ƊIN ƘAWAYE

Jigon wannan fim ɗin ba ya wuce nunawa ‘yan mata muhimmancin kamun kai. Idan aka ce kamun kai ana nufin natsuwa da yin abun da ya kamata da kuma kama mutuncin kai.
A wannan fin ɗin mun ga yadda ƙawar Ruma wato Fatima ta so ta sa ƙawarta a hanyar daidai amma ta ƙi, don akwai inda ta ke ce mata;

“Wai ke Ruma ba za ki canza halinki ba? Kin ga irin abun da nake faɗa miki ko, ba kya jin magana wannan tsalle-tsallen da kike yi ya yi yawa, yau ke ce kwaso wannan gobe ki ɗakko wancan, me ye amfanin shi? Ya kamata ki zauna ki ma kanki karatun ta-natsu ki riƙe mutuncinki, ke fa mace ce aure za ki yi wata rana……….”
An samu wuri da dama inda aka nuna tana zama domin yi mata faɗa a kan halayen ta amma ta ƙi.

KAMMALAWA

Kamar yadda muka ji ma’anar fina-finai daga bakin masana da kuma jigon fim da kuma tarihin ɗaya daga cikin masu bayar da umarni a harkar fim ɗin, sannan da yadda muka yi sharhi a wasu daga cikin fina-finan, wato Burin Fatima, da Izzatu, da Kawaye. Haka koma mun ga muhimmancin fina-finai da kuma yadda mai ba da umarnin yake kallon harkar fim ɗin.

MANAZARTA

Sadik, L.A (2021) “Karatun Jami’a A Fina Finan Hausa” :Nazari Daga Wasu Fina-Finan Hausa. Kundin Digiri Na Ɗaya Jami’ar Jahar Kaduna.
G.P Bargery, (2016) “A Hausa-English Dictionary And Englsh-Hausa Vocabulary” Jami’ar Ahmadu Bello University Press Limited.
Chamo I.Y (2016), Saƙo A Fina-Finan Hausa: Nazari Kan Jigo Da Rabe-Rabensa, Kundin Binciken Digirin Na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero Kano.
Gidan Dabino, A.A da Wani (2004) “Matsaloli Da Nasarorin Masu Shirya Fina-Finan Hausa Musamman Na Kano” A Cikin Adamu da Wasu (Editoci). Gidan Dabino Publishers, Kano.
Hira da Ali Gumzak Da Muka Yi A Ranar Laraba 27-10-2021, A Garin Kaduna.

Don Karanta Adana Harshe (LANGUAGE PRESERVATION) danna nan

Edita@rumasau-kallamu

 

 

 

labarin da ya wuceTarihin Farfesa Abdallah Uba Adamu