1.Mahaifinsa: Shi ne Abdullahi ɗan Hashim ɗan Abdulmanaf ɗan Ƙusayyun ɗan Kilab.
2.Mahaifiyarsa:- Ita ce Aminatu ‘yar wahabu ‘yar Abdulmanaf ‘yar Zuhra ‘yar Kilabu.
3.Mahaifiyarsa da Mahaifinsa;- Sun haɗu a kakansa na biyar (5), shi ne Kilabu.
4.Haƙiƙa Baffansa ya rasu, yana ɗan shekara goma sha Takwas (18), an rufe shi a garin Madinah, bai bar masa komai ba na daga dukiya.
Sharhi:
A lamba ta ɗaya (1), ya ce Mahaifinsa shi ne Abdullahi (shi ne wanda ake masa inkiya da Abu-alƙamata), shi ne wanda ya auri Aminatu ‘yar Wahab, Azzuhriyyatu Baƙuraishiya, sai Abdulmuɗalib, wanda ya auri Fatimatu ‘yar Amiru Almakazumiya (Abdulmuɗalib yana ɗaya daga cikin manyan mutane Ƙuraishawa, wanda Ƙuraishawa, suke haɗuwa akan ra’ayinsa, sannan suna gabatar da shi a wajen Mu’amalarsu).
Sai Hashimu shi ne wanda ake kira da Abu-Haris Za’im Baƙuraishe a lokacin Jahilya, sannan yana ɗaya daga cikin manya-manya labarawa. Ya kasance yana shayar da masu aikin Hajji ruwan Zam-zam. Sannan shi ne wanda ya auri Salma ‘yar Amru Alnajariyatul Khazrajyya.
Sai Abdulmanaf yana ɗaya daga cikin Kakannin Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam), an ce sunansa Mugira Abdulmanaf, laƙabinsa ne, shi ne wanda ya auri Aitika ‘yar Murra Assalamiyatu (ɗaya daga cikin ƙabilar Ƙaisun-ilani bin Madhar).
Sai Ƙusayyun (Shi ne shugaban Ƙuraishawa, sannan kuma shi ne wanda aka yake kula da ɗakin Harami) shi ne wanda ya auri Hubayyu ‘yar Hulilu Alku Za’iyatu (Alkhuza’atu Bin Iliyasu Bin Madhar) sai Kilabu (ana yi masa laƙabi da Kilab ne, saboda ya kasance yana yawaita yawan farauta da Kare.
Amma sunansa Hakimu ko Uwarta), Shi ne wanda ya auri Fatimatu yar Sa’adu, sai Murrata shi ne wanda ya auri Hindu ‘yar Sariru daga ƙabilar Banu Fahra Bin Malik (Shi ne Abu-Husaisu) Shi ne ya auri Mahaifiyar Ka’abu Mariyatu ‘yar Shaibana daga ƙabilar Fahra. Sai Lu’ayyi shi ne wanda ya Mahaifiyar Ka’abu Mariyatu ‘yar Ka’abu daga ƙabilar Kadha’ata.
Sai Ghalib shi ne ya auri mahaifiyar Lu’ayu Salma ‘yar Amaru Alkhuza’i l, sai Fahra (shi ne wanda ƙuraishawa suke yi masa laƙabi da Ahlul Ashira), shi ne wanda ya auri mahaifiyar Ghalib, Laila ‘yar Sa’adu daga Haulin. Sai Malik shi ne wanda ya auri Jundilatu ‘yar Haris daga ƙabilar Jurhum).
Sai Nadhir ya auri Atika ‘yar Adwana daga ƙabilar ƙaisun I’ilani, sai kinanatu shi ne wanda ya auri Burratu ‘yar Murra Addi, sai Mudrakata, amma sunansa Amru) shi ne ya auri Salma ‘yar Aslama daga Kabilar Kudha’atu, sai Nazar shi ne wanda ya auri Saudatu ‘yar Akka sai Ma’adu.
Danna nan don karanta jikokin annabi
Edita; Rumasa’u Muhammad kallamu