Azumin Watan Ramadan

1
42

SALMANU FARISS ADAMU

Azumin watan Ramadan, wajibi ne a kan kowane musulmi, kuma wanda yake baligi, sannan kuma mai hankali, saboda mara hankali zai iya aikata duk abin da ya ga dama kuma a lokacin da ya so, ba tare da yin la`akari da halaccin ko haramcin abin da yake aikatawa ba, saboda babu hankali a tare da shi a lokacin da yake aikata haka.

Haka kuma azumi yana zama ko tabbata ne, saboda cikar watan sha`aban (kwanaki ashirin da tara ko talatin) ko kuma saboda ganin jinjirin watan Ramadan da yamma, kafin ko bayan sallar magariba ta hanyar gani da ido ko samun labarin ganinsa (wata) a  wata jihar ko  garin ko unguwa, ta hanyar wasu mutane amintattu kuma masu halaye masu kyau haɗi da mu`amala mai kyau a tsakaninsu da mutane.

Saboda haka da zarar mutane sun ga wata ko sun samu labarin ganin wata daga wajen irin waɗancan mutane, to azumi ya zama wajibi a kan mutum sai ya yi ko ya ɗauka, haka kuma za a aikata ko lura a lokacin ajiye azumi, ta hanyar ganin sabon tsayuwar watan shauwal ko ta hanyar cikar watan Ramadan kwana lokacin talatin(30).

Bugu da ƙari kuma, ana iya ɗaukar niyyar azumin watan Ramadan ne, bayan ko a lokacin da mutum ya samu labarin ganin wata ko ya gani da idonsa kafin fitowar alfijir, saboda tabbatar tsayuwar watan Ramadan.

Sannan kuma idan mutum ya ɗauki abincisa zai ci, to kafin ya fara cin abincin, dole ne sai ya tabbatar ya wanke hannunsa ko cokalin da zai ci abinci da shi haɗi da bakinsa, sannan kuma sai ya ƙulla niyyar yin azumin watan Ramadan guda ashirin da tara ko takatin.

Misali, idan mutum ya ɗauki abincinsa ya ajiye a gabansa, kafin ya fara cin abincin, sai ya yi Bismillah,  sannan yace “Allahumma Inni nawaitus siyamu Ramadan tis`a wa ashiruna au salasuna” ko kuma mutum yace “Nawaitus siyamu Ramadan tis`a wa ashiruna au salasuna” .

Ma`ana ya Allah na yi niyyar yin azumin watan Ramadan guda ashirin da tara ko guda talatin.

Saboda haka idan mutum ba zai iya faɗar wancan kalma ba da larabci, to zai iya faɗar kalmar da harshen Hausa ko Fulatanci, Barbanci, Yarabanci ko harshen da yake iya magana da shi, hakan ya halatta, Misali “Na yi niyyar yin azumin watan Ramadan guda ashirin da tara ko guda talatin”,. amma kuma an fi so mutum ya faɗa da larabci.

Bugu ƙari kuma, idan mutum ya yi niyyar yin azumin watan Ramadan tun a daren da aka ga wata, ma`ana tun niyyar da ya yi na azumin sa na farko,to wannan ya isar masa a cikin dukkanin azuminsa na wannan watan, saboda babu wani sharaɗi a kan mai yin azumi na sake yin niyya a cikin kowane azumi ko rana, matuƙar azumin na sa a jere zai yi, amma kuma idan ba a jere zai yi su ba, saboda wata matsala, to dole ne a kansa  sai ya sake yin niyyar azumin a duk lokacin da zai yi(azumi).

Sannan kuma  yana daga cikin sunnah yin azumi gaggauta shan ruwa da jinkirta yin sahur, ma`ana da zarar mutum ya ji an kira sallar magariba, sai ya yi saurin shan ruwa (da dabino ko “yayan itatuwa ko ruwa) kafin mutum ya yi sallar magariba, saboda haka ne ma yake da matuƙar kyau ko ake buƙatar a samu kamar mintuna  huɗu ko biyar a tsakanin kiran sallah da yin sallah.

saboda mutane su samu damar aikata wancan sunnah ta azumi kafin suyi sallah, amma kuma ba dole ba ne sai mutum ya aikata haka, amma kuma aikata haka yana da matuƙar kyau sosai, soboda sunnah ce ta annabi Muhammmad (Sallallahu alaihi wasallam).

Sai kuma jinkirta yin sahur, ma`ana kada mutum ya tashi cikin dare ya yi sahur, ma`ana kamar misalin ƙarfe biyu na dare ko kafin a kira sallah na farko, amma kuma idan mutum ya aikata haka azuminsa ya yi, sai dai bai aikata sunnah ba.

Haka kuma mutum ya nisanci cin abinci ko abin sha a lokacin da alfijir yake fitowa ko a lokacin da ake kiran sallah na biyu, saboda ana buƙatar a samu kamar mintuna goma  ko mintuna goma sha biyar(15) a tsakanin kiran sallah da gama yin sahur, amma idan mutum ya sa abinci a cikin bakinsa, sai kuma ya ji ana kiran sallah na biyu ko asubah, to sai ya yi sauri ya fitar da abin da yake bakinsa, saannan kuma ya kuskure bakinsa sai ya ci gaba da yin azuminsa.

Danna nan don karanta Yaƙe-yaƙen Annabi SAW A Watan Ramadan

Edita:@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceChinese Rice
Labarin na GabaTambayoyin Azumi Da Amsoshi

SHARHI ƊAYA