Author: Dr Aisha health talk

  • Ciwon Ciki Da Ciwon Mara Lokacin Al’ada

    Ciwon Ciki Da Ciwon Mara Lokacin Al’ada

    Budurwa ko matar aure me fama da wannan matsalar kisamu wadannan magungunan

    • Garin hulba
    • Garin habbatussauda
    • Garin kiswatul hindi

    Saiki hadasu waje daya ki zuba ruwa da zuma aciki sannan ki dafasu idan ya dafu saiki ajiye wannan ruwan da safe ki debi karamin kofi kisha kafin kici komai anaso ki dafa wanda zai miki sati daya kafin ya kare kin huta da wannan matsalar insha allahu

     Bayani Dangane Da Haila 

    Ana haihuwar yara mata da wasu ƙwayaye biyu (ovaries) waɗanda ke ƙunshe da dubban ƙwayayen da ba su nuna ba,bayan yarinya ta balaga,a kowane wata tana sakin kwai daya da ya nuna,ana kiran wannan ‘saukar kwai’ (ovulation),kuma wannan na faruwa wajejen kwana goma sha hudu kamin soma al’ada. Idan ƙwan bai hadu da maniyyi ba sai ya mutu,a kowane wata mahaifa na shirya wa yiwuwar daukar ciki,kuma fata ta cikin mahaifa na zama da kauri da kuma taushi,idan jikin macce ya gane cewa ba maganar daukar ciki,sai fatar da ke cikin mahaifa,tare da kwan su zama haila su fice ta farji.

    Karanta cikekken bayani akan Fibroid (Karin Mahaifa)

    Ba za a iya ganin ƙwan ba saboda ya cika ƙanƙanta,ana fara kirga lokacin haila daga ranar da aka fara,zuwa jajibirin ranar da za a fara wata al’adar,zagayowar al’ada na canzawa,don zai iya kasancewa kwana ashirin da daya ko kuma ma zai iya kai wa ƙwana arba’in,idan macce na al’ada,tana iya amfani da tawalin al’ada ko kuma fad,ko audugar al’ada don ta tare jinin da ke zuba,kina iya yin amfani da littafin tsarin lokaci watau diary domin sanin lokacin da za ki fara al’ada,ba dukan mata ne ke yin al’ada a kan lokaci ba,kuma lokacin fara al’ada ya bambanta,wasu ‘yan matan na farawa tun da wuri (alal misali tun suna da shekara takwas),yayin da wasun ke dadewa basu fara ba,haka ma,tsawon lokacin da ake dauka ana hailar ya bambanta daga mace zuwa macce.

    Yawanci suna yin ƙwana biyar zuwa baƙwai,amma kuma wannan na iya sauyawa,don a wasu lokutan ba a kaiwa kwana biyar,da zarar yarinya ta fara al’ada, zai dau lokaci kamin jikin ta ya saba. a shekarar farko mai yiwuwa ta ketare wata daya ko fiye da haka bata ga haila ba,amma yau da gobe jikin nata zai saba.

    Domin karanta bayani akan Ƙurajan Pimples Danna nan

    Irin canjin da ake samu na yawan sinadarin (hormone) da jikin mace ke samarwa kamin lokacin yin al’ada,ko kuma a lokacin al’adar,mai yiwuwa ya shafi halin da macce zata nuna, ko kuma abinda zata ji a ran ta,mai yiwuwa ta ji karin kuzari,ko kuma ta ji tana sha’awar namiji,ko kuma ran ta ya baci,ta ji kamar ta yi kuka,ko kuma ta rika yawan fushi a lokacin saukar ƙwai ko kuma jim kadan kamin ta fara haila,mai yiwuwa nonuwan ta su rika ciwo ko su kara girma;kuma a wasu lokutan wasu kananan kuraje kan fito a fuska.,wasu matan sun dara saura jin bambam a jikinsu a lokacin da suke haila,kuma wannan na iya sauyawa a rayuwar mace,ta haka ne mata ke sakin ƙwayaye har zuwa lokacin da suka daina haila,a yawancin lokuta hakan na faruwa idan macce ta kai karshen shekaru arba’in zuwa hamsin,bayan wannan lokacin,ba zata kara yin al’ada ba,kuma ba zata dauki ciki ba,idan kina matukar jin ciwo a lokacin al’ada, ko kuwa kina da wata damuwa,sai ki nemi shawara daga likitan da ki ka yarda da shi,ko kuma ki tuntubi kungiyar tsara iyali.

     

  • Fibroid (Karin Mahaifa)

    Fibroid (Karin Mahaifa)

    Mai Ya Kamata Ku Sani Akan Fibroid: Cuta ce dake da alaka da mata,idan tsiro ke fitowa a mahaifa,wannan tsiro ka yi iya fitowa a 

    • Cinkin mahaifar
    • Tsakiyar naman mahaifa
    • Bangon wajen mahaifa

    Karanta cikekken bayani akan Zazzabin Typhoid

    Mene Ke Kawo Fibroid

    Babu takamaiman abinda ke kawo wannan ciwo,sai dai masu hatsarin kamuwa da shi sune:

    • Fara jinin al’ada da wuri.
    • Rashin aure da wuri.
    • Bakar fata (African)
    • Mace mai kiba.
    • Rashin haihuwa.
    • Idan dangin ki da masu shi.
    Mene Alamun Fibroid 
    • Ƙaruwar wayan jinin al’ada.
    • Matsanancin ciwon mara lokacin al’ada
    • Zuwan wani jinin kafin lokacin al’ada.
    • Karuwar kwanakin al’ada
    • Barin ciki(miscarriage)
    • Rashin haihuwa.
    • Girman ciki( da juna biyu ko babu)
    • Ciwon baya.
    • Zafin saduwar aure.
    • Cushewar ciki.
    • Yawan fitsari.

    Note: samun wasu daga cikin wannan alamu baya nufi  dole Fibroid ne,bincike ne kawai zai tabbatar da haka a asibiti.

    Domin karanta bayani akan Ƙurajan Pimples Danna nan

  • Zazzabin Typhoid

    Zazzabin Typhoid

    Wannan cuta ce da wasu rukunin kwayoyin halitta da ake kira salmonella typhi ke haddasata,salmonella typi ido baya iya ganinta.

    Ta Wacce Hanya Ake  Kamuwa Da Ita

    Wanda ya kamu da wannan cuta ya warke,kwayoyin cutar kan iya zama a jikin sa na gomannin shekaru ba tare da yana nuna alamun ta ba,amma sukan hayayyafa suna fita ta bayan-gari  da kuma fitsarin sa,don haka duk wani abinci ko na sha da ya baci da bayan gari ko fitsarin mai dauke da wannan cuta,idan aka ci ana iya kamuwa.

    Danna nan domin karanta cikekken bayani akan Peptic Ulcer Diseases

    Hanya Mafi Saukin Kamuwa Da Wannan Cuta Sune:
    • Ruwan sha mara tsafta
    • Abinci mara tsafta
    • Kayan marmarin da ba wanke ba,kamar karas,kabeji da sauran su.
    Alamomin Wannan Cuta
    • Zazzabi wanda zafinsa ka karuwa kullum.
    • Rashin kwarin jiki.
    • Ziffa
    • Ciwon kai (daga goshi) wani lokacin mai tsanani.
    • Tari
    • Cushewar ciki ko gudawa (mai launin Kore da yalo)
    • Kashin jini.
    • Yellon ido.

    Domin karanta Menene Amfanin Folic Acid Ga Mata Masu Juna Biyu Danna nan 

  • Peptic Ulcer Diseases

    Peptic Ulcer Diseases

    Ciwon olsa  ta zama daya daga cikin manyan cutuka da suke damun al’ummah a kasar mu ta Najeriya.

    Peptic Ulcer Disease: 

    (Gyembon Ciki) general name na na ulcer ciki gabaki daya,ita Peptic ulcer ( gyembon ciki ko ciwon ulcer ) 

    Ya Kasu Kashi Uku Kamar :
    • Gastric Ulcer (Gyenbo wadda take kama Fatar ciki ciki)
    • Duedenal Ulcer ( Gyenbo wanda take kama hanji)
    • Esophagus Ulcer  (Gyenbon maqogwaro)
    Ciwon Olsa tana zuwa da alamomi diyawa gasu kamar haka: 
    • Konawar zuciya
    • Ciwon Cikin
    • Rashin cin abinci
    • Tashin Zuciya 
    • Amai
    • Ciwo har a gadon baya
    • Kashi da jini  ko bakkin kashi
    • kumburin ciki
    • ciwon cikin
    • Daukewar numfashi.
    Me Yake Kawo Ciwon Olsa ?

    Kwayar cutar bakteriya mai suna H- pylori shi yake kawo ciwon Olsa,haka kuma yawan shan maganin dauke ciwo kamar su  aspirin,Shan taba (sigari) da kuma shan giya suna taimaka sosai wajen kawo ciwon olsa.

    Yana dakyau ka karanta Ciwon Yatsan Hannu Na Gaga Cikin Ciwukan Hannu Mafi Raɗaɗin Ciwo

    Ta Wacce Hanya Ake Daukan Ƙwayar Cutar Olsa 
    • Mutum yakan iya daukan wannan koyar cutar ta hanyar musyar yawu (saliva) ko lokocin kiss.
    • Mutum yakan iya daukan wannan kwayar bakteriyan  ta hanyar ruwan sha da kuma abinci.
    • Idan ruwan sha ko abinci ya gurbanta da bayan gida ko fitsarin mai ciwon,wanda hakan yana faruwa ne ta hanyoyi da yawa.
    Mesa Ita Ciwon Olsa Ba’a Warkewa Da Wuri 

    Ba ba’a warkewa bane,ana warkewa daga cutar olsa ko wacce iri amma abinda yake faruwa shine :

    • Rashin shan magani yadda yakamata,yau anwayi gari shan magani barkatai yazama ruwa dare a najeriya,mafi yawa kwayoyin cutar ansaba musu da wannan maganin har yazama suna jurewa .
    • Za kaga mutum ana bashi maganin wata daya ko sati biyu a ranan da yafara shan maganin idan yaji sauki shikenan ya rabu da maganin dai lokocin da alamomin cutar yasake zuwa zaici gaba da shan magani. 
    • Misali ace kwayar cutar ana samunshi daga gurbaceccen ruwa,to ana shan magani kuma ana cigaba da shanceccen ruwan kaga babu maganar warkewa .
    • Rashin bin ka’idojin likita yana gaba gaba wajen hana warkewan wannan ciwo na Olsa.
    • Shan magunguna barkatai ba tareda Izinin likita ba musamman magungunan olsa da sunan zai warkar maka da olsa,da kuma amfani da magunguna na gargajiya wanda ba’asan kanta ba.
    Shawara Ga Masu Ciwon Olsa:

    (1)   A kauracewa wadannan Abinci :

    • Abinci mai yaji
    • Abinci mai daci
    • Abinci mai sami
    • Abinci masu Gas
    • Abinci masu dauke da acid kakar tumaturi.

    (2)   A daina amfani da hayaki ko wacce iri ko tabar sigari,wiwi ko shisha sabida suna daga cikin abubuwan da suke haddasa olsa kuma suna sananta olsa.

    (3)   Adaina amfani magungunan dauke ciwo irinsu aspirin,ibuprofen,cataflam, naproxen, feldene, da sauransu.

    (4)   A rage shan giya domin yawan shan giya yana  daga  cikin abubuwan  da suke kawo olsa kuma suke sananta olsa.

    (5)   A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da ake da kwawato akai kafin amfani.

    (6)   A yawaita amfani da kayan lambu musamman cavage (kabeji) yana taimaka wajen dakile ciwon olsa.

    (7)    Sai Kuma zuwa ga likita domin Tabbatar da cutar da kuma bada magani.

    Domin karanta Alamomi Masu Hatsari Lokocin Juna Biyu Danna nan

  • Menene Amfanin Folic Acid Ga Mata Masu Juna Biyu?

    Menene Amfanin Folic Acid Ga Mata Masu Juna Biyu?

    Folic acid Nau’i ne na vitamin B9, kuma yana ɗaya daga cikin vitamin da aka narkar da shi a cikin ruwa (Water-Soluble Vitamins) wanda ake samu a cikin abinci da yawa, mafi mahimmanci daga cikinsu shi ne abinci mai ganye, kuma ana ƙera shi a matsayin ƙwaya.

    ƙwayar Folic acid ( Folic acid tablets) wasu ƙwayoyi ne ƙanana yellow mafi yawa yana zuwa da nauyi 5 (5mg).

    Ana amfani da ita wajen magance ƙarancin jajayen ƙwayoyin jini wanda rashin sinadaran iron ya kawo.

    Waɗanda Ke Da Buƙatar Amfani Da Folic Acid:
    •  Mata masu juna biyu
    •  Mata masu shayarwa.
    •  Masu ciwon cutar hanta.
    •  Masu ciwon sikila.
    Menene Hikimar Ba Wa Mata Masu Juna Biyu Folic Acid Ko Da Ba Su Da Matsalar Ƙarancin Jini?

    Folic acid yana ɗaya daga cikin muhimman sinadaran Vitamin da mata masu juna biyu suke buƙata, saboda amfaninta a jikin su.

    Ga Kaɗan Daga Cikin Amfanin Sinadaran Folic Acid A Jikin Mata masu Juna Biyu:

    Sati ukun farko na ɗan tayi a ciki , shi ne lokacin da wasu a ƙwayoyin halittarsa suke haɗuwa don Samar da ginshiƙi a kan yadda wasu sassa da kuma tsare-tsaren jikinsa za su kasance,  saboda haka wannan lokaci ne mafi haɗari a yadda gobensa za ta kasance ta yadda matsala a haɗuwar wasu ƙwayoyin halittar, za su sa ko da ya yi tsawon rai to zai rayu ne da matsala ta har ya mutu. To folic acid yana taimakawa wajen haɗuwar waɗannan halittun dai dai.

    Domin karanta Ciwan Farfadiya (Epilepsy/Seizure) Danna nan

    Birth defects: Binciken masana ya nuna sinadaran folic acid yana ba da kariya daga haihuwar yaro mai nakasa.

    Folic acid deficiency: Yana kare mata masu juna biyu daga samun ƙarancin sinadaran folic acid.

    Ƙarancin Sa Zai Iya Kawo Matsalar:
    •    Zubewar ciki
    •     Naƙuda kafin lokaci
    •     Mutuwar yaro a ciki
    •     Mutuwar uwa.

    Heart and blood vessel disease: Binciken masana ya nuna sinadaran folic acid suna taimaka wajen daidaita sinadaran homocysteine wanda hakan zai iya ba da kariya ga cututtakan zuciya.

    Cancer: Binciken masana ya nuna sinadaran folic acid yana iya rage hatsarin kamuwa da ciwon cancer.

    Depression: Binciken masana ya nuna sinadaran folic acid yakan iya taimaka wajen magance matsalar damuwa.

    Dementia: Haka nan akwai ƙishin-ƙishin na yana taimakawa wajen ba da kariya daga cutar ƙwaƙwalwa wanda yake saka mantuwa

    Wassu Daga Cikin Amfanin Ta:

    •  Yana gyara fata
    •  Yana gyara gashi
    •  Yana saka cin Abinci
    •  Yana kare matsalolin jijiyoyi.
    • Yana taimakawa kula da kyakkyawan ƙwaƙwalwar ajiya.

    Idan kin yi amfani da ƙwayar folic acid yana kawo miki waɗannan alamomi maza ki dakatar da ita sannan ki je ki ga likitanki.

    •    Ƙaiƙayin jiki
    •    Ƙurajen Jiki
    •    Canza launin fata
    •    Riƙewar numfashi

    Idan kina amfani da waɗannan magunguna kada ki ki sha folic acid sai kin shawarci likitan ki.

    Anticonvulsants: Magungunan jijjiga kaman su  fosphenytoin (Cerebyx), phenytoin (Dilantin, Phenytek), primidone (Mysoline).

    Barbiturates: Magungunan da suke aiki a jijoyoyi wanda suke kai sako ga ƙwaƙwalwa.

    Antimalarial: Magungunan cutar cizon sauro.

    Methotrexate (Trexall): Magungunan da ake amfani da shi domin magance matsalar cancer.

    Abinci Mai ɗauke Da Sinadaran Folic Acid A ciki :
    • Koren ganye da kayan lambu
    • Nama da Kifi
    • Wake
    • Hatsi
    • Dawa
    • Brown Shinkafa

    Domin karanta bayani akan Ƙurajan Pimples Danna nan

  • Nau’in Jinkiri Guda Uku Da Suke Sabbaba Mace-macen Mata Masu Naƙuda a Nigeria

    Nau’in Jinkiri Guda Uku Da Suke Sabbaba Mace-macen Mata Masu Naƙuda a Nigeria

    Ko kun san adadin mata nawa ke rasa rayukan su duk shekara yayin naƙuda a nigeria da kuma dalilan faruwar hakan?

    Jinkiri na farko:

    Da ake samu shine zaka ga mutane suna ƙoƙarin neman taimako a gida, kamar neman maganin gargajiya a yi ta bawa mai naƙudar,ko a ce a saurara mu gani,da sauransu,wanda hakan ba komai yake kawo ba face matsala ga mai naƙudan yayin haifar da ita da kuma ɗan dake cikinta,rashin neman taimakon likitoci a kan lokaci ko rashin kai mai naƙuda asibiti a kan lokaci,haye-shayen rubutu ko maganin gargajiya suna ƙara cikawa mai naƙuda mara da fitsari ne kawai,har yakai ga janyo mata yoyon fisari a wasu lokutan.

    Jinkiri na biyu shine: 

    Rashin samun abun hawa kamar mota ko adaidaita sahu ko wani abu na hawa a kan lokaci,ko rashin hanya mai kyau na ababen hawan ta yadda za su sami isa da mai naƙudan asibiti a kan lokaci,wannan ya fi faruwa ne ga mutane mazauna ƙauyuka da unguwannin dake fama da munin hanyar sufuri.

    Domin karanta bayani akan Kansar Bakin Mahaifa Danna nan

    Jinkiri na uku shine:

    Jinkiri wajen tunanin wani ingantaccen asibiti ne ya kamata a kai ta, wasu lokutan mace na samun damar tsallake jinkiri na farko da na biyun amma sai ta afkawa wani sashin jinkiri na uku sakamakon rashin ƙwararrun ma’aikata ko rashin isassun kayan aiki a asibitin. 

    Yan’uwa masu daraja ku sani,rashin kai mace mai juna biyu asibiti don duba lafiyar ta da abunda ke cikinta na janyo mata matsala babba da kuma jefa rayuwar ta cikin barazana.

    Domin karanta bayani akan Larurar  Gaggartowar Saurin  Balaga (Precocious Puberty) Danna nan

    Rashin mayar da hankali ko rashin gaggauta kai mata masu naƙuda asibiti a yayin da suke naƙuda zalunci ne dake sabbaba yawan mace-macen matan a nigeria,wannan mummunar ta’asar dai tafi faruwa ne Arewacin ƙasar nan, Jikirin, akwai buƙatar wayar da kan wadanda basu fahimta ba da kuma hukunci ga masu ganganci.

    Daga ƙarshe muna miƙa shawarar mu ga mata da su mayar da hankali wajen kulawa da  ziyartar asibiti a kan ƙa’idar da likita ya basu,sannan suke bada haɗin kai yayin da likita ke duba su. Su kuma Mazaje su zama masu tausayawa iyalansu a irin wannan yanayi da suke cikin mafi wahalar yanayi,suke gaggauta kai iyalansu asibiti lokacin naƙuda,suke tallafa musu gun ziyartar Asibiti lokacin da suka ɗauki ciki don duba lafiyar su da abunda ke cikin su,haka nan,muna riƙon hukumomi da masu hannu da shuni suke taimakawa ƙananan asibitocinmu domin hakan shine hanyar farko na inganta lafiya.

    Domin karanta Ciwon Yatsan Hannu Na Gaga Cikin Ciwukan Hannu Mafi Raɗaɗin Ciwo Danna nan

  • Ciwon Yatsan Hannu Na Gaga Cikin Ciwukan Hannu Mafi Raɗaɗin Ciwo

    Ciwon Yatsan Hannu Na Gaga Cikin Ciwukan Hannu Mafi Raɗaɗin Ciwo

    Ciwo ne sakamakon harbin ƙwayar cuta musamman bairos da bakteriya,harbin ƙwayar cutar na faruwa ne idan ƙwayar cutar ta samu kafar shiga yatsa bayan fatar yatsa ko farce sun samu rauni,miki,yanka,tsaga ko kurjewa.

    Alamun Ciwon Sun Haɗa Da:
    • Ciwo,zogi,raɗaɗi da ƙaiƙayi.
    • Kumburi,kumewa tare da bayyanar ja a fatar yatsan.
    • Ɗurar ruwa ko jan ruwa.
    • Fitar ruwa ko fitar ɗiwa.

    Da zarar an ji waɗannan alamu a garzaya domin ganin likita,sai dai wani abin lura shi ne bayan ciwon ya warke sai kuma gaɓoɓin yatsan su ƙale ko su ƙage ko kuma su riƙe,saboda haka,idan aka yi buris da yatsan sai ya nakasa.

    Da zarar ciwon yatsan ya warke likitan fisiyo zai taimaka wajen dawo da aikin gaɓoɓin yatsan domin kada ya nakasa,idan aka yi buris da yatsan har aka bari jijiyoyin tantanin yatsan suka gama riƙewa hakan na iya tilasta yin tiyata domin sakin jijiyoyin tantanin,domin kauce wa nakasar yatsa  bayan wannan ciwo,tuntuɓi likitan fisiyo da wuri.

    Domin karanta Alamomi Masu Hatsari Lokocin Juna Biyu Danna nan

  • Alamomi Masu Hatsari Lokocin Juna Biyu

    Alamomi Masu Hatsari Lokocin Juna Biyu

    • Zubar jini daga mara.
    •  Cizon harshe da yawan mika.
    •  Ciwon kai da rashin gani ko gani dishi dishi.
    •  Zazzabi da ciwon jiki.
    •  Ciwon ciki
    •  Karanci ko yawan numfashi.
    •  Yawan ciwo.
    • Kumburin kafa,yatsu,da kuma fuska.

    Idan mace taga alamomin tsorota (alamomi masu hatsari  to tayi gaggawar zuwa asibiti koda lokocin awun ta baiyi ba.

    Wadan Su Abubuwa Da Mai Juna Biyu Za Ta Kiyaye

    {1} Ya kamata mai juna biyu ta guji aikata duk wani abu da zai rika sanya mata gajiya,ana so mai juna biyu ta rika aikata aikin da ba zai bukaci karfi da yawa ba.

    {2} Ya kamata mai juna biyu ta rika hira da mutane domin cire mata gajiyar ƙwaƙwalwa, wanda gajiyar ƙwaƙwalwa na haifar da gajiyar jiki,yakan kuma sanya mai juna biyu ta rika jin kamar ba ta da lafiya (queasy ko nausea).

    {3} Ya kamata mai juna biyu ta rika hutawa,sannan ta rika motsa jiki a hankali.

    {4} A lokacin da ciki ya fara girma kamar daga wata biyar ko shida.,yakamata mai juna biyu ta guji:

    • Kusantar sinadarai masu cutarwa.
    • Daukar lokaci wajen aiki.
    • Dadewa a tsaye.
    • Daga abu mai nauyi.
    • Zama a wajen da ake yawaita hayaniya ko surutu mai karfi.
    • Zama a wurin da akwai injina masu kara.
    • Zama a muhallin da ke da sanyi da yawa,ya kamata mai juna biyu ta guji shan ruwa mai sanyi,ko yawaita zama a karkashin na’urar AC na tsawon lokaci.
    • Zama a muhallin da ke da tsananin zafi.

    Domin karanta Cewa Uwa Zata Iya Samun Juna Biyu Bayan Sati Shida Da Haihuwa Danna nan

  • Ko Kun San Cewa Uwa Za Ta Iya Samun Juna Biyu Bayan Sati Shida Da Haihuwa?

    Ko Kun San Cewa Uwa Za Ta Iya Samun Juna Biyu Bayan Sati Shida Da Haihuwa?

    Na san tambayar da zai zo muku shi ne ta yaya za ku kare kanku daga samun cikin da baku shirya ba bayan haihuwa.

    Ga Hanyar:

    Da zarar an haihu ma’urata ku yi amfani da hanyar shayar da nonon uwa zalla ba tare da an haɗa da abinci ko ruwa ba, sannna kuma ma’aurata su fara amfani da wata hanyar ba da tazarar haihuwa bayan shayar da nonon uwa zalla, zai ƙara taimakawa wajen tabbatar da ba da tazarar haihuwa cikin ƙoshin lafiya, a ƙalla idan mace ta haihu ana buƙatar tazarar shekara guda zuwa biyu kafin ɗaukar wani cikin.

    Ga kaɗan daga cikin amfanin tazarar haihuwa ga iyaye mata da yaransu:
    • Yana ƙarawa yaro/yara annashuwa, sakamakon kulawar da suke samu daga wajen iyayensu.
    • Yana sa yara su samu kulawa ta ɓangaren lafiyarsu da kuma samun ingantaccen ilmi.
    • Mace za ta samu isasshiyar dama wajen cigaba da rayuwarta, sannan ta taimaka wajen bunƙasa cigaban iyalinta.
    • Mace za ta samu isasshen lokacin kula da mijinta da kuma samun ƙarin danƙon soyayya.
    • Yana rage damuwa da kasala ga mata a gidajensu.
    • Za ta ba wa mace damar shayar da jaririnta na tsawon lokaci, inda yin hakan kan ba da kariya daga cututtuka da dama.
    • Tazarar haihuwa kan bai wa maigida damar kulawa da iyalansa yadda ya kamata.
    • Maigida yakan samu ƙarancin damuwa da kasala a rayuwarsa ta yau da gobe.
    • Haka nan zai samu isasshen lokacin zama da iyalinsa a gida da kuma ba su tarbiyyar da ta dace.
    • Zai ba wa maigida damar sauke nauyin da ke kansa na tarbiyya da sauran haƙƙoƙin da ke wuyansa na rayuwar ‘ya’yansa.

    Domin karanta Halayen Da ke Haddasa Lalacewar Ƙoda [Kinney Dx] Danna nan

  • Halayen Dake Haddasa Lalacewar Ƙoda [Kinney Dx]

    Halayen Dake Haddasa Lalacewar Ƙoda [Kinney Dx]

    Ƙoda abace mahimmiya kamar yadda nasha fada,infa ta sami matsala toh babu sauran labari,lokaci kankani cikin wata 3 kana iya zamowa tarihi,domin galibi tana da kokarin gyara kanta inta sami matsala,amma zarar matsalar takai ga bayyana to fa lokacin an makaro. ƙoda da kake gani tana kuka tai hawaye kamar yadda kake hawaye in andokeka kaji zafi itama.

    Don haka kai tsaye aikata wadannan ɗabi’un ga mutum ba abune mai kyau ba ga ƙodarsa,inkaji ko kinji wani abu da kunsan halinku ne to ku daina kurum.

    RIKON FITSARI

    Jinkiri wajen yin fitsari,akwai cutar da kai ace mutum duk sanda fitsari ya kamasa yanaji amma bazaije yayi ba,saidai yaita rikonsa yana takurewa,hakan ganganci ne babba,kusani duk sanda ƙoda ta tace fitsari ta turo shi zuwa ga mafitsara ba abunda da akeso irin afitar dashi domin inkana rikeshi to ahankali wani zai fara komawa ga ƙodar (reflux) wanda daga nan kuma matsala zata fara afkuwa kuma kwayoyin cuta su sami hanayar zuwa su baibayeta.

    Karanta amsar wannan tambayar anan Nakan Ji Tamkar Wani Abu Ya Tsayamun A Maƙoshi [Lump Sensation In Throat ]

    YAWAN TA’AMMALI DA GISHIRI

    Yawan shan gishiri akwai matsala ga ƙoda basai ga mai hawan jini ba,musamman a mutanen dake da irin dabi’ar nan ta karama abinci ko miya danyen gishiri saboda kurum su bai musu daidai ba,komai so suke sujisa zau a baka! in gishiri yai yawa ƙoda bata iya tsotse daga circulation baki daya,hakan ke nuna yai mata yawa kuma zai mata illa ta yadda bayan ya illata ta dole ta sakesa yaci gaba da yawo ajika wanda hakan matsala ne agareka.

    Matsala ne tunda zaisa pressure wato matsi cikin jijiyoyin jininka ta ƙaru abunda ake kira hypertension shiyasa hatta masu hawan jini abu na farko zakuji da ake fadamusu su kiyayi gishiri da dangoginsa irinsu maggi saboda ba jinin ba kadai hatta kodarsu don karta sami matsala,domin duk mai hawan jini ko ciwon suga shi akaran kansa yana cikin hatsarin ciwon k’oda akoda yaushe inbai kiyaye ba. 

    Domin karanta bayani akan Larurar  Gaggartowar Saurin  Balaga (Precocious Puberty) Danna nan

    Don haka a kiyaye tunma ba in mutum cikin mahaifansa uwa ko uba dama akwai mai hawan jini ko ciwon suga ba,saboda kaima kana iya wayar gari dashi akoda yaushe.

    Shan Magunguna Dake Tare Da Rashin Daukar Ciwon Da Mahimmanci

    Rashin daukar kananun cututtuka da mahimmanci wanda mutum ke ganin ko ba’a je ga likita ba xa’a warke kamar jin ciwon kuiɓin,zafin fitsari,ko fitar farin ruwa daga gaba,ko mura wacce daga karshe aka kaiga jin kaikayin makogoro duk mutum yai watsi dasu… har suci suci su bari. 

    Ko ya zamto mutum ya zama shine likitan kansa saidai yaita dannawa jikinsa magunguna antibiotics ko NSAIDS daka ba tare da shi kansa yasan menene taka maiman matsalarsa ba shidai shan magungunan kurum yake ba bisa kaida ko umarnin likita ba,musamman mata masu ciwon mara yayin haila,ko kaji wata har recommeding ma wata magani take akan aini magani kaza nake sha kema ki nema kisha… ko kuma mutum yaje yaga likitan ma amma yazo yana shan maganin ba yadda likita ya tsara ba….

    Wadannan halayen na cutar da ƙoda kwarai da gaske don haka duk mai irin wannan shima ya kwan da sanin yana mikawa ciwon koda katin gayyata duk randa akace an fara samun angwada jininka creatinine yai sama,ko angwada fitsarinka ansami proteins,glucose ko jini aciki to karkai mamaki kuma alamace ta ƙoda ba lafiya.

    (1) Sannan kananun jami’an lfy wani lokacin kuna taimakawa wannan barnar mutum baisan pharmacotherapeutic dynamic da kinetic effect na magani ba kurum symptoms din da yake kawarwa ya sani amma sai yaita rubutawa marasa lfy batare da binkitar ko da taya ciwo ko matsala ta faro ba,hakan na ƙara cutar da mara lafiyar batare da saninsa ba 

    Kananun jami’an lafiya  bisa aiki da lura da amana in baka da training ko kwarewa akan bada magani toh kabar aikin ga masu shi ko ka tura mutum ga babban asibiti yafi,domin akwai wanda already kodarsu ta fara failing zasu zo amma abunda tazo korafi akai kila shine ciwon mara… kai kuma ka dau maganin rukunin masu rage zogi ko zafi ka bata wato irin ibuprofen,feldin,diclofenac ko aspirin ka bata… ta tafi taje tasha taji sauki,amma azahiri wadannan magungunan da take cigaba da amfani dasu kara lalata mata koda suke amma saboda ciwon koda bai bayyna lokaci guda sanda ciwo zai zo ya kwantar da mutum sannan an makaro.

    Wani zaizo yace ma ciwon hannu ne ko kafa kai tsaye ka bashi maganin ciwon jiki amma ainishin matsalar ba anan take ba,referred pain ne,matsalar ciwon zuciya ce ke alarming a hannunsa amma baka sani ba,wano kirjin ne zai zo yana ciwo…. ka zaci ulcersa ce ainishi shima kila already heart attack yake fuskanta sai ya tafi kwana daya biyu ace ya mutu arika ciwon ulcer yai.

    (2) Wani kuma zaizo ciwon daga tsakiyar cibiya yake… zaice ma ciwon ciki ne kurum,kila kai ko tambayar daga daidai inda ciwon yake ma bakai ba,shidai yace ciwon ciki,sai kuma amai ko tashin zuciya kai kuma ka dau maganin ciwon ciki ko ulcer ka bashi babu binkice ya tafi yaje gida ya kwanta karshe ya mutu….. alhalin appendicitis ne yake damunsa sakaci da rashin sani aikinka yasa appendicitis din yai distention yakai ga fashewa infection ya watsu acikinsa yabi jini kafin aje ko ina ya mutu.

    Wani ciwon kafa ne zaizo da ita amma azahiri ciwon sugar ne dashi wanda shi kansa bai sani ba,ciwon kafar already complications na diabetes kaga ko ka bashi magani yaita dawowa kenan domin maganin ciwon kafa kake bashi bawai maganin matsalar ba,wani kuma zai fadama yana da ciwon suga amma kila tunda ba abune da aka koyar dakai ba bakasan kome game da abunda sugar zata iyayi ba don haka zakace bari zan baka magani, ka gabza masa nsaids ya tafi karshe ashe babu ma blood supply kafin a farga wani sashi ya fashe kafar ta fara rubewa ta ciki tana bushewa ta waje karshe sanda za akai ga manyan likitoci saide ai zancen yanketa.

    Don haka likitanci yana da fadi,a wannan gaɓar kananun ma’akatan lafiya dole sai kun lura, ya dace gwamnati tai tsari da za ake karamuku sani,domin musamman a yankunan karkara gaskiya kymune kukafi kusa da mutane saidai gashi kuna missing din medical cases da yawa wanda wasu mace macen ana iya kauce musu.

    Kada kuke sake wajen tura mutum ga manyan likitoci in abu yafi karfin fahimtarku,sannan kada ko yaushe kake kankanta ciwo matsayinka na karamin jami’in lafiya ba haka abun yake ba,inakyi sau 1 aka dawo toh na biyu kurum fadamusu abun ya wuce tunaninka amma ga shawara suje asibiti iri kaza da kaza suga babban likita kurum.

    YAWAN CIN  JAN NAMA

    Yawan cin nama fiye da kima kullum kullum,ko akai-akai ba birgewa bane indai don ka damu da lafiyarka ne,masu wannan dabi’ar su sani cewa ba burgewa bane ace kunmai da cin nama kullum kullum ko kuwa kwana 1 ko 2 kurum kake daga kafa musamman naman shanu,raguna kai har na kajin ma,hasali ma ƙila baka ko baki da kokarin motsa jiki,mutum inya samu abu sai yaji yaci-yaci yai hani’an toh hakan ba abune mai kyau ba mutum ya kiyayi kansa.

    ƘWAURON CIN ABINCI

    Rashin cin wadataccen abinci matsala ne,haka kurum bawai babu ba,amma mutum ya rika ma kansa kwauro da gangan Saboda tsurfa ko kuwa tunanin kar yai kiba, bazai saki jiki yaci abinci ba ko kuwa yaci yadda ya dace har sai ya fara ganin jiri to masu irin wannan suma su kuka da kansu kodarku na iya lalacewa akoda yaushe,ina nan da rubutu kan masu wannan halayyar takin cin abinci wai don tsoron karsui kiba.

    KIN SHAN ISASHSHEN RUWA

    Rashin shan ruwa wadatacce yadda ya kamata babbar matsala ce ga jiki,lamba 1 ma kuwa. ya zamto mutum yana jin kishi sai yasha kadan ko kuwa ma mutum ya gama cin abinci amma yaki shan ruwan kwata-kwata haka kurum don wani dalili na kansa na shirme da cutar kai. 

    Masu irin wannan hali su kuka da kansu shi ruwa anso kake shan sa basai in kana jin kishi bama,kuma irin wadannan ne insukaje kashi da zaka matsa kusa da bandakin saika rantse mace ce ke nakuda,nishi hadda wayyo,ko mutum ya rika ciccije baki yana yunkuri,kai wani lokacin sai sun sa hannu sun kamo kashin sun jawo da kansu galibi saboda they are constipated.. akan me irin wannan shirmen. 

    Don haka kake shan ruwa kuma.da kaji toilet ko fitsari to babu jira maza ka tafi kayi,sai kaji kayi tsugunonka cikin sauki,amma daga lokacin da kake jin kashi ka matse kaki zuwa kayi toh inkaje yi agaba dole kasha wuya.

    A karkashin wannan rashin shan ruwan ga kuma karin wasu alamomin da zaka gane lallai baka shan ruwan isashshen ruwa:

    Alamomi 5 Dake Nuna Baka shan Isashshen Ruwa

    RAGUWAR FITSARI

    Lafiyayyen mutum akalla kanyi fitsari sau 6 zuwa 7 arana (akalla yawan da yakai kofi 3 zuwa 8 kenan) arana,don haka daga lokacin da kaga ko kikaga kin koma fitsari sau 1 zuwa 3 arana wannan alamace dake nuna ba’a shan isashshen ruwa kuma kodar mutum na cikin mawuyacin hali.

    BUSHEWAR FATA

    Karancin ruwa ne kan gaba cikin abinda kan jawo bushewar fata aga har furfuri take,mutum zaiga komi man da zai shafa jimawa kadan zaiga ta daďa bushewa,ko kuma yaga inya jawota ya tale irin yadda likitoci ke dubawan nan… zata dau fiye dai sekonds 10 bata gama komawa daidai ba… don haka sai akula. 

    CIWON KAI

    Rashin shan isashshen ruwa na jawo ciwon kai,irin ciwon kan da akan jisa haka kurum batare da zazzabi ko jin tempreture jiki tai zafi ba, kuma babu wasu sauran alamu kawai suddenly akaji ciwon yazo kai yahau harbawa toh karancin ruwa na janyo hakan… musamman in mutum ya zamo busy so stressful hakan bai rasa nasaba da karancin ruwa ajika. 

    BUSHEWAR BAKI

    Bayan bushewar fata a wasu lokutan akanji miyau ya dauke abaki gaba daya,ko bakin mutum har yaji ya rika ďaci ko jin kamar wani lump ya tsaya masa awuya wannan ma na daga alamun rashin isashshen ruwa ajika. 

    CANZAWAR LAUNIN FITSARI

    Wato inma dai kana iya yin akalla mai yawan da yakai kofi 3 zuwa 5 ayini toh amma sai ya zamto kalarsa ta canza kamar yadda zan bayani akasa toh hakan na nuna jikinka ya raina ruwan da kake sha don haka ba yawan fitsarinka ne ma’auninka ba… A’ah da kalarsa za kake tantance kanka,saboda wasu suna da kibar da suna buƙatar shan ruwa sosai… wasu kuma metabolism dinsu ne mai zafi.

    Fitsarin lafiyaye mai isashshen ruwa ajika ya kamata ya zamo clear wato kaga fitsarinka kamar kalar ruwan da kasha ko kuwa ya zamto launin ya canza kadan zuwa amber color amma ba sosai ba. 

    Kamar yadda hoton kasa ya nuna launi hawa-hawa har uku “3” na yadda fitsarin mai shan isahshen ruwa (Hydrated), mai karancin ruwa (Dehydrated) da kuma mai tsananin karancin ruwa (extremely dehydrated) suke. 

    Kasani kamar yadda in andakkeka kaji zafi kake kuka haka fa kodarka ke kuka inka ƙi shan ruwa ko inta shiga mawuyacin hali,tana yin duk yadda zatai ta kwaceka amma in abun ya zamo halinka kullum-kullum tohfa karfinta na tafiya daga lokacin ta rasa lafiya kuma da wuya likitoci su iya cetoka sai anyi da gaske umba sa’a ba tafiyarka tazo. 

    Domin karanta bayani akan Sanƙaran Nono Wato {Breast Cancer} Danna nan 

    Domin kamar yadda nace koda tana lalacewa to ko inafa ajikinka sai ya lalace… bar ganin amfanin zuciya… in koda ta lalace tafita hatsari,domin zuciya zata iya dan aiki na wasu ƙwanaki kafin ta tsaya cak… koda kuwa kai tsaye zata kasa tace komi daga nan gubace “uremia” zata fara zagayawa cikin jininka tunda koda ta gaza taceta tana shiga ƙwaƙwalwa shikenan ka gama yawo kwanaki kadan inba ai komi ba mutuwa zakai kuma saika rika abubuwa tamkar mai taɓin hankali kafin ma ka mutu abunda muke cewa uremic encephalopathy… mutum yai hankali da kanshi. 

    Yanzu jikkunan mu bafa irin na iyaye da kakannin mu bane,bamu da inganci irin nasu dam, saboda su sunyi ciye-ciye daidai da jikinsu irinsu (kwadon rama zogale,dinkin,dawa-da kulli, burabusko,kunun tsamiya,tubani, atural fura da nono,zuma mai inganci,nama mai inganci, suna tafiyar kasa me nisan gaske,man kadanya,man zaitun da sauransu) shiyasa suka zauna lafiya.

    Amma mu yau in ma munce zamuci irin nasun toh sai mun kashe abun yadda bazai wani aiki ajikin mu ba sannan mutane ke ci wai su wannan shine daďin (kaga zogale duk an gabza masa yajin magi da mangyada,da tarin tarkace na banza taya zaka sami amfanin zogale da akace? haka ma dan wake za’a gabza masa hade-hade da duk amfanin nasa da za’a samu angama lalatashi shiyasa da mutum ya gama ci sai kashi da gudu zuwa ban daki.

    Ciye ciyen mu duk tarkacen banza yafi yawa kadan ne masu cin abunda zai fishesu,su pizza,chocolates,wainar fulawa, hinkafa ma sai antoyeta ko an mata dahuwar da baza asami wani fa’ida ba saide mutum yaci glucose kurum,taliya sai an lalatata,su indomie din nan, toyayyen kwai wani yamai dashi kullum.

    Kuma kunsan wani abu wani nashan kayan maiko rukunin protein amma zakaga yana shan tea,kaga anyi ba aiba,domin sinadarin dake jikin lipton bazai bari ka amfanu da protein din ba,shiyasa karshe saide ka tara kitse,in namiji kaga yana tumbi,mace kuma kaga tana aje duwawu duk su dauka lafiya ce bayan jikin ku ne ke muku warning cewa abubuwa basa tafiya daidai ku dau matakin gyara kafin jijiyoyin jininku su fara dodewa ku shadu da mugun hawan jini da atherosclerosis da zai shutdown din kodarku.

    Domin karanta bayani akan Sanƙaran Bakin Mahaifa (Cervical cancer) Danna nan

    Shifa jikin dan adam yanason service da kulawa kafin ya zauna da lafiya kamar yadda mota in ana mata juye tafi lafiya,don haka jiki ma na buƙatar hutu,wanka,sanya tsaftataccen tufafi, ruwa da kuma abinci mai kyau ba mai tsada ba.

    • A daure ake shan isashshen ruwa musamman lokacin da aka fitar da zufa sosai ko lokacin zafi,haka har lokacin sanyi koda kuwa ba’a jin kishi saboda jiki nason haka, kuma adaure da asuba in antashi ake fara shan ruwa a emptyn stomach kafin cin komi akalla kofi 2.
    • Sai wani abu mahimmi dana sha fada; musamman wajen motsa jiki,mata aikin gida ba motsa jiki bane musamman ga mata,akoyi yin tafiyar ƙasa wacce zuwa da dawowa batafi minti 30 zuwa 40 kar ace kullum saidai a hau abun hawa,arika motsa jiki,a kuma ke cin abinci mai tsafta,a daina yiwa girki ko vegetable hade-hade
    • Cin ingantaccen abinci mai kyau bame tsada ko hade-hade ba,jikinmu mu bakar fata bafa daya bane dana turawa,karku rudu da cimar wasu ku saki taku baza kuga da kyau ba,suma turawan yanzu babbar masifar dake damunsu bakamar cutar teɓa wato obesity,akalla duk mutum 2 cikin 3 nauyinsu ya wuce ƙima
    • Muma yanzu haka akwai tarin overweight kuma inbakuyi hankali ba toh duk hakace zata faru daku,ba zakakewa cikinka zube-zube ba kace kuma kanaso ka zauna lafiya kamar yadda kaso… 
    • A tarihin likitanci bamu taɓa ganin wani mai kiba ko overweight da ya rayu kusa da shekara 100 ba aduniya,don haka idan kanason rayuwa mai tsayi cikin inganci to kayi cima me kyau.
    • Ake cin fruits da vegetables,da koyar canza abinci,yana da kyau karka maida cikin ka koda yaushe abinci iri guda kake zuba masa wato kaita cin abinci maisa kuzari kullum ko mai gina jiki kurum  jiki bayason haka shiyasa masu yawan cin abinci maisa kuzari batare da aikin komi ba kanyi fama da teɓa ajika domin abunda kakeci baka iya aiki ko matsa jikin da zaka konesa.
    • Abinci maisa kuzari shi ake kira (carbohydrates) wato inkana cin wadannan abincin; Masara,tuwo, dankali, shinkafa, doya, macaroni, spaghetti, roogo, garin kwaki, wainar fulawa,cin-cin da duk wani abincin flour ko hatsi,abu daya fa kaketa ci kullum domin duk carbohydrate ne sunane kurum ya bambanta amma a ciki duk abu daya zai zamo, wato glucose ya baka kuzari akarshe wanda baka iya konewa ba ya zamo kitse a turosa kasan fatarka aga kafara kumbura kana kiba,don haka ake gaurayawa da vitamins na fruits,vegetables,protein su kifi,wake,awara,dafaffen kwai da sauransu jefi jefi duk sanda aka sami iko basai kullum ba.
    • Ake fita fitsari akan kari da zarar anji alamunsa.
    • Da anji ko anga alamun cuttukan sanyi wato kaikayin gaba,ko fitar farin ruwa agaba ga mace ko namiji anemi magani,haka ciwon makogoro bayan mura.
    • Yawan ciwon baya ta kuɓin ciki daga kasa sama da ƙugu kadan ko sama zuwa kafada
    • Canzawar dandano abaki zuwa kalar kanwa ko kamar ansa karfen da yai tsatsa ko lamba abaki
    • Canzawar fitsari zuwa duhu kuma aga yana fita kadan-kadan in anje yi
    • Yawan jinin jiri da kasa sukuni
    • Yawan kasala
    • Ganin kuraje ajika wanda da anshafa magani zasu ɓace amma su kuma dawowa.

    To a hanzarta zuwa aga likita domin wadannan na daga alamun ciwon koda,fata anji za kuma akiyaye umba haka ba,toh gadajen mu dai na asibiti ko yaushe suna maraba da mutum,kazo ka kwanta in abunda ka tara ya ƙare a neman lafiya daga nan likitoci suka kasa cetoka kaga sai ka wuce lahira ka huta.

    Domin karanta Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Daukar Ciki Danna nan