3 RUBUCE-RUBUCE
Ya rubuta littattafai da maƙalu sama da 100 da aka wallafa a cikin gida Nijeriya da ƙasashen waje. Ya gabatar da kimanin maƙalu 20 a tarukan ƙara wa juna sani. Edita ne na mujallu daban-daban a ƙasashen da suka haɗa da Nijeriya da Amurka da Indiya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Shi ne ya assasa babbar kafar intenet ta Hausar nan wato Amsoshi (www.amsoshi.com). A yanzu yana koyarwa a Sashen Harsuna da Al’adu da ke Jami’ar Tarayya Gusau. A duba: www.abu-ubaida.com.