1) Kai kanka a matsayinka na marubuci za ka ƙaru da ilimin da ba ka sani ba.
2) Gamsar da mai karatu ta hanyar bayar da hujja a ilimance, ba wai kawai ra’ayi ko iya fahimta ba.
3) Za ka koyi kallon al’amura ta fuskoki daban-daban.
4)Duk lokacin da wani ya karanta littafinka, zai ji kamar labarin ba ƙirƙirarre ba ne. Tun da ka kawo wasu abubuwa na gaske.
5) Littafin zai zama kamar reference book.
6) Ba a cika saurin manta labari mai ɗauke da bincike ba.
HANYOYIN TATTARA BAYANAI
Babu wata tartibiyar hanya guda ɗaya da za ace dole sai ta nan ake tattara bayanai. Ya danganta daga marubuci zuwa marubuci. Kuma ya danganta da saƙon da labarin ya ƙunsa.
Wani labarin ya fi wani zurfin bincike.
1) TSARA YADDA ZA KA YI BINCIKE
Ya bambanta daga mutum zuwa mutum.
Misali wanda ya karanci ɓangaren lafiya, idan zai yi rubutu kan abinda ya shafi lafiya; ba zai ɓata dogon lokaci wajen yin bincike ba, kan wanda ba wannan fannin ya karanta ba.
Abin nufi wanda yake expert a fage ya bambanta da yadda ba expert ba zai gudanar da nasa binciken. Wanda ba a fagen yake ba dole sai ya yi bincike mai zurfi.
2) ABIN DA KA SANI
Za ka fara rubuta abinda ka sani game da matsalar da ka ke so ka yi rubutu akai kafin ka nemi shawarar kowa. Misali littafin Rai da motsi na Maryam Muhammad Sani. Ta yi dogon bayani kan cutar ‘Down syndrome.’ Ta san yanayin ciwon sosai tun da tana da alaƙa mai ƙarfi da mai cutar.
Kamar yadda Hauwa Shehu ta yi bayani kan Cyber Crime a littafinta na Harin Gajimare, tun da har certificate ta yi kan Cyber security. Zama za ka yi ka fara rubuta abinda kai ka sani ko da ɗan kaɗan ne kan abinda ka ke so ka yi bincike akai.
Ko kina son yin rubutu kan yadda wayar hannu ke jawo matsala tsakanin ma’aurata. Sai ki fara tuna duk wani labari da ki ka taɓa ji kan yadda waya ta taɓa jawo matsala. Idan ke ma abin ya taɓa shafar ki kaitsaye, to kin ga kina da experience. A matsayinki na marubuciya experience na da matuƙar muhimmanci kan abinda ki ke son yin rubutu akai.
3) TAMBAYA
Ka ɗauki takarda ka jera tambayoyi kan abinda ka ke so ka yi bincike akai. Misali ina so na yi rubutu kan matsalar mantau ta ‘amnesia.’ Duk da cewa na sha karantawa a novels kuma na sha ganin yadda lalurar ta ke a films, amma ina buƙatar na rubuta tambayoyi kamar haka;
Mece ce amnesia? Me ke jawo ta? Ya rabe rabenta yake? Ta wacce hanya matsalar ke sauya halin mutum? Ta wacce hanya ake bi a warke? Shin me matsalar zai iya tunawa da abinda ya aikata lokacin da yake cikin matsalar? Ya bayanin matsalar take a likitance?
Ina kyautata zaton Sanah Matazu ta yi irin waɗannan tambayoyin kafin ta rubuta littafin Fitsarin fako. Jera waɗannan tambayoyin za su taimaka ƙwarai wajen saƙa zaren labarin yadda ya kamata.
4) INTERNET
Sheik Google zai iya zama malaminka na farko da za ka fara tuntuɓa. Sai dai ka da ka dogara da sakamako guda ɗaya kawai. Kana buƙatar bibiyar shafukan da aka yarda da su ta fuskar bincike na ilimi. Za ka sami bayanai da dama da za su ƙara maka ideas kan abinda ka ke nema.
5) HOTUNA
Akwai hotunan da za su taimaka maka wajen rubutu. Akwai hoto mai magana wanda ganinsa kaɗai zai iya ƙara maka idea a matsayinka na marubuci. Ruƙayya Ibrahim ta fara samun idea rubuta littafin Wata duniya ta hanyar kallon wani hoto da ke jikin foodflask ɗin wani yaro. Ta ga hoton ɗan sama jannati. Daga haka ta fara saƙa zaren labarin.
Idan kana googling kan wani abu, to ka ke kula da hotuna. Wani hoton zai taimake ka fiye da yadda ba ka zato.
6) MASANA
Internet ba kodayaushe zai wadatar da kai ba. Kana buƙatar tattaunawa da masana.
Kana buƙatar ka yi tambaya a ba ka amsa. Kana buƙatar a ba ka labari a zahiri idan ta kama a nuna maka misali. Lokacin da Maimuna Beli za ta rubuta littafin Gwanin na iya, har gidan yari ta je ta yi bincike.
Lokacin da Bala Anas zai rubuta littafi mai suna Zinaru. Labari ne kan ‘yan Kano to Jidda. Sai da ya tattauna da ‘yan Kano to Jidda da dama baya ga waya da ya yi da wasu da ke zaune a can. Sai dai akwai abinda ya dace mu kula da shi.
Duk lokacin da za ka tattauna da expert a wani fage, to kada ka je ba tare da ka tsara tambayoyi ba. Kuma ka yi ƙoƙari ka san wani abu a fagen. Hakan zai sa masanin ya yi maka bayani. Kwanan nan wata marubuciya ta ba ni labarin ta haɗu da wata masaniya a wani fage. Amma sai ta rasa tambayar da za ta yi mata, saboda ba ta tsara tambayoyi ba.
Idan kika kuskura kika ƙara irin wannan shirmen sai na ambaci sunanki.
Don karanta babban kundi danna nan
7) ZAMA CIKIN SHIRI
Ba ka san takamaimai lokacin da idea za ta faɗo maka ba a matsayinka na marubuci. Wataƙila kana cikin wanka abin zai zo maka, kamar yadda ya taɓa faruwa da wani masanin Physics Archimedes yana banɗaki yana wanka wata idea ta faɗo masa wacce ya daɗe yana nema. Tsirara ya fito daga banɗaki ya fita waje yana tsalle cike da murna. Sanadiyyar haka aka samu ‘Law of floatations’
Haka marubuciyar Ƙaddarar rayuwa, Wato Bilkisu Garkuwa; jin Muryar mata daga wajen wani mai adaidaita sahu ya ƙara mata idear da ta yi rubutun da ya zo na ɗaya a gasar Gusau ta shekarar 2022.
Ana buƙatar marubuci kodayaushe ya zama cikin shirin yin jotting ɗin idea.
Wani sa’in wani ɓangare na labari zai iya faɗowa ƙwaƙwalwarka a wani irin yanayi. Idan ba ka rubuta ba sai ka manta.
8) KARATU
Akwai falsafar da ke cewa kamar yadda idan mutum ya sha ruwa mai yawa, to zai yi fitsari da yawa. Haka ma karatu da rubutu. Idan mutum yana yin karatu da yawa, to abu ne mai wahala ya rasa abin rubutawa. Ko da ka rasa yadda za ka yi a wani waje, sannu a hankali idea za ta faɗo maka wacce za ta taimaka maka wajen ɗaure zaren labarinka yadda ya kamata.
Akwai mamaki samun marubuci amma kuma wanda ba ya yin karatu. Na taɓa saurarar hira da wani marubuci Robert Greene, duk da dai shi ba Novel yake rubutawa ba, amma yace kafin ya rubuta littafi ɗaya, a ƙalla yana karanta littafi 250 zuwa 300. Ke littafi nawa ki ke karantawa kafin ki rubuta guda ɗaya?
9) MUƘALA
Karanta journals za su taimaka maka sosai musamman idan labarinka ya shafi wani fanni na daban (profession). Lokacin da zan rubuta littafin Ciwon rai, sai da na karanta journals kan abnormal psychology na samu bayani sosai kan cutar Alzheimer disease. Wannan ya taimaka min sosai wajen ƙulla zaren labarin ta yadda na iya bayyana alamun ciwon sosai kan Nuraini mijin Falmata.
10) SAURARO
Wani sa’in kana buƙatar sauraron wasu bayanan ta audio don ƙara fahimtar abinda kake bincike. A binciken da Ruƙayya Ibrahim ta yi wajen rubuta Wata duniya, ta saurari wata lakca da Abou Uthymin ya yi kan astronomy. Wannan ya taimaka mata wajen saƙa zaren labarinta wanda ya zo a mataki na biyu na gasar Gusau a shekarar 2023.
11) TAFIYA
Idan da hali ana buƙatar marubuci ya ziyarci wuraren da ya yi bayaninsu a cikin littafinsa. Sydney Sheldon yace duk wani waje ko da wajen cin abinci ne da ya kwatanta a littafinsa sai da ya je wajen. Ta sanadiyyar haka sai da ya je ƙasashe fiye da 100.
Lokacin da Bala Anas zai rubuta littafin Sara da sassaƙa. Kasancewar labarin ya faru ne a ƙasar South Africa. Sai da ya nemi map ɗin ƙasar. Duk wani tudu da kwari da sunan ƙoramu da daji na gaske ya yi amfani da shi.
Haka lokacin da zai rubuta littafin Zinaru, sai da ya yi waya aka kwatanta masa tun daga airport har zuwa tituna da kantina duk sunayen na gaske ne. Hakan ne ya sa wasu da suka karanta littafin a can, suka yi tsammanin cewa ya taɓa zuwa Saudiyya alhali bai taɓa zuwa ba.
11) TSAYAR DA RANA
Tun daga lokacin da za ka fara bincike har zuwa lokacin da za ka kammala, ana so ka sa rana. Don marubuta da yawa sun sha kasa ƙarasa aikin bincike saboda rashin sa ranar dakatawa.
“Ban kammala binciken ba…” Da haka idan ba a yi wasa ba sai mutum ya shiririce.
12) FARA RUBUTU
Da zarar ka kammala haɗa bayanai, abu na gaba shi ne; ka fara rubuta abinda ake cewa first draft. Ba lallai a rubutun farko za ka shigar da komai ba, sai a second draft, wani ma sai a third draft.
Danna nan domin karanta hanyoyin bincike a rubutu
Edita; Rumasa’u M’ Kallamu
[…] Danna nan don karanta amfanin bincike a rubutu […]