Abubuwan Dake Rage Ƙaunar Miji Gurin Matarsa

0
56
KAI ƘARA

Ba a son miji a kan abu kaɗan, ya zama mai yawan kai ƙarar matarsa ga iyayenta. Wannan na jawo ƙiyayya. Domin galibi ma’auratan za su manta da rigimar, su ci gaba da rayuwarsu. Amma iyaye ba za su manta ba.

FAƊA A GABAN JAMA’A

Ya kamata miji ya dinga haƙuri kada ya dinga faɗa da matarsa a gaban mutane. Domin hakan na ba wa wasu mutanen dama su yi zuga a tsakanin ma’aurata. Sai ka ji ana cewa, “Daman haka yake yi miki? Kai! Amma kina da haƙuri”. Wani kuma a gaban yaransa zai ta yi wa matarsa faɗa. Ka ga duk wannan na iya haifar ma da ƙiyayya.

Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan

RASHIN KAMUN KAI

Wani namijin a duk inda ya haɗu da mata sai ya yi caraf ya sa mu su baki a hirarsu. Su ma matan marasa kamun kai, sai su ci gaba da hirar da shi. Alhali babu wani uzuri, don ba su taɓa sanin juna ba, ƙila ma haɗuwa ce ta zaman motar haya. Ko kuma waɗanda suke zama a bakin hanyoyi su yi ta ƙura wa mata idanu. Idan miji ya zamo irin waɗannan, to hakan zai ja masa ƙiyayya a wajen matarsa.

Ya kamata ka zamo kamili, mai kau da ido. Saboda Annabi (SAW) ya gargaɗi maza a kan zaman bakin hanyoyi.bSai dai idan sun kasance za su bai wa hanya haƙƙinta. Da sahabbai suka tambaye shi mene ne haƙƙin hanya? Sai ya ce, “Rintse idanu, juyo da sallama da umarni da kyakkyawn aiki da hani da mummuna”. Bukhari da Muslim duk sun rawaito wannan Hadisin.

Domin karanta Abubuwa Da Ya Kamata Mace Ta Kiyaye Lokacin Al’ada Danna nan 

Bari ma dai in tuna mana da ƙissar Annabi Musa Alaihissalam. Bayan da ya taimaka wa ƴan matan nan da suka fito da dabbobinsu kiwo. Ya buɗe musu rijiya suka shayar da dabbobinsu. Da matan nan suka je gida suka faɗawa babansu karamci da ƙarfi irin na Annabi Musa Alaihissalam. Sai babansu ya ce, “Su kira shi”. Ƴa saka masa. Da ta je ta kira shi, ta wuce gaba, suna tafiya sai iska ta ɗan ɗaga kayanta, sai ya ce, “Ta dawo baya”. Shi kuma ya wuce gaba, ya ce, “Ta dinga faɗa masa inda zai yi”. Ka ga wannan hali ne mai kyau.

Wasu abubuwan da mata ba sa so, sun haɗa da mita da girman-kai da sauran su.

Domin Dauko Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceYadda Ake Yi Wa Maigida A Lokacin Fushi
Labarin na GabaAbubuwan Dake Sa Wa Miji Ya Zamo Mafi Soyuwa A Wajen Matarsa