A siyasa, a ko’ina a faɗin duniya ana amfani da harshen ‘biyayya, jagoranci gami da magajin mulki’. Shugabanni da dama su kan ce suna “gina shugabannin gobe”, ko “naɗa magaji”, ko kuma “tallafawa amintattun mabiyansu na siyasa”, amma a ƙarƙashin wannan zance akwai lamari mai tsauri.
Siyasar ubangida (godfatherism) tsari ne da ikon siyasa ke zarcewa ta hannun mutane masu ƙarfin iko bayan cikar wa’adinsu, ba lallai ta hanyar hukumomi ko dokoki ba.
A nahiyoyi daban-daban, wannan tsari yana bin salo iri ɗaya: uban-gida ya ɗora yaronsa na siyasa, yaron nasa ya samu iko, sannan daga baya rikici ya raba kawunansu.
Wannan maƙala tana nazarin bayanai ne na duniya da na Najeriya game da silar rikicin siyasar ubangida da kuma dalilin da yasa Siyasar ubangida ke ci gaba da aukuwa, da dalilan da yasa take karyewa, da Kuma yadda take ƙarewa a mafi yawan lokuta.
Don haka za mu fara yin nazarin ta waɗannan sigogi:
1. a. Siyasar Uban-Gida a Matsayin Fasahar Siyasa ta Duniya
Siyasar ubangida ba ta keɓanta ga Afirka ko Najeriya kaɗai ba. Ita wata fasahar siyasa ce ta duniya, musamman a wuraren da:
- Hukumomi suke da rauni, samun adalci yake da tsada.
- Jam’iyyun siyasa suke mallakar ɗumbin magoya baya,
- Kuma samun iko yake da mafi tsadar farashi.
A Latin Amurka, ana kiran Siyasar Ubangida da suna ‘caciquismo’, ma’anarta shugabannin yankuna masu sarrafa ƙuri’u da makomar mutane. A wasu sassan yankunan Asiya, musamman Philippines, Siyasar Ubangida na bayyana a matsayin siyasar gado, inda wani ahali kan mamaye muƙaman da ake zaɓe a kansu na tsawon ƙarni.
A Amurka, a farkon ƙarni na 20, ƙusoshin siyasa kamar su Tammany Hall a New York suna aiki ne ta hannun shugabanni da suke “ƙirƙirar” gwamnoni da magajin gari.
Duk da bambancin wurare, binciken siyasa da kamanceceniyarsa ya nuna abu guda:
“A duk inda zaɓen ’yan takara ya dogara da masu hannu da shuni fiye da masu zaɓe ko hukumomi, siyasar ubangida tana bunƙasa”.
b. Nazari: Bayanin ƙididdiga na duniya
Binciken ƙasashe da dama ya nuna cewa a wasu ƙasashe masu dimokiraɗiyya mai raunin tsarin jam’iyya, kashi 60–75% na muƙaman majalisa ko kujerun zartarwa suna hannun mutanen da ke da alaƙa da manyan ahali ko wasu iyayen gida. Wannan haɗuwar iko ke sa rikicin ubangida da yaron gida ya zama babbar matsala mai girgiza tsarin siyasa baki ɗaya.
2. Me Yasa Ubangida Ke Ƙirƙirar Yaron-Gida (Kuma Me Yasa Yaron gida ke Kware Masa Baya?)
Ubangida ba ya ɗora yaron-gida saboda tsananin biyayya, ko tausayi ko kyautatawa kawai. Ilimi ta nuna hakan wani tsari ne na dabarar siyasa: Saboda dalilai kamar haka;-
1. Kare iko – Mai mulki na son yaga ya cigaba da tasiri ko da bayan wa’adinsa ya ƙare.
2. Tsaron tattalin arziki – kare kasuwanci, kwangiloli, da hanyoyin samun kuɗin shiga.
3. Garkuwar siyasa – kariya daga bincike, cin zarafi ko samun babbar daraja a tsarin siyasa.
4. Gina tarihi – mayar da iko na mutum zuwa “ɗariƙar siyasa” ko daular siyasa Wanda tarihin zai rinka tunawa dasu.
Amma yaron gida yana gadon muƙami ne, ba ƙarƙashin biyayya kaɗai ba. Don haka da zarar ya hau mulki, matsin lamba za ta bayyana, biyayyar da ya jima Yana yi wa Ubangidansa na iya sauyawa Saboda dalilai kamar haka:
1. Ikon kundin tsarin mulki da zai rinƙa yi wa biyayya,
2. Haƙƙin jama’a da ya rataya a wuyansa na zuwa da muradai mabanbanta
3. Hamayya daga manyan masu ruwa da tsaki na kusa da na nesa,
4. Bujirowar burika na wannan mai mulki.
Daga nan ne tsarin ke fara tsagewa..
3. Yanayin Najeriya: Dalilin da Yasa Siyasar Ubangida Ta Fi Zafi a tsarin siyasar Najeriya ba ya rasa nasaba da dalilai guda huɗu:
1. Tsarin “wanda ya yi nasara ya ɗauke komai” watau samun iko a Nigeria yana nufin samun iko da dukkan albarkatu.
2. Raunin dimokiraɗiyyar jam’iyya – ’yan takara sunfi fitowa ta hanyar sulhu ko masalaha (nune), ba zaɓen gaskiya ba.
3. Tsadar kamfen – Tun daga zaɓen cikin Gida, kudi sunfi tasiri wajen samun kuriun daliget Sama da nagartar ɗan takara. Haka Nan uwa uba babban zaɓe, masu dangwala kuriun sun fi zaɓar Dan takarar daya basu ihsani. Don haka ’yan kaɗan ne za su iya tsayawa takara har suyi nasara ba tare da masu kuɗi sun tallafesu ba.
4. Ƙarfafa mutum fiye da karfafa doka – rigar mulki a Nigeria tafi ƙarfafa mutum fiye da bin dokokin ƙasa.
Binciken zaɓukan Najeriya tun 1999 ya nuna cewa yawancin gwamnoni da suka yi nasara sun samu goyon bayan manyan ubangida ko ƙungiyoyi masu ƙarfi. Amma a lokaci guda, da dama daga cikin waɗannan alaƙa sun rushe bayan samun nasara.
4. Yadda Siyasar Ubangida ta kasance a wasu Jihohin Najeriya
i. Jihar Rivers: Daga Gado zuwa Yaƙi
Rikicin da ya ɓarke tsakanin tsohon Gwamnan Nyesom Wike da Gwamnan mai ci Siminalayi Fubara a Jihar Rivers shi ne mafi tsanani a wannan zamanin. Tsarin gadon mulki mai kyau ya koma:
- Toshe ayyukan majalisa,
- shari’o’i a kotuna,
- tsaikon kasafin kuɗi,
- sa hannun gwamnatin tarayya.
Abinda hakan ya haifar: lalacewar hukumomi na dogon lokaci, sulhu na ɗan lokaci, da rabuwar bangarorin siyasa abinda za a iya cewa har abada.. sai dai wasu na ganin kwatankwacin haka Nweson Wike ya yi ga waɗanda suka raine shi a siyasa.
ii. Jihar Kaduna: Uban-Gida ga Gwamna
A Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya tallafa wa Uba Sani wajen zamowar sa Gwamna. Bayan da ya hau mulki, sai gwamnan ya nemi ’yancin kansa, abin da ya haifar da:
- zarge-zargen jama’a,
- binciken majalisa ga Gwamna El-rufai
- yaƙin cacar baka musamman a kafafen yaɗa labarai.
- Abubuwan da hakan suka haifar: rabuwar manyan ’yan siyasa da ɓata suna daga ɓangarorin biyu.
iii. Jihar Kwara:
Daular Saraki — ƙarƙashin Olusola Saraki, daga baya Bukola Saraki — ta nuna wani tsari na daban.
Uba (Sola) ya Dora ɗansa (Bukola), bayan cikar wa’adinsa ya yunkura maye gurbinsa da Kanwar Bukola.. Amma sai Bukola ya bijerewa mahaifinsa tare da ɗora Abdulfatah Ahmed..
iv. Jihar Kano: Tafarkin Siyasa da Sarrafa Iko
A Jihar Kano , Jagoran darikar Kwankwasiyya Engr Rabiu Musa Kwankwaso ya gina gagarumar ɗarikar siyasa. Amma gwamnan farko (Abdullahi Umar Ganduje) daya gajeshi ya raba gari dashi, sannan a yanzu haka Gwamna na biyu (Abba Kabir Yusuf) da ya ɗora shi ma ya raba sheƙarsa ta siyasa da jagoransa Rabiu Kwankwason
v. A takaice, an samu irin wannan salo a yawa-yawan jihohin ƙasar Nan misalin Zamfara, Borno, Yobe, Kogi da makamantansu
5. Ƙididdigar Sakamako: Abin da Bayanai Ke Nunawa
daga siyasar jihohin Najeriya (1999–2025).
Taƙaitaccen bincike ya nuna:
1. ≈Kashi 70% na alaƙar ubangida da yaron-gida tana rushewa daga ƙarshe.
Daga cikin waɗanda suka rushe:
kaso~40% sun ƙare da sauya jam’iyya ko sake tsayuwa da ƙafafunsu.
kaso ~25% sun kai ga rikicin shari’a na tsawon lokaci,
kashi ~20% sun haifar da rugujewa ko tuge injin siyasar ubangida a zaɓe,
ƙasa da kashi <15% ne kawai suka kai ga tsananin biyaya da sulhu mai ɗorewa misalin abinda ake gani ga Gwamna Ododo da Yahaya Bello a Kogi.
A Siyasar duniya ma, waɗannan kaso suna kama da juna a ƙasashen da siyasar Ubangida ta yi ƙarfi.
6. Me Yasa Rabuwa Kusan Dole Ce a Siyasar Ubangida?
A kusan dukkan lamurra, abubuwa biyar ke haifar da rabuwa:
1. Saɓanin ra’ayi wajen iko da albarkatu; misalin kasafin muƙamai, kwangiloli da sauransu.
2. Tsoron dusashewar tauraro – a mafi akasari, Ubangida ba ya son a manta dashi ko a daina tuntuɓarsa akan kamurori.. don haka idan ya hango haka zata faru, yana iya yunkurin sauya shugabancun daya ɗora.
3. Sauyin halaccin mabiya – yarongida yana iya samun iko daga ɗumbin jama’ar da yake shugabanta, hakan na iya bashi damar auna ƙwanjinsa da Ubangidansa.
4. Fargabar magajin gaba – bayan kammala waadin mulkin yaron gida, shin wake da halascin sake ɗora magaji? tayaya hakan zai amintar da babban ubangida ko yarongida?.
5. Tasirin mulkin mai mulki wajen sarrafa kansa da muradan zuciyarsa
A taƙaice: siyasar ubangida tana haifar da cibiyoyin iko biyu a ofishi guda sai dai ita siyasa sam ba ta lamuntar iko biyu.
7. Yadda Siyasar Uban-Gida Ke Ƙarewa Galibi
Shaidu daga Najeriya da duniya suna da nuni da cewa mafi yawan Siyasar ubangida :
* Ba ta ƙarewa cikin nutsuwa.
* Tana raunana shugabanci.
* Tana rarraba jam’iyyun siyasa.
* Wani lokaci tana ƙarfafa jama’a idan suka haɗu (kamar Kwara).
Abin mamaki, tsarin da aka ƙera don rage rashin tabbas shi ne ke haifar da rashin kwanciyar hankali na dindindin.
8. Hasashe na Ƙarshe: Rikicin Siyasar Biyayyar Ubangida
Siyasar uban-gida tana cigaba ne saboda tana magance matsalolin gajeren lokaci kamarsu cin zaɓe, tara kuɗi, kauce wa hukumomin bincike da sauransu. Amma tana karyewa bayan dogon lokaci saboda ta saɓa da ma’anar mukamin dimokiraɗiyya.
> Da zarar yaron-gida ya zama gwamna, to fa Allah ɗaya ne kurum, babu mai iya tabbatar da ƙarshen lamarin. Har sai jam’iyyun siyasa, kuɗin kamfen, da hukumomi sun maye gurbin ubangida a matsayin hanyar samun iko, sannan zagayen zai ci gaba: amma abinda alƙaluma suka nuna, a duk siyasar ubangida huɗu, ɗaya ce kawai ake wanyewa lafiya, sauran ukun kuwa duk da ɓacin rai ake ƙarewa saboda saɓanin fahimta da bijirowar sabbin buƙatu masu sauya lamurori.
Sadiq Tukur Gwarzo GGA.
Karanta Falalar Malamai Da Ta’aziyyar Masani Shehu Ahmad Bamba (Ƙala Haddasana)
Edita@rumasau-kallamu









