Tarihin Sarkin Musulmi Muhammad Bello

0
11

Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ɗa ne ga Shehu Usmanu bn Fodiyo, kuma yana daga cikin fitattun almajiransa, waziransa, sannan daga ƙarshe magajinsa. Mutum ne mai tarin ilimi, jarumta, hazaƙa da fasaha, kuma marubuci ne mai zurfin tunani. Tarihi ya tabbatar da cewa jarumtar Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ta bayyana ƙwarai, domin shi ne ya jagoranci yaƙin da aka kwace birnin Alƙalawa, cibiyar Daular Gobir.

Ya shiga har cikin fadar sarki, ya fatattaki jama’ar Sarki Yunfa, kuma a wannan yaƙi ne aka kashe sarkin. Haka kuma, ya halarci yaƙe-yaƙen jihadin Shehu Usmanu bn Fodiyo sama da arba’in, yana daga cikin ginshiƙan da suka ɗora jihadin bisa ƙafafunsa.

An haife Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo tun kafin fara kiran Shehu Usmanu bn Fodiyo. Tare da shi aka fara kiran, tare da shi aka yi hijira, tare da shi aka aiwatar da jihadi, sannan daga ƙarshe shi ne ya kafa birnin Sakkwato, inda ya gina wa Shehu gida da masallaci wanda daga baya ya zama cibiyar Daular Musulunci ta Sakkwato.

Wannan ya nuna irin rawar da ya taka tun daga matakin farko har zuwa kafuwar daula. Muhammadu Ballo ɗa ne ga Shehu Usmanu bn Fodiye, mahaifiyarsa kuma ita ce Hauwa’u. An haife shi a ranar Laraba, cikin watan Zilƙa’ada na shekarar 1195 hijira, a Gidan Shehu na Ɗagel.

Wannan na nufin an haife shi shekaru bakwai bayan fara kiran Shehu, wanda ya fara ne a shekarar 1188 hijira. Sunansa Muhammad, yayin da laƙabinsa Ballo, kalma ce ta Bafilatani wadda ke nufin mataimaki, kamar yadda Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana a tsokacinsa kan littafin Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur.

Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya taso cikin kyakkyawar tarbiyya a hannun mahaifinsa, Shehu Usmanu bn Fodiye, wanda shi ne malaminsa na farko. A hannunsa ya fara karatun Alƙur’ani da sauran ilimomin wajibi. Daga baya ya koma hannun baffansa Abdullahi bn Fodiye, ƙanin Shehu kuma almajirinsa, wanda ya zurfafa masa ilimin harshen Larabci tun daga ilimin harshe, nahawu, sarfu, balaga da sauran rassa na ilimi.

Haka kuma, ya yi karatu a hannun Shehi Muhammadu Nur az-Zaman, inda ya koyi fassarar Alƙur’ani, ilimin Usuluddin, ilimin Haƙiƙa da sauran manyan ilimomi. Ya ci gaba da neman ilimi ba tare da kasala ba har ya zama babban malami mai cikakken basira. An rawaito cewa ya karanta littattafai sama da dubu ashirin da ɗari uku, ko ma fiye da haka, abin da ke nuna zurfin neman iliminsa da himmarsa.

Bayan rasuwar Shehu Usmanu bn Fodiyo, Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya zama halifa a daren da Shehu ya rasu. Musulmi suka yi masa mubaya’a a gidan Malam Shafa, inda ɗan’uwansa Muhammadu Sambo ya fara yi masa mubaya’a. Da zamowarsa halifa, jihadi bai tsaya ba, sai dai ya ci gaba da ƙarfi da tsari.

A watan Rajab na shekarar farko da halifancinsa, wasu daga cikin jama’ar Zamfara suka yi ridda, abin da ya sa Sarkin Musulmi ya jagoranci runduna zuwa Burmi, inda aka yi yaƙi mai tsanani har aka samu nasara. Haka kuma, a watan Zulƙa’ada, Malam Abdussalam ya kauce ya haɗa kai da kafirai, sai Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya fuskance su da yaƙi, har ya ci Kware a ƙarshen watan Safar.

Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya yi yaƙe-yaƙe da Kadaye, Gunki Ganƙa, Kalambaina da Dakarawa. Haka nan ya doke rundunar haɗaka ta Sarkin Gobir Ali tare da Auzinawa na Azbin da Abaru ya jagoranta, inda ya fatattake su har suka tsere. Ya kuma yi yaƙi da rundunar haɗaka ta Zamfara da Bauchi, da wata runduna da ta tattara mayaƙa daga Katsina, Gobir, Azbin da Maraɗi.

Dukkan waɗannan yaƙe-yaƙe sun ƙare da nasara. An ƙiyasta cewa Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya gudanar da yaƙe-yaƙe sama da arba’in da bakwai, abin da ya tabbatar da jajircewarsa wajen kare daular Musulunci da ya gada.

A ƙarshe, Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo ya rasu a gidansa da ke Wurno, gidan da yake amfani da shi wajen keɓewa domin ibada da kusanci ga Allah, wato ribaɗ. Ya rasu a ranar Alhamis da yamma, cikin shekarar 1253 hijira. Kalmominsa na ƙarshe su ne: La ilaha illa Allah, Muhammadu Rasulullah.

An yi jana’izarsa bisa Sunna, sannan aka binne shi a wannan gida kamar yadda ya yi wasiyya. Tarihi ya bar shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan Daular Sakkwato, malami, jarumi, shugaba kuma abin koyi ga al’umma.

Danna nan don karanta Tarihin Kafuwar Ƙasar Kuwait

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Ciwon Kunne Yake
Labarin na GabaWaƙa Mai Taken Kowa Ya Bar Gida…