Duk yanda take cikin damuwa da zarar Mustapha yana waje to sai ta shiga walwalarta da yara, yayin da shi kuma duk wasu shirye-shiryensa na tarbar amarya ne. Har ta kai ba ya iya ɓoye murnarsa; shi da yara kullum hirarsu ta Anti Naja ce. Musamman Afaf wadda zuwa yanzu kusan gaisuwa ce kawai take haɗa ta da Khadeeja.
Lafiya suka tare a sabon gida kuma kamar yanda ta zaɓi ɗakin sama haka ya haƙura ya ba ta ɗakin saman; duk da daga baya ya yi nadamar hakan. Domin da a ce ya san ta riga ta san da maganar aurensa to da tabbas zai gaya mata amarya zai saka a sama. Sai dai a lokacin tunaninsa ba ta san da maganar auren ba kuma ɓoye mata yake son ya cigaba da yi.
Tsaf ta gyara ɗakinta da parlor, ɗakin su Afaf kuwa tunda ta ga ra’ayoyinta suna cin karo na da Afaf kuma tana nema ta yi mata rashin kunya sai ta haƙura. Sosai ɗakinta ya yi kyau, ta tsara musu komai nasu ita da Hammad, don Baffanta ma da Mommy sai da suka ƙara mata kuɗi ta yi sayayya.
Sati yana zagayowa kuma aka shiga hidimar bikinsa. Babu yanda ba ta yi da Mustapha ba a kan ita ba ta so a yi mata taro amma ya ƙi amincewa; domin yace Hajia tace dangi ba su san sabon gida ba don haka za su zo su karɓi amarya sannan su ga gida.
Tun dare ta sanar da shi cewa idan gari ya waye za ta bi ‘yan makaranta ta je gida wajen Mommy, kuma ba tare da wani musu ba ya amsa. Bayan ya kai ‘yan makaranta ya dawo suka zauna tare a parlor ɗin sama suna cin abinci yayin da Hammad yake hannun Rashida. Shiru suke cin abincin babu wanda yake magana, kamar ma dai ba sa cikin walwala.
Ya ajiye cokalin da ke hannunsa yace ‘Kin ce babu wani abu da kuke buƙata saboda taryar baƙi ko? Ba tare da ta daina cin abincinta ba tace ‘Eh. Ni kam ma ai don dai ka hana ne da sai na yi tafiyata wajen Mommy idan aka kawo ta aka tafi sai na dawo da daddare ko ma da safe.’
‘No, don Allah ki bar wannan maganar. Ai ya kamata dai a ce a samu a karɓi baƙin nan cikin mutunci. ‘Um. Suka cigaba da cin abincinsu, jimawa kaɗan yace ‘Hajia ma tace a nan za su zo su yi biki ranar Lahadin, in ya so sai su tsaya su karɓi amarya sannan su tafi.’
Ta kalle shi suka haɗa ido sannan ta kawar da kanta, wani malolo ya zo ya tokare mata maƙogoro; su Hajia za su yi biki a nan? Saboda suna murna za a yi mata kishiya ko me?Ta ɗauki kofin shayinta mai zafi ta kurɓa da fatan zafin shayin zai tafiyar mata da abinda ya tokare mata maƙogoro amma hakan bai samu ba.
Ta kalle shi a jigace tace ‘Ka ga shikenan sai na tafi gidan Mommy ko? Tunda ka ga masu karɓar amarya za su zo.’Ya ɗan zaro ido yana cewa ‘Haba dai! Hakan kuma ai bai yi tsari ba, kina matar gida kuma a zo biki gidan ba kya nan. Ko ba haka ba ma kin san Hajia za ta ga kamar kin raina ta ne shi yasa za ki tafi ki bar su su kaɗai su yi bikin. Please ki yi haƙuri kawai saboda kada abun ya zama wata fitina kuma. Kin ji?’
Ta ɗaga kai tana cewa ‘Uh. Yauwa, please ki yi haƙuri a gama taron nan ba tare da wata matsala ba. Ta yi gajeran murmushi tace ‘In sha Allah. Ya ture kwanon bayan ya kurɓe ɗan ragowar shayinsa sannan yace ‘Zan saka miki kuɗi a account ɗinki saboda na san za ki iya buƙatar wani abun ko don baƙi.
Akwai ruwa da lemo wanda zan kawo, abincin kuma dama tunda kika ce ba za ki yi a nan ba na bayar da kuɗin don haka su Hajia za su taho da shi. ‘Ok. ‘Idan kuma da buƙata za ki iya yin wani abincin a nan ko da kaɗan ne. ‘Ok, babu damuwa. Ya miƙe ya shige ɗakin domin ya ƙarasa shiryawa.
Nan take ita ma ta ture kwanon indomie ɗin ta miƙe ta haye sama. Kuka take son ta yi ko za ta ji sanyi a ranta, amma ba ta so ta ɓata lokaci musamman da yake yana jiranta kuma tare za su fita. Haka ta yi sauri ta shirya suka sauko tare, ta karɓi Hammad a wajen Anti Binta suka fice suka bar Anti Binta da Hafsu wadda ƙanwar Rashida ce aka kawo mata bayan an yi auren Rashidan tun kafin ta haifi Hammad.
Haka suka zauna a mota babu wanda yake magana da ɗan uwansa; ya riga ya kula da yanda take nema ta tayar masa da fitina a wajen bikin nan amma ba zai bar ta ba. Sosai ya ji daɗi da Hajia tace za su zo nan su yi biki don ba ya so ta bayar da matsala idan an kawo amarya, amma ya san tunda Hajia tana nan babu wata matsala da za ta ba su. Haka ya je ya ajiye ta a gidansu sannan ya wuce.
Tana shiga gidan ta sami Ahmad a parlor yana shan shayi; nan da nan ya miƙe ya karɓi Hammad daga hannunta. ‘Ina Mommy?’ ta tambaya bayan ta amsa gaisuwar da yake mata. ‘Tana ɗakin Baffa. Ba tare da ta ba shi amsa ba ta bar masa Hammad ta wuce ta nufi ɗakin.
A zaune ta hango Mommy a kan dadduma ta miƙe ƙafa da waya a hannunta, ta jefar da mayafinta ta ƙarasa gaba daya ta faɗa jikin Mommy ta rushe da kuka. ‘Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un! Khadeeja me ya faru? Ina Hammad ɗin?’ Mommy ta tambaya cikin tashin hankali.Da ƙyar ta buɗe baki tace ‘Yana hannun Ahmad.’
Ita kanta sai da ta ji ajiyar zuciyar da Mommy ɗin ta yi, sanna ta cigaba ‘To me ya faru kike wannan kukan haka? Ko Mustaphan sakinki ya yi ne? Ta jijjiga kai alamar a a ba tare da ta ɗago ba, ta cigaba da kukanta. Kawai sai Mommy ta haƙura da tambayar ta zuba mata ido, a hankali ta ɗaga hannunta tana shafa kanta; ta dai san da maganar saura kwana uku a ɗaurawa Mustapha aure don haka wataƙila wani abun ya yi mata wanda ya sosa mata rai shi ne ta taho nan tazo tana wannan kukan.
Sai da ta ɗauki loakci tana wannan kukan sannan ta ɗan numfasa ta ɗago ta kalli Mommy, suna haɗa ido kuma sai ta sake fashewa da kuka. Cikin sheshekar kuka tace ‘Mommy ba zan iya ba, ba zan iya ba Mommy. Ta ɗago fuskarta tana share mata hawayen tace ‘Menene ba za ki iya ba Khadeeja?’
Ta tsagaita da kukan sai dai hawayenta ya kasa daina fita; ta sa bayan hannunta ta goge hawayen ta kalli Mommy suka haɗa ido na ɗan lokaci. Ta kawar da kanta tace ‘Mommy ban san me Mustapha yake so da ni ba. Bayan ya gama raina min hankali lokacin da yana neman aure yanzu kuma duk da ban ba shi matsala ba amma ba zai bar ni na zauna lafiya ba.
Ta share mata hawaye tana cewa ‘Me ya yi miki kuma? Mommy nace masa ina so ranar da za a kawo amarya na taho nan idan sun gama kai ta sai na koma ya hana ni, na haƙura nace zan zauna amma ba zan yi taro ba; su kawo amaryarsu kawai su tafi. Da farko har ya yarda amma yau yake gaya min wai babarsa tace za ta zo a nan gidan namu za ta yi biki, kuma yace ba zan tafi na bar su ba.
Mommy so suke baƙin ciki ya kashe ni? Ɗansu zai yi min kishiya kuma su zo suna celabrating a gaba na? Da mamaki Mommy tace ‘Ikon Allah, ita mahaifiyar tasa ce za ta yi biki saboda zai ƙara aure? Ta sa hannu ta goge ragowar hawayen da yake kan fuskarta sannan tace ‘Eh Mommy, wai za su zo suyi biki. Kin ga kenan na ce ba zan karɓi amarya ba amma za su yi min dole.’
Mommy ta kama hannunta ta kalle ta sannan tace ‘Ki yi haƙuri kin ji, za ki iya. Kishiya ba ta kashe kowa ba in sha Allahu ke ma ba za ta kashe ki ba. Ki bi su a hankali, dare ɗaya ne a yi ya wuce. Da an kwana biyu ita ma za ta zama kamar ke kuma yanda ya yi miki haka zai yi mata.
Ta jijjiga kai tana murmushi mai ɗauke da ma’anoni tana cewa ‘Hmm! Mommy ba zai taɓa yi mana adalci ba. Kina ganin yanda tun kafin ta shigo shi da yaransa da ‘yanuwansa suka karkata wajenta. Gaskiya ban saka rai Mustapha zai iya yi min adalci ni da matarsa ba, sai dai kawai nace Allah ya ba ni haƙuri ko kuma ya kawo min mafita mafi alkhairi.’
‘Kada ki damu, ai ba shi ya yi kansa ba, in sha Allahu Allah ba zai bari ya cutar da ke ba daga shi har ‘yanuwan nasa gaba ɗaya.’‘Hmmm!’ ta sunkuyar da kai tana kallon yatsunta da take wasa da su. Jimawa kaɗan tace ‘Mommy ba na son a yi min biki a gida, bana son a kawo min amaryarsa a ce za a ba ni amanarta ko a yi mana faɗa tare. Amma kinga duk sun shirya hakan za su yi.’
Mommy ta sake kamo hannuwanta duka biyun ta kalle ta suka haɗa ido sannan tace ‘Kada ki damu, kamar yanda na gaya miki na ranar ne kawai. Kuma ke ma ‘yan uwanki za su zo, duk da kin ce kada a zo da yawa toh yayarki za su zo da kamar mutum huɗu haka. Nabila kuma tace gobe za ta taho ta taya ki kwana zuwa lokacin da za su gama bikin. Kada ki damu in sha Allahu komai zai wuce.’
Haka suka zauna Mommy ta yi ta ba ta baki har zuwa yamma. Ta samu zuciyarta ta yi sanyi amma dai ba ta da tabbacin ko za ta iya ɗauka, ta dai haƙura ta ga yanda za ta kaya kamar yanda Mommy tace. Sai da yamma sanna ta shirya ta koma gidan zuciyarta cike da wasi-wasi.
Washegari ‘yan uwan amarya suka zo suka yi kafi. Ba su ja fitina ba don haka lafiya aka rabu, ta sa Hafsa ta miƙa musu kuloloin abincin da ta bayar aka dafa musu; don ita tunda suka shigo gidan ta haye sama kuma har suka gama ba ta sauko sun haɗu ba. Sun tura Hafsa ta je ta kirawo ta sau ba iyaka amma haka Hafsan take dawowa tace musu saman a rufe yake.
Haka suka gama kafinsu suna ta rangaɗa guda, ga turare da suka baɗe gidan da shi. Sai da suka kusan gamawa sannan yara suka dawo daga makaranta, nan da nan suka shige cikinsu da yake sun saba da ƙannenta saboda yawan zuwa gidansu da suke yi.
Dawowarsu daga gidan kafi ya yi daidai da dawowarta daga wajen lalle, a zaune ta same su a farfajiyar gidan ana ta hirarraki. Ta dubi yayarta Ummi tace ‘Yaya har kun dawo daga kafin? Ta taɓe baki tace ‘Hmmm! Mun dawo. Ta ɗan kalle ta da alamar tambaya tace ‘Ya na ga kina yatsina fuska? Komai dai ya tafi dai-dai ko?’
Salma wadda cousin ɗinta ce tace ‘Um babu laifi. Amma fa mu a ƙasa Mustaphan ya nuna mana ɗaki guda biyu da parlor yace nan ne naki kuma a nan muka yi kafi. Saman gidan nan ma dai ‘yar mulkin uwargidan taki ba ta ko bari mun hau ba ta ja ƙofa ta rufe don ba mu ko isa ta sauko mu gaisa ba ta aiko mana da kulolin abinci kamar wasu mayunwata.’
Ta zumɓuri baki ‘Ban gane a ƙasa ya ba ku ɗaki ba? Ai ni sama muka yi da shi kuma ya amsa min a kan haka. ‘To ai kuwa dai bai isa ba don Hajia Babba ta haye sama, ba ta ko saukowa idan ba ta ba wa baƙo mahimmanci ba. Nan da nan idonta ya kawo ƙwalla, ta miƙe ta ɗaga waya ta nufi cikin gidan. Ba tare da ɓata lokaci ba Yaya Ummi ta miƙe ta bi bayanta.
A ɗaki ta same ta har ta lalubo lambar Mustapha za ta buga. Ta dafe wayar tace ‘Ba sai kin kirawo shi ba domin ƙarya kawai zai yi miki ya sake ɓata miki rai, alamu dai sun nuna ita ce mai gidan. Kada ma ki ɗaga hankalinki a kan wannan maganar balle ki hana ku morar satin amarcinku, don in kika hana muku wannan kwanakin to kin yi mata alfarma ne don ita za ta so haka.
Ko da ma kun yi magana da shi ɗin ki nuna masa babu komai. Ta kalle ta tana zumɓura baki tace ‘Yaya babu komai fa kika ce? Ai ba haka muka yi da shi ba. Tun lokacin da ya sayi gidan fa muka je da shi nace sama nake so kuma ya amince, shi ne zai je kuma ya canja magana.’
Ta yi murmushi tace ‘Kika san me aka yi masa ya canza? Wannan mata duk da ban ganta ba amma na san a shirye take, idan ba mu dage ba zuwa za ki yi ki zama ‘yar kallo don da alama tana shimfiɗa mulki yanda ranta yake so. ‘To yanzu ya za a yi?’
Ta yi murmushi ‘Kada ki damu zan yi magana da Inna, dama kin ga tunda aka fara maganar bikin nan take faman nemar miki taimako. Kin ga yanzu sai a mayar da hankali a yi aikin da za ki haɗa kan gidan ki mallake a sauke miki ita daga benen kuma a cire ta daga zuciyarsa gaba ɗaya.’
‘Anti dama fa ba ta zuciyarsa gaskiya, don gaskiya haƙuri kawai yake yi da ita ba tun yau ba. Da bakinsa ya gaya min babu ragowar ƙaunarta a zuciyarsa…..’ ‘Ke rabu da shi, namiji ai munafiki ne. Za dai mu yi maganinsa tunda mun ga kamun ludayinta.’ Ta katse ta tana yarfe hannuwa.
Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Takwas
Edita@rumasau-kallamu








