A zaune yake a parlor ɗin Alhaji, yayin da Hajia take zaune a kusa da Alhajin. Zuwa ya yi musu da labarin auren yana son ya ƙara don har ma yana gaya musu sati me zuwa yake so a je a kai kuɗin aure.
Cikin walwala Alhaji yace ‘Ai kwanaki da muka yi magana da kai da na ji ka shiru na zata ka fasa. Ya yi ‘yar dariya ‘Ba fasawa na yi ba Alhaji, na dai ɗan tsaya ne na ƙara shiryawa, na gaya maka zan sayi gida ai.
To dama tsayawa na yi a samo gidan, kuma yanzu an samo, cinikin ne ma bai faɗa ba saboda ina so su ɗan yi min ragi. Amma in sha Allahu ina sa ran za mu daidaita shi yasa nake son yanzu a kai kuɗin auren.’
Murmushin Alhaji ya ƙara faɗi, ya dubi Hajia sannan ya dubi Mustapha yace ‘To ma sha Allahu. Wannan ai sai dai mu sa albarka kawai. Ka je ka sami babanka Safiyanu ka yi masa bayanin ita yarinyar idan ya gama bincikensa ya tabbatar gidan mutunci ne ai sai su je su kai kuɗin. Allah ya sa albarka, Allah ya ƙara buɗi.’
Suka haɗa baki shi da Hajia suka ce ‘Amin. Hajia tace ‘To ka gayawa Khadeejan ko? Me tace? Ya shafa kai yana murmushi ‘Ban gaya mata ba tukunna, amma in sha Allahu zan gaya mata. So nake sai an gama magana tukunna idan ya zama saura kamar sati uku ko huɗu sai na gaya mata ko don saboda gudun fitina.
Kafin nan na siya gidan mun koma. Alhaji yace ‘Eh, to hakan ma ya yi. Sai dai kuma Allah ya sa kada mata su riga ka gaya mata. Hajia tace ‘A a babu wanda zai gaya mata, ka yi abinka a hankali idan ka shirya ka gaya mata. Nan suka ƙare hirarrakinsu daga baya ya yi musu sallama ya kama hanya.
Abu ɗaya ne yake ci wa Khadeeja tuwo a ƙwarya rashin haihuwa, domin har yanzu tun bayan cikin da ta samu ya ɓare ba ta sake ko da ɓatan wata ba. Ga shi yanzu har sun shiga final year amma babu wani labari.
Duk lokacin da ta yi yunƙurin zuwa asibiti Mustapha sai ya nuna halin ko in kula ko kuma yace lafiyarta ƙalau za ta je ta fara neman fitina, don haka ta tattara ta haƙura. Sai dai ta yankewa kanta hukuncin cewa da zarar ta gama final exam za ta je asibiti a duba ta a tabbatar mata da abinda ya hana ta samun ciki; ko babu komai ita ma tana so ta ga ta haifi dan cikinta.
Tunda idan ta gama karatu ba ta san lokacin da za ta sami aiki ba. Haka ta haƙura ta mayar da hankali a kan karatunta tana addu’a. Zamanta da yaran Mustapha kaɗai ya isa ya sa ta ji tana son haihuwa; domin yanzu yaran sun girma tunda Shukra auta ma tana primary 1 yayin da Afaf take SS.
Kusan gaba ɗaya yaran yanzu ba daɗinsu take ji ba, domin abinda suka ga dama suke yi. Habib ne ma kawai wanda ya damu da rayuwarta kuma yake neman shawara a wajenta kamar uwa, amma Afaf da Nasreen ma ba ta san wanene yake ba su shawara ba.
Ta dai san duk wani abu na wulaƙanci da suke yi mata da sa hannun Yaya Jidda. Ga wani mahimmanci da Musttapha yake ba wa Afaf ta yanda ko da sun gama magana da Khadeejan Afaf tana iya saka shi ya canza. Duk abinda ya shafi yaran kuma ko da Khadeeja ce ta gaya masa to a ƙarshe da Afaf ɗin zai yi shawara.
Hatta kitchen ɗin gidan ya zama kamar na mata biyu; domin a lokuta da damam sai ta gama girka abinda kowa zai ci ta fita daga kitchen ɗin sai Afaf ta shiga ita ma ta dafa abinda ta ga dama tace ba ta cin wanda Khadeejan ta dafa. Ta yi magana har ta gaji, tunda Mustaphan ya fara nuna tana so ta takurawa Afaf ne saboda ba ita ta haife ta ba.
Tana kwance a ɗakinta tana jiyo hayaniyar yaran a parlor; Afaf ta shigo ta same ta ta miƙa mata waya tana cewa ‘Anti Abba ne yake waya yace yana kiran wayarki ba ta shiga. Ta tashi zaune ta karɓa ta ɗan kalli wayar ta ga whatsapp call ne, sannan ta kara a kunnenta.
Yace ‘Ina kika shiga ne nake kiran wayarki ana ta cewa not reachable? Ta yi ‘yar dariya tace ‘Sai dai ko idan network ne don ga wayar ma a hannuna. ‘Kin san Ali Ahmed ko? Abokina da muke zuwa zance tare. ‘Eh na san shi mana.’
‘Yauwa da Allah shi ne ya shigo gari nan da kamar awa ɗaya za mu zo gidan, me za ki iya dafa masa sai mu yi dinner tare. Yana dai son tuwo ‘Ok, to sai a yi tuwon ai. Amma dai ka bari na duba freezer tukunna na ga yawan kazarmu yadda za a samu a yi muku peppersoup ma ko?’
‘Eh, ƙwarai kuwa da zobo ma please. Duba idan babu kazar sai na bayar a kawo miki yanzu, riƙe wayar ki duba ki ba ni amsa. Ta miƙe ta dubi Afaf da take tsaye tana jiran wayarta ta nufi kitchen.
Suna fitowa parlor Afaf ɗin ta ga Nasreen ta canza channel ta mayar Disney Junior, da sauri ta yi kanta tana cewa ‘Wane mara kunyan ne ya canza min channel ban gama kallo ba. Anti idan kin gama wayar ina nan.’
Ta shige kitchen ta bar su. Tana shiga ta ƙarasa ta buɗe freezer ta duba sannan ta ce masa ‘Za ta isa ma, amma dai idan za ka dawo sai ka siyo wata don gaba ɗaya zan kwashe na dafa muku yanzun. Suka yi sallama ta katse wayar.
Sunan da ta gani a jerin chats ɗin kan wayar shi ya ja hankalinta ta fasa fitowa daga kitchen ɗin tana ƙarewa sunan kallo; Anti Naja aka rubuta da alamar zuciya ta emoji. Daga haka da take kallon hoton da yake kan sunan kuma tabbas Naja ce sakatariyar Abbansu.
Ba tare da ta yi wani tunani ba ta danna kan sunan ya buɗe mata chats ɗin, har za ta yi sama sai kuma wani saƙo da yake cikin jerin saƙunan da ke ƙasa ya ja hankalinta. Afaf ce ta turawa Naja saƙon kamar haka “Congrats Anti, Abba ya ce min an kawo kuɗin auren ko?”
“Eh my girl, sun kawo har da sadaki ma. Saura kawai ya gama gyaran sabon gidan mu shikenan. “I can’t wait to have you here with us Anti.”“Soon my girl. Amma dai ta daina ba ki matsala ko? “Ta daina, tunda ta ga babu riba. Yanzu ba sosai ma take kula ni ba dama ni haka nake so. Habib ne kawai sarkin rawar kai ya manne mata.”
“Kada ki damu kwanan nan zan zo na gyara mata zama. Motsin da Khadeejan ta jiyo ne ya sa ta yi sauri ta rufe saƙonnin ta dire wayar a kan teburin da yake kusa da freezer ɗin ta kama murfin freezer ɗin ta ɗaga kamar a lokacin ta rufe. ‘Anti ina wayar?’ Afaf ta faɗa bayan da ta ƙarasa shigowa kitchen ɗin.
‘Kin ganta nan a kan tebur, ɗauki. Ta ƙarasa ta ɗauki wayarta ta fice ta koma parlor ɗin. Cikin sanyin jiki Khadeeja ta tsaya a ta jigina da freezer ɗin ta kafa tagumi. Kusan wata takwas da suka wuce Mustapha ya kalli tsabar idon Baffa da Mommy yace musu ba auren Naja zai yi ba, amma ga shi daga waɗannan chats ɗin da ta karanta yanzu har an kai kuɗin aure da sadaki.
Wato ma Afaf ta san komai ita ce kawai ba ta san mijinta zai ƙara aure ba kenan; kuma kamar dai ba shi ma da niyyar gaya mata. To me ta yi wa Mustapha ne? Me yake tunanin za ta yi a a kan ƙara aurensa da yake ɓoye mata?
Ita dama da ya kai ta gidan da ya siya yanda ta ga gidan ta san sai ya ƙara aure, kawai dai ba ta zata Naja zai auro ba don kwata-kwata ba ta sake ganin wata alama da take nuna yana tare da Naja ba tun bayan da suka je wajen Baffa.
Wato dama da take zargin Yaya Jidda ce take hure mata kunnen yara ashe Naja ce, tunda ga shi nan ta gani har tana gayawa Afaf cewa za ta shigo ta gyara mata zama. Ta jijjiga kai, ta goge gumin da ya fara tsattsafowa daga goshinta sannan ta tuna ce mata fa ya yi nan da awa ɗaya za su zo.
Jikinta a sanyaye ta koma cikin gidan ta kirawo Rashida sannan suka fito suka kama aiki. Haka ta haɗiye duk wani ɓacin rai ta yi ta haba-haba da abokinsa, sai bayan sallar isha’i sannan ya yi musu sallama ya tafi.
Ta san cewa ya kula da yanayinta yanda ya sauya, amma bai yi mata magana ba. Duk da dai ko da ya yi mata maganar ma za ta gaya masa gajiya ce kawai. Haka dai suka kwana shi yana baccinsa ita kuma Khadeeja duk lokacin da ta yi juyi sai ta kalle shi tana tambayar kanta wai me ta yi masa ne yake mata abubuwa kamar wata wadda aka aura ba don soyayya ba?
Haka ta haƙura ta yi ta danne zuciyarta har gari ya waye. Sai ƙarfe biyu na rana take da lecture amma haka ta shirya da wuri lokacin da Mustapha ya shirya zai tafi office tace ya wuce da ita ya kai ta gidan Mommy, in ya so daga can sai ta wuce makarantar ta kuma dawo gida. Haka kuwa aka yi.
Tunda ta shiga gidan Mommy ta karanta damuwa a fuskarta, ta dai kyale ta har Baffa da Nabila suka gama shirinsu suka fice. A nan parlor ɗin inda suka bar su Mommy ta zuba mata ido na ɗan lokaci, har ta ji a jikinta Mommy ɗin kallonta take. Tana juyowa kuwa suka haɗa ido; ta ɗan yi dariya tace ‘Mommyy.’
Ita ma ta yi dariyar tace ‘Ya aka yi ne? Kamar dai kina da damuwa. Ko kuma ba kya jin daɗi ne? Ta jijjiga kai tace ‘Mommy Mustapha aure zai yi.’Ta ɗan zaro ido ‘Aure? Ikon Allah.’ Sai kuma ta saki fuskarta ta cigaba ‘Ko da yake wannan ba abin mamaki ba ne ai don haka kada ma ki saka wa kanki damuwa.’
Ta sunkuyar da kai cikin damuwa tace ‘Mommy ni ma ba damuwa na yi ba, kawai dai yayanyin abun ne. Ban gane ba. Nan ta sanar da ita wadda zai aura sannan ta sanar da ita a inda ta ga labarin auren da kuma irin saƙonnin da Afaf take tura wa Najan da kuma yanda take fama da Afaf ɗin a ‘yan kwanakin nan.
Duk da Mommy ba ta yi mamaki ba amma dai ta ji babu daɗi, musamman yanda Afaf ta zama ‘yar rahoton Naja. Tace ‘Ikon Allah, to shi me yasa yake ɓoye miki auren? Tace ‘Wallahi ban sani ba, ko da wasa bai taɓa gaya min ba kuma danginsa ma babu wanda ya gaya min.
Amma kin ga yaran har sun sani, tunda ga shi har ana gaya musu za a zo a gyara min zama. Lallai mutum sai a bar shi. Dama na gaya miki Mommy tunda na ga gidan da ya saya nace miki gidan nan ba na mace ɗaya ba ne, kin ga maganata ta tabbata.’
Suka yi shiru na ɗan lokaci, jimawa kaɗan Mommy tace ‘To da ce mata aka yi ba ki zauna daidai ba da take cewa za ta gyara miki zama ko me? Amma kafin ta gyara miki zama ke ce za ki bi dare ki gyara zama ta hanyar addu’a, idan gari ya waye kuma ki ɗora da sadaka.’
Ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin ɓoye ƙwallar da ta gangaro a kwarmin idonta; wannan kalmar ta za a gyara mata zama ta tsaya mata a rai. Domin dai kalma ce da za ta iya ɗaukan kowacce ma’ana. Amma kamar yanda Mommy ta faɗa hakan za ta yi tunda ta san ba ta da gatan da ya wuce Allah.
Haka suka cigaba da hira Mommy tana ta ba ta baki kuma tana yi mata alƙawarin daga nan ma za ta dinga yi mata addu’a kuma da sadaka, ta tabbatar mata ba za ta yi nasara a kanta ba.
Da wuri Mommy ta sauke abinci saboda Khadija ta ci kafin ta tafi makaranta, tana daga kitchen ɗin ta ƙwalawa Khadeejan kira. Tana shiga kitchen ɗin ta fara gatsina fuska tana cewa ‘Mommy wannan wane irin kifi ne kika dafa me azabar ƙarni? Allah ya sa dai ba da shi kika yi abincin ba.’
Mommy ta ƙare mata kallo na ɗan lokaci sannan tace ‘Wane kifi da aka dafa tun jiya da daddare aka cinye, ni shinkafa da wake ma na dafa. Nana da nan fara’arta ta ƙaru, ta ɗauki plate ta matsa tana miƙawa Mommy tana cewa ‘Yauwa Mommy zuba min na fice don wallahi kitchen ɗin nan ƙarni yake.’
Ta karɓi plate ɗin tana cewa ‘Ciki ne da ke ko? Ta kalli Mommy da baki a buɗe, suka ɗan zuba wa juna ido sannan ta rufe bakin tace ‘Anya kuwa Mommy, tunda dai ni ban ji wani sauyi na a zo a gani ba.’Ta zuba mata abincin ta miƙa mata tana cewa ‘To ki dai bincika tukunna kafin ki yi saurin cewa a a, don tunda kika shigo nake kula da ke gaba ɗaya ma na dauka abinda ya kawo ki kenan.’
‘To ban sani ba gaskiya Mommy, amma zan duba yau ɗin nan kuwa. Bayan ta gama cin abincin ta yi sallah sanna ta fice ta kama hanyar makaranta. Sai da ta tsaya a chemist ta sayi abun pregnacy test sannan ta wuce. Ta riga ta san su Rahma suna jiranta a hostel don haka kai tsaye can ta wuce, tana ajiye jakarta a ɗakin ta fice ta faɗa toilet.
Tana tsoma abin nan a fitsarinta ya nuna raɗau positive; wato tana ɗauke da ciki. Ta yi murmushi tana ji kamar ta daka tsalle saboda murna, nan da nan idonta suka ciko da ƙwalla saboda jin dadi. A take kuma jikinta ya yi sanyi da ta tuna cewa Mustapha ne ya yi mata ciki kuma shi ne yake shirin auro matar da ta ke ikirarin za ta shigo ta gyara mata zama.
Ta sunkuyar da kai ta saki takardar a ƙasa sannan ta fito daga banɗakin cike da damuwa. Yanayin da ta shiga ɗakin ya tabbatar musu da akwai matsala, don haka tun kafin ta Zauna Farida ta miƙe ta tare ta tana cewa ‘Ya na ganki haka, lafiya dai ko?’
Ta zauna a kan gado Rahma kamar wadda aka jefa, ta kalli Farida suka haɗa ido sannan ta saki murmushe wanda yake haɗe da takaici tace ‘I am pregnant Farida. Nan da nan su Rahma da Amina da ke zaune suka dako tsalle suka faɗa jikinta sun ihu.
Sai da suka fahimci ita ba ta taya su ihun kamar yanda suka saba sannan suka tsaya suna kallonta. ‘Girl, wannan ai abun murna ne na ga kamar ke ba ki ji daɗi ba.’ Amina ta faɗa tana riƙe da hannun Khadeejan.
Ta sunkuyar da kai ta zare hannunta ta goge ƙwallar da ta faɗo daga idanunta. Ta ba su labarin auren Mustapha da kuma abinda ta gani da ma yanda yake ɓoye mata. Tace ‘Ban ma san wanne zan yi ba; murna ko baƙin ciki? Ni da za a zo a gyarawa zama ina zan miƙe ƙafa na fara haihuwa; haihuwar da ni ban ma tabbatar zai yi murna da ita ba.
A yanzu ma gaba daya kai na ya kulle. Mommy dai tace kada na kuskura na yi masa maganar ƙara aurensa, na bar shi har sai ya zo da kansa ya gaya min, a lokacin sai a yi duk wadda za a yi. Amma wallahi ban sani ba ko zan iya jurewa. Gaba ɗaya ma yanzu ban san matsayina a wajen Mustapha ba, kuma ga ciki.’
Suka yi shiru na ɗan lokaci. Amina ce ta katse shirun nasu tana cewa ‘Gaskiya mutumin nan dan wulaƙanci ne, haba!’ Rahma tace ‘Amma gaskiya ina bayan Mommy, ki bar shi kawai kada ki yi masa magana in ya so idan ya zo zai gaya miki da kansa sai ki yi masa wankin bargo tunda dai babu abinda zai sa ya fasa wannan auren da yayi niyya.’
Tace ‘Haka ne. Nan suka ɗauki lokaci suna ba ta baki, sannan daga baya Farida da Rahma suka fice suka tafi lecture ɗin suka bar su a ɗakin ita da Amina wadda ta tsaya ta taya ta zama don tace ba za ta iya zuwa lecture ɗin ba.
Danna nan don karanta Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Shida
Edita@rumasau-kallamu









