Da asubar fari ya tashi, bayan ya gama alwala ya fito da niyyar tafiya masallaci ya ƙarasa ƙofar ɗakinta ya murza hannun ƙofar ko zai ji ta a buɗe amma sai ya ji ta a rufe, sai dai ya hango fitila ta ƙasan ƙofar ɗakin a kunne. Don haka ya kaɗa kai ya wuce masallaci ya san ta riga ta tashi.
Tun kafin ta tayar da sallah cikinta yake ƙugi saboda jiya ba ta ci abincin dare ba ta kwanta, don haka tana idar da sallah ta gama azkar ɗinta ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito ta wuce kitchen; a lokacin Rashida da su Afaf babu wanda ya tashi domin dama ita ce take tashin Rashida kafin ta yi sallah su kuma su Afaf bayan ta idar da sallar.
Tana shiga ta ɗora ruwa kofi ɗaya ta jira ya tafasa, ta haɗa shayinta mai kauri a babban kofi ta ɗauki burodi ta gutsura ta ɗauka ta nufi ɗaki. A falo ta ci karo da shi ya shigo daga masallaci, ya dube ta yace ‘Shayi za ki sha da sanyin safiya kuma.’
‘Um.’ Ta ba shi amsa sannan ta wuce ɗakin. Da hanzari ya bi ta don kada ta rufe ƙofar, ya cimmata a daidai lokacin da take zama a kan dadduma tana ajiye shayin nata. Ko kallon inda yake ba ta yi ba balle ta nuna ta san mutum ya shigo. Ya ƙarasa ya zauna a gefen gado yana cewa ‘Sai kin gama za ki taso yaran ne? Akwai school fa.’
Ta gutsiri burodi ta tsoma a shayin sannan tace ‘Ba ni da lecture sai 9am so idan na gama zan ɗan koma ne na rage bacci zuwa kamar 8am sai na tashi na shirya. Ya ɗan yi dariya a kaikaice don ya san kwanan zancen, yace ‘Haba dai, ai kya daure ki shirya yaran kafin ki koma ki kwanta ko?’
‘Oh, ai kuma ka cire al’amarinsu daga hannuna ka saka a hannun sakatariyarka kamar yanda ka sanar da ni a aikace jiya don idan ban manta ba ma ita ce ta kawo muku dinner. Ko ba komai ma ka huta da mita ta. Ta ɗauki kofin sahyinta ta cigaba da kurɓa.
Ya ɗan tsaya yana ƙare mata kallo saboda yanda ya kasa fassara yanayin fuskarta domin kamar ranta ba a ɓace yake ba kamar ma dai tana cikin yanayi na nishaɗi. Yace ‘Common Khadija, na riga fa na gaya miki cewa ban same ki a waya ba shi yasa nace ita ta je ko? Ko da wani abu ma ai sai ki shirya su idan na kai su makaranta sai mu ƙarasa maganar kin ga lokaci yana ƙurewa.’
‘Babu ma wani abu, na riga na fahimci saƙon. Ya miƙe yana cewa ‘To don Allah ki fito ki shirya su kin ga idan suka makara rufe gate za a yi. Ta cigaba da shan shayinta kamar ba da ita yake magana ba, ya fara kosawa don haka kamar a hasale yace ‘Kina ji ina miki magana ko?’
Ta kalle shi suka haɗa ido tace ‘Na ji. Ya kalli agogon bangon da yake ɗakin ya ga ƙarfe shida saura kwata, ya juya ya fice ba tare da yace komai ba. Ya wuce ɗakin yaran don ya kula so take yi su makara. Idan ya taso su in ya so sai su zo da kansu su gaya mata ta taso ta shirya su.
Yana ficewa ta tashi ta tura ƙofar a hankali ta mayar ta kulle ta bar mukullin a jiki, domin yau babu wanda za ta shirya sai dai a yi duk abinda za a yi. Tana zama a kan daddumar ta ji Nasreen tana buga mata ƙofa tana cewa ‘Anti mun tashi. Har ta gaji da bugun ta ruga banɗaki ba a buɗe mata ba.
Ya fito daga ɗakin nasu Rashida tana biye da shi, ya dube ta yace ‘Je ki taya mana ku shirya yara, kun kusan makara fa. Ta wuce kitchen yayin da ya nufi ɗakin Khadeeja, ya murza hannun ƙofar yana turawa ya jita a rufe ‘Ya juyo da mamaki yana hango kitchen yana cewa ‘Ko kina kitchen ne?’
Ya wuce ya nufi kitchen ɗin, yana shiga ya dubi Rashida yace ‘Ba ta fito ba? Tace ‘Eh. Ya yi tsaki ya juya ya fice. Ya koma kƙfar ɗakin nata ya ƙara ƙwanƙwasawa, sai sai har ya gaji da ƙwanƙwasawa ba ta buɗe ƙofar ba, yana kallo ta ƙasan ƙofa ya ga duhu alamar an kashe fitilar ɗakin. Ya ja tsaki ya wuce ɗakinsa, yana shiga ya ɗauki wayarsa ya fara kiran lambarta.
Sai dai har ya gaji da kira ba ta ɗauka ba. Don haka ya ajiye wayar a kan gadon ya fito daga ɗakin ya wuce kitchen, yana shiga ya tarar da Rashida tana tattare fulawar da ta kwaɓa jiya za a yi shawarma wadda Khadija ta bar ta a nan a buɗe ta kwana har ta bushe. Yana shiga ta bar abinda take yi ta tsaya tana kallonsa.
Yace ‘Ya ba ki fara komai ba kika tsaya kina kallona? Uhm ai ban san me zan fara ba. Me kuke yi ke da ita idan za ta shirya ‘yan makaranta? Um, ai ita ce take yin abincin ni taya ta nake yi, kuma yanzu ban san me za ta dafa ba. Mtsewww!’ Ya ja tsaki sannan ya juya kamar zai fice sai kuma ya dawo yace ‘Ki ɗora ruwan shayi mana da abincin tafiya makaranta.’
Ya juya zai fita tace ‘Um to abincin makarantar me za a dafa? Ya kalle ta cike da takaici; wai wannan wacce irin daƙiƙiyar yarinya ce? Yace ta dafa abincin ma sai kuma ya gaya mata abincin da za ta dafa. Kamar zai fice kuma sai ya tsaya yace ‘Ki dafa indomie. ‘To.’ Ta amsa jikinta na rawa ta juya ta shige store domin ɗauko indomie.
Yana dawowa parlor ɗin ya jiyo Afaf tana hayaniya da Shukra a kan shiryawa, har ya nufi ɗakin sai kuma ya fasa ya wuce ƙofar ɗakin Khadeeja ya ƙwanƙwasa ƙofar a hankali yana cewa ‘Khadija ki buɗe mana. Babu wanda ya ba shi amsa don haka ya koma parlor ɗin ya zauna yana jiyo hayaniyar yaran a ɗakinsu suna shiryawa.
Jimawa kaɗan ya tashi ya nufi ɗakin inda ya sa hannu ya fara ƙoƙarin taya su shiryawa. Nan da nan suka gama sannan ya taso su a gaba suka fito inda ya saka su a gaba suka sha shayi da burodi sannan a gurguje Rashida ta zuba musu indmie ɗinsu a flask ya tasa su a gaba suka fice.
Khadeeja tana jin fitarsu da mota ta fito daga ɗakin a shirye ta sallami Rashida ta sanar da ita idan ya dawo ta fice ta tafi maƙota in ya so idan zai fita sai ya yi mata magana ta dawo; Haka suka saba tunda Shukra ta shiga makaranta; idan dai ba tare da yara zai fita ba sai dai Rashida ta je maƙota ta jira idan ya gama zai fita sannan ta dawo ta shiga gidan.
Bayan ta gama sallamar Rashida ta fice ta tafi makaranta. Suna dab da ƙarasawa makarantar aka rufe gate ɗin, gaba ɗaya masu gadi da sauran ma’aikatan suka shige ciki suka rufe ƙofa; wanda hakan yake nufi babu yaron da zai sake shiga. Ya tsaya ya cije leɓe na ɗan lokaci sannan ya kunna motar suka kama hanyar komawa gida.
Nasreen tace ‘Mun makara, ga shi ba mu taɓa makara ba. Yace ‘E, kun tsaya kuna ta faɗa ba ku shirya da wuri ba. Afaf tace ‘Abba Anti ba ta da lafiya ne? Ya shafa kansa yana cewa ‘Eh, ba ta jin daɗi. Shigowa gidan suka tarar da Rashida a tsaye a bakin ƙofa kamar yanda ta saba jiransa, tana ganin su ta bi su suka shige.
Shi kuma Abbansu ya ƙarasa ƙofar ɗakin Khadeeja ya fara ƙwanƙwasawa yana yi yana cewa ‘Khadeeja da Allah ki buɗe mana. Rashida ta fito daga ɗakin su Afaf tace ‘Antin ta tafi makaranta. Ya kalle ta da mamaki yace ‘Makaranta? Yaushe? ‘Bayan kun fita.’
Ya wuce ɗakinsa ya bar ta a nan. To me Khadija take nufi ne? Daga yin abu ta ma ƙi ta zauna a yi magana tana ta wulaƙanci, ga shi har ta sa yara sun rasa makaranta. Yanzu ga shi dole ya fita ya bar su a gidan su kaɗai abinda ba ya so. Amma wannan wulaƙancin na Khadeeja fa ya fara yawa, ta ma ƙi ta saurare shi gaba ɗaya. Yanzu ya take so a yi?
Haka ya wuce ɗakinsa ya zauna ya fara kiran wayar Khadeeja amma har ya gaji da kira ba ta ɗauka ba. Ya duba lokaci ya ga karfe takwas da rabi, ga shi yana da meeting ƙarfe tara. Don haka a gurguje ya tashi ya shiga wanka ya shirya. Ko abinci bai tsaya ci ba ya fice ya bar yaran.
Babu wanda ta gayawa yanda suka yi da Mustapha, don ko su Rahma ba ta cewa komai ba; su kuma da suka kula ba ta son magana sai kawai suka ƙyale ta. Haka ta yi zamanta a makaranta har wajen ƙarfe biyar na yamma sannan ta kamo hanya ta dawo gidan. Tana shigowa yara suka fara yi mata oyoyo; da murnarta ta amsa sannu da zuwansu kamar yanda ta saba.
Ta kalli Afaf tace ‘Bari na je ɗaki na sha magani na huta, kaina ciwo yake yi. Ba tare da ta saurari amsarta ba ta shige ɗakin ta turo ƙofa. Sai bayan sallar isha’i sannan ya dawo, lokacin Afaf ta sa Rashida ta dafa musu taliya sun ci abincin dare saboda Khadeeja tace kada wanda ya sake buga mata ƙofa.
Yana shigowa gidan ita ya fara tambaya suka ce masa tana ɗaki, sai dai ga mamakinsa yana taɓa ƙofar ya ji ta a rufe. Nasreen ce ta sanar da shi cewa tace a daina buga mata ƙofa ba ta da lafiya. Don haka shi ma sai kawai ya ƙyale ta ya cigaba da harkokinsa har sai da yara suka kwanta.
Wajen ƙarfe goma na dare ya sake ƙwanƙwasa mata ƙofar, ta yi banza da shi ba ta ce komai ba. Ya matsa jikin ƙofar yace ‘Wallahi Khadeeja idan ba ki buɗe ƙofar nan ba zan ɓalla ta. Tana daga ciki ta ɗauki ‘yar saman rigar baccinta ta saka sanna ta zo ta buɗe masa ƙofar tana riƙe da wayarta tana chatting.
Ta koma ciki ta ƙarasa kan gado ta zauna ta miƙe ƙafarta ba tare da ta ce masa komai ba. Yana daga tsaye ya ƙare mata kallo sannan yace ‘Wai wanne irin wulaƙanci ne wannan kike yi ne Khadeeja? Kin bar min yara sun makara a makaranta kuma kin fice kin bar gida ba tare da wani bayani ba?’
‘To ai ka san dai yau ina da lecture ko?’ Ta ba shi amsa sannan ta sake mayar da hankali a kan wayarta. To don me ba ki tashi kin shirya yara ba kuma da kika dawo kika sake rufe ƙofa kika bar su. Au wai Najan ba ta zo ba? Ai na zata ta yi musu komai tunda yau ita ce da aiki.’
Ya cije leɓe sannan ya ja dogon tsaki ya fesar da iska saboda yanda Khadeeja take ƙure shi ‘Na gaya miki babu komai a tsakanina da ita sakatariyata ce kawai, don Allah wai me kike so na yi miki ne a kan wannan maganar. Idan kuma don ta je makarantar yara ne to ki yi haƙuri ba za ta sake zuwa ba, babu wata alaƙa tsakanina da ita dama sai ta office.’
‘Ai na ga alama.’ Ta faɗa ba tare da ta daina kallon wayara ba. A fusace yace Khadeeja ni nake miki magana kina danna waya ko kallo ban ishe ki ba? Ta ajiye wayar a gefenta ta kalle shi tace ‘Shike nan, na ji duk abinda ka faɗa. Please kada ki sake rufe ƙofar nan, kuma ga yara can sun kwanta da safe ki tashe su da wuri kada su makara.’
‘Ok. Har ya juya zai fita ya ɗan tsaya yace ‘Kuma kin san ke ma ba a nan kika saba kwana ba. Ok. Ya fice ya bar ta.Ta murguɗa baki kamar yana kallonta tace ‘Ɗan rainin hankali, ba ka yi laushi ba tukunna ka je ka ɗauko Naja ta zo ta dinga yi maka hidimar kai da yaran. Yana fita ta zame ta yi kwanciyarta sai dai ba ta rufe ƙofar ba.
Tana jinsa ya dawo ɗakin ya leƙa fuskarta ta yi kamar bacci take, don haka ya fice ya bar ta bayan ya kashe mata fitila. Ya yi zaton kamar yanda ta amsa masa da daddare za ta tashi ta shirya yara, sai dai abinda ta yi jiya shi ta sake maimaitawa. Ta saka mukulli ta kulle ɗakin, ya buga har ya gaji ba ta buɗe ba.
Don haka ba tare da ɓata lokaci ba ya tsaya a kan yara suka shirya ya kwashe su ya kai su makaranta. Kafin ya dawo ta fice ta bar masa Rashida a gidan. Takaici ne ya sake kama shi; to me Khadeeja ta mayar da shi ne? Wannan wane kalar taurin kai ne take yi haka? Kuma me take nufi?
Yanzu me take so ya yi mata; yaya ma zai yi da ita don gaskiya idan ba so take ya doke ta ba bai san me zai yi mata ba. Haka ya shirya ya fice ya nufi office. Har ya kusa ƙarasawa office ɗin dabara ta faɗo masa; ya karkata kan motar ya nufi gidan su Khadeeja.
Gara ya je ya kai ƙararta waje Baffa in ya so su tsawatar mata don shi yanzu idan ba duka ba bai san me take so ya yi mata ba. Ya ci sa’a ya sami Baffa yana shirin fita, bayan sun gaisa Baffa yace ‘Lafiya kuke dai na ganka da sassafe ko?’ Nan ya mayar masa da abinda ya faru da kuma yanda Khadeejan take rufe kanta a ɗaki, sai dai ce masa ya yi ya rasa Khadeejan ne a waya shi yasa ya tura sakatariyar tasa.
Baffa ya yi dariya yace ‘Kishi ne nasu na mata ya motsa, ka san a kan wata macen komai son da matarka take maka to za a ji kanku. Kada ka damu bayan Magriba ka ɗaukota ku zo nan. Zan kirawo ta don ma kada tace za ta yi taurin kai. To Baffa, na gode.’
Ya yi musu sallama ya fice yana jin daɗin matakin da ya ɗauka tunda ya san ko babu komai Baffa zai yi mata faɗa kuma ya san dole ta shiga hayyacinta. Suna shirin shiga lecture wayarta ta yi ƙara, tana dubawa taga Baffanta ne don haka ta ja da baya ta nemi waje ta amsa. Bayan sun gaisa yace ‘Khadeeja, na cewa Mustapha ku zo bayan magriba ke da shi kin ji ko?’
Tace ‘Um Baffa yau? Wani abu ya faru ne? Babu abinda ya faru, ku dai zo ɗin. To Baffa in sha Allahu za mu zo, in ya dawo zan gaya masa. Kada ki damu na gaya masa ma, yanzu ya bar nan. Ta amsa suka yi sallama da Baffa tana dariya, don ta san inda zancen ya dosa, ta gane Mustapha ƙararta ya kai duk da ba ta zaci haka ba.
Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Huɗu
Edita@rumasau-kallamu







