khairatu.shehu
Ko da gari ya waye Khadeeja ba ta ma san lokacin da Ummi ta zo ba don tun daga bakin gate ya tare ta yace ta koma kada ta sake zuwa sai bayan Sallah. Sai wajen sha ɗaya sannan ta fito ta ɗan gayggyara gidan, wanke-wanke ne ma ya ɓata mata lokaci don yana da yawa sosai. Haka ta wanke su gaba ɗaya a famfon waje sai da shigo kifewa sannan Afaf ta taya ta.
Tana gamawa ta shige ɗakinta ta kwanta; ba ta taɓa jin gajiya irin wannan ba a rayuwarta, ga shi duk wata gaɓa da take jikinta ciwo take yi. Tun 3pm ta shiga kitchen ta fara ƙoƙarin haɗa kayan shan ruwa; dankali da ƙwai za ta soya sai jollof sphagetti sannan ga peppersoup ɗin nama. Da akwai ragowar zoɓo na jiya don haka ba za ta sake haɗa wani ba.
Yaran suna zaune a parlor ta zo ta wuce ta shiga kitchen, tana wucewa Afaf ta bi bayanta. Ta so ta koro Afaf ɗin daga kitchen amma dai ta haƙura ta bar ta, suna yin aikin. Ba su daɗe da farawa ba Habib ya shigo kitchen ɗin, ya kalli dankalin da aka ajiye a tsakiyar kitchen ɗin yace ‘Anti wannan ferayewa za a yi?’
Tace ‘Eh, so nake na ɗora kifin nan sai na zauna na feraye shi.’ ‘Kawo wuƙa na feraye Anti.’ Ya faɗa yana buɗe cabinet, ya zaro roba ya tara ya ɗebu ruwa. Tace ‘Ka bar shi Habib zan feraye. Ya sa hannu ya ɗauki wuƙa a kan sink yana cewa ‘Na iya feraye dankali fa Anti, idan na feraye miki sai ki yanka.’
Bai saurari amsarta ba ya tsuguna ya fara feraye dankalin. Afaf ta ajiye kayan miyan da ta gama wankewa a kusa da Khadeejan tace ‘Anti na wanke kayan miyan.’ ‘To ki yanka mana albasar nan, rabi slicing za ki yi rabi kuma ki yanka ƙanana sai a saka a soup da fried egg.’ Ta ɗauki albasar ta wanke ta zuba a chopping board ta fara yankawa.
Ba su ji lokacin da Mustapha ya ƙaraso bakin ƙofar kitchen ɗin ba; a dai-dai lokacin nan wuƙar da Afaf take yanka albasa ta goce ta yanke mata hannu. Ta dire albasar ta make murya tana cewa ‘Waiyo Anti na yake.’ Da sauri ta saki abinda yake hannunta ta nufi wajen Afaf ɗin tana murmushi cike da kulawa tana cewa ‘Sorry, garin yaya Afaf. Ki…’Da sauri ya ƙarasa ya kama hannun Afaf ɗin yana cewa ‘Garin Yaya kika yanke, me ya sa kika dauki wuka?’
Ya juya ya dubi Khadijan yana cewa ‘Na gaya miki sai kin san aikin da za ki dinga sa yaran nan amma ke gani kike kamar kawai bana son su taya ki aiki ne. Yaushe Afaf za ta iya wani yanka albasa.’ Afaf ta zare hannunta daga nashi hannun ta juya ta wanke a sink, ta dube shi tace ‘Ya ma daina jinin Abba bari na je na daure.’
Yana juyawa ya dubi Habib wanda yake ta ferayar dankali ya daka masa tsawa ‘Ka ajiye wuƙar nan ka tashi, namiji da kai kana wani feraye dankali. Tashi ka ba ni waje.’ Ya juya kan Khadeeja wadda ta riga ta cigaba da aikinta kamar ba da ita yake magana ba, yace ‘Na gaya miki ki daina sa yaran nan aikin da ya fi ƙarfinsu, bana so. Shi Habib ma da yake namiji me ya haɗa shi da wani harkar girki? Bana so.’
Bai ga alamar za ta ba shi amsa ba don haka ya juya shi ma ya fice suka barta ita kaɗai a kitchen ɗin. Ta rasa me ma za ta yi, ta goge fuskarta ta cigaba da aikinta. Haka ta lallaɓa ta gama komai, zuwa magriba ta zubawa kowa aka sha ruwa. Ta gaji iya gajiya don haka ba ta ma da kuzarin da zata iya wani musu da shi, ta dai riga ta gama yanke wa kanta hukunci da zarar an buɗe gari za ta tafi gidansu ba za ta dawo ba sai ta haihu ko kuma ya ɗauki mai aiki.
A haka aka cigaba da azumi, kullum cikin wannan yanayin Khadeeja take haɗawa da hidimar gidan da ta yaran ta yi ta fama. Kullum sai ta yi wa Shukra da Nasreen wanka, tsarkin kashi tsarkin fitsari duk ita take musu. Duk wata fitinarsu ita ce me kulawa. Ga shi tana fama da Shukra wadda sai yanzu ne da suka kwana biyu ta fara hana ta kashin wando.
Yanzu idan dai ba wasa take yi ba ba ta kashin wandon ta iya zuwa ta gayawa Anti za ta yi kashi. Amma idan tana wasa haka za ta tsuguna a wajen wasan sai ta gama kashinta sai dai a ji wari. Haka dai take ta fama.
Juma’a ce yau ɗin, gaba ɗaya a jigace take jin ta saboda azumi na sha ɗaya kenan za a kai kuma kullum ita kaɗai take hidimar gidan da ta yara. Gashi kuma ta ƙi ta ajiye azumin saboda ko ba ta yi azumin ba ma ba iya cin abincin kirki take ba. Haka dai ta tashi jikinta duk babu ƙwari, ta ɗan yi iya abinda za ta iya ta koma ta kwanta.Tun wajen 2pm ta taso ta fara aikin abincin shan ruwa don tana so ta gama da wuri, tunda zuwa yanzu yaran ma sun hakura sun daina yunkurin tayata.
Sai dai ita ɗin ma ta rage aiyukan da yawa don duk abinda ta kasa rabuwa take da shi. Dankali da ƙwai kawai ta soya ta dafa shinkafa ta ɗumama ragowar stew ta juye a flask, ta kawo ruwan shayi ta zuba a flask. Saura wajen rabin awa a sha ruwa ta gama ta kawo komai ta jera, ta wuce ɗaki ta kwanta bayan ta gayawa Afaf ta kula kada kannenta su yi ɓarna.
Ba ta yi minti goma da kwanciya ba Nasreen ta shigo ɗakin da gudu tana taɓa ta tana cewa ‘Anti Shukra ta yi kashi, Abba ya ce ki zo ki wanke mata.’ Ta tashi zaune tace ‘A toilet ɗinku ta yi kashin?’ ‘A wandonta ta yi Anti.’ ‘Je ki ina zuwa.’ Ta ja tsaki ta koma ta kwanta bayan Nasreen ta fice daga ɗakin. Jiri take ji sannan a wani ce ta zo ta wanke kashi, kashin da tace a daina yi mata a wando.
Ta yi zaton ma a toilet ta yi kashin ta je ta yi mata tsarki. Kafin ta gama yanke hukuncin da za ta ɗauka Abbansu ya shigo, bayan ta amsa sallamarsa yace ‘Ki zo ki wankewa Shukra ta yi kashi.’ Ta dafe kanta ta tashi tana cewa ‘Ba lallai na iya ba ne don wallahi jiri nake ji gashi yau tun safe marata take ciwo.’
‘To na ce ki ajiye azumin kin ƙi, ki bar shi haka ki huta. Ki taso ki gyara mata alwala zan je na yi an kusa kiran sallah.’ Ta miƙe a hankali ta biyo bayansa suka fito daga ɗakin. Tana shigowa parlor ɗin Shukra ta sunkuyar da kai, ta harare ta tace ‘Kin sani ai mara kunya, nace ki daina yin kashi a wando amma kin ƙi ko? Yau gidansu ƙyanƙyaso za ki kwana a can ake kashi wando.’
‘Don Allah ki yi mata a hankali, komai lokaci ne ai za ta daina ne a yi mata haƙuri.’ Ya faɗa yana shirin komawa ɗakin ya yiwo alwala. Ta tsuguna za ta ɗauke ta ta ji kanta ya biyo ta kamar zai faɗo, ta dafe goshi ta koma ta tsaye tace ‘Kai! Ba zan iya ba fa.’ Ya juyo ya tsaya ‘Menene?’
‘Ba zan iya tsugunawa ba fa, jiri kwasa ta yake.’ ta ƙarasa kan kujera ta zauna ta dafe goshi. Ta dubi Afaf tace ‘Ba ni ruwa na sha Afaf, ga kiran Sallah nan an fara. ’Nan da nan ta cika Kofi da ruwa ta miƙa mata, ta sha kaɗan ta jingine kanta tana riƙe da ruwan. Kukan Yusra ne ya katse su tana cewa ‘Anti na daina ba zan kuma ba, mantawa na yi daman.’
Ta yunkura za ta miƙe Afaf ta yi sauri ta dafe ta. Abbansu ya dubi Khadija yace ‘Don Allah ki lallaɓa ki wanke mata kashin nan, Wannan wane irin abu ne? Yanzu wa kike so ya wanke mata kashin?’ Afaf ta aika Nasreen ta ɗauko fo a toilet ta cire wandon da yake cike da kashi ta jefe a fo ɗin sannan ta ɗauke Shukran ta nufi banɗaki. Ta wanke mata sannan ta dawo ta gyara wajen, zuwa lokacin Abbansu ya fito daga alwala.
Ya zauna ya sha ruwa sannan ya miƙe zai tafi masallaci. A daidai lokacin ita ma Khadeeja ta ɗago kanta tace ‘A dawo lafiya.’ Yana jin ta ya yi banza da ita saboda yanda yake jin haushinta, kuma tabbas sai ya kora mata bayani in an sha ruwa. Daga yau ma ba za ta sake yin azumin ba tunda dama mai ciki tana da damar ajiyewa. Ta miƙe tana gatsina fuska, kawai sai gani ya yi ta sulale za ta faɗi.
Ya zabura zai tare ta ya yi fatali da casserole ɗin dankali, a lokaci guda Habib ya saki jug ɗin zobon da ya fito da shi daga kitchen ya tarwatse a wajen ya ƙarasa kanta. Duka su biyun kafin su ƙaraso ta zube. Abbansu ya ɗago kanta yana jijjigawa ‘Khadeeja, Khadeeja, Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, Khadeeja.’ Ko motsawa ba ta yi.
Ya sunkuce ta ya kwantar da ita a kan three seater, ya ƙara gudun fanka sannan ya kunna AC. Ya cire mata ɗankwalin da yake kanta ya fara yi mata fifita. Yaran gaba ɗaya suka jeru a kanta suka yi tsuru-tsuru; Afaf ta leƙa fuskarta ta kafaɗar Abbansu tace ‘Abban ita ma mutuwa za ta yi ta bar mu ko?’
‘Ke bana son rashin hankali, ba mutuwa za ta yi ba.’ A take yaran suka saka masa kuka mai ban tausayi. Afaf ta rungume Nasreen da Shukra suka haɗa kai suna kuka. Habib ya taɓa shi yace ‘Abba ka kai ta asibiti kada ta mutu ta bar mu.’ ‘Kai rufe mana baki.’ Gaba ɗaya shi ma ya ruɗe, jikinsa har rawa yake yi. Ya janyo jug ɗin ruwan sanyi ya jiƙa hannunsa ya shafa mata a fuska. Ta ja numfashi ta buɗe idonta, sai kuma ta mayar ta rufe.’Khadeeja.’
Ya kirawo sunanta da ƙarfi yana jijjiga ta. Da gudu su Afaf suka ƙarasa kanta suna kira ‘Anti, Anti.’ ‘Khadeeja.’ Ya kara kiran sunanta a firgice. Ta buɗe ido ta sake rufewa. Ya miƙe tsaye ya ɗan tura yaran yana cewa ‘Ku zauna na ɗauko mukullin mota, asibiti zan kai ta yanzu, babu abinda zai same ta in sha Allahu.’
Ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauko mukulli ya fito, ya je ya buɗe kofar motar ya dawo ya ɗauke ta bayan ya yafa mata mayafi ya wuce yaran suna biye da shi ya kwantar da ita a bayan motar. Bayan ya rufe ƙofar motar ya juyo ya kalli yaran yana tunani; to yanzu ya zai yi da su? Wa zai bar wa su? Ya san shi kansa ma sai ya amsa tambayoyi a checkpoints ga shi ma’aikatan asibitin ma kamar tsoron mutane suke balle ya kwashi yara su tafi.
Ya shafa kai sannan ya sake kallonsu cike da damuwa; da a ce gari a buɗe yake da sai ya wuce da su ya ajiyesu gidan Hajiya to amma ya san ba zai yiwu don zai yi ta ɓata lokaci a checkpoint. A take dabara ta faɗo masa. ‘Ku tsaya a nan ina zuwa.’ Ya ba su umarni sannan ya fice daga gidan ya turo gate ɗin.
Yana fitowa ya ƙarasa gidan su Ummi, ya yi sa’a yana tsayawa maigidan yana dawowa daga masallaci. Bayan sun gaisa ya sanar da shi so yake Ummi ta zo ta zauna masa da yara ya je ya kai Khadeeja asibiti. Ya janjanta masa sannan ya shige gidan ya turo masa Ummin. Haka ya sako ta a gaba ya dawo gidan ya bar mata yaran ya ja motar ya nufi Aminu Kano Teaching Hospital da ke Kano.
Yana zuwa asibitin aka nuna masa gynae emergency inda nan ne ake karɓar masu ciki waɗanda suke buƙatar taimako na gaggawa, nan da nan suka karɓe ta aka fara duba ta; duk da dai su kansu ma’aikatan za ka gane cewa suna cikin yanayi na tsoro saboda Covid19. A nan wajen aka nuna masa benchi ya zauna yayin da ita kuma aka tura ta a kan gadon marasa lafiya aka shige da itaɗdakin bincike.
Tana kwance a kan gadon yayin da take amsa tambayoyin ma’aikaciyar jinya sai wata ma’aikaciyar wadda ta ji suna kira matron ta shigo, ma’aiakaciyar ta juya tana kallon matron tana cewa ‘Matron wannan fa sai an yi mata scaning, cikin nan na jikinta kamar ficewa zai yi duk da dai tace ba ta fara bleeding ba amma dai tana jin alamunsa.’
Matron ɗin ta ƙaraso ta tsaya a kanta, tace ‘Ah! Wannan ai Khadeeja ce, wa ya kawo ta?’Jin an ambaci sunanta ya sa ta buɗe idonta a hankali, ta yi murmushi a gajiye lokacin da suka haɗa ido ta gane wadda ta ambaci sunan nata. Cikin sanyin murya tace ‘Anti Iyami.’ ‘Na’am, Khadeeja. Wa ya kawo ki?’ ‘Mustapha ne.’
Ta juya ta kalli abokiyar aikin nata tace ‘’Yata ce ai, ita ce wadda muka yi biki kwanaki fa yarinyar Habiba wadda nace miki childhood friend ɗina ce.’ Da fara’a tace ‘Aaah! Allah sarki, to abun ya zo kenan haihuwa yaƙin mata.’ ‘Ai kuwa. Bari na kirawo Dr. Jamil ya zo ya duba min ita sai mu je na kai ta scanning ɗin mu ga ko za a iya sallamarta a daren nan.’
Har ta juya za ta fice Khadeeja ta riƙo hannunta, ta juyo tana cewa ‘Akwai wani abu ne Khadeeja?’ Ta yi murmushin yaƙe ta goge ƙwallar da ta gangaro daga gefen idonta tace ‘Kada ki sallame ni Anti Iyami, ki yi wa Mommy waya ta zo ta ɗauke ni gida zan tafi.’ Ta ɗan ranƙwafo tana shafa kanta tana duban fuskarta tace ‘Ok, kada ki damu, ki samu ki huta tukunna likita ya duba ki. In sha Allahu yanzu zan kirawo ta ko ba ta zo ba da safe idan na tashi daga aiki sai na tafi da ke gidan Mommy ɗin. Kada ki damu.’
Ta juya ta fice yayin da Khadijan ta mayar da idonta ta rufe. Tare da likitan suka dawo, bayan ya duba Khadeeja aka je aka yiwo scanning tare da Mustaphan aka dawo. Bayan likita ya duba scanning ɗin yace cikin jikinta ya lalace fita zai yi, don haka za a yi mata wankin ciki sannan akwai allurai da ruwa da za a saka mata.
Da kansa ya je ya siyo komai ya kawo sannan suka koma wajen Khadeeja tare da matron; a nan Khadeejan take sanar da shi cewa martron kawar Mommy ce. Ya sake gaisheta cike da girmamawa, bayan ta amsa ta dubi Khadeejan tace ‘Likita ya ce cikin jikinki ya lalace don haka za a yi miki wankin ciki, ga magunguna kuma ya rubuta miki sannan ga drip idan an gama wankin cikin zan saka miki kin ga yau a nan zamu kwana da ni da ke.’
Ta yi murmushin yake, ta dubi Mustapha tace ‘Ka tafi, ka bar yara a gida. Anti Iyami za ta kirawo ka idan akwai wani abu tunda ka ga tare zamu kwana ma, zuwa da safe za mu yi waya in sha Allah. Matron ta fice ta ba su waje. Bayan ta fice ya matsa kan Khadeejan yana shafa fuskarta yace ‘Sannu, kin ba ni tsoro fa.’
Ta yi murmushi.Ya cigaba ‘Kafin safiyar ta yi sai ki samu ki yi min message ɗin duk abinda kike so na taho miki da shi, idan kuma Allah ya sa da safen za su sallame ki ma shikenan sai kawai na zo mu tafi. Na yi maganar abinci ma Anti Iyami tace na bari za ta kawo miki, but in ana son wani abu kiyi min magana sai na saka miki kuɗi a account ɗinki ko transfer ne sai ki yi musu.’
Ya sa hannu a aljihunsa ya zaro wayarta ya miƙa mata yana cewa ‘Ga wayarki, ba zan kirawo ki ba don kada na dame ki ko na tashe daga bacci, but please da kin farka ki kirawo ni.’ Ta karɓa tana murmushi tana cewa ‘Ok, ka gaishe min da su Yaya Afaf.’ Ya fice ya bar ta a kwance. Yana fitowa ya sami Anti Iyami da abokan aikinta a station ɗinsu, ya yi mata sallama bayan ta ƙarbi lambar wayarsa sannan ya wuce.
Tun a daren Anti Iyami ta kirawo Mommy ta sanar da ita halin da ake ciki, sai dai ba ta gaya mata cewa Khadeejan tace gida zata taho ba. Ta dai sanar da ita cewa tana hannunta idan akwai wani abu za su ji zuwa wayewar gari. Tana tsaye aka yi wa Khadeeja wankin ciki sannan aka ba ta ɗaki, ta saka mata drip da alluranta sannan ta haɗa mata shayi mai kauri.
Ta sakata a gaba bayan ta shanye sannan ta zuba mata shayi da kwai ta cinye sannan ta ajiye mata saucer da kankana da lemon ɓawo tace ta shanye kafin a jima. Ta sha tambayoyi a wajen Anti Iyami wadda take ƙoƙarin gane dalilin da yasa Khadeejan take son tafiya gida; sai dai ba ta sami komai ba don da a tunaninta ko Mustaphan yana abusing ɗinta ne. Ita kuma ta sanar da ita kawai ba ta da lafiya ne sannan kuma ga aikin gida da raino wanda ya yi mata yawa shi yasa take son ta je gida ta huta.
Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Huɗu
Edita@rumasau-kallamu