Labarin Kalala Da Kalalatu

0
4

Akwai wani mutum wai shi Kalala, yana da matarsa wadda a ke kira Kalalatu. Kalala Allah ya yi shi wani irin mutumin da ne, ba abin da ya fi da ƙi illa a yi masa abinci ya ci shi kaɗai. Da suna ci tare da wani makwabcinsa, sai makwabcin ya zama wani iri ne mai mita. Yakan riƙa cewa Kalalatu ba ta iya miya ba, wai kullum miyarta daga ta cika gishiri sai ta cika ruwa.

Da Kalala ya ga tsegumin ya fa yi yawa sai ya bar kai abincinsa wurin mabwabcin. Ya riƙa fita karauka yana nemo baki, yana kawowa gidansa suna ci tare.

To, Kalalatu ba ta ƙaunar wannan ɗabi’a ta mijinta, domin bisa ga misali, ran da Kalala ya yanka kaji biyu, iyaka Kalalatu ta sami cinya, domin duk Kalala zai kai wurin baƙin da ya jawo ne su cinye. Ta yi, ta yi ta hana shi wannan ɗabi’a, ya ki hanuwa.

Saboda haka sau da yawa in ya ba ta dahuwa sai ta tsame rabi ta cinye, in Kalala ya yi magana ta ce ya ƙone ne, ko kuwa ta ce ta sauke ta shiga ɗaki ɗauko kwano, kafin ta fito ta tarar kyanwa ta cinye rabi. Dalilai dai irin waɗannan marasa kan gado ga su nan kullum Kalala na ta sha, amma saboda haƙurin da Allah ya zuba masa ba ya cewa kome.

Rannan, ko ina Kalala ya sami kuɗi sai ya tafi kasuwa ya nemo daƙwalen kaji guda biyu ya sayo. Ya yiwo cefane ya kawo gida, ya ce wa Kalalatu ta soye kajin nan gaba ɗaya. Ta tashi, bayan ya fige ya gyara mata, ta sa tukunya ta shiga suya. Abu ga daƙwalen kaji, duk kitse yâ cika tukunya, sai wani abu su ke coi, coi, coi, in tana juya su.

Duk kuwa kwaɗayi ya kama ta, da ma ga ta idonta idon nama sai ka ce kura sai yawu ke zuba dalala. Ta sa dan yatsa ta ɗanɗana ta ji ko gishiri ya yi daidai, sai ta ji abin daɗi ya kamo ta har ga ƙeya, ta ce, “Kai, waɗannan kaji yau suna shirin ganin wata irin gajerar suya. Amma dubi duk yawan kajin nan, rabona bai fi cinya ba daga cikinsu. Ka san dai halin mai gidan nan ya miskile ni.”

Ta ci gaba da suya ƙamshi na jifarta, ta yi kamar ta jure ta kasa, sai ta fara tsame tana ci, wai ta kau da mugun yawu. Kafin su soyu ta kusa cinye rabin kaza. Da ta sauke sai ta je ta gaya wa mijin sun soyu. Kalala ya ce, “To, sai ki cire cinya guda, taki ke nan. Saura kuwa a ajiye, har in je in samo abokan ci.”

Kalalatu ta ce, “To.” Ta tafi ta cinye ’yar cinyar da aka ce ita ce tata, ta tsuguna tana kallon saura, sai mai ke zuba nash, nash. Ta ruga wajen ƙofar zaure ta leƙa ko ta hango mijin tafe da baƙin, ba ta ga kowa ba, ta komo wajen kaji ta tura musu ido. Sai ta ce, “Af, ashe ma fikafikai guda biyu sun kone tun ɗazun, bari in cinye na ɗayar kuma don su zo daidai, kada mai gida ya gane.” Sai ta kama fikafikai ta fiffizge ta laƙwame. Ta sake rugawa bakin zaure ta gani ko mijin na tafe, ba ta ga kowa ba.

Ta dawo, ta tsaya bisa kwanon da kaji su ke, ta ce, “Shin mai gidan nan zai zo dai? Ga kaji har sun fara yin sanyi. To, ni Kalalatu, yanzu in ya zo ya tarar wannan kazar duk na fiffige ta, ya tambaye ni, in ce me? Ba abin da yafi sai in cinye ta gaba ɗaya, in ya zo in ce kyanwar gidan nan ta sace ta.” Sai ta tsuguna ta cinye ta sarai, ta kwashi kasussuwa ta kai masai ta zuba.

Ta koma ƙofar zaure ta hanga, ba ta ga mai gida ba. Da ta ga haka sai ta dawo, ta ce, “A bari ya huce shi ya kawo rabon wani. Bari in ƙarƙare cinya guda, kowa ya huta, in ya so in ya dawo kome ta tafasa ta ƙone.” Sai ta kama kazar guda kuma ta laƙwume. Ta nufi randa ta ɗebi ruwa ta kora, ta yi gyatsa, ta ce, “Madalla, kome ta ke zama ta zama.”

Ta zauna kenan, sai ga mai gida ya shigo. Ya ce wa Kalalatu, “Yi maza ki niƙa yaji ki barbaɗa musu, kin san yanzu lokacin sanyi ne, ba abin da ya fi yaji amfani. Na manta ne in gaya miki ki niƙa yaji ɗazun. Yi hakuri, yau dai kin sha aiki.”

Kalalatu ta ce, “Ai ba kome, ku dakata mini dai kaɗan.’ Ta shiga ɗaki tana ta shawarwarin abin da za ta ce wa mijin ya faru ga kaji. Tana can cikin ɗaki, sai Kalala ya ɗauki wuƙa ya nufi maniƙa yana wasawa ƙararas, ƙararas, wai don ta yi kaifi ya sami ta yanka kaji ƙanana ƙanana, in an kawo.

Kalala na can na ta fama da washin wuƙa, sai Kalalatu ta ji ana sallama. Ta yi farat ta fita bakin zaüre wajen mai sallama, ta dube shi ta riƙe baki, ta ce, “Kai baƙo, kai ne mai gidan nan ya kirawo, wai ku zo kuci abinci? Baƙo yace, “I, Allah ya saka muku da alheri.”

Kalalatu ta ce, “Kai, tafi can, sakarai ba ka san abin da a ke ciki ba. Kana tsammani mutum mai hankall ya sa a yi masa abinci ya fita karauka neman abokin ci? In kana kama gabanka ka ruga, tun da wuri ka ruga. Ka ji shi can yana washin wuka, kunnenka guda zai yanke. Kullum haka ya ke yi, motsattse ne.”

Baƙon nan, ko da ya saurara ya ji Kalala na washin wuƙa sai ya dafe ƙeya ya zura a guje. Kalalatu kuma ta ruga wajen Kalala, ta ce, “Ga irin jaye-jayen naka nan, ba ka san irin mutanen da ka ke jawowa gida ba.”

Kalala ya ce, “E? Mahaukaci ne?”

Kalalatu ta ce, “Mahaukaci mana, ko ba mahaukaci ba ne ai ɓarawo ne, da ɓarawo ko da mahaukaci ai duk tafiyarsu kenan. Kajin da na barkaɗawa yaji, ko da ya gan su sai na ga ya yi wuf ya fizge, ya shafa a guje da su. Ga shi can ya miƙa, ya tasarwa kasuwa.”

Kalala ya fusata, ya ce, “Allah wadan ɗan banza! Mutanen duniya ba wanda ke iya musu. Da ma ya bar mini ko da guda ɗaya, ai da na sami ta kalaci. Daƙwalen kajin nan duk ya cinye shi kaɗai? Bari in leƙa ko na hango shi, mu raba.” Sai ya ruga wajen zaure ya hanga, sai ga baƙon nan can ya tattake da gudu kaca kaca kaca yana korar iska. Kalala ya ce, “Kai abokina! Kai tsaya, don Allah ko guda ɗaya ka ba ni! Wallahi su kenan, mai ɗakina ko lasawa ba ta yi ba, ka ɗauke.” Baƙo ya yi kamar bai ji ba.

Kalalatu ta ce wa mijin, “Bi shi mana, a guje dai na san ba ya tsere maka. Duk wahalan nan da na sha ta zama a banza, ko lasawa ban yi ba, ai ka san ka ɗauki alhakina.” Sai Kalala ya runtuma a guje da wukarsa a hannu, ya bi baƙo yana kira, “Tsaya don Allah, ɗaya kaɗai na ke so, na bar maka ɗaya!”

Bako tsammani ya ke Kalala na nufin kunnensa ɗaya kaɗai ya ke so ya yanka. Ya waiwaya sai ya ga ya taso masa da wuƙa tsirara a hannu. Saboda haka ya ƙara mai, ya dai yi wa Kalala fintinkau yana ji yana gani.

Da Kalala ya ga abin ba girma, sai ya juyo ya nufo gida da wuƙarsa a hannu, yana kutawa, yana Allah ya isa. Da matar ta ganshi ya dawo yana zage-zage sai ta tarye shi, ta ce, “Ya ba ka? Ka ga irin abin da na ke gaya maka nan tuni.”

Kalala ya ce, “Ko tarad da shi na yi? Wannan akwai ɗan banza da gudu! Ga shi kamar tsoho, amma da ya zura sai ganinsa a ke kamar ba ya taka ƙasa. Bar shi ya je ya ci, ban dai yarda masa ba duniya da lahira. Allah ya isa. Daga yau ko sai yau, ba na sake kiran ɗan kowa yaci abincina, tunda duniya ta sake. Mts, Allah wa- dai! Talaka dai ba aboki ne ba, ko ka so shi ran biki kwa ɓata.”

Wannan labari an ciro shi ne daga Magana Jari Ce littafi na biyu wanda Margayi Alhaji Abubakar Imam ya wallafa.

Domin karanta Amfanin Ganyen Shuwaka Ga Lafiyar Ɗan Adam danna nan

Edita@rumasau-kallamu

 

 

labarin da ya wuceTarihin Nana Asmau ‘Yar Shehu Usman Ibn Fodiyo
Labarin na GabaTarihin Dr. Yusuf Bala Usman