An haifi Hassana Abdullahi a garin Hunƙuyi a shekarar 1980. Tana zaune da maigidanta da yaransu a garin Hunƙuyi, Ƙaramar hukumar Kudan, jihar kaduna.
Ta yi karatun firamare, a central firamare school Hunƙuyi, daga nan sai ta wuce makarantar kwana ta ‘yammata da ke Kaduna (G.G.S.S KAWO KADUNA). Tana da takardar shaidar malanta ta (NCE). Inda take aiki da sashin ilimi na ƙaramar hukumar Kudan. Tana riƙe da muƙamin (Head mistress) shugabar malamai.
Haka kuma ɗaliba ce a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Inda take karatun digiri ɗinta a fannin library and information science. Sannan kuma, ita ce mataimakiyar Ameerah ta biyu(2) a ƙungiyar Muslims students’ society of Nigeria a Kaduna Area Unit, Maƙarfi /Kudan Area council. Haka kuma, ita ce mataimakiyar magatakardar ƙungiyar marubutan Arewa ta ƙasa Nijeriya (Arewa Writers Association of Nigeria).
Har wa yau, ta yi aiki tare da wata ƙungiya da ke tallafawa ‘ya’ya mata, don ci gaban karatunsu, wato adolescent girls iniative Center for Girls Education. Ta taɓa cin Gasar Rubuta ƙagaggun ƙananun labarai, wanda makarantar malam banbadiya tare da haɗin gwuiwar pleasant library and book club, Katsina suka shirya, inda ta zo ta biyu a labarinta mai taken “A SASANTA”
Ita marubuciyar littattafan Hausa ce, ta rubuta littattafai kusan ashirin, ga kaɗan daga cikin su:
1. Makircin Zuciya.
2. GSM Kururuwar Iblis.
3. Kinfin Kishiya.
4. Hangen Nesa.
5. Komai da Lokacinsa.
6. Mummunar ƙaddara.
7. Illar Kwaɗayi.
8. Tsananin Kiyayya.
9. Rashin Jituwa.
10. Dogon Buri.
11. Dubu Ta Cika.
12. Kin Yi Bajinta.
13. Ya Fi Dare Duhu.
14. Akwai Babbar Matsala.
15. Mizanin Hankali.
16. Ragayar Dutse .
Da sauran su.
(Mun samu waɗannan jawaban ne daga bakin Hassana Abdullahi Hunƙuyi ta hanyar rubutawa da ta yi ta turo min ta imel ɗina a ranar Lahadi 12/07/2020).
Don karanta larabci da yanda ya shigo ƙasar Hausa danna nan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu