Tarihin Marigayiya Hajiya Gude Mai Magani

0
25

An haifi hajiya Gude mai magani a Ƙofar Arewa gidan malam Tanko, ta yi aure a gidan malam Tanko, wanda aka yi haɗin zumunci da Yusha’u (wakili), hajiya Gude ta shahara wajen bayar da magani kowace cuta, wanda sai mutum ya tafi asibiti sun kasa sai a turo mutum wajen ta wanda da yardar Allah kuma sai ka ga an samu nasara.

Hajiya Gude tana aiki ne da aljanu wajen warkar da mutane cutar da take damunsu, wanda hakan kuma ya faru ne  bayan an ɗaura mata aure, wata rana tana daka da rana, sai kawai aka ga ta tsaya ƙyam tana  lallauyewa,  tana yin ƙasa, tana faɗuwa ƙasa sai kawai aka ga ta kasa tafiya, to tun daga ranar ƙafar ta ba ta sake miƙewa dai-dai ba har sai da ta rasu.

Idan an kai mace asibiti ɓangaran haihuwa, sai likitoci suka yi iya bakin ƙoƙarin su, amma kuma ba a samu nasara ba, sai a turo mace wajen ta, to da zarar ta dafa kan mace,  ta yi waɗansu addu’o’i haɗi da ba mace rubutu, sai kawai can sai a ga mace ta haihu lafiya. Haka kuma, idan mace ma tana da ciki suna zuwa wajenta domin karɓan magani.

Don karanta tarihin ranar demokraɗiyya a Najeriya danna nan

Bugu da ƙari kuma, akwai wani aljani wanda yake zuwa kanta wanda ake kiransa da suna “Ɗan malam”, wanda shi ne yake zuwa kanta duk ranar Laraba, wanda mutane da dama suna jin daɗin aikin ta, sannan  kuma idan mutum kayansa ya ɓace ko yana yin sata  ko dai wani abu mara kyau, to da zarar an kai mutum wajenta akan samu mafita.

Har ila yau, idan ta gama aikin, to kuɗin da ta samu a wannan ranar takan ɗauka ta raba wa yara, haka kuma akwai wani mutum ana kiransa da suna Magaji yana ɗaya daga cikin mutanen da suke yi mata rubutun sha, wanda take ɗebowa ta ba mara sa lafiya idan ta yi musu aiki.

Hajiya Gude mai magani ta shahara wajen bayar da magun-gunan gargajiya wajen warkar da marasa lafiya akan cututtaka daban-daban kamar su cutar Aljanu da cutar jiki (Ciwon kai, ciwon ciki, ciwon baya, ciwon ƙafa, ciwon ƙirji, rashin haihuwa da kuma maganin naƙuda), ta rasu a shekara ta 2012 ta bar ‘ya’ya guda huɗu daga ciknsu akwai Maryam (Dogara) da Abdullahi da Mustapha (muɗɗafa) da kuma Balaraba.

Danna nan don karanta maganin damuwa

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceTarihin Hassana Abdullahi Hunƙuyi
Labarin na GabaTarihin Marigayi Alaramma Suraj Yunus Kudan