Ƙamus

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Jami’i - Ma'aikaci, musamman na  gwamnati ko wata masana'anta da ya samu  horo
Janairu - Watan farko ne a shekara. Misali; Bikin sabuwar shekara na kasancewa a ranar ɗaya ga watan Janairu. ENG; January (A turance yana nufin watan farko a shekara)  
January - A turance yana nufin watan farko a shekara. Misali; Bikin sabuwar shekara na kasancewa a ranar ɗaya ga watan Janairu. HAU; Janairu (Watan farko ne a shekara)  
Joint Admission & Matriculation Board (JAMB) - Hukumar Jarabawar Shiga Jami'a
Joint Health Sector Union (JOHESU) - Kadaurar Ƙungiyoyin Malaman Lafiya
Joint Task Force (JTF) - Rundunar Hadin Guiwa
Judiciary Staff Union of Nigeria (JUSUN) - Ƙungiyar Jami'an ma'aikatar Shari'a Ta Najeriya
July - A turance yana nufin wata na bakwai a shekara. Misali; A watan Yuli zai cika shekara biyar da gama makaranta. HAU; Yuli (Wata ne na bakwai a shekara)
Juma’a - Rana ce ta biyar a ranakun mako.  Misali; Yara na ɗokin zuwa masallaci ranar Juma'a. ENG; Friday (A turance tana nufin rana ta biyar a mako)
June - A turance wata ne na shida a shekara. Misali; Damina na kankama a watan Yuni. HAU; Yuni (Wata na shida a shekara)