Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

- A turance tana nufin cifjoji. Misali; Ai wanda ya yi mana shari'ar cifjoji ne, kuma ya kwatanta adalci. HAU; Cifjoji (Tana nufin alƙalin alƙalai)
A fragrant herb - A turance tana nufin ɗaɗɗoya. Misali; An yi amfani da ganyen ɗaɗɗoya wajen haɗa maganin. HAU; Ɗaɗɗoya (Tana nufin wani ganye mai ƙamshi wanda ake magani da shi)
A large edible toad - A turance tana nufin bududdugi. Misali; Matasan na gasa bududdugi a dandali. HAU; Bududdugi (Tana nufin ƙaton kwaɗo wanda ake iya ci)
A less favoured wife - A turance tana nufin bora. Misali; Lami bora ce a gidan Alhaji Mato. HAU; Bora (Tana nufin matar da ba ta da cikakken gata a gurin mijinta)
A moment ago - A turance tana nufin ɗazu. Misali; Ɗazu na dawo daga gidan bikin. HAU; Ɗazu (Tana nufin lokacin da be daɗe da wucewa ba) Kishiyarsa; Yanzu
A traditional title - A turance tana nufin galadima. Misali; An naɗa malam Sani galadima jiya da safe. HAU; Galadima (Tana nufin muƙamin sarauta)
Abarba - Abarba na ɗaya daga cikin kayan marmari mai zaƙi, tana da amfani sosai a jikin ɗan adam. Jam'i : Abarba
Ability to endure hardship or pain - A turance tana nufin dauriya. Misali; Tanko yana da dauriya. HAU: Dauriya (Tana nufin juriya)
Abinci - Yana nufin duk abinda za a ci ya kawar da yunwa. Misali; Muna cin abinci sau uku a rana. ENG; Food/Meal (A turance yana nufin abinci)
Abuja Geographic Information System (AGIS) - Hukumar Tsara mahalli Ta Abuja
1 2 3 201