Tag: yadda ake

  • Manufar Makokin Husaini Da ‘Yan Shi’a Suke Yi

    Manufar Makokin Husaini Da ‘Yan Shi’a Suke Yi

    Baƙin ciki da kururuwa da koke-koke da dukan jiki da waƙe-waƙen ta’aziyyar wanda yake kaiwa ga zagin magabata da la’antar su alhali ba su ji ba ba su gani ba; da karanta labaran kashe Husaini wanda yawancinsa ƙarya ne; manufar masu yin haka ita ce haddasa gaba da rarraba kawunan al’umma.

    Saboda yin hakan ba wajibi ba ne, ba mustahabbi ba ne; kai ƙirƙirar raki da baƙin ciki ga musibun da suka wuce babban abu ne da Allah da Manzo suka hana”

    Domin karanta cikakken bayani a kan Maganganu Na Ƙarya A kan Kashe Husaini danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Azumin Watan Muharram danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A Kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Taƙaitaccen Tarihin Ibrahim Yaro Yahaya (1944–1995)

    Taƙaitaccen Tarihin Ibrahim Yaro Yahaya (1944–1995)

    Ibrahim Yaro Yahaya ya kasance mashahurin masani marubuci a fannin harshen Hausa. Yahaya ya bayar da gudunmawa wajen rubuta litattafai a ɓangaren harshe da adabin Hausa.

    Rayuwa Da Ilimin Ibrahim Yaro Yahaya.

    An haifi Ibrahim Yaro Yahaya a shekarar 1944. Ya yi karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano, inda ya ƙware a fannin Hausa da adabin gargajiya. Ya kasance malami a Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya (Centre for the Study of Nigerian Languages) a Jami’ar Bayero, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen koyarwa da bincike kan harshen Hausa da adabinsa.

    Yahaya ya rubuta littattafai da dama da suka taimaka wajen bunƙasa ilimin Hausa, kaɗan daga ciki sun haɗa da:

    Ga jerin wasu daga cikin litattafan da Ibrahim Yaro Yahaya ya rubuta, waɗanda suka shahara a fannin harshen Hausa da adabinsa:

    1. “Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa” (1988)
    Wannan littafi yana bayani kan tarihin rubuce-rubuce cikin harshen Hausa, tare da jerin littattafan da aka wallafa daga 1930 zuwa 1980.

    2. “Labarun Gargajiya”
    Wannan littafi ya ƙunshi tatsuniyoyi na gargajiya da ke koyar da darussa da nishaɗi.

    3. “Da Koyo A Kan Iya” (1975)
    Littafi na uku a jerin karatun Hausa, wanda aka wallafa a 1975.

    4. Tatsuniyoyi da Wasanni: Littafi na Shida
    Wannan littafi ya ƙunshi tatsuniyoyi da wasannin gargajiya na Hausa.

    5. “Sunayen Hausawa na Gargajiya da Ire-Iren Abincin Hausawa” (1979)
    Littafi da ke bayani kan sunayen gargajiya da nau’o’in abincin Hausawa.

    6. “Jagoran Nazarin Hausa: Don Makarantu”
    Littafi da ke taimakawa wajen koyar da harshen Hausa a makarantu.

    7. “Darussan Hausa: Don Manyan Makarantun Sakandare: Littafi na Ɗaya”
    Littafi na farko a jerin darussa na Hausa don manyan makarantu.

    8. “Darussan Hausa: Don Manyan Makarantun Sakandare: Littafi na Biyu” (1996)
    Waɗannan su ne wasu daga cikin litattafan da Yahaya ya wallafa.

    A matsayinsa na malami da marubuci, Yahaya ya kasance ginshiƙi wajen bunƙasa harshen Hausa da adabinsa. Ya kuma taka rawa wajen shirya tarukan ƙasa da ƙasa kan harshen Hausa, kamar taron farko na ƙasa da ƙasa kan Hausa da adabinta da aka gudanar a Jami’ar Bayero a shekarar 1978.

    Ya rasu a shekarar 1995, amma har yanzu ana jin tasirinsa a fannin Hausa da adabin gargajiya.
    Muna roƙon Allah Ya gafarta masa amin.

    Don karanta Kafar Sadarwa Amfani Da Ƙalubalenta danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Zaurancen ‘Yan Maye

    Zaurancen ‘Yan Maye

    Zaurancen ‘yan maye wasu kalamai ne da ‘yan maye suke amfani da su a tsakaninsu. Sau da yawa wasu mutane masu yin sana’a ko kasuwanci ko aiki ko ma ɗalibai suna da wasu kalamai da suke amfani da su don su ɓatar da bami (mutum) daga gane manufarsu. Ba kuma mai ganewa sai su ko kuma wanda ya zauna da su ko aka gaya masa shi ne zai gane abin da suke nufi da irin waɗannan kalamai.

    Su ma ‘yan maye suna da wasu kalamai da suke yi a tsakaninsu wanda kusan su kaɗai suke sanin ma’anar abubuwan da suke nufi sai kuma wanda aka yi wa bayani ya fahimta ne kawai yake iya gane manufarsu. Yawancin wannan zaurance shi ma wata alama ce ta buguwa da gushewar hankali da rashin gaskiya da aikata laifi wanda ke da alaka da illolin shaye-shaye. Ga wasu daga ciki kamar haka:

    • Za mu je dubun nahiya (wurin shan kayan maye kenan)
    • Muna cikin dubun aiki (an shawo ƙwaya kenan)
    • Mun murɗe masa kai (murfin kwalbar abin da suka sha )
    • Mun hau network (kai ya ɗauki caji kenan)
    • Mu je zubi (za a je shan ƙwaya ke nan)
    • Mun je madiri (suna cikin maye kenan)
    • Muna so mu yi slow (ana so a yi maye kenan)
    • Za mu kara wa sama hazo (za a sha wiwi ko taba)
    • Buguwa ma sai a can (wato buguwa sai a lahira)
    • Haɗin da ba duk kai ba (a haɗa ƙwayoyi da maganin mura iri daban-daban)
    • A sha komai (ma’ana ba su bar kowane abin maye ba)
    • Yaya ruwa? (ba za a sha ba ne yau?)
    • Weza (weather) ta ba da haɗin kai (yanayin gari ya yi daɗi kenan)
    • Aiki to, aiki kurum (wato in ba a sha ba a sha)
    • Akwai gem, za a fasa eriya (za a je wata matattara inda manyan gayu suke haɗ uwa don yin shaye-shaye).

    Don karanta Waƙar Shan Ƙwaya ta Alhaji Dr Adamu Ɗanmaraya, Jos danna nan

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Rataye na 3: Waƙar Shan Ƙwaya ta Alhaji Dr Adamu Ɗanmaraya, Jos

    Rataye na 3: Waƙar Shan Ƙwaya ta Alhaji Dr Adamu Ɗanmaraya, Jos

    To kar a sha ƙwaya,

    Ƙwaya ko ba ta da kya,

    Jama’a ku saurara.

    To kar a sha ƙwaya,

    Ƙwaya ko ba ta da kya,

    Dubban mutanen gida,

    Daji suna zance,

    “Ƙwaya ko ba ta da kyau”,

    To kar a sha ƙwaya,

    To kar a sha ƙwaya,

     

    Kakanka ba ya sha,

    Babanka ba ya sha,

    Me ya kai ka shan ƙwaya?

    To kar a sha ƙwaya,

    Ƙwaya ko ba ta da kyau,

    Matarka ba ta sha,

    Mamarka ba ta sha,

    ‘Ya’yanka ba ya sha,

    Me ya kai ka shan ƙwaya?,

    To kar a sha ƙwaya,

     

    Ƙwaya fa ba ta da kyau,

    Ta kan sa a lalace,

    Ƙwaya fa ba ta da kyau,

    Ta kan sa a lalace,

    Ƙwaya ku saurara,

    Ƙwaya ku bar sha dai,

    Ƙwaya fa ba ta da kyau,

    Don Allah ku saurara,

    To kar a sha ƙwaya,

    To kar a sha ƙwaya,

    Kwaya fa ba ta da kyau,
    Jama’a ku saurara,

     

    Ƙwaya ku bar….

    To tun ba na sha,

    Wani nawa ba ya sha

    To kar a sha ƙwaya,

    Ƙwaya fa ba ta da kyau,

    Jama’a ku saurara,

    Kakanku ba ya sha,

    Kakarka ba ta sha,

    Me ya sa ka sha ƙwaya?

    Ƙwaya!

    Ƙwaya!

    Na tsine ‘yan ƙwaya,

    Na la’anci ‘yan ƙwaya,

    Ƙwaya fa ba ta da kyau,

    Jama’a a saurara

    Na la’anci ‘yan ƙwaya,

    Na tsine ‘yan ƙwaya,

    Jama’a a bar sha dai,

    Wallai ba ta da kyau,

    Wallahi ba ta da kyau.

     

    Don karanta Waƙar Hana Shan Ƙwaya da Sauran Kayan Maye danna nan

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Rataye na 2: Waƙar Hana Shan Ƙwaya da Sauran Kayan Maye Ta Marigayi Abdullahi Sani Makarantar Lungu

    Rataye na 2: Waƙar Hana Shan Ƙwaya da Sauran Kayan Maye Ta Marigayi Abdullahi Sani Makarantar Lungu

    Kuma babu ƙarfi wajen mai shan ta ni na faɗi,

    Domin jininsa takan tsotse ya bar tafiya.

    Bacci kwa in har ya kwanta sai ya kai mako,

    Ba wanda zai ce da kai ya gan shi ya juya.

     

    Aiki fa ja a gaban mu a taimaka jama’a,

    Don alhaki ne wuyan kowanmu kar mu ƙiya

    Gyaran ƙasa dole sai an kau da shashanci,

    Sannan fa duk ci gaban jama’a ya zam tafiya

     

    A ɗau matakin da za a ga babu kwaya sam,

    Domin mu tsere ta kaicon rayuwar duniya.

    A hukunta mai sha da mai saida ta kar a raba,                                                              Laifinsu ya yi kama da fashi a Nijeriya.

     

    Burinmu ya bar cika in har ba mi azama,

    Mun kau da ƙwaya ba ƙarshe za mu sha kunya.

    Wannan masifar fa ba birni kawai ta tsaya,

    Har ƙauyuka ta gama duk ‘yan uwa ku jiya.

     

    A wajen manoma akan ce wai da sun sha ta,

    Wai sai su kwana suna aiki fa ba gajiya.

    In masu neman karatu sunka je gunsu,

    Wai sai su ce maganin niyya fa kar ku ƙiya.

     

    In ban da ƙarya ina wani maganin niyya,

    Da za ya sanya ƙwaƙwalwa har ta zama tawaya

    In na tuno lamarin kan ba ni mamaki,

    Hanyar da za a bi gyaran nan ya zam tafiya.

     

    Ƙwaya takan ɓata dukkan rayuwar jama’a,

    In har aka yi sakaci ba a tashi an aniya.

    In har ana so ƙasa ta zamo cikin tsari,

    Sai an kawar da abin maye da sa tawaya.

     

    Wasu sanya ƙwaya suke randa ta kan hanya,

    Jama’a ku gane da makircinsu kar ku biya.

    Duk ci gabanmu suke nema ya salwanta,

    Don tun da farko fa su ba su samu tarbiyya.

     

    Kuma har da mata a wannan kar ku ce ƙari,

    Da masu aiki da kwaya babu wai ku jiya.

    A gidan biki ko ko suna sai a same ta,

    A cikin ruwa ko kunun zaƙi da za a biya.

     

    Wallahi duk wanda ya ba ɗan uwansa guba,

    Ya sani haƙiƙa Ta’ala zai yi sakayya.

    Duk mai nufin cutatar da waninsa ya wahala,

    Shi zai ga cuta a kansa fa babu wai ku jiya

     

    Duk ɗan ƙasa nagari burinsa ai kirki,

    Ba za ya so ‘yan uwansa cikin rashin shiriya.

    A kiyayi ƙwaya da ganye kar a raɓe su,

    In dai da son a ji daɗin rayuwar duniya.

     

    In anka ce hankali kuma ya gushe babu,

    Ai rayuwa ba ta amfani a nan ku jiya.

    Komai muƙamin mutum wa za ya raɓe shi?

    Domin kwa ya cusa kansa a surƙuƙi da ƙaya.

     

    Na bayyana muku kwayar nan fa cuta ce,

    Domin takan hana barci har ido ya tsaya.

    In babu barci ko tilas hankali ya gushe,

    Domin ƙwaƙwalwar mutum ta ɓaci ta tawaya.

     

    Daga nan mutum sai ya hau yawon da ba gaira,

    Bare dalilin da za a ji tausayi a biya.

    Sai zantuka marasa kai babu gindinsu,

    Ƙwaya fa ta fara narkewa a nan ku jiya.

     

    Kuma sai ya zauna ba zai wanka bare wanki,

    Suma da annakiya sun san gurin ɓuya.

    Sai tsince-tsince a bola ko cikin kwatami,

    Tsumma a gunsa kwa ya wuce ai ta jayayya.

     

    Ai ba batun wani jin daɗi a kan wannan,

    Sai jefa kai a tsiya da barin abin kunya.

    Wa zai ga wannan ya nuna har yana sha’awa?

    Sai dai a nemi tsari da halin maƙi shirya.

     

    Domin karanta Rataye Na 1: Waƙar ‘Yar Maye Ta Ahmad Tijjani Gandu danna nan

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Rataye Na 1: Waƙar ‘Yar Maye Ta Ahmad Tijjani Gandu

    Rataye Na 1: Waƙar ‘Yar Maye Ta Ahmad Tijjani Gandu

    Ahmad Tijjani Gandu

    ‘Yar Maye ‘yar maye,

    ‘Yar maye ya kamata ki bar shaye-shaye, Shaye-shaye, Ya kamata ki bar shaye-shaye.

    Amshi

    ‘Yar uwa ki lazumci karamci kada ki sa ni na zub da hawaye,

    Ta zamo, mai kayan maye mujiya a cikinsu ƙawaye.

    Namiji

    Ni kalar ki tana burge ni,

    Kina da kyau a cikin mataye,

    Nai zaton ki kina da mutunci,

    Sai na gan ki kina shaye-shaye,

    Ga shi ƙauna ta kuma kullu,

    Ƙafa jikinmu zuwa hannaye,

    Da ina murna na dace,

    Ga shi yanzu ina ta hawaye.

    Mace

    Dakata ka ji labarina,

    Na kasance ‘yar shaye-shaye.

    Kuma iyayena sun nunan,

    Tarbiyyarsu da kyan halaye.

    Yau da gobe a kwana a tashi,

    Saurayi ya kira ni kiranye.

    Shi ya ce na raka shi wurin party,

    Can na tadda dukan ‘yan maye.

    Namiji

    Na ji zancan yai mini muni,

    Duk da dai na so ki a ɓoye.

    Yanzu ne na fito in gaya maki,

    ‘Yar’uwa buɗe kunnaye.

    Shi halin da kike kai yanzu,

    Bai da kyau a cikin sunaye.

    Shawara ce yau zan ba ki,

    Ya kamata ki bar shaye-shaye.

    Mace

    Ni fa zancena a taƙaice,

    Ba na so ka gaya wa ƙawaye.

    In kana so mu yi soyayya,

    Za mu yi amma fa a ɓoye.

    Ga waya ta sai ka buga mini,

    Za ka ganni ina nanaye,

    Kar ka damu ka bi ni masoyi,

    Kar ka ce in bar Shaye-shaye

    Amshi

    ‘Yar Maye ‘yar maye,

    ‘Yar maye ya kamata ki bar shaye-shaye, Shaye-shaye, Ya kamata ki bar shaye-shaye.

    Namiji

    Hafsa ke na riƙa zan aura,

    Taimake ni ki bar shaye-shaye.

    Kuma ki tuba zuwa Allahu,

    Yai maza shi yai mataye,

    Hailala da Salati sannan,
    Tarbiyya ki yowa iyaye.

    Kuma ki kamu da istigifari,

    Ba ƙawa da dukan ‘yan maye.

    Mace

    So da ƙauna ta kama ni,

    Ɗan uwa mai kyan halaye.

    Tarbiyyarka tana burge ni,

    Kai daban da zubin wawaye.

    Ko ina na yi sai a gaya min,

    An gan ka kana ta hawaye.

    Mai kake so in maka sahibi,

    Ba ni son ka da zubda hawaye.

     

    Na bi na ɗauka kuma ɗan uwa,

    Karɓi wannan share hawaye.

    Ga jikina har ya canja,

    Nai daban a cikin mataye.

    Da ana ta kira na Hafsat,

    Yanzu na koma ‘yar maye.

    Na shiga uku wayyo Allah,

    Dan’uwa saitan halaye.

    Namiji

    Hafsa ɗan natsu kadda ki damu,

    Rabbi zai yafe halaye,

    Tun da dai kin daina babu ji,

    Yau ido ya daina hawaye,

    Godiya gun Sarkin Allah,

    Shi ya gyara dukan halaye,

    Mu yi zaman aure da mutunci,

    Mun shigo hanyar angwaye.

    Danna nan don karanta Illolin Shaye-Shaye

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Kumburin Mahaifa Mai Sanya Zubar Jini (ENDOMETRITIS)

    Kumburin Mahaifa Mai Sanya Zubar Jini (ENDOMETRITIS)

    Endometritis kumburin bangon mahaifa ne (endometrium) wanda yake haddasa zubar jini daga gaban mace. Zai iya kasancewa mai tsanani amma ba ya ɗaukar dogon lokaci (acute). Haka nan zai iya zamowa mai tsanani kuma mai ɗaukar dogon lokaci (chronic). Mafi yawanci ƙwayoyin cutar bacteria ne suke kawo shi, musamman waɗanda suke kama al’aurar mace bayan ta haihu, ko kuma a lokacin da ake yi mata aikin tiyata a mahaifa ko mara.

    Bincike ya tabbatar da cewa manyan dalilai masu kawo endometritis su ne:

    1. Haihuwa (childbirth): Idan ƙwayoyin cutar bacteria suka shiga cikin mahaifa a lokacin da mace take yin naƙudar haihuwa, to, za su iya haddasa mata matsalar endometritis, musamman idan ta yi doguwar naƙuda (prolonged labour), ko yagewar jakar ruwan mahaifa (amniotic sac rapture), ko yawan duba mata buɗewar farjinta (multiple vaginal examination-VE).

    2. Aikin tiyatar cire jariri (caesarian section-CS): Matan da aka yi wa tiyatar CS sun fi kowa hatsarin kamuwa da endometritis, duk da kasancewar kayan aikin da kuma ɗakin tiyatar masu matuƙar tsabta ne. Hakan yana da nasaba da tsanin yawa, naci, da kankantar bacteria ɗin ne.

    3. Ayyukan tiyatar da suka shafi farji da marar mace (gynaecological procedures): Waɗannan sun ƙunshi wankin ciki (dilation and evacuation), aikin duba mahaifa (hysteroscopy), ɗaukar wani abu daga cikin mahaifa domin yin awon wata cuta (endometrial biopsy). Ƙwayoyin cutar bacteria za su iya shigar mahaifa a lokacin waɗannan ayyukan.

    4. Cututtukan da ake ɗauka a wajen jima’i (sexually transmitted diseases – STDs): Waɗannan sun ƙunshi chlamydia, gonorrhea, staphylococcus, da sauransu. Duk suna iya haifar da endometritis idan suka shiga mahaifa.

    ALAMUNSA (SYMPTOMS)

    Alamun endometritis su ne:

    1. Zubar ruwan da mace ba ta saba gani ba daga gabanta (abnormal vaginal discharge): Ruwan zai iya kasancewa mai wari ko ƙarni, sa’annan mai launin ruwan ƙwai (yellowish) ko ruwan ganye (greenish).

    2. Ciwon mara (pelvic pain): Mace mai matsalar endometritis za ta riƙa fuskantar ciwon mara mai tsanani, ko dai mai daɗewa bai bari ba ko kuma mai zuwa ya tafi.

    3. Zazzaɓi da jin sanyi (fever and chills): Shi ma zai iya zamowa mai tsanani, sa’annan mai zuwa ya tafi ko mai daɗewa.

    4. Jin zafin fitsari ko yawan yin fitsari (dysuria or polyuria): Shi ma zai iya zama mai zuwa ya tafi ko mai daɗewa.

    5. Zubar jini mai yawa lokacin al’ada ko rashin tsayayyar al’ada (heavy or irregular menstrual bleeding): Shi ma zai iya zama mai zuwa ya tafi ko kuma mai daɗewa.

    TASIRINSA A JIKIN MACE (EFFECTS)

    Idan ba a magance endometritis ba, zai iya haifar da:

    1. Rashin haihuwa (infertility): Hakan zai faru ne sakamakon raunana da kuma lalata halittun mara na haihuwa.

    2. Taruwar ruwan gunya a cikin mara (pelvic absess): Zai iya haifar da gyambo mai tara ruwan gunya a cikin mahaifa.

    3. Kumburin dukkan jiki (sepsis): Hakan zai iya faruwa ne sakamakon yaɗuwar ƙwayoyin cuta a dukkan sassan jiki ta hanyar jijiyoyin jini.

    HANYOYIN RIGAKAFI (PREVENTION)

    Za a iya rigakafin kamuwa da endometritis ta hanyar:

    1. Inganta tsabta a lokacin karɓar haihuwa, da lokacin yin tiyatar mahaifa a marar mace, domin kaucewa yaɗuwar ƙwayoyin cuta.

    2. Tsabtace kayan ayyukan tiyata yadda ya kamata.

    3. Tabbatar da cewa ma’aurata ba su ɗauke da cututtukan da ake ɗauka a wajen jima’i.

    MAGANI (TREATMENT)

    Hanyar magance endometritis ita ce zuwa asibiti domin likita ya yi aune-aune kuma ya ɗora mace a kan maganin antibiotics da ya dace. Idan abin ya ta’azzara, to, sai an kwantar da ita.

    Don karanta Halin Da Ake Ciki Yanzu Dangane Da Allurar Tazarar Haihuwa Ga Maza danna nan
    Edita@rumasau-kallamu

  • Halin Da Ake Ciki Yanzu Dangane Da Allurar Tazarar Haihuwa Ga Maza (CURRENT STATUS OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

    Halin Da Ake Ciki Yanzu Dangane Da Allurar Tazarar Haihuwa Ga Maza (CURRENT STATUS OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

    Akwai jita-jitar cewa an kammala gwaji ko kuma ana kan hanya wajen samar da allurar hana haihuwa ga maza. Wannan gaskiya ne cewa ana gudanar da bincike, amma har yanzu babu wata allura da aka amince da ita a duniya domin yin tazarar haihuwa ga maza.

    Wasu daga cikin alluran da aka fi duba yiwuwar yin amfani da su, sun haɗa da:

    1. Reversible Inhibition of Sperm Under Guidance (RISUG) a Indiya, wacce ta ƙunshi ɗura ruwan magani mai maiƙo a cikin bututun ajiyar maniyyi (injecting gel into vas deferens). Amma har yanzu wannan dabarar ba ta samu amincewa daga hukumomin lafiya na duniya ba.

    2. Allurar sinadarin testosterone da progestin wacce take hana samar da ruwa da ‘ya’yan maniyyi. A shekarar 2016, wani bincike na hukumar kula da lafiya ta duniya (World Health Organization – WHO) ya dakatar da yin wannan gwajin saboda zai haifar illolin da suka haɗa da fushi, baƙin ciki, taɓin hankali, da matsalar ƙarancin sha’awa ga maza, illolin da suka fi na alluran tazarar haihuwa na mata muni.

    MATAKAN SAMAR DA MAGANI (STAGES OF DRUG DEVELOPMENT)

    Domin fahimtar dalilin da yasa ba a samu nasarar fitar da alluran tazarar haihuwa na maza ba, ya kamata a fahimci matakai guda shida waɗanda ake bi kafin a ƙirƙiro magani har ya fita kasuwa:

    1. Gwajin yin amfani da maganin a cikin ɗakin gwaje-gwajen kimiyya da dabba (discovery and preclinical lab testing using guinea pigs) – Ana yin sa ne don a fahimci ingancinsa da yadda yake aiki, amma a jikin dabba.

    2. Gwaji a mataki na farko (Phase I Trials) – A jikin mutane kaɗan, wato marasa yawa, don tabbatar da ingancinsa a kan lafiyar mutanen.

    3. Gwaji a mataki na biyu (Phase II Trials) – Ana yin gwajin ne ga mutane masu buƙata don a duba inganci da illolinsa a jikinsu.

    4. Gwaji a mataki na uku (Phase III Trials) – Gwaji mai faɗi ta hanyar ƙara yawan jama’ar da za a yi gwajin a kansu don tantance amfanin maganin da illolinsa a jikinsu.

    5. Amincewa daga hukumomin lafiya (Regulatory review and approval) – Hukumomi, kamar NAFDAC a Nigeria ko FDA a America, za su bayar da sanarwar amincewa da maganin a hukumance, domin mutane su cigaba da yin amfani da shi.

    6. Bibiya bayan an fara amfani da maganin (Post marketing surveillance) – Don cigaba da sa ido a kan illolinsa.

    Yawancin alluran tazarar haihuwa na maza da ake ƙoƙarin ƙirƙirowa suna kasa samun nasarar gwajin ne tun a mataki na biyu ko na uku saboda mummunan sakamakon da suke nunawa ga lafiyar maza, ko rashin daidaiton sakamakon (inconsistent test results).

    DALILIN DA YASA ALLURAN TAZARAR HAIHUWA NA MATA SUKA FI DACEWA DA JIKIN MATAN (REASONS THAT FEMALE INJECTABLE.CONTRACEPTIVES REMAIN MORE SUITABLE)

    1. Jikin mace ya fi sauƙin sarrafa sinadaran estrogen da progesterone, saboda tsarin al’ada na halittar jikin mace yana aiki da sinadaran estrogen da progesterone ɗin ne, wanda ake iya kwaikwayon su cikin sauƙi da magunguna. Allurar tazarar haihuwa ta mata tana hana mace yin ovulation cikin sauƙi da aminci, kuma illolinta sun daɗe ana yin nazari a kansu, kuma ana iya sarrafa su.

    2. A jikin namiji kuwa, ana samar da miliyoyin ‘ya’yan maniyyi a kullum, waɗanda in har za a yi amfani da allurai na tazarar haihuwa domin rage yawansu, to, hakan yana nufin sai dai a dakatar da samar da su gaba ɗaya, wannan abu ne mai wahala da hatsari.

    ILLOLIN DA ZA SU IYA BIYO BAYAN AMFANI DA ALLURAN TAZARAR HAIHUWA GA NAMIJI (POTENTIAL REGRETS AND CONSEQUENCES OF MALE INJECTABLE CONTRACEPTIVES)

    Idan aka gaggauta yin amfani da su ba tare da yin cikakken bincike ba, to, ana iya fuskantar matsaloli kamar:

    1. Matsalar rashin haihuwa ta dindindin (permanent infertility) – Saboda hana samar da ‘ya’yan maniyyi na dogon lokaci yana iya lalata ƙwayar haihuwa har abada.

    2. Taɓarɓarewar hankali da rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai (mood disorders and hormonal imbalances) – Hakan yana iya haddasa damuwa, fushi da cututtukan zuciya.

    3. Ƙarin hatsari ga dangantakar aure – Mace tana iya ɗaukan cewa an ɗauki matakin hana haihuwa alhali namiji yana fama da illoli ko ya manta. Daga nan sai ciki ya samu ba tare da an shirya masa ba.

    Wani bincike da aka wallafa a “The Journal of Clinical Endocrinology & Metabolism” ya nuna cewa yin amfani da sinadaran testosterone da progestin yana iya aikin samar da tazarar haihuwa ga maza, amma yana haddasa hawan jini, lalacewar hanta, da hauhawar kitse (cholesterol).

    SHAWARA GA YAN’UWANA MATA

    Ya kamata mu kasance cikin shiri da fahimta. Duk da cewa alhakin yin tazarar haihuwa ya rataya ga maza suma, yana da muhimmanci mu san cewa jikin mace ne yafi dacewa da irin waɗannan magunguna, tunda an ɗauki dogon lokaci ana yin nazarin su kuma an riga an tabbatar da ingancinsu.

    Idan aka gaggauta yin amfani da alluran tazarar haihuwa na maza ba tare da cikakken bincike da tabbatar da ingancinsu ba, to, duniya za ta yi nadama kamar yadda aka yi da wasu magunguna a tarihi.

    Har zuwa lokacin da aka samu cikakken gwaji da tabbatar da ingancinsu, alluran tazarar haihuwa na mata su ne mafi aminci da sahihanci.

    Danna nan don karanta Rashin Kawowar Mace A Lokacin Jima’i (ANORGASMIA)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Illolin Shaye-Shaye

    Illolin Shaye-Shaye

    Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi suna da illoli masu ɗimbin yawa ga mashayansu. Wasu daga cikin waɗanṇan illoli kan shafi dangin mashayan da ma al’umma baki ɗaya. Masu shan ƙwayoyi ko kayan da suke sa su maye suna fuskantar matsaloli iri-iri. Misalin wasu daga ciki su ne:

    • Rashin tsayar da ibada (Bauta wa Allah)
    • Gushewar hankali
    • Ɗaukar cututtuka
    • Shiga mummunan hali
    • Mummunar kama
    • Aukar da fyaɗe
    • Shiga haɗari
    • Yin sata
    • Yin fashi
    • Kura daga makaranta
    • Rasa aiki
    • Shiga ƙungiyoyin asiri
    • Rasa rayuwa
    • Yawan haɗura a kan abubuwan hawa
    • Mutuwar fuju’a (mutuwar fad-daya)
    • Mutuwar aure da sauransu.

    In muka ɗauki batun mutuwar aure da shaye-shayen abubuwan sa maye suke haifarwa, za mu tabbatar da hakan babbar illa ce in muka karanta waɗannan labarai guda biyu da suka faru a wasu gidajen ma’aurata:

    1. Wata matar aure ce wadda take shaye-shaye amma mijinta bai sani ba, kullum sai ta sha wani magani ta yi ta barci, amma shi mijinta bai gane ba cewa maganin maye ne, kullum ya same ta tana barci sai ta ce ai mura ce ta yi mata babban kamu. In kuma ya ce a kai ta asibiti sai ta ce a a, ai tana samun sauƙi, ko kuma ta ce ai likitoci ne suke cewa mai mura ya dinga samun barci shi ne maganin mura.

    Da abu ya yi nisa miji ya ga barci ya ƙi ƙarewa, sai ya fara damuwa. Da dubu ta cika sai wata rana dalili ya kai shi duba ƙarƙashin kujeru, nan fa ya ga tarin maganin mura da tari turmis, a ranar ne  ya gane cewa maganin nan ba don mura take sha ba, dọn maye kawai take shan sa.

    Da aka matsa bincike sai da aka gano wasu kwalaye da kwalabe a cikin ma’ajiyar tufafinsu. Ana cikin haka kuma sai mai kantin sayar da magani na unguwarsu ya turo a ba shi kuɗin maganin da matar take aikawa tana karɓowa bashi. Wannan shaye-shaye ne sanadiyyar mutuwar auren.

    2. Shi kuma wani ango da aka yi masa rufa-rufa ya auri ‘yar maye, kullum gidansa cike da ‘yan mata, kuma abin da ke kawo su shi ne su haɗu da amaryar su yi ta shaye- shayen ƙwayoyi da magungunan mura da tari da kuma tabar wiwi.

    Kuma har faɗa ake yi a gidan nasa, wanda haka ya dami maƙobtansa suka gaya masa, shi kuma ya cewa matarsa ba ya son wannan tara ƙawaye da take yi. Kai abu dai ya ƙi daɗi kullum tashin hankali shi da matar, har dai aure ya rabu, an zo kwashe kaya ya ga kwalaben magungunan mura da na tari da kwalayen magunguna sun kai guda ɗari uku.

    Bayan haka kuma, wasu daga cikin fasiƙai mata ko maza suna amfani da ire-iren waɗannan magunguna wajen juyar da hankalin ‘yan mata don su yi lalata da su, wato su yi zina da su ko maɗigo, ko masu yin luwaɗi su yi da su, musamman idan sun neme su cikin girma da arziki suka ƙi yarda, to sai su yi amfani da waɗannan magunguna a cikin lemo ko wani abin sha, da zarar sun sha, shi ke nan sai su sami damar yin abin da suke son yi da su.

    Don karanta Wasu Wuraren da Aka fi Koyon Shan Kayan Maye danna nan

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Wasu Wuraren da Aka fi Koyon Shan Kayan Maye

    Wasu Wuraren da Aka fi Koyon Shan Kayan Maye

    Wasu daga cikin masu sha da kuma waɗanda suke zaune da masu shan ƙwayoyin, musamman mata, sun bayyana an fi koyon waɗannan shaye-shaye a waɗannan wurare:

    • Wajen liyafa (party) wato taron mata da maza a wajen biki
    • Zuwa kwana gidan ƙawaye masu shaye-shaye
    • Zuwa wajen zaman ‘yan daba
    • Wuraren kallon wasanni
    • Zama direban ‘yan maye (a bisa hanya yayin tafiya cikin adaidaita-Sahu ko akan babur Acaɓa
    • Zaman makarantun kwana, a sakandare ko gaba da sakandire, kamar jami’o’i da manyan kwalejoji da cuɗanya da ɗalibai masu shaye-shaye a makarantar, a gida Nijeriya da kuma a ƙasashen waje
    • Gidajen biki ko suna
    • Ƙananan da manyan otal-otal
    • Filin dambe
    • Gidajin wasannin kwaikwayo na daɓe da gala
    • Wuraren da ake yin sababbin gine-gine (kangwaye)
    • Tashoshin mota
    • Wuraren masu gyaran motoci da Babura
    • Gidajen saukar baki
    • Sababbin gidaje da ke wajen gari da sauransu

    Domin karanta Hanyoyin Ta’ammali Da Kayan Maye danna nan

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu