Tag: waka

  • Musa Ɗanƙwairo A Koyo Da Biyayyar Waƙa

    Musa Ɗanƙwairo A Koyo Da Biyayyar Waƙa

    Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya tashi, ya girma a gidansu; ya tarar da ana harka ta kiɗa da waƙa. Magabatansa tun daga Kaka Maiganga da mahaifinsa dukkansu makaɗa ne na noma; da yaƙi da kuma Sarauta da suka aiwatar da kiɗa da farar ganga da kuma gangar kotso.

    A bisa ɗabi’a ta gadon gida, mutum zai koyi abin da ya tarar ana gudanarwa a gidansu. Hausawa sukan ce, gadon gida alala ga rago, a yayin da Musa Ɗanqwairo ya fara tasawa, sai ya karkata wajen koyon abubuwa na hukunce-hukuncen addinin Musulunci da kuma hidimomin kiɗa da waƙa waɗanda suka shafi wasu harkoi na zamantakewar Hausawa.

    Musa Ɗanƙwairo ya fara biyayya ta sanin makamar waƙar baka tun a wajen mahaifinsa, Makaɗa Usman Ɗankwanagga24. A wajen mahaifin nasa ya koyi kaɗa kanzagi da karɓin waƙa da jajircewa a karin waƙa da samar da rauji na waƙa (Gusau, 2019: sh. 10-11).

    Haka kuma Musa Ɗanƙwairo ya daɗa gwangwajewa a zuba ɗiya na waƙar baka a biyayyar da ya yi a yayin Halifantakar da ya yi wa wansa Abdu Kurna. Domin himmar Musa Ɗanƙwairo da ƙwazonsa da basirarsa, wansa Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun Abdu Kurna, ya naɗa shi ya zama Daudun Kiɗa kuma Ɗangaladimansa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Musa Ɗanƙwairo a Gayaunar Waƙa danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan Waƙar Shawara Ga Mai Bilicin danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙar Neman Zaman Lafiya

    Waƙar Neman Zaman Lafiya

    Mawaƙi: Jamilu Alhassan
    Amshi: Zaman lafiya muke so,
    Allah daɗo ƙasata Rabba.

    Bisimilla Sarkin baiwa, Baiwarka ta ishe kowa,

    Bara nake kai nawa, Baiwar Ka yo ƙarawa,

    Bari nai nasiha babba.

    Ƙaro salati Jallah, Gare sa Manzon Allah,
    Ƙaunarsa ɗan Abdullah, Silar barin yin kwalla,
    Faɗar Ma’aikin Rabba.

    Waƙa nake ƙullawa, Zaman salam roƙowa,
    Allah Ka zam ƙarowa, Ƙasarmu Naija tawa,
    Mu daina yin tababa.

    Ku tabbata dangina, Kwai batu ruhina,
    Ku zo ku ji ikhwana, Ku daina yaƙar juna,
    Kuu san hakan ba riba ba.

    Zaman lumana duba, Yana da rana babba,
    Rashin sa ba riba ba, Mu daina yin wata gaba,
    In ji Shi Sarki Rabba.

    Ku tsaya ku ji wani zance, Mu riƙe shi sai mu yi dace,
    Fitina tana nan kwance, La’ana ta gun Mahalicce,
    Ga masu ta da ta duba.

    Aya cikin Anfali, Ashirin biyar ɗan kalli,
    Halin masifa kalli, Ba ta barin mai hali,
    Yaro fa har ma babba.

    Zama idan ai ba fis, Da ka ji an ce zan ƙis!
    Tamkar baru an ce is! Kowa yana yin tinƙis,
    Ba mu so ganin wannan ba.

    Wa’atasimu faɗar Mahalicci, Bihablillahi har da maƙoci,
    Jami’an, babu mai yin ƙunci, Idan mun farraƙe zai ɗaci,
    Rayunmu ban ƙarya ba.

    Idan ka ɗauki Afirka, Akwai ƙasashe leƙa,
    Waɗanda akke yaƙa, Wasunsu na yin kuka,
    Ba su samu zaman aunu ba.

    Burundi in ka dubi, Ruwanda har ma Libi,
    Ka tabbata sun ƙi bi, Kundi na mulki kitabi,
    Ba su daina yin yaƙi ba.

    Laberiya Somali, A nayinti-wan ɗan kalli,
    Sun ƙaurace nasu mahalli, Waɗansu an bar kwalli,
    Domin ba su ma zauna ba.

    Itofiya ita wannan, Iritiriya shi ke nan,
    Nayinti-et su biyun nan, Sun yaƙi juna rannan,
    Ba suy yi adalci ba.

    Sierra Leone har Sudan, Mutum fa wane metan,
    Gidansu sun bar wannan, Zaman rashin fis ke nan,
    Ya sa ba sa zauna ba.

    Idan ka zo nan Naija, Farin ido sai yai ja,
    Kano fa babbar haja, Na Marwa ne kuma yaj ja,
    Amman fa bai kyauta ba.

    Muhammadu na Marwa, Gyauronsa na can Yarwa,
    Ƙala-ƙato ban mantawa, Fitinar da sun shukawa,
    Da yawa akai binnewa, Ka ji halin ‘yan zamba.

    Zangon katab, wayyo ni! Hausa Birom kaico ni!
    Tivi-Jukun can ƙarni, Da yawansu ai sun rauni,
    Wasu ma ba su ko shura ba.

    Idan ka zo nan Yarwa, Boko haram kwai tsiwa,
    A Bama ban mantawa, Wasunmu na a kushewa,
    Abin fa bai kyawu ba.

    A Mubi har ma Gombe, Ba yau ba har ma gobe,
    Addu’arsu hannu tuɓe, Tamkar kwari ba kube,
    Salam salam, ya Rabba.

    Zaman salam kwai auki, Ya zarce ma ɗan sarki,
    Kowa yana nasa aiki, Ticas muna yin maki,
    Ba mu zam muna ganda ba.

    A Yobe nan ce jahata, Abin fa ya so ƙazanta,
    Gwamnanmu ai ya kyauta, Ya ce a bar yin wauta,
    Bai bar mu muna ihu ba.

    A 1st Disemba fotin, A YSU can hostel ɗin,
    Aka zo da kutse domin, A kashe ake yin yaƙin,
    A Monde ba zan manta ba.

    Salmanu sannan Sulfa, Sun zo suna sassarfa,
    Sawunsu sam ba safa, Sauran suna shan suffer,
    Subhana Sarki Rabba.

    Ciza nake tun ɗazu, A Yobe ai dai yanzu,
    Zama na lau ya wanzu, Mun roƙi Sarki Azizu,
    Bai ƙi ya yo amsa ba.

    A yanzu zan yo busa, Na ba ku labarinsa,
    Zaman lumana kansa, Ya zarce daɗin masa,
    Ta Bauchi ban ƙarya ba.

    Ga shawara zan bai wa, Gwamnanmu har ma kowa,
    Ga wanda ke son yalwa, Gun zaman lumana aiwa
    Mu kama Allah Rabba.

    Ina ƙiranmu jumulla, Mai ɗan kwali ko mai hula,
    Rawani da mai jan akala, mu kama Allah walla,
    Mafuta ba za mu rasa ba.

    Shi dai fa rai kwai tsada, Sojojinmu har ‘yan sanda,
    Sun ce sun ji sun kuma yarda, Su nasu ran sun sai da,
    Don kare ƙasata babba.

    A bar batun ɓangaranci, A bai wa kowa ‘yanci,
    Musulum, Kirista maƙoci, Mu mutunta juna.

    Domin karanta cikakken Yabo Daga Waƙar Maryam Fantimoti danna nan.

    Domin karanta cikakken Yabo A Waƙoƙin Baka danna nan.

    Don karanta cikakken Dangantakar Harshe da Waƙa danna nan.

  • Taƙaitaccen Tarihin Kamilu Almajirin Mawaƙa

    Taƙaitaccen Tarihin Kamilu Almajirin Mawaƙa

    An haifi Kamilu Hussain a shekarar 1980 a ƙauyen Beta Ƙaramar Hukumar Sumaila da ke Jihar Kano a Tarayyar Nijeriya. Cikakken sunansa shi ne Kamilu, amma alkunyarsa ita ce “Almajirin Mawaƙa”. 

    Sunan mahaifin Almajirin Mawaƙa shi ne Malam Hussaini wanda shi ne Na’ibin Limamin Masallacin Juma’a na Ƙauyen Beta a wancan lokacin; kafin daga baya ya yi Ƙaura zuwa Ƙaramar Hukumar Nguru da ke Jihar Yobe.

    Kamilu tun yana ɗan shekara huɗu mahaifinsa ya tura shi Ƙaramar Hukumar ta Nguru; inda ya fara karatun Alƙur’ani mai girma a wurin Malam Sani Dogon Ƙwami.

    Bayan ya fara tasowa ne, sai ya shiga neman ilmin littattafai; inda ya tafi wani ƙauye mai suna Ƙauyen Mamuda a can ƙasar Wudil da ke Jihar Kano, inda ya yi karatu a wurin Malam Hamidu, daga bisani ya koma Ƙaramar Hukumar Nguru.

    Bayan ya ɗauki kamar shekaru goma sha biyar, sai mahaifansa suka yi ƙaura suka koma Nguru (wato inda yake gardanta).
    A ɓangaren sana’a kuwa, bayan ya gama karatunsa na Alƙur’ani da wasu littattafan Addinin Musulunci, sai ya fara sana’ar ɗinki, inda ya ƙware matuƙa; har ma yana da yara a ƙarƙashinsa.

    Bayanin Almajirin Mawaƙa Ta Fuskar Waƙa

    Ta fuskar waƙa kuwa, Kamilu taka-haye ya yi, domin bai gaje ta daga iyaye ba, sha’awa ce ta sanya shi fara waƙa; inda kuma ya fara a shekarar 2008, amma bai iya tuna waƙar da ya fara ba. Kamilu ya dai tabbatar da cewa akwai waƙar da ta fito da shi duniya aka san shi; wato waƙar da ya yi mai taken “Kai Ka Zagi Bala”.

    Bugu da ƙari, Kamilu ya bayyana cewa waƙa ta yi masa komai na rayuwa, domin a dalilinta sunansa ya ɗaukaka, ya je aikin Hajji, ya mallaki kayan more rayuwa na duniya. Yanzu haka shi ne mai kamfanin Beta Studio da ke kan kwanar Total titin Zoo Road; sannan yana zaune a Birnin na Kano tare da iyalansa.

    Ya yi waƙoƙi da dama a ɓangarori daban-daban, amma sunansa ya fi haskawa a ɓangaren waƙoƙin siyasa (Adamu, 2014).

    Ba mu sami tsayayyiyar rana ko watan da aka haife shi ba; Har yanzu yana raye, kuma yana zaune a ɓangaren Shuwarin da ke unguwar Hausari a Ƙaramar Hukumar Nguru.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Wayon Roƙo a Adabin Baka: Nazarin Roƙo a Wasu Waƙoƙin Kamilu Almajirin Mawaƙa wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Roƙo a Wasu Waƙoƙin Kamilu Almajirin Mawaƙa danna nan.

    Domin karanta bayani akan Asalin Kiɗan Fiyano danna nan

  • Wuraren Da Ake Kiɗan Fiyano (Situdiyo)

    Wuraren Da Ake Kiɗan Fiyano (Situdiyo)

    (Situdiyo) : Shagunan da ake kiɗan fiyano ana kiransu da situdiyo.

    Gusau (2016:27) ya bayyana situdiyo da cewa:

    “Ɗaki ne da ake shiryawa wanda ake sarrafa murya tare da samar da amo na kiɗa ta amfani da wasu na’urori”.

    Wasu daga cikin wuraren da ake yin kiɗan fiyano a wasu sassan yankunanmu sun haɗa da:

    3.1.1 Sahibul Bushira Musical Studio, Galadima Maikyari Street Nguru.
    3.1.2 Mazeeka Sound Studio Nguru.
    3.1.3 Barewa Multi-Media, Shy Plaza, Ƙofar Gadon Ƙaya, Kano.
    3.1.4 Taskar Ala Global Limited, Farm Centre, Kano.
    3.1.5 Lafazi Entertainment, Habiba House, Zoo road, Kano.
    3.1.6 Prince Zango Sound Studio, Kaduna

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Kiɗan Fiyano A Wajen Hausawa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta Masu Yin Kiɗan Fiyano A Ƙasar Hausa danna nan

    Domin karanta bayani akan Asalin Kiɗan Fiyano danna nan

  • Waƙar Shawara Ga Mai Bilicin

    Waƙar Shawara Ga Mai Bilicin

     Allah ka daɗo aminci ga Rasulu uban zumunci, da sahabbai ‘yan halacci, shiriya ce bin su babu cuta.

    • Allah ƙaran basira,
    • Hikima da yawan ishara,
    • Na yi waƙa ba Gadara,
    • Burina duk a daina wauta.
    • ——————————–
    • Faɗakarwa za na kunce,
    • Za na yi shi a ɗan taƙaice,
    • ‘Yar ƙwar huɗu kar ku mance,
    • Daudu zan faɗakar da kyan halitta.
    • ————————————
    • Kun san tushen bayani?
    • Mai bilicin zo ka ji ni,
    • Ke zan wa ƙira da nuni,
    • Manufata yau ki dai rabauta.
    • ———————————-
    • Yau mata idan ka lura,
    • Sun faɗa cikin lalura,
    • kuma sun nufaci sahun fitsara,
    • dan sun raina Ubangijin halitta.
    • ———————————
    • Yarinya mai bilicin,
    • Burinki ki zarce cincin,
    • Sai kin zama ja da nacin,
    • Don bilicin kin yi ja ya gauta.
    • ————————————
    • ‘Yar’uwata ga nasiha,
    • A gare ki, ki ƙyale rahha,
    • Ki riƙe ta ki daina haha,
    • Dariyar ƙeta cikonta cuta.
    • ————————————-
    • In ka lura da har mazan ma,
    • Wasu sun koma zilama,
    • Sai bilicin babu ƙima,
    • Sun zubarta da sauya fata.
    • ——————————-
    • Na mazan ma ya fi haushi,
    • Laifinsa kwa ya fi kaushi,
    • Ya yi daudu da illimin shi,
    • Wai fari ne salsalar rabauta.
    • ———————————
    • Mai bilicin bar gadara,
    • Allah ya yi hanin tijara,
    • In kana so zo ka tsira,
    • Bar wa kanka baƙi a fata.
    • ——————————
    • Ɗan iska ɗan asara,
    • Shashasha uban fitsara,
    • Ɗan daudu uban tijara,
    • ——————————
    • Allah wadaran ka daudu,
    • Ɗan iska mai fasadu,
    • Mai raina kyautar Wahadu,
    • Wanda yai masa baƙi a fata.
    • ———————————
    • Shashasha ɗan bala’i,
    • Kullum aikin jafa’i,
    • Ba ka komai sai kata’i,
    • Da nufin umma da cuta.
    • ———————————-
    • In ka amshi batun ga nawa,
    • Kafin ka shige kushewa,
    • Fata ka rabauta dan’wa,
    • Daina girman kai da nuna wauta.
    • ———————————–
    • In ka juya batun ga baya,
    • Za ka sha dukan taɓarya,
    • Za ka sha matsa a baya,
    • A Kufai kake babu mai jiɓinci.

    domin samun karanta cikakkiyar shawara ga me billicin danna koren rubutu.

  • Saƙo Ga Masoyiyata

    Saƙo Ga Masoyiyata

    Salam ya ke muradina, Da safe na antayo ƙauna, Na bayyana sirrikan raina, Gare ki ina makwancina, Zo amsa min cikin son rai.

    • Abar sona abar sona,
    • Ya abar ƙauna abar ƙauna,
    • kin zam abar marari a rayina,
    • Yau ga ni da so cikar ƙauna,
    • Cikar buri cikar komai.
    • Gare ki masoyiya tawa,
    • Ki ji ni da zantukan baiwa,
    • Na ƙaunar nan da ba tsiwa,
    • Cikin mararin cikar sowa,
    • Na bayyana baitukan so dai.
    • Idan na gane ki don ƙauna,
    • Na manta abin dake raina,
    • Cikar buri ki zo guna,
    • Ki amshi buƙatuwar raina,
    • Ki share min duhun komai.
    • Ranar wanka Bahaushe de,
    • Ya ce cibi waje buɗe,
    • Nufinsa a wangame buɗe,
    • Kowa ya gano ido buɗe,
    • A san shi a san kalar komai.
    • Kin san so ba a mai yarfe,
    • Ba a ƙyamar tuwon safe,
    • Zoben so ba a sa ƙarfe,
    • Burina na tattaro lefe,
    • Na kai ki garin da ba kome.
    • Kin san so ba a mai kulle,
    • Gararinsa yawa na ‘yan talle,
    • Shuhurarsa a zuciya zille,
    • A ganta a fuska ba kyalle,
    • A san ya zarce duk komai.
    • Idan na taho a motata,
    • Cikin tafiya ta ƙasaita,
    • Idan na gane ki ‘yar auta,
    • Kina tafiya ta ƙasaita,
    • Na manta batu na tuƙin dai.
    • Kalarki daban a mataye,
    • Sunanki daban na ‘yar yaye,
    • Sautinki daban a ƙaraye,
    • A soyayya ana maye,
    • A sonki ko za na yo komai.
    • Naman da ake kira soye,
    • A cakuda kafi zabaye,
    • A sa naman a sa maye,
    • A sa gishiri a yo soye,
    • A so haka duk ake komai.
    • Maimaita aji fa sai dolo,
    • A so kam ba a son gwalo,
    • Ba a kome cikin salo,
    • Jifa kam sai da ɗan qwallo,
    • A so ba a barin komai.
    • Baitin ƙarshe na ce santsi,
    • Ya ɗebi mutum ya yo watsi,
    • Ya farfasa kai ya yo rotsi,
    • A soyayya a bar kutsi,
    • Aure a gare ki ne komai.
    • Ni Nayaya na ce ki dube ni,
    • Ki min kallon da ba raini,
    • Da zai mai she ni ɗan birni,
    • Na sa kaya na sa rawani,
    • Na so domin na zam komai.

           domin samun karanta saƙo ga masoyiyata danna koren rubutun nan

  • Waƙar Yabon Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo

    Waƙar Yabon Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo

    Ɗalibi a matakin digiri na biyu, Sashen Harsuna, Jami’ar Jihar Bauchi. Malami mai aikin Hidimar Ƙasa, Sashen Nazarin Harshen Hausa, Kwalejin Addinin Musulunci da Sharia ta Aminu Kano, Jihar Kano.

    Wadda aka gabatar a taron bikin taya Farfesa Abdulƙadir ɗangambo murnar samun Emiratus farfesa a ranar Lahadi 14/07/2019, A Ɗakin Taro na American Corner dake Laburaren Jihar Kano

    • Sallama gare ku karin fari,
    • Godiya ga Allah mai khairi,
    • Allah ban basira nai ƙudiri,
    • Nai yabon ƙwararren mai nazari,
    • Ɗangambo Baban nan nagari.
    • —————————
    • Gaisuwa ga Ɗaha miji nagari,
    • Shugaba a duniya har kabari,
    • Bin Sa babu zancen bin garari,
    • In ka gane son sa fa ka ci gari,
    • Lalle fa ni kam nai katari.
    • ————————–
    • Manzo na Allah ɗa nagari,
    • Sahibansa, matayen khairi,
    • Har da ‘ya’ya masu gudun garari,
    • Sanya tabi’an nan masu gari,
    • Ka daɗo aminci mai sukari.
    • —————————–
    • Gani nan da waƙa ba fahari,
    • Har na tsara baiti ku yo nazari,
    • Babu batsa ko zancen sharri,
    • Don yabon Ubanmu da bai kuri,
    • Wanda bai wa al’umma sharri.
    • ———————————
    • Ana na gaishe ku tun da wuri,
    • Taron da kun shirya don fahari,
    • Na tayo Ubanmu Uba nagari,
    • Murnar Emiratus mun fahari,
    • A Kano muna nan muna zikiri.
    • ———————————
    • Duk garin da babu sani da ɓari,
    • Ilimi fa gyara ne na gari,
    • In akwai gidanku fa kun ci gari,
    • In ka ba da ka zarce sukari,
    • Kai batun ga sai mai kyan ƙuduri
    • —————————-
    • Rayuwar karatu ba garari,
    • Mai biɗarsa shi ne ɗa nagari,
    • Malami ko shi ne uba nagari,
    • Samuwarsa dole a yo fahari.
    • Ɗangambo lalle ka ci gari.
    • —————————–
    • Rikicin Fulani ƙona gari,
    • Rigimar fatake ce gagari,
    • Rigar mutunci ce fahari,
    • Riƙi gaskiya ka zamo nagari,
    • Riƙi ɗa na Gambo ka zarce gari.
    • ——————————–
    • In ka nemi maciji ka je shuri,
    • Shi Ɓarawo sa shi cikin fa mari,
    • Kankana tana kayan marari,
    • Ɗangamo sa shi cikin nagari.
    • Ni ko sai ka je layin nazari.
    • —————————
    • Malami jakadan alheri,
    • Rayuwarsa bai ƙullo sharri,
    • Mutuwarsa ke sa ai garari,
    • Wanzuwar sa ke kawo sarari
    • Ɗangambo kanka mu yo fahari.
    • —————————–
    • In ka kalli B.U.K nazari,
    • Ɗalibanta duk sun yo katari,
    • Sun naƙalci harshe ba fahari,
    • Lugatan da Turanci a gari,
    • Ga biyayya gunsu cikar fahari.
    • ——————————–
    • Ɗangambo fannunu ne nazari,
    • Ɗalibansa sun zamto ƙwari,
    • Fannukansu sun san duk lamari,
    • Ba su birki balle a yo turi,
    • Ba su yi wa kowa alfahari.
    • ——————————
    • In ka je gari aka ma fahari,
    • Kar ka damu lura ka yo nazari,
    • Ƙila babu Malam a wanga gari,
    • Je ka sashikan Hausar nazari,
    • Ba rabo da kai ba shiga haɗari
    • ——————————–
    • Ɗangambo ka zarce zuma maɗari,
    • Wane farin can wai sukari,
    • Ka yi taka kai ta rago a gari,
    • Ka faranta rayin masu gari,
    • Zuciyarsu ta zamto fa fari.
    • ——————————-
    • Baban Samira uwar nazari,
    • Na gaida Dakta da ba ta ɓari,
    • Ma’ana Halima dake nazari,
    • Harshe na Hausa yana fahari
    • Da ke da Abbanmu masu gari.
    • ——————————-
    • Manyan furofesa sun nazari,
    • Sun koyi Adab da kyau da wuri,
    • Dakta da masters sun yo nazari,
    • Sun zarce hamsin wane fa ɗari,
    • Lalle gwanin namu ka ci gari.
    • ——————————-
    • Na san ka tun kan na zo ni gari,
    • Sanadin karatunka nai nazari,
    • A rubutukanka na yo nazari,
    • Na nazarci waƙa, adab da kari,
    • Har ma da ƙage na labari.
    • ——————————-
    • Ni Nayaya na yo alfahari,
    • Na zamo cikin ‘ya’ya tari,
    • Wanda sun ka yo wannan katari,
    • Sun ka yo rubutu mai fahari,
    • Don na waƙe Ɗangambo a gari.
    • ——————————-
    • Zan taƙaita kan waƙar sukari,
    • Kai! Maɗi fa zance ba kuri,
    • G. Nayaya uban nazari,
    • Suna gare ni a wanga gari,
    • Nguru a ce tammat khairi.

    domin samun karanta waƙar gargajiya danna koren rubutu

  • Waƙar Yabon Manzon  Allah(S.A.W).

    Waƙar Yabon Manzon Allah(S.A.W).

    Domin  shiga gasar mawaƙa wadda ƙungiyar gamayyar marubuta da yadda manazarta waƙoƙin Hausa ta ƙasa, ta saka a ƙarshen shekarar  2018 zuwa farkon  2019.

     

    • Allah na roƘa cikin ɗa’a,
    • A baitukan nan da babu ba’a,
    • Allah na ɗaro daɗin sa’a,
    • A baitukan nan da ba bidi’a,
    • Albarka sa min na ɗau ƙuri’a.
    • —————————–
    • Na yo salati ga Manzona,
    • Na Khadija, Hafsat, Uban Nana,
    • Na Sadiƙu, Umar, Usumana,
    • Na Aliyu zaki kisan arna,
    • Na Mu’awiyya sahihin ƙima
    • ————————–
    • Zuma farar gani farar saƙa,
    • Na ƙulla baiti cikin waƙa,
    • Na tsara ɗango cikin sarƙa,
    • Domin yabon Ɗaha kun ji haka,
    • In ka bi Manzonmu ka fi haka.
    • ——————————-
    • Kyawun ɗabi’unsa sun fi ɗari,
    • Kufurun, musulmanmu sun nazari,
    • Zama da Manzon fa ba haɗari,
    • Rayuwa a tsarinsa ba garari,
    • In ka bi Manzonmu ka ci gari.
    • ——————————–
    • An haifi Manzo a Makkiya,
    • Ran Litinin sha biyun ku jiya,
    • Auwal Rabiyun na ɗan juya,
    • Shekara ta giwa a Habshiyya,
    • Islam kalanda ta Hijriyya.
    • —————————-
    • Nasabar Mahaifinsa Abdallah,
    • Abdulmuɗallib cikin jumla,
    • Haashim fa Kaka ga Abdallah,
    • Abdulmanaf ɗan Ƙusai Allah,
    • Ya sa Kilab don cikar falala.
    • ——————————
    • Umminsa Babba Aminattu,
    • Yar Wahab, Manafi, Zuhuratu,
    • Sun haɗe a Kaka taƙaita batu,
    • Na biyar Kilab sai ku gane batu,
    • Sirarsa Manzon da bai shantu.
    • ———————————
    • Matansa sha ɗai na lobayya,
    • Khadija farkonsu kun ji ɗaya,
    • Assha da Hafsat suna baya,
    • Ummu Habiba da Salmayya,
    • Hindattu, Saudat ba sa ƙarya
    • —————————-
    • Sai Zai nabu bintu Jahshiyya,
    • Maimunatu bintu Harisiyya,
    • Zainab Khuzaima na jerayya,
    • Sai kam ta ƙarshe Juwairiyya,
    • Matansa cif-cif da sha ɗay
    • —————————-
    • ‘Ya’yanSa bakkwai cikar sunna,
    • Ibrahim a farko mai suna,
    • Abdallah, Ƙasim da ba su tsana,
    • Fatima, Kulsum cikar ƙauna,
    • Ruƙay da Zainab cikon juna.
    • ——————————
    • Manzo yana nan da mu’ujiziyya,
    • Ƙur’an da ba wasa ba ƙarya,
    • Tatsuniyar nan ta yan zolaya,
    • Ba shirme danniyar nan ku jiya,
    • Halinsa ne kun ji khairiyya.
    • ——————————
    • Halinsa Manzo cikar kunya,
    • Nutsuwarsa Manzo a taffiya,
    • Maganarsa ƙamshi yake zirya,
    • Dattijo ne mai halin manya,
    • Ƙur’an dalilinsa baki ɗaya
    • —————————
    • Dini na Manzo da ba ƙarya,
    • Ba yaudara ko kisan hanya,
    • Shi gaskiya ce zancensa ɗaya,
    • Dinin da Shaiɗan yake baya,
    • Ba ya kusantarsa don kariya.
    • ——————————-
    • Islam ya kawo a Makkiya,
    • Ya ƙira Ƙuraishi su bar ƙarya,
    • Sata da shirka da camfiyya,
    • Da kisa na juna da shirya tsiya,
    • Su riƙe ƙiran nan na kimtsiyya.
    • ——————————-
    • Rukunai shida ne na Addini,
    • Zan ambato su ku ɗan ji ni,
    • Kalma ta farko shahadataini,
    • Sallah, Azum, Zakka ba raini,
    • Hajji a ƙarshe ga mai sukuni.
    • ——————————-
    • Iman ku gane ajinsa shida,
    • Iman da Allah, Mala’iku da;
    • Littattafan nan na aƙida,
    • Manzanni, Lahira kui shaida,
    • Ƙaddar fa wajib cikon na shida.
    • ——————————-
    • Ya yaƙi arna cikin sa’a,
    • Ya rusa daular da ba ɗa’a,
    • Ya ce gumaka mu yo bara’a,
    • Kisa na juna mu bar bidi’a,
    • Kushe da juna mu bar ta ba’a.
    • ——————————
    • Yaƙi talatin na yo nazari,
    • Ya yo su ba ɗai Ya buɗe gari,
    • Islam ya zamto cikin fahari,
    • Kufurun suna can suna garari,
    • Aljanna ce duk cikar guzuri.
    • ——————————-
    • Daula ta zamto ta Islama,
    • Kowa ya zamto cikin hidima,
    • So, taimakon juna ba ƙyama,
    • Ba soke-soke da yin gulma,
    • Cab! Kun ji hanyar mutan ƙ
    • —————————–
    • Zan dakata zana sa birki,
    • Tamkar fa mota a kan tuƙi,
    • Nayaya ƙanin Bilki,
    • Yobe gari na da ba raki,
    • Tammat salamun na yo birki.

     

                  domin samun karanta cikakkiyar waƙar danna koren rubutu

     

     

  • Waƙar Hamdala .

    Waƙar Hamdala .

    Allahu Wahabu mai komai, Mai sa zaki ya kar birrai, Mai sa kuturu ya hau jakai, Mai bai wa mutum sanin ilimai, Karimu, Wahabu mai komai.

    • Sa’a na rika a tun farko,
    • Ka ban ilimin mutan farko,
    • A waka kar na zam soko,
    • Ka ban hikima na sa saƙo,
    • A gari, birni da duk loko.
    • ————————-
    • Ku biyo ni ki ji ni baitoci,
    • Na tsara batu na lakcoci,
    • A Gadau ta Jiharmu can Bauci,
    • Garin da na je a motoci,
    • ————————
    • Na je ni Shira na je Zaki,
    • Na je ni Gaɗau da ba gunki,
    • A nan na zamo ya ɗan zaki,
    • Jama’are na je cikin tuƙi,
    • Na kwan Azare cikin ɗaki.
    • —————————-
    • Mu ɗan koma batun na Shira,
    • Garin dutse garin Gora, kara;
    • Rumfa, Dutsen Gabas a Shira,
    • Ruwan ƙirci akwai a Shira,
    • Kare, Margi, Habe a Shira.
    • —————————–
    • Wata ran a Guru na tasowa,
    • Na je ni Bade garin Gashuwa
    • A Potiskum ban yi hutawa,
    • Sai ga ni Bagauda yan mowa,
    • Bulkachuwa ma na gotawa.
    • ——————————
    • Tafiya daɗi cikin mota,
    • Bulkacuwa nan na dan gota,
    • Damban na wuce ina mota,
    • Zan je ni Gaɗau garin tsafta,
    • Na shige Azare a kan kwalta.
    • ——————————
    • Na je ni Gamawa yan barka,
    • Garin Shehin da bai shirka,
    • Ɗan Sa’idu Ali na gaishe ka,
    • Sakwa a garin da babu
    • Allah ya saka ku kere haka.
    • ——————————
    • Na gode wahabu mai khairi,
    • Da ya ban ilmin da ba sharri,
    • Abun ga uku cikin jeri,
    • Na yi su ku ji su ba kuri,
    • Certificate two abin fahari.
    • ——————————-
    • Masters kuwa gefe can na shiga,
    • Tinƙis-tinƙis ina ta buga,
    • Karatu babu yin burga,
    • Ga aiki ga yawan sabga,
    • Allah ya nufa na kere duga.

     

    domin samun karanta cikkakken littafin danna koren  rubutu.

  • Waƙar Gulma .

    Waƙar Gulma .

    A baitukan yau na tsaya, Na fara zancen shiriya, Na tsara baiti ku biya, Na sanya zancen anbiya,  Ku bi ni sala-sala.

     

    • Na gode Allah a gaba,
    • Salati sallam na zuba,
    • Gurin Nabiyyi mai haiba,
    • A gun Sa ba a giba,
    • Sai dai ka koyo sallah.
    • ———————-
    • Ka gode Allah ɗan’uwa,
    • Ya yo ka mai kyan ƙwalwa,
    • Ya ba ka ilmu da yawa,
    • Ya ba ka hikmar baiwa,
    • Waninka ko sai ƙ
    • ————————–
    • Ka daina kallon kowa,
    • Ni’im suna nan da yawa,
    • Fa Rabbi ne mai kai wa,
    • Gare ka dukkan bawa,
    • Ka gode wannan falala.
    • ————————-
    • A yau na gane jama’a,
    • Suna da kyawun ɗa’a,
    • Fahimta ce ke bara’a,
    • Ta kauce tsarin ɗa’a,
    • Hakan ko babbar illa.
    • ————————-
    • Ka gane komai ka faɗa,
    • Idan kana son hulɗa,
    • Ana ɗaga shi a yaɗa,
    • A ɓata zancen a haɗa,
    • Domin a kushe falala.
    • ———————-
    • Idan ka ce an ƙi ka,
    • Ka ƙara kallon kanka,
    • Ka seta ƙalbin naka,
    • Sannan ka kalli waninka,
    • Akwai dalilai ƙanana
    • ————————
    • Ga shawara zan ba ka,
    • Ka gyara harshen naka,
    • Ka bar batun an ƙi ka,
    • Da ni da kai mui harka,
    • Haza ɗabi’armu Allah.
    • —————————
    • Ku duba zancen nan dai,
    • Da kyau da kallon daidai,
    • Ina ganin nai daidai,
    • Ban kauce zancen sai dai,
    • Ɗanbarno zo kai lela.

     

    domin samun karanta cikakkiyar waƙar danna koren rubutu