Tag: Waƙafi

  • Rukunan Waƙafi

    Rukunan Waƙafi

    Waƙafi yana da rukunai guda huɗu kamar haka:

    – Mai waƙafi: sharaɗin mai yin waƙafi shi ne, ya kasance mai hankali; mai cikakken mulkin abin da zai yi waƙafi da shi na dukiya ko kadara, wacce za a iya amfana da ita, ko a bayar da ita haya, a yi amfani da kuɗin hayar.

    – Waƙafi ya zamo an yi shi ne da abin da za a iya aiwatar da shi.

    – Waƙafin ya kasance an yi shi ne da abin da yake akwai shi; don ba zai yiwu mutum ya yi waƙafi da abin da yake tunanin mallaka nan gaba ba.

    – Waƙafin ya kasance na har abada.

    – Amfanin da aka sadaukar na waƙafin ya kasance zai isa ne ga wata hanya ta neman kusanci ga Allah da biyayya a gare shi. Don ba ya halatta a sadaukar da amfanin waƙafi ga wata hanya ta saɓon Allah.

    – Yin waƙafin ya kasance ta hanyar furta wata magana da take tabbatar da niyyar mai yin waƙafi, ta yin waƙafin a bayyane.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sharuɗɗan Mai Kula Da Waƙafi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Masu Amfani Da Waƙafi Ko Hubusi danna nan.

    Wannan baya nin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmawar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Ma’anar Waƙafi

    Ma’anar Waƙafi

    Waƙafi kamar yadda kuma ake iya kiran sa da “hubusi” ko “tasbil” ko “tahbis”; a shari’ance na nufin sallama dukiya ko kadara, sallamawa ta har abada don neman yardar Allah Maɗaukakin Sarki; ga waɗanda mai waƙafin yake son su amfana da dukiyar ko kadarar.

    Wannan ya haɗa da gina masallatai don masu yin sallah, ko makarantu ko haƙa rijiya; don amfanar jama’a ko gina gidajen marayu ko gajiyayyu da dai sauran su.

    Domin karanta cikakken bayani akan Taƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Takaiceccen Tarihin Rayuwar Dr. Yahaya Tanko danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmawar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Taƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci

    Taƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci

    Ba shakka addinin Musulunci ya kwaɗaitar da mabiyansa dangane da waƙafi a matsayinsa na sadaka; wacce ladan ta yake ɗorewa har bayan rayuwar wanda ya yi ta. Kamar yadda ya zo a cikin faɗin Allah Maɗaukakin Sarki; “Kuma ku tsayar da sallah kuma ku bayar da zakka kuma abin da kuka gabatar; domin kanku daga alheri za ku same shi a wurin Allah, lalle ne Allah ga abin da kuke aikatawa mai gani ne”. (Baƙara aya ta 110).

    Haka kuma ya zo a hadisin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana cewa; a lokacin da ɗan Adam ya rasu dukkan ayyukansa sun tsaya in ban da abubuwa guda uku; sadaka mai gudana (waƙafi), ko wani ilmi da ake amfana da shi; ko ɗa nagari da yake yi masa addu’a.

    Haka nan fassarar abin da ake nufi da sadaka mai gudana ta zo a wani hadisi da Ibn Majah ya ruwaito; wanda a cikinsa ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa; “Lalle abin da kawai zai cigaba da iske mumuni na kyawawan ayyukansa bayan mutuwarsa. Shi ne wani ilimi da ya yaɗa ko ɗa na ƙwarai da ya bari ko wani Alƙur’ani da ya bar gadonsa; ko wani masallaci da ya gina ko kuma gida da ya gina don (amfani) matafiya.

    Ko wata ƙorama da ya tona take gudana ko kuma wata sadaka da ya fitar daga cikin dukiyarsa; a lokacin da yake da lafiya sanda yake raye wacce ladanta zai ci gaba da riskarsa har bayan rayuwarsa”.

    Haka nan kuma ya zo a cikin littattafan sirah cewa; a lokacin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi Hijira daga Makka ya sauka birnin Madina. A duk faɗin birnin, babu wata hanya ta samun ruwan sha mai daɗi, sai wata rijiya da ake kira rijiyar Rumah, wacce a wancan lokaci mallakar wani marowacin mutum ce; wanda yake tsawwalawa mutane wajen sayen ruwanta.

    Ganin haka sai Ma’aiki Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwaɗaitar da sahabbansa da cewa; “Wane ne zai sayi rijiyar Rumah (ya sadaukar da ita) Allah ya biya shi da mafiticinta a gidan Aljannah wanda nan take kuwa Sayyidina Uthman ya saye ta dirhami dubu talatin da biyar, kuma Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi “Ka sadaukar da ita ga musulmai, Allah zai ba ka lada, shi kuwa bai yi wata-wata ba ya aikata hakan.

    Haka nan Bukhari da Muslim sun ruwaito daga sayyidina Umar ɗan Khaɗɗab (Radiyallahu Anhu) cewa; ya ce da ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na sami wata gona a Khaibara; wacce ban taɓa samun wata dukiya da ta kai darajarta a tsawon rayuwata ba”.

    Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; “Idan ka ga dama kana iya riƙe asalinta ka sadaukar da amfaninta da Sayyidina Umar. Ya ji haka sai ya sadaukar da ita bisa sharaɗin cewa, ba za a sayar da ita kanta gonar ko a kyautar da ita ko a ci gadonta ba; tare da sadaukar da duk wani amfani nata ga talakawa, da ‘yan uwa, da bayi; da hanyoyin ɗaukaka addinin Allah, da baƙi, da kuma matafiya.

    Babu laifi ga masu kula da ita su ci ‘ya’yan itatuwanta; su kuma yi kyauta ga abokansu gwargwadon yadda aka sani a al’adance ba da sayarwa ba.

    Wannan al’amari na waƙafi ya watsu matuƙa a cikin sahabban Ma’aikin Allah; tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bayan kwaɗaitarwar da ya yi da aikata hakan. Domin kuwa sun yi waƙafi na abubuwa daban-daban da suka haɗa da masallatai da gonaki; da rijiyoyi da kayan jihadi don ɗaukaka kalmar Allah.

    Ya tabbata cewa adadi mai yawa na sahabban Ma’aikin Allah; tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun yi waƙafi. Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da Khalid ɗan Walid, da Jabir ɗan Abdullah, da Sa’ad ɗan Ubadah; da Ukbat Abdullahi ɗan Zubair, da Sa’ad ɗan Abi Waƙƙas, da uwar muminai Sayyidatina A’isha; da kuma Asma’u yar Abubakar – Allah ya yarda da su gaba ɗayansu.

    Babu wani mai hali daga cikin sahabban Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; wanda bai yi waƙafi ba, Haka kuma an rawaito daga Imam ash-Shafi’iya na cewa; “Labari ya ishe ni cewa mutum tamanin daga cikin sahabban ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; ‘yan Madinah kowanne a cikin su ya yi waƙafi” .

    Domin karanta cikakken bayani a kan Manufofin Waƙafi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Masu Amfani Da Waƙafi Ko Hubusi danna nan

    Wannan baya nin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmowar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma. Wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Dangogin Waƙafi

    Dangogin Waƙafi

    Ana iya yin waƙafi a ɓangarori da dama da suka haɗa da:

    Ɓangarorin yaɗa addini da ilmantarwa:

    1. Gina masallatai da samar da abubuwan Jin daɗin masallata:

    A cikin su waɗanda suka haɗa da rijiyoyi don samun ruwan alwala da sauransu. Ba shakka musulmai magabata sun yi ƙoƙari matuƙa ta yadda suka samar da masallatai daban-daban; tare da ƙawata su da fitilu, da cika su da Alƙur’ani da shimfiɗu, tare da ɗaukar nauyin ɗawainiyar kulawa da su, da biyan albashin masu yi musu hidima; ta hanyar karantarwa da ilmantarwa da kiran sallah da sauransu.

    Kaɗan daga cikin misalan waɗannan sun haɗa da abin da masana tarihin Musulunci suka bayyana a litattafansu cewa; yawan masallatan da suke birnin Kurɗubah ta ƙasar Andalus a ƙarni nan a uku bayan Hijira (ƙarni na goma a shekarar Miladiyya) sun kai kimanin ɗari shida. Kowannen su an samar masa duk wani abu da ake buƙata don jin daɗin masu amfani da shi.

    Kamar yadda sanannen abu ne cewa har zuwa wannan zamani namu, akwai ragowar irin masallatai daɗaɗɗu; irinsu masallacin Azhar da ke birnin Alkahira da Masjid al-Amawiy dake birnin Dimashk; da Masallacin Kairawan da a halin yanzu yake Tunisiya da sauran ire-irensu a sauran wurare daban-daban a faɗin duniya.

    2. Gina makarantu da samar musu da kayan aiki:

    Ba shakka tarihin Musulunci cike yake da labarai na waƙafi a ɓangarorin gina makarantu da samar da cikakkun kayan aiki a cikinsu; waɗanda suka haɗa da wuraren kwanan ɗalibai da wuraren hutawar su da lafiyarsu da sauran su. Kaɗan daga cikin misalan waɗannan sun haɗa da abin da aka samo a littattafan tarihi cewa yawan makarantu da aka yi waƙafin su a birnin Skilliya (ƙasar Italiya a wannan a zamani namu); a ƙarni na huɗu shekarar Hijiriyya, wanda yayi daidai da ƙarni na goma sha ɗaya na Miladiyya, sun kai kimanin makarantu ɗari uku; kowacce a cikinsu cike take da ɗalibai a fannoni daban-daban na matakan karatu daban-daban, da jin daɗin na kyautatawa.

    Wannan nau’i na makarantu za a gan shi a ko ina a manyan biranen Musulunci irinsu; Makkah da Dimashƙ da Halab da birnin Ƙudus da Bagdad da Alƙahira da Istanbul da kuma sauran garuruwa.

    3. Waƙafin ɗakunan karatu da na bincike:

    A irin wannan nau’i na waƙafi za ka iske an samar da ɗakunan karatu an kuma cika su da littattafai na fannonin ilmi daban-daban; kamar yadda akan samar musu da ma’aikata ƙwararru da za su rinƙa kulawa da su da suka haɗa da kwararru a fannin fassara da rubutu da kwamiti na amintattu da dai sauransu.

    Ɓangaren kula da jin daɗin al’umma

    1. Wannan ya haɗa da gina asibitoci da wuraren shan magani:

    Haka nan tarihin Musulunci cike yake da labarai na waƙafi a fannin kulawa da lafiya; ta hanyar gina asibitoci da kulawa da ma’aikatansu da samar da cikakkun kayan aiki da bayar da kyakkyawar kulawa ga marasa lafiya. Asibiti na farko da aka gina a tarihin Musulunci shi ne wanda aka gina a zamanin halifancin Walid ɗan Abdul-Malik wanda ya keɓance shi musamman don masu fama da larurar kuturta, aka kuma ɗauki likitoci ƙwararru, aka kuma ware musu albashi.

    Bugu da ƙari kuma, hatta su kansu marasa lafiya aka yanka musu kuɗaɗen alawus na kula da su. Waɗansu daga cikin misalai na irin wannan nau’i na waƙafi sun haɗa da asibitin Mustashfa Al ‘adudiy dake birnin Bagdad; wanda aka gina ƙarni na huɗu bayan Hijira (ƙarni na goma sha ɗaya na Miladiyya); da Almustashfa Annuriy dake birnin Dimashk wanda Sultan Nuruddin ya gina a shekara ta 549 bayan Hijira da Almustashfah Almansuriy dake birnin Alƙahirah.

    Kuma wani abin ban sha’awa a nan shi ne, tun tsawon wancan lokaci, an samu waɗanda suka yi waƙafi na waɗansu asibitoci na musammman kamar ciwon ido; da na ƙashi, da na fata da cututtukan taɓin kwakwalwa, da sauransu. Kamar yadda kuma aka gina asibitoci aka kuma yi waƙafi da su musamman ga waɗansu makarantu; don amfanin malamansu da ɗalibansu da kuma na talakawa da miskinai.

    2. Gina Wurare Na Musamman Don Kulawa Da Gajiyayyu:

    Ma’anar gajiyayyu da aka ambata a nan sun haɗa da marayu da ‘yan tsintuwa da nakasassu da makafi; kai har ma da tallakawa gidajen marasa ƙarfi wajen ɗaukar nauyin aurar da ‘ya’yansu da hidimomi masu dangantaka da waɗannan.

    3. Samar Da Ruwan Sha Da wurare Kwana Ga Dukkan Masu Buƙata:

    Ba shakka addinin Musulunci ya kwaɗaitar da mabiyansa wajen sadaukar da dukiya ta hanyar waƙafi a wannan bangare; haka nan musulmi sun yi namijin ƙoƙari matuƙa wajen aiwatar da wannan umarni; kamar yadda muka gani a baya na sayen rijiya da sayyidina Uthman ya yi, ya kuma sadaukar da ita ga ɗaukacin al ‘umma.

    4. Taimakon Talakawa Da Masu Ƙaramin Ƙarfi:

    Wannan ɓangare ya shafi sadaukar da amfanin wata dukiya ko kadara ga mabuƙata; kamar yadda sayyidina Umar Allah ya yarda da shi ya yi da gonarsa dake Khaibara, kamar yadda muka gani a baya; marasa lafiya ko talakawa ko matafiya ko ɗaliban ilmi da sauransu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Masu Amfana Da Waƙafi Ko Hubusi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarbiyyar Addini danna koren rubutun nan.

    Wannan baya nin an ciro shi ne daga Littafin Gudunmawar Waƙafi/Hubusi Da Tasirinsa Wajen Gina Tattalin Arzikin Al’umma; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.