Tag: Hawan Jini

  • Yadda Hawan Jini Yake (HYPERTENSION)

    Yadda Hawan Jini Yake (HYPERTENSION)

    Jini ruwa ne mai launi ja-zur da ke kewaya sassan jikin dabbobi masu ƙashin baya (vertebrates), kamar mutane (humans), mage (cats), ƙadangare (reptiles), tsuntsu (birds), kwaɗo (amphibians), kifi (fish), da sauransu.

    Bincike ya tabbatar da cewa banda mutum, akwai dabbobin da suke kamuwa da matsalar hawan jini. Amma wannan matsalar tana maganar hawan jinin mutum ne.

    Jini yana gudu da ƙarfi a cikin jijiyoyin jikin mutum idan zuciya ta feso shi. Aikinsa shi ne isar da kayan abinci zuwa sassan jiki, da fitar da ruwan dattin jiki ta hanyar fitsari ko zufa.

    Ƙarfin tafiyar jini yana buɗe jijiyoyi (arteries), kuma shi ne “blood pressure”. Akwai adadin blood pressure da ake buƙata wanda ba zai cutar da jiki ba. Idan ya yi yawa shi ne “hypertension”, kuma matsala ne. Idan ya yi kaɗan shi ne “hypotension” shi ma matsala ne. Idan ya yi daidai shi ne “normotension”, kuma shi ake buƙata.

    NA’URAR AWON GUDUN JINI (BLOOD PRESSURE MEASUREMENT DEVICE)

    Na’urar awon gudun jini ita ce “sphygmomanometer”. Tana da jakar ledar “polyester” da “nylon” mai suna “inflatable arm cuff”, wacce ake hura ma iska da ƙwallon roba mai suna “bulb pump”. Sa’annan tana da fuska (screen) mai nuna sakamakon awon, wato “pressure gauge”.

    A maƙale da ita akwai na’urar jin sautin bugun zuciya da jin gudun jini (stethoscope). Lokacin yin awon, ana ɗaura inflatable arm cuff ɗin a damtsen hannu, a hura iska a ciki. Cuff ɗin zai matse damtsen. Hakan zai sa na’urar ta iya ɗosano ƙarfin gudun jinin, ta nuna shi a screen, kuma za a ji sauti bugun zuciyar ta stethoscope.

    Nau’rar awon iri biyu ce:

    1. Ta farko ita ce na’urar da ake sarrafa ta da hannu (manual blood pressure monitor): Tana da stethoscope, inflatable cuff, da pressure gauge, kuma iri biyu, kamar haka:

    a. Mercury sphygmomanometer, wacce ake ganin sakamakon awon a jikin tsinken ruwan “mercury” a tsakiyarta.

    b. Aneroid sphygmomanometer, wacce take amfani da “spring” da “gauge”.

    2. Ta biyu ita ce na’urar da ke sarrafa kanta: (digital blood pressure monitor): Tana da maɗosanin bayanai (sensor) wanda yake ba ta damar yin aiki da kanta (automatic). Tana da inflatable cuff, amma ba ta da stethoscope. Idan aka ɗaura inflatable cuff ɗin, za ta hura iska da kanta ta hanyar motorized pump. Sai screen ɗin ya nuna sakamakon awon.

    KARANTA SAKAMAKON AWON GUDUN JINI (READING OF BLOOD PRESSURE MEASUREMENT)

    Sakamakon awon yana da lambobi biyu ne.

    1. Lamba ta farko ita ce ta sama, kuma ana kiranta “systolic”. Tana nuna ƙarfin gudun jini ne lokacin da zuciya ta kumbura domin ta feso shi.

    2. Lamba ta biyu ita ce ta kasa, kuma ana kiranta “diastolic”. Tana nuna ƙarfin gudun jini ne lokacin da zuciya ta sace bayan ta feso shi.

    Lambobin awon suna fitowa ne da alƙaluman millimetre of mercury (mm Hg).

    Tun farko na faɗi cewa sakamakon awon blood pressure iri uku ne:

    (a) Gudun jinin da ya yi sama, wato hypertension.

    (b) Gudun jinin da ya yi daidai, wato normotension.

    (c) Gudun jinin da ya yi ƙasa, wato hypotension.

    Matsakaicin gudun jini da ake buƙata (normal range of blood pressure) ya danganta da shekaru ko yanayin mutum ne. Wato ana buƙatar lambar sama (systolic) da lambar ƙasa (diastolic) su kasance tsakanin da’irori kamar haka:

    1. Jariri: Systolic = 72 mm Hg zuwa 104 mm Hg.

    2. Ɗan shekara 1 zuwa 2: Systolic = 85 mm Hg zuwa 113 mm Hg. Diastolic = 37 mm Hg zuwa 69 mm Hg.

    3. Ɗan shekara 3 zuwa 5: Systolic = 91 mm Hg zuwa 120 mm Hg. Diastolic = 46 mm Hg zuwa 60 mm Hg.

    4. Ɗan shekara 6 zuwa 12: Systolic = 96 mm Hg zuwa 131 mm. Diastolic = 55 mm Hg zuwa 62 mm Hg.

    5. Ɗan shekara 13 zuwa 17: Systolic = 80 mm Hg zuwa 120 mm Hg. Diastolic = 45 mm Hg zuwa 80 mm Hg.

    6. Ɗan skekara 18 zuwa 50: Systolic = 120 mm Hg zuwa 130 mm Hg. Diastolic = 80 mm Hg zuwa 85 mm Hg.

    7. Mace mai juna biyu: Systolic = 120 mm Hg zuwa 130 mm zuwa. Diastolic = 80 mm Hg zuwa 85 mm Hg.

    8. Tsoho: Systolic = 120 mm Hg zuwa 140 mm. Diastolic = 80 mm Hg zuwa 90 mm Hg.

    TASIRIN HAWAN JINI KO SAUKAR JINI DA ALAMOMINSU (EFFECTS AND SYMPTOMS OF HYPERTENSION OR HYPOTENSION)

    Tasirin hawan jini ko saukar jini yana bambanta a tsakanin mutane, kamar haka:

    1. Jarirai: Ba a cika samun hawan jini ga jarirai ba. Idan aka ga jariri da hawan jini, to, lallai an haife shi da nakasar zuciya ne (heart defect), ko matsalar ƙoda (kidney problem). Alamominsa su ne yawan kuka, kasa shan nono, da rashin girma. Sa’annan ba a cika samun saukar jini ga jarirai ba.

    Idan aka samu, lallai dalilinsa zai zamo rashin ruwan jiki (dehydration), ko zubewar jini (blood loss), ko ciwon zuciya (heart disease). Alamominsa su ne rashin shan nono, rashin walwala, da koɗewar fata (pale skin).

    2. ‘Yan shekara 1 zuwa 10: Ba a cika samun hawan jini ga yara masu wannan shekarun ba. Idan kuwa ya same su, alamominsa sune ciwon kai (headache), gajiya (fatigue), riƙewar numfashi (shortness of breath), haɓo (nose bleeding), sanƙarewa (seizures), da rashin gani (vision problems). Idan ba a magance shi ba, zai iya lalata zuciya, ƙoda, da ƙwaƙwalwa.

    Haka nan ba a cika samun saukar jini ga yara masu wannan shekarun ba. Idan aka samu, alamominsa su ne jiri (dizziness), suma (fainting), saurin bugawar zuciya (rapid heartbeat), da rashin ƙwarin jiki (weakness). Rashin magance shi zai iya lalata aikin ƙwaƙwalwa (impaired brain function), tsumburewa (growth retardation), da rikicewa (hypoxia).

    3. ‘Yan shekara 11 zuwa 17: Ana samun hawan jini ga matasa masu wannan shekarun. Alamominsa su ne ciwon kai (headache), zafin kirji (chest pain), da zafin jiki (abdominal pain). Idan ba a magance shi ba, zai iya lalata zuciya, ƙoda, da ƙwaƙwalwa, da jijiyoyin jini.

    Kuma zai iya kawo shanyewar tsagin jiki (stroke). Haka nan ana samun saukar jini ga matasa masu wannan shekarun. Alamominsa su ne ciwon kai (headache), zafin ƙirji (chest pain), da zafin jiki (abdominal pain). Rashin magance shi zai iya lalata zuciya, ƙoda, ƙwaƙwalwa, da jijiyoyin jini.

    4. Baligai ‘yan shekara 18 zuwa 50: An fi samun hawan jini ga masu wannan shekarun. Alamominsa su ne ciwon kai (headache), jiri (dizziness), da rashin gani sosai (blurred vision). Idan ba a magance shi ba, zai iya haddasa ciwon zuciya (heart disease), shanyewar tsagin jiki (stroke), da lalacewar koda (kidney failure).

    Haka nan an fi samun saukar jini ga baligai masu wannan shekarun. Alamominsa su ne jiri (dizziness), suma (fainting), da gajiya (fatigue). Rashin magance shi zai iya lalata ƙwaƙwalwa (impaired brain function), rikicewa (hypoxia), da gigicewa (shock).

    5. Tsofaffi: An fi samun hawan jini ga tsofaffi. Alamominsa su ne ruɗewa (confusion), mantuwa (memory problems), kasa tafiya (difficulty in walking). Idan ba a magance shi ba, zai iya haddasa ciwon zuciya (heart disease), shanyewar tsagin jiki (stroke), da cutar mantuwa (dementia).

    Haka nan an fi samun saukar jini ga tsofaffi. Alamominsa su ne jiri (dizziness), suma (fainting), da ruɗewa (confusion). Rashin magance shi zai iya lalata ƙwaƙwalwa (impaired brain function), rikicewa (hypoxia), da gigicewa (shock).

    6. Masu juna biyu: Ana matuƙar samun hawan jini ga mata masu juna biyu har yakan kai matakin farko na ciwon jijjiga (preeclampsia). Alamominsa su ne kumburin jiki (abdominal swelling), ciwon kai (headache), rashin gani sosai (blurred vision), da ciwon jiki (abdominal pain).

    Idan ba a magance shi ba, zai iya haddasa haihuwar bakwaini (preterm birth), haihuwar ƙanƙanin jariri (low weight of newborn), da matsaloli masu yawa ga uwa da jaririnta. Haka nan ana matuƙar samun saukar jini ga mata masu juna biyu. Alamominsa su ne jiri (dizziness), suma (fainting), da gajiya (fatigue).

    Rashin magance shi zai iya hana samar da isasshen jini ga jariri a cikin mahaifa (impaired blood flow to fetus), ƙanƙancewar jariri (fetal growth restriction), ko ɓari (miscarriage). Idan ciki ya tsufa, to, saukar jini alama ce ta preeclampsia.

    RABE RABEN HAWAN JINI (TYPES OF HYPERTENSION)

    Hawan jini ya rabu gida biyu:

    1. Hawan jini na asali (primary or essential hypertension): Shi ne wanda ba a san asalin abinda yake kawo shi ba, amma tsarin rayuwar mutum take haɓaka shi, kamar cin gishiri da yawa, rashin motsa jiki, tsufa, shan giya, ƙiba, gado, da sauransu.

    2. Hawan jini mai dalili (secondary hypertension): Shi ne wanda wasu cututtuka ko amfani da wasu magunguna yake kawo shi, kamar matsalolin ƙoda, zuciya, ƙwaƙwalwa, da magungunansu.

    MAGANI (TREATMENT)

    Magance hawan jini yana da matuƙar alaƙa da tsarin rayuwar mutum, kamar motsa jiki, rage ƙiba, cin abinci mai kyau, da shan magani bisa umurnin likita. Shi ma saukar jini magance shi yana da alaƙa da magance abubuwan da suke kawo shi, kamar yawaita shan ruwa, da kauce ma abubuwan da jikin mutum yake bijire musu.

    Karanta Bayani A Kan Budurci Da Kuskuren Da Ake Yi A Kan Rashinsa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Hatsarin Yin Wasa-rere Da Hawan Jini

    Hatsarin Yin Wasa-rere Da Hawan Jini

    Kamar yadda kwanaki kuka ji na yi bayani kan ciwon sugar cewa shi ne kan gaba wajen haddasa chronic kidney failure toh Hawan jini shi ne a matsayi na biyu da ke take masa baya wajen lalata ƙoda.

    Nephr(o)tic syndrome shi ne abinda ciwon suga ke jawo wa wanda nace muku in an yi gwajin fitsari ga wanda ƙodar ta fara taɓuwa za a ga sinadrin Protein ko Albumin a ciki ba ya ga hauhawar serum Creatinine da kumburi a ƙafafu ko ciki a wasu lokutan in ya yi ƙamari.

    To a masu Hawan jini kuma Nephr(i)tic Syndrome shi ke faruwa. Su kuma a fitsarin abinda ake gani shi ne jini wato cast na Red blood cell. Wani ƙila zai ce ai fitsarina koyaushe yellow ne ko kuwa fari tas don haka babu alamar jini. Ina ba haka abin yake ba.

    Akwai jinin da in abin ya yi ƙamari kai da kanka za ka ke ganin fitsarinka ya canza wannan shi muke kira GROSS HEMATURIA toh amma akwai wanda ba za ka taɓa gani ba sai an yi urinalysis, gwajin fitsari an sa High field microscope shi ne muke kira MICROSCOPIC HEMATURIA. To wannan fa shi ke nuna cewa hawan jini ya fara cin ƙodar mutum dole ne ya yi wani abu, in kuwa sai bayan abu ya ɓaci aka farga toh gaskiya in dai ya fara shiga Chronic sai dai a yi management ai ta ƙoƙari. Amma in yana Acute Kidney disease akan yi nasarar ƙwato ƙodar ta hanyar control na hawan jinin da sauran maganin da zai aiki a ƙodar da kuma canza abincin mutum zuwa KETO DIET

    Hawan jini abu ne mai hatsari idan aka yi sake da shi to fa ba ƙoda ba a hankali zai lalata ƙwaƙwalwa, yana motse jijiyoyin jini ta kai ga haddasa shanyewar ɓarin jiki, cutar mantuwa, lalata ido yadda mutum zai sami Retinopathy ya makance, da uwa uba bugun zuciya ko heart attack ko heart failure ko Coronary artery disease wanda duk sanda aka kai haka musamman zuciya, to fa mutum ba shi ba kuma yin duk wani aiki da ya saba sai dai a ƙiyama domin ya nakasa abin da yake jira shi ne mutuwa.

    Yawanci ciwon zuciyar ya fi faruwa bayan an ba shekaru 50 baya. To amma fa yanzu ga shi hawan jini da sai an ba shekara 40 baya aka fi samu amma yanzu har yara ƙanana masu ƙananun shekaru fama suke.

    ‘Yan Shekara 20 da wani abu ko ‘yan goma sha sai ka gan su da hawan jini. Wasu kuma basu ma san suna da shi ba har yau. Babbar illar hawan jini shi ne ba za ka taɓa jin alamun rashin daɗi a jika ko kana da shi alhalin cikin jikinka yana ta maka illa, shi yasa ake kiransa da silent killer.

    A sabon jadawalin da AMERICAN HEART ASSOCIATION ta fitar yanzu kafin tabbatar da hawan jini sai an auna mutum a lokuta 2 zuwa 3 mabambanta na rana guda idan har an sami Bp ɗinsa sama da 140 to tabbata yana da hawan jini. Wajibi a ɗora shi kan magani.

    Amma yawanci akwai wani abu da nake musamman ƙananun ma’aikatan lafiya su sani duk inda kuka ga mutum ɗan ƙasa da shekaru 10, ko 20 ko ƙasa da 30 ɗauke da hawan jini kai ko da ya ba wa 30 baya da kaɗan toh ku yi hanzarin tura shi ya yi KIDNEY FUNCTION TEST musamman a yara ‘yan goma sha yawanci ciwon ƙoda ne ke haddasa hawan jininsu.

    Da an je an yi gwajin fitsari da Blood chemistry za ka samu CREATININE ɗinsu ya yi High ana fara ba su magani insha Allahu shike nan za su sami lafiya, ciwon ƙodar zai kau sannan hawan jinin ma zai tafi dama ciwon ƙodar ne ya kawo shi. Wanda in kuwa ka fara ɗora mutum a maganin hawan jini to fa kullum a magani zai tafi alhalin an bar tushen matsalar ƙarshen complications ɗin ya kashe shi.

    Na faɗa muku da yawa ciwon ƙoda sai ya yi muni ake jin alamu. Sai dai a yara masu High Bp idan ƙodar ta taɓu wasu ana ganin kumburin fuska da ƙafafu kai tsaye.

    Akwai wani bawan Allah da ya rasu a Kano satin da ya wuce sakamakon ciwon ƙoda na ga labarinsa inda aka riƙa neman milyan 15 don kai shi India a yi masa dashe. A bayanin da ya yi farkon matsalar hawan jini ne tun a 2001 yace bai sani ba sai da aka duba jininsa lokaci har 220 ya je. Tuni ya ɓata ƙodar amma saboda in pressure ta yi pressure ƙwaƙwalwa ma daina kai saƙo take shi yasa wani za ka ga jininsa a 160 ko 180 amma yace shi ai ƙalau yake jinsa ba abin da yake damunsa.

    Shi ma ɗin to zuwa 2006 shekara 5 kaɗai duk ƙodojinsa biyun suka kasa, a nan ne ya samu aka masa dashen ƙoda ɗaya, aka cire ɗayar Allah sarki zuwa 2010 shekara 4 kacal saboda na faɗa muku in aka sama Organ ɗin wani ba kurum sawar ba akwai Rikicin Rejection da garkuwar jikinka za take yaƙar organ ɗin toh shi ma ya sami CHRONIC REJECTION shekaru huɗu ƙodar da aka sama ta mutu, shi ne fa yake ta fama har zuwa yanzu da Allah ya karɓi ransa.

    Yace daga wannan lokaci zuwa sanda yake kwance yana neman taimako an masa wankin ƙoda sama da sau dubu ɗaya da ɗari huɗu da sabain da uku, inalillahi wa’inna ilayhir rajiun. Ya sha wahala ban da ciwon cancer na ƙoda da za ka iya haɗuwa da shi a sakamakon dialysis ɗin kanshi tare da ƙarancin jini.

    Don haka kuskuren da ƙananun ma’aikatan lafiya kuke ku gyara, kukan rubutawa me hawan jini maganin sha na kwana 10 ya tafi kurum shikenan ko ya aka duba aka ga jini ya yo kasa, ba kwa kuma faɗawa mutum me ya dace ya yi ko ya kiyaye. To ku sani da maganin ciwon sugar da na hawan jini shan su ba ya ƙarewa har ƙarshen rayuwa kullum ne kuma ko da jini ya dawo normal level in dai ba ƙasa da 90 aka ga ya tafi ba, ba za a taɓa cewa ka ɗaga ƙafa ba. Sannan wajibi ne kafin ka ba mutum kowanne irin maganin hawan jini ya zamto kana da masaniya a kai da side effect, dose ɗin da ya dace da kuma HALF LIFE na maganin wannan wajibi ne.

    Wani combination wani kuma magani ɗaya ne. Don haka a ƙalla ka rubutawa mutum maganin wata 3 wato kwana 90 in ya kare a kuma ƙara masa haka za a yi ta tafiya, kuma za a ci gaba da bibiyarsa, shi yasa muke cewa a sayi abin gwajin mutum ya riƙa recording a littafi duk sanda zai zo asibiti ya zo muna da shi muke ganin progress ɗin.

    Don haka kar ku yi sake da hawan jini ku kiyayi gishiri; yawancin maiƙo da su chocolates. Kar don kuna shan magani ku ɗauka za ku ci komai musamman mu baƙaƙen fata da hawan jinin mu bai fiye jin magani ba sai an yi da gaske abu kaɗan na sa shi ya hau.

    Idan ka kula da kanka za ka rayu cikin aminci kamar kowa kuma hawan jini ba zai ma illar can ba. In ko kai wasa toh sai dai Allah ya tsare. Allah ka yaye mana abinda ya dame mu amin.

    Domin karanta Hawan Jini Ga Mace Mai Juna Biyu danna nan

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Hawan Jini Ga Mace Mai Juna Biyu

    Hawan Jini Ga Mace Mai Juna Biyu

    Hawan jini yayin da mace ke da juna biyu ba lallai ba ne ya zama wani abu da ke da hatsari a ciki musamman idan aka ba shi kulawar da ta dace.

     Ga abubuwa da ya kamata mace ta sani domin ta kula da kanta da kuma jaririnta. 

    Yayin da mace ta san ta na da hawan jini a lokacin da ta ke ɗauke da juna biyu to ya kamata ta kasance a cikin kula na likitoci /ma’aikatan lafiya wato (close monitoring) ke nan a Turance.

    Ire_iren hawan jini ga mai ciki 

    Wani lokacin mace na kasancewa ta na da hawan jini kafin ma a ce ciki ya shige ta. Wasu lokutan kuma hawan jinin na samuwa ne lokacin da ta riga ta yi cikin, wato bayan ta ɗauki cikin ke nan.

    Domin karanta Abubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki Danna nan 

    1. Gestational hypertension . Mata da ke da irin wannan hawan jini sukan same shi ne bayan sun ɗauki ciki da sati 20. Ba a samun furutin (protein) fiye da kima a fitsarinsu ko wani alamu na lalacewar wani daga cikin muhimman gaɓoɓin jikinsu (organ damage).
    2. Chronic hypertension. Chronic hypertension wato hawan jini ne da ya tsananta wadda kuma yana nan ne a jikin mace kafin ma a ce ta sami juna biyu ko kuma kafin cikinta ya kai sati 20. Saboda ita cutar hawan jini ba kasafai ta ke nuna alamunta ba, to yana da wuya a san lokacin da cutar ta shigi mutum.
    3. Chronic hypertension with superimposed preeclampsia . Wannan yanayi na faruwa ne ga matan da suke da chronic hypertension kafin shigan ciki waɗanda suke fama da tsananin hauhawar jini (worsening high blood pressure) da kuma furutin a fitsarinsu ko kuma wasu matsaloli na daban da hawan jini ke kawowa a lokacin juna biyu.

    _hatsarurrukan hawan jini ga mai juna biyu

    _yaya za ki gane kina da hawan jini

    _matsayin shan maganin hawan jini ga mai juna biyu

    _abubuwan da mace mai hawan jini ke buƙata wajen likita

    _hanyar kariya

    Sannan yana da kyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

  • Hawan Jini (Hypertension)

    Hawan Jini (Hypertension)

    Menene Hawan Jini?: Hawan jini ciwo ne da yake samuwa sakamakon ƙaruwa ko hawa da jinin mutum ke yi fiye da kima (persistent rise in blood pressure).
    Yayin Kamuwa Da Cutar

    Jijiya, wato makwarara ko kuma hanyoyin da jini ke bi (blood vessels), sukan zama ƙanana ko kuma su toshe saboda wasu dalilai da su ma wasu cututtuka ke kawo su to da zarar jijiyoyin jinin sun matse sai yanayin ya haifar da haurawar jini, wato (increase in blood pressure), wannan haurawa na jini yakan ƙarawa zuciya ɗawainiya.

    Saboda da wannan ɗawainiya da zuciya ke yi sai jijiyoyin zuciyar su riƙa samun rauni a kai-a kai har a ƙarshe sai a samu matsalar ciwon zuciya, (wato cardiac falure )

    Alamominsa

    Alamomin hawan jini sun danganta ne daga mutum to amma akwai wasu manyan alamomi da ake samunsu ga kowa: 

    • Matsanancin ciwon kai
    • Ciwon ƙirji
    • Matsalar gani
    • Ciwon jiki
    • Numfashi da ƙyar
    • Faɗuwar gaba 
    Abubuwan Da Ke Haifar Da Ciwon

    Yanayin rayuwar mutane da ɗabi’un su na yau da kullum suna taka rawar gani sosai wajen haifar ko kawo masu wannan ciwo na hawan jini kamar su.

    • Shan taba 
    • Shan giya
    • Yawan cin abu mai gishiri

    masu wannan ɗabi’a suna cikin haɗarin kamuwa da cutar hawan jini.

    Hanyar Kariya
    • Rabuwa da shan giya: Shan giya na da matuƙar haɗari ga lafiyar mai ta’ammuli da ita ƙwarai ainun ciki har da ƙara ruruta wutar ciwon hawan jini.
    • Motsa jiki a kai-a kai (regula excersise): Motsa jiki na da muhimmanci ga rayuwa sosai haka nan ma yake da amfani wajen yaƙar ciwon hawan jini.
    • Cin abinci mara gishiri: Wannan irin abinci na taimakawa wajen daidaita electrolyte a jiki sannan zai yi controlling blood pressure.
    • Yawan cin ‘ya-‘yan itace da ganyayyaki (fruits and veggies): Yawan cin ‘ya-‘yan itace da ganyayyaki wato vegitables na rage cholesterol wadda ke taimakawa wajen rage hauhawan jini.
     Jan Hankali

    Mai hawan jini ya kamata ya kiyaye umarnin likita na shan magani, kiyaye amfani da gishiri kaɗan, haƙura da amfani da kanwa, sannan da zuwa asibiti domin ganin likita ba sai lokacin da matsala da faru ba.

    Rashin kula da ƙa’idar da likita ya shimfiɗa kan iya haddasa matsalar zuciya a ƙarshe.

    Domin karanta bayani a kan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya Shiga nan