Tag: Haƙuri

  • Amfanin Haƙuri

    Amfanin Haƙuri

    Haƙuri: Shi ne danne zuciya a kan wani abu mara kyau, wanda ya baƙantawa mutum zuciya.

    Haƙuri yana da matuƙar amfani ga mutane, kamar yadda ya zo a cikin littafin Sheikh Abdulrahim bin Ahmad Alkadhi mai suna “Daƙa’ikul khabar” shafi na 17 babi na goma sha biyu yace, labari ya gangaro cewa wanda aka jarabce shi da wata masifa, sai ya yaga tufafin sa ko ya bugi ƙirjin sa (to hukuncin wanda ya aikata haka) kamar (wanda) ya riƙi makami ne zai yi yaƙi da Allah (Subhanahu wata’ala).

    Sannan kuma an ruwaito daga Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yace wanda ya ɓalle ƙofa ko ya yaga tufafin sa ya yi da wata masifa ta same shi ko ya bugu wajan zaman sa ko ya sare bishiya ko ya yanke gashin kan sa (saboda tsanani masifar da ta same shi), to za a gina masa gida na wuta a kan kowane gashi (wanda ya cire), sa’annan kuma Allah ba zai karɓi aikin sa na farilla ba ko na nafila matuƙar yana kan wannan hali.

    Har ila yau, Allah zai ƙuntata ƙabarinsa, kuma zai tsananta yi masa hisabi, sannan kuma dukkanin mala’ikun da suke sama da ƙasa za su dunga tsine masa, haka kuma za a rubutawa laifuffuka guda dubu a gare shi, sannan zai tashi a cikin ƙabarin sa tsirara.

    Haka kuma, wanda ya karya gefan jikin sa, saboda wata masifa, to Allah zai karya addinin sa, idan kuma ya bugi ko ya mari kumatun sa ko ya azabtar da fuskar sa, to Allah (Subhanahu wata’ala) ba zai kalle shi ba da rahmar sa ba ranar alƙiyama.

    Bugu da ƙari, kuma ya zo a cikin shafi na 18, babi na goma sha huɗu a cikin wannan littafin yace Sayyadina Aliyu bin Abu-ɗalib (karramallahu wajhahu) yace “haƙuri ana yin sa ne ta hanyoyin guda uku; na farko yin haƙuri a kan yi wa Allah biyayya, na biyu yin haƙuri a kan saɓawa Allah, na uku haƙuri a kan wata masifa wacce ta samu mutum.

    Saboda haka, duk wanda ya yi haƙuri a kan yi wa Allah biyayya, to Allah zai ba shi daraja guda ɗari, sa’annan kuma ko wace daraja yawanta ta kai tsakanin sama da ƙasa.

    Wanda kuma ya yi haƙuri a kan saɓawa Allah, to Allah zai ba shi daraja guda ɗari shida ranar lahira, haka kuma kowace dajara yawan ta ta kai faɗin sama da ƙasa, wanda kuma ya yi haƙuri a kan wata masifa wacce ta same shi, to Allah zai ba shi lada ba tare yi masa hisabi ba (ranar lahira).

    Karanta Tarihin Farfesa Abdallah Uba Adamu

    Edita@rumasau-kallamu

  • Matakan Zaman Lafiyar Kishiyoyi, Haƙuri Da Junansu A Kan Kurakurai

    Matakan Zaman Lafiyar Kishiyoyi, Haƙuri Da Junansu A Kan Kurakurai

    Haƙuri da kau da kai game da kura-kuren kishiya; shi ne mafi girman abubuwan da suke wanzar da zaman lafiya a tsakanin kishiyoyi. Ga abin da Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce a game da muhimmancin haƙuri: 

    “Ka yi haƙuri a kan duk abin da ya same ka, haƙiƙa yin hakan na gaba cikin muhimman al’amura”. 

    Kyautata wa Junansu Zato: 

    Watsi da tseguma tare da nisanta munanan zace-zace marasa dalilai game da kishiya, shi ma yana daga cikin abubuwan da kishiyoyi ya kamata su yi, kuma dimantar kulawarmu da hakan, shi zai ba mu damar aiki da tarbiyyar da addininmu ya ɗora mu a kai ta kyautata wa junanmu zato. Allah (Subahanahu Wata’ala) ya ce: 

    Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

    Ina dai ma lokacin da kuka ji (mummunan zato da aka yi wa A’isha) uwar muminai maza da muminai mata sun yi wa junansu zaton alheri, kuma su ce wannan ai ƙage ne bayyanan ne”. (Suratun Nur,12). 

    Kuma an Karɓo hadisi daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Na hana ku mummunan zato, haƙiƙa, mummunan zato shi ne mafi ƙaryar zance”. (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi). 

    Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

    Sanin Haƙƙoƙinsu Da Kiyaye Su da Isar da Su a Junansu: 

    Kyautata wa kishiya da kuma mai da komai ba komai ba, dalili ne ƙwaƙƙwara da yake tabbatar da zaman lafiyar a tsakaninin kishiyoyi

    Imamul Bukhari da Muslim sun rawaici hadisi da aka karɓo daga A’isha, Allah ya yarda da ita, ta ce: “Yayin da Saudat ƴar Zam’a (matar Annabi) ta manyanta ta ba wa A’isha ranar kwananta, sai Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya zama yana raba wa A’isha kwanan Sauda (ƙari a kan nata kwanan). 

    Wannan kyakkyawan misali ne da yake sanar da matanmu yadda ya kamata su zauna da kishiyoyinsu. 

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan