Tag: gidan miji

  • Haƙƙin Zaman Gidan Miji

    Haƙƙin Zaman Gidan Miji

    Tabbatar mace cikin gidan mijinta doka ce tabbatacciya daga Allah Maɗaukaki, ga abin da Allah yace: “(ku mata) ku tabbata cikin gidajenku, kada ku bayyanar da adonku irin bayyanar da adon maguzancin farko”. 

    Bisa dogaro da wannan ayar, haramun ne mace ta fita daga gidan mijinta ba tare da izininsa ba, ko da kuwa ta leƙa waje ne. 

    Wannan yasa wani ɗan uwa ya gargaɗi mata da cewa: 

    Sai ta ukunsu gadangama ke nan, 

    Ba ta nufin gyara sai cuta. 

    Bata nufin khairi ga mijinta, 

    Baga kishiyoyi ba ga mafiotaba. 

    Ba ta nufin gyara sai ɓarna, 

    Sai duka safe ta cuci mijinta. 

    Ya tafi ofis ko kuma kanti, 

    Ba ta ƙara zama ɗakinta. 

    In mai noma ne ko zage, 

    Ka tafi gona zaure za ta. 

    Ta na neman ta ga masu wucewa, 

    Wai ita dai su ga kyan fuskarta. 

    In ta ga sun ƙi shiga harkar ta, 

    Sai ka ji ta ce za ta maƙobta.

    AYYUKAN CIKIN GIDA 

    Imamul Bukhari da Muslim sun rawaici hadisi da aka karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas, Allah ya yarda da su, daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: “Dukkanku makiyaya ne, kuma dukkanku ababan tambaya ne game da abubuwan kiwonku,…. Mace ma makiyayiya ce a kan gidan mijinta da ‘ya’yansa, kuma ita ma abar tambayace game da abubuwan kiwonta”. 

    Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

    Sannan an karɓo hadisi daga Asma’u ‘yar Abubakar Siddik, Allah ya yarda da su tace: “Na kasance ina yi yi wa zubairu (mijina) hidindimun gida baki ɗaya, kuma ya kasance yana da wani doki da nake wahala da shi, ina yi masa ciyawa kuma ina kula da shi”. Iman Ahmad ne ya rawaito shi. 

    A wata ruwayar kuma (Asma’u) ta ƙara da cewa, tana ɗinke guga, da kwaɓa gari. Ahmad ne ya rawaito shi. 

    Sannan kuma dai an karɓo hadisi daga Aliyu, Allah ya yarda da shi, yace, haƙiƙa matarsa Faɗima da ta sami labarin an kawowa Annabi (Tsira da amincin Allah ya su tabbata a gare shi) bayi, sai ta je gida domin ta kokawa Annabi (tsiri da amincin Allah su tabbata a gare shi) game da kantar da hannunnta yake yi a sakamakon amfani da dutsen niƙa (ko ya agaje ta da baiwa). 

    Da ba ta sami Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) a gida ba, sai ta gayawa Aisha (R.A), da Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) ya dawo, sai Aisha ta faɗa masa saƙon Faɗima, sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya tafi gidan ‘yarsa Faɗima; ko da ya isa sai ya tarar da ita da mijinta Aliyu (R.A)

    Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

    Sun riga sun kwanta bacci, da suka yunƙura za su ta shi domin taro shi, sai yace da su ku yi zamanku a inda kuke, sannan sai ya zauna kuma yace da su: “Ashe bana sanar daku abin da ya fi wanda kuka tambaya ba, idan za ku kwanta bacci ku yi tasbihi talatin da uku, hamdala talatin da uku, takbir kuma sau talatin da huɗu”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito. 

    Duba da waɗannan dalilai da wasunsu ne wasu daga cikin malamai suka yanke hukuncin cewa: ɗaukar ɗawainiyar aikace-aikacen da suka shafi cikin gida nauyi ne da ya rataya a wuyan matar aure.

    Ko da yake ba laifi ba ne a shari’ance ga wanda yake da iko ya samo wa matarsa ‘yar aiki, sai dai fa ba ita ba samun ladan da ake ba wa waɗanda suka tsayu da kansu domin aiwatar da waɗannan ayyuka na cikin gida yaku ‘yan uwa mata! ku sani fa ba ƙasƙanci ba ne ku tsayu da: 

    ⮚ Ba wa dabbobin miji abinci da kuma share garkensu. 

    ⮚ Wanke banɗaki. 

    ⮚ Sharar tsakar gida. 

    ⮚ Dafa abinci. 

    ⮚ Gyara shimfiɗa. 

    Da sauran su. 

    Waɗannan abubuwa dukkansu share fagen shiga Aljanna ne, shi yasa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) da sahabbansa ba su goyi bayan ‘ya’yansu da matansu su yi watsi ko sakaci da su ba. Wannan ke nan. 

    Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

  • Ladubban Tarewa A Gidan Miji

    Ladubban Tarewa A Gidan Miji

    A daren tarewa abubuwa guda goma sha ɗaya (11) ya kamata ma’aurata masu addini da wayewa su aikata:

    1. Addu’ar shiga gida
    2. Sallama
    3. Shigowa da abincin da ya dace
    4. Sallatar nafila raka’a biyu tare
    5. Karanta wannan addu’o’in
    “Allahumma baarik liy fiy ahliy wa baarik lahum fiyya. Allahummaj ma’a bainana ma jama’ata bi khairin wa farriq bainana iza farraqta ila khairin” ko kuma “Allahumma baarik liy fiy ahliy wa baarik li ahli fiyya, Allahummar zuqhum minni warzuqni minhum, Allahummaj ma’a bainana ma jama’ata fi khairin wa farriq bainana iza farraqta fi khairin’’

    6. Sannan ango ya kama goshin amaryarsa ya karanta

    Allahumma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi wa a’azu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi’’

    7. Taƙaitacciyar hirar ɗebe kewa da soyayya

    8.  Su yi wanka da brush

    9. Idan ba ta jinin al’ada a yi mu’amalar aure su karanta ‘Bismillahi, Allahumma jannabinas shaidan wa jannaibis shaidana ma razaqtana’’

    10. Kiyaye ladubban mu’amalar aure

    11. Bayan an gama a yi wanka ko alwalla kafin kwanciya.

    Washegarin tarewa, ma’aurata suna zaunawa dogon lokaci domin meeting, su tattauna a kan yadda za su rayu har ƙarshen rayuwa cikin ƙauna da haɗin kai, a tsara gida da yadda zamantakewa za ta kasance, domin rayuwa ta ilmi, ƙauna da tausayawa, su fahimci manufofin juna da tsare-tsaren juna, tafiya a kan tsari shi ne asasin saurin isa ga manufa. Masu hikima na cewa “Zo mu zauna zo mu tsara

    RUFEWA

    Kiyaye ladubban zamantakewar aure shi zai bai wa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon, shi zai sanya al’umma ta zama a kan saiti da ci gaba, wanda akasin haka zai jefa al’umma cikin mummunar makoma. Allah jalla wa Alaa ya kiyaye.  Dr. Muhammad Sani Umar ya na cewa: “Masu miyagun tunani sun ɗago kai, suna aiki dare da rana domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida. Idan miji da mata suka sami hada kansu bisa turba ta musulunci to sai ka samu yayansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya, To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba akan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.

    Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.

    Subhanakallahumma wa  bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.

    karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki  ko domin sauki cikakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutu