Tag: Aure A ƙasar Hausa

  • Aure A Ƙasar Hausa

    Aure A Ƙasar Hausa

    MA’ANAR AURE A ƘASAR HAUSA

    Wata yarjejeniya ce, wacce ake ƙulla ta a tsakanin namiji da mace, wacce ta dace da shari’ar musulunci. A ƙasar Hausa, za  mu iya cewa aure, wata hanya ce, wacce Bahaushe yake bi, don samun yaɗuwar iri, wanda yake zama da matarsa, kuma al’ada da shari’a suka amince da haka. Ƙasar Hausa, idan mutum zai auri mace, ana buƙatar ya;

    1. Tuntuɓi iyayenta.

    2. Amincewar yarinyar.

    3. Sadakin aure.

    4. Kayan aure.

    5. Matsuguni.

    6. Sana’a.

    7. Goro.

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Ma’anar Aure A Ƙasar Hausa

    Ma’anar Aure A Ƙasar Hausa

    Auren Hausawa – Auren nan na da ma’anoni da dama daga masana; domin sun yi ƙoƙarin faɗaɗa ma’anar zuwa ga ɓangarori da dama; amma a nan za mu kalli ma’ana guda ɗaya wadda ta dace da batunmu.

    Auren Hausawa – CNHN (2006:22) ya bayyana shi da cewa, “Dangantaka tsakanin namiji da mace ta hanyar shari’a”.

    Domin ƙarin bayani a kan aure danna nan https://wikihausa.com.ng/maanar-aure/

    A nan, za mu iya cewa, aure nufin haɗuwar mutane biyu (namiji da mace) bisa wasu sharuɗa da shari’a ta gindaya domin tabbatar da zaman tare na har abada.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga Littafin Nazarin Matsalolin Aure a Ƙasar Hausa Daga Mahangar Zabiya Lawisa da Fatima Jalo wanda Ibrahim Baba(Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Muhimmancin Aure a Ƙasar Hausa danna nan

    Domin karanta bayani akan Manufar Rayuwar Aure A Addini Da Wayewar Zamani danna nan