Tag: abincin gyada

  • Yadda Ake Groundnut Sweet potato Pie

    Yadda Ake Groundnut Sweet potato Pie

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah. A yau zamu koyar da yadda ake yin groundnut, sweet potato pie, ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san dankalin Hausa na ɗauke da sinadarin vitamin B,C,E da vitamin K wanda yake yaƙi da kwayoyin cuta a jikinmu.

    Abubuwan Buƙata

    Yadda za a haɗa pie                                           yadda za a yi Fillings
    1. fulawa kofi 2                                                   Dankalin Hausa guda ɗaya.
    2. Baking powder babban cokali ɗaya                   Gyaɗa ½ kofi
    3. Man gyada Albasa
    4. Gishiri ½ ƙaramin cokali                                  Attaruhu 2 matsaƙaita
    5. Ƙwai guda ƙaya (na shafawa kafin gashi)          Tafarnuwa 1
    6. Man suya                                                       Sinadarin ɗanɗano  guda1
                                                                            Thyme ½ rabin ƙaramin cokali
                                                                            Fulawa 2 cokali babba iyu
                                                                            Kori curry½ ƙaramin cokali

    Yadda ake haɗawa

    1. A cikin tukunya a zuba gyaɗa a dafa ta dahu da kyau, idan ta dahu sai a saka dankali, idan ya dahu, sai a tace su, a ajiye a gefe
    2. Cikin tukunya mara zurfi a zuba mai chokali biyu, a zuba albasa, a ɗan ba ta tsoro, sai a zuba attarahu tare da tafarnuwa da sinadarin ɗanddano, thyme da kori(curry) a juya na minti 1-2
    3. A zuba dankali da gyaɗa a ɗan juya
    4. A cikin ƙaramin kofi, a haɗa fulawa da ruwa ,sai a zuba cikin wannan haɗin dankali da gyaɗa dake wuta, sai a bar shi ya ɗan hade na minti biyu kafin a kashe wuta.

    Yadda zamu haɗa pie ɗinmu

    1. A murza fulawa da man gyaɗa sosai, sai a zuba ruwa da gishiri a murza, ya murzu da kyau, sai rufe shi na minti 5-7 domin ya haɗe da kyau
    2. Bayan wannan mintuna, sai a sake murza shi, sannan a yi rolling a sami meat pie cutter, in babu a sami ɗan roba ko kofi mai ɗan girma, sai a ringa yanka fulawa da shi circle-circle
    3. A zuba wanna hadin gyaɗa  da dankali a tsakiya, sai  a shafa ruwan fulawa a gefe sannan rufe, a danna cokali mai yatsu
    4. A shafawa pie din ruwan ƙwai
    5. A gasa na minti 30 ko sama ko kuma idan ya yi ruwan ƙasa wato golden brown.