MUHIMMANCIN SANIN TARIHI (NA 1)

0
1189

Abin da ake cewa tarihi shi ne, sanin haƙiƙanin labarin abin da ya gabata na wata al’umma ko jama’a ko kuma wani zamani da ya gabata.

Sanin hakan, na daga cikin abin da zai faɗaɗa tunanin mutum, da kyautata dabi’unsa ta hanyar ganin kurakuren da suka faru don kauce musu. Da kuma ganin wuraren da suka dace don koyi da su da zartar da su ta sahihiyar hanya.
Wannan ne yasa ga duk wanda yake bibiyar karatun Alƙur’ani mai girma (amma karatu na fahimta) zai ga tarihin al’ummomin da suka gabata da Annabawansu,
Nagartattunsu da kuma lalatattunsu da irin hasara da ribar da kowa ya samu.
Wannan ce ta sanya duk wanda bai san sahihin tarihi na gaskiya ba, ke afkawa cikin wahala da kwaikwayo da halaka, har ta kai shi, ga matsayin da bai san a ina yake ba.
Shi ya sa Allah maɗaukakin Sarki yake cewa:
يا ايها آلذين آمنوا ان جائكم فاسق بنىا فتبينوا ان تصيبوا قوما بجهالة فتصبحوا على ما فعلتم نادمين.
Ma’ana”-
“Ya ku waɗanda kuka bayar da gaskiya, idan wani (fasiqi) ya zo muku da labari, to, ku yi bincike don kada kuje ku afkawa wasu jama’a bisa rashin sani, kuma ku wayi gari kuna masu nadama,(wato dana sani)”.

Don haka, a wannan taƙaitaccen rubutu za mu gabatar da tarihin wannan addini tun daga ranar da Annabi (S.A.W) ya fara jinyarsa ta rashin lafiyarsa na barin duniya, har zuwa inda Allah (S.W.T)ya ba mu iko gwargadon abin da malaman tarihin Musulunci suka faɗa a littattafai sahihai, tare da yin bayanai filla-filla don a fahimci gaskiyar lamari, don wanda zai shiriya ya shiriya bisa hujja, wanda kuma zai ɓata ya ɓata bisa dalili.
ALLAH YA SA MU DACE

labarin da ya wuceYadda Ake Haɗa Brownies Na Musamman.
Labarin na GabaMUHIMMANCIN SANIN TARIHI (2)