-
Faisal Haruna Hunkuyi posted an update 1 year, 2 months ago
MATAKA KULA DA TARBIYYA
Kalmar tarbiyya, ararriyar kalma ce daga Larabci (التربية aka Hausantar da ita. Kalma ce magamaiya, wacce ke iya ɗaukar ma’ana ta rainon jikin yaro; hanyoyin kyautata ruhi da kuma koyar da kyakkyawar cuɗanya da jama’a. Abin da ake nufi a nan shi ne cewa, tarbiyya ta shafi gangar jiki, ruhi da kuma yadda mutum yake cuɗanya da sauran jama’a, a al’ummance da kuma ɗaiɗaiku.
Ƙololin buƙatar tarbiyya ita ce gina cikakken mutum mai amfanar da kansa da kuna waninsa.
Kaɗan daga cikin abubuwan lura yayin dasa tubalin tarbiyya;
1-Zagin yaro tare da kushewa ko da yaushe hakan na iya zamw sanadin lalacewarsa.
2-Tsangwama ga yaro na jawo masa rashin walwala.
3-Kushe Yaro kullum nasa shi ya raina kansa.
4-Kunyata yaro nasa shi ya dinga zargin kansa.
5-Koyawa yaro juriya nasashi ya zama mai hakuri.
6-Idan ana yaba yaro yakan tashi da kishin zuci.
7-Idan ana kyautatawa yaro hakan na sanyashi ya zama mai gaskiya.
8-Tarbiyya ga yaro takan sanya shi ya zama amintacce.
9-Idan aka amince da yaro hakan yakan sanyashi ya ji dadi.
10-Sakin fuska ga yaro shi ke janyo shi cikin jama’a. Iyaye mu kiyaye.
Gida Activity