Activity

  • Faisal Haruna Hunkuyi posted an update 1 year, 2 months ago

    MATAKA KULA DA TARBIYYA
    Kalmar tarbiyya, ararriyar kalma ce daga Larabci (التربية aka Hausantar da ita. Kalma ce magamaiya, wacce ke iya ɗaukar ma’ana ta rainon jikin yaro; hanyoyin kyautata ruhi da kuma koyar da kyakkyawar cuɗanya da jama’a. Abin da ake nufi a nan shi ne cewa, tarbiyya ta shafi gangar jiki, ruhi da kuma yadda mutum yake cuɗanya da sauran jama’a, a al’ummance da kuma ɗaiɗaiku.
    Ƙololin buƙatar tarbiyya ita ce gina cikakken mutum mai amfanar da kansa da kuna waninsa.
    Kaɗan daga cikin abubuwan lura yayin dasa tubalin tarbiyya;
    1-Zagin yaro tare da kushewa ko da yaushe hakan na iya zamw sanadin lalacewarsa.
    2-Tsangwama ga yaro na jawo masa rashin walwala.
    3-Kushe Yaro kullum nasa shi ya raina kansa.
    4-Kunyata yaro nasa shi ya dinga zargin kansa.
    5-Koyawa yaro juriya nasashi ya zama mai hakuri.
    6-Idan ana yaba yaro yakan tashi da kishin zuci.
    7-Idan ana kyautatawa yaro hakan na sanyashi ya zama mai gaskiya.
    8-Tarbiyya ga yaro takan sanya shi ya zama amintacce.
    9-Idan aka amince da yaro hakan yakan sanyashi ya ji dadi.
    10-Sakin fuska ga yaro shi ke janyo shi cikin jama’a. Iyaye mu kiyaye.