-
Abba Yusuf posted an update 1 year, 3 months ago
HAUSAWA DA YAREN LARABCI
Da yake addinin Musulunci yana tafiya ne ɗanɗan da yaren Larabci ta yadda duk in da aka ga ɗaya to ba shakka ɗayan ma ya na nan in akayi duba na tsanaki, duk da kuwa cewa shi Larabci bai cika neman rakiyar Musulunci ba in yai aniyar shiga wani lardi. Akwai zantuka mabanbanta dangane da shigowar waɗannan tagwaye ƙasashen yammacin Afirka.
Ustaz sa’id galadanci a littafinsa mai suna (حركة اللغة العربية وآدابها في نيجيريا) ya ambaci wasu hanyoyi da masana suka bayyana cewa ta su ne addinin Musulunci da yaren Larabci suka sami shigowa wannan yanki na mu na ƙasar hausan waccen lokacin. Idan muka ajiye batun shigowar Sahabin Annabi (saww) Wasil bin Aɗa(ra) wanda aka ce shi ne ya kawo Musulunci Afirka ta wannan lokacin, ko in ce akace da’awarsa ta dangane da wani yanki na lardin, kamar yanda wasu suka ce Libiya ce ƙasar da ya dakata, amma bayan wafatinsa da’awa ta ci gaba har ta mamaye yankin gaba daya.
Duk da cewa ba maganar shigowar addinin Musulunci wannan yanki na ke ba, amma babu lefi da na ɗan ci ramaniya na wuce. Ba kamar sauran yankuna da addinin Musulunci ya je musu ta ƙarfi ba, wannan kuma har yankin labarawan mu nan ba a kashe ko daki ko mutum ɗaya da sunan ya yi imani ba, waɗanda sukazo da’awa sukayi ba jahadi ba.
Mu koma ga batun shigowar larabcin da na faro. Maganar da ta tabbata cikin littatafan tarihin zuwan Larabawa wannan yanki ta nuna cewa lalle Larabci shi ya fara zuwa qasar Hausa kafin addinin Musulunci ya shigo, domin kuwa a tarihi akwai wadanda aka qira da “TUJJARU” da kuma “DU’ATU”.
Tujjaru wadansu mutane ne da suka shigo ƙasar Hausa domin kasuwanci, waɗanda su ne bakuwar Al’umma ta farko da bahaushen wannan yanki ya fara mu’amala dasu daga ƙabilun da ke nesa sosai da ƙasar Hausa. Lokacin da wadannan rukuni suka shigo ƙasar Hausa sun iske al’ummar da ba ta jin yarenta haka suma ba sa jin na ta yaren.
Manyan abubuwan da waɗannan ƴankasuwa suke siyarwa su ne Dabino da kuma makamai, irinsu Masu, takuba da sauransu. An ce lokacin da waɗancan Larabawa suka fara tallata dabinon da suka zo da shi sun fuskanci matsalar saɓanin harshe, Wanda kuma shi ne ya basu haske tun farko kan cewa lalle suna da buƙatar sanin harshen waɗannan al’umma da suka tarar domin sauƙaƙa harkar siye da siyarwa. Bahaushen wancan lokacin baisan kalar dabino irin na ƙasashen larabawa ba sai a wannan karo dan haka yana da buƙatar farko ya san menene ma tukunna sannan ya siya idan yana da buƙata. Da larabawa suka fahimci Hausawa suna yiwa wannan haja ta su kallon ko meye wannan? Sai suke amfani da kalmar “KUL” wacce a yarensu ta ke nufin “CI” ma’ana dai ya kai wannan da ya ke kallon wannan abu wanda kallon ke nuna kamar bai san menene ba, “CI” ka ji yanda yake, sai akayi rashin sa’a domin kuwa kalmar “Kul” a yaren Hausa tana nufin “BARI” ko “KAUCE” ma’ana dai kalma ce da take nuni da hani, a can kuma tana bufin Umarni, dan haka duk mutumin da ya zo zai sayi Dabino sai Balarabe ya ce masa “KUL” sai mutum ya kauce ya basu guri abinsa, wannan itace abin da ya fara hada wadannan yaruka mu’amala.
Su kuma DU’ATU sun shigo ne domin yaɗa addinin Musulunci duk da kuwa ance waɗancan ƴankasuwar sunyi abin da sukayi wajen yaɗa Musulunci su ma, musamman yanda waɗanda suka sauƙesu da waɗanda suka ɗauka yara a kasuwancin da suke suka karɓi Musulunci, amma dai ba kamar yanda DU’ATU suka yi ba, a nan zamu iya cewa DU’ATU sune kamar missionaries da suka shigo don yada addinin masihiyanci.
Da yake zanyi magana ne a kan alaƙa ba tarihi ba kai tsaye, amma babu lefi idan na tsagaita haka na kuma dunfari abin da zai fissheni na bayyana wannan daɗaɗɗiyar alaƙa ta fuskar yare da al’adu.
Kamar yanda yake a bayyane cewa Larabci da larabawa sun sami tagomashin girmamawa da soyayya ne kasancewarsu wasu kayan aiki ko alamomi manya da ke nuni kai tsaye ga samuwar addinin Musulunci a duk bigeren da aka ji ko aka gansu. Wannan tasa yaruka da dama kan saki al’adu wani lokacinma da shi kansa yaren na su su rungumi Larabci da al’adun Larabawa a tsammaninsu da ƙoƙarinsu na zama yanda Musulunci yake son su zama.
Misali mu ɗauki yaren Hausa da al’adun Malam Bahaushe, ba na jin a tarihi an taba samun wata ba’ajamiyar Al’umma da ta ke ganin mutuncin Larabci da Larabawa kamar Hausawa, na san da cewa wasu ma barin yarensu su ka yi su ka runguni Larabcin Wanda ta Kai ga yau babu ɗuriya bare labarinsa. Duk da muma ana cewa kaso 60 cikin ɗari na kalmominmu Larabci ne (duk da akwai waɗanda suke ganin adadin bai kai haka ba, kuma sahihin bincike ya gaskata su) wanda hakan ta faru ne sakamakon kasancewarsa harshen ƙetare na farko da Bahaushe ya fara mu’amala da shi.
Daga cikin tagomashin da Larabci ya samu akwai karɓuwar wasu kalmominsa zuwa yaren Hausa kamar yanda na bayyana da farko wanda maikaratu zai so yasan dalilin da yasa ake ganin kalmomin ba na Hausa ba ne asalaninsu, da kuma yanda ake bi a gano.
Ga masu karantar kimiyyar harshe akwai hanyoyi da dama da ake iya gane asalin inda kalma ta tsiro, shigowa ta yi ko ƴarsalai ce, daga cikin hanyoyin da ake bi a gano asalin kalmar Larabci a yaren Hausa akwai la’akari da harufan “AL” (ma’arifa) a farkon kalma, ma’ana kusan duk kalmar Hausa da ta fara da “AL” to ana kyautata zaton balarabiyar Kalma ce asalinta, misalinsu sune:
1-Alkama – Al-ƙamha
2-Alkaki – Al-ka’aka’a
3- Allo – Al-lauhu
4- Almakashi – Al-miƙsu
5- Albasa -Albaslu.Amma kuma in mukayi duba ya zuwa irin wadannan kaomomi za muga daman yawancinsu kalmomi ne da suke nufin abubuwan da larabawan ne suka fara shigo mana da shi, Dan haka bahaushe yake amfani da sigar da yaji mai su “Balarabe” yana kiransu shima yake kiransu da shi.
Alhamdlilah gwara kalmomi ma daman anayi domin shima larabcin ya aro da dama daga Farisanci, ga wanda yake karantar kimiyyar harshe na Larabci ya san da wannan ƙadiyar. Kuma dama aro ba kashi bane ga yare, bilhasli ma duk yaren da baya aro to akwai yiwuwar ya mutu.
Abban Marke
Ɗalibi mai nazartar Yaren Larabci a matakin digiri na biyu a jami’ar Sule Lamido da ke Kafin-Hausa ta jahar Jigawa.
Gida Activity