Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

A large edible toad - A turance tana nufin bududdugi. Misali; Matasan na gasa bududdugi a dandali. HAU; Bududdugi (Tana nufin ƙaton kwaɗo wanda ake iya ci)
A less favoured wife - A turance tana nufin bora. Misali; Lami bora ce a gidan Alhaji Mato. HAU; Bora (Tana nufin matar da ba ta da cikakken gata a gurin mijinta)
Abarba - Abarba na ɗaya daga cikin kayan marmari mai zaƙi, tana da amfani sosai a jikin ɗan adam. Jam'i : Abarba
Abinci - Yana nufin duk abinda za a ci ya kawar da yunwa. Misali; Muna cin abinci sau uku a rana. ENG; Food/Meal (A turance yana nufin abinci)
Abuja Geographic Information System (AGIS) - Hukumar Tsara mahalli Ta Abuja
Abundantly - A turance tana nufin birjik. Misali; Kaya ne birjik a shagon su Bala, sai wanda ka zaɓa. HAU; Birjik (Tana nufin da yawa ko adadi mai yawa)  
Academic Staff Union Of Polytechnics (ASUP) - Ƙungiyar malaman manyan makarantun fasaha
Academic Staff Union Of Secondary Schools (ASUSS) - Ƙungiyar Malaman Makarantun Sakandare
Academic Staff Union of Universities (ASUU) - Kungiyar Malaman Jami'a
Academy - Makaranta, Cibiya
1 2 3 146