Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
- A turance tana nufin cifjoji.
Misali; Ai wanda ya yi mana shari'ar cifjoji ne, kuma ya kwatanta adalci.
HAU; Cifjoji (Tana nufin alƙalin alƙalai)
A fragrant herb - A turance tana nufin ɗaɗɗoya.
Misali; An yi amfani da ganyen ɗaɗɗoya wajen haɗa maganin.
HAU; Ɗaɗɗoya (Tana nufin wani ganye mai ƙamshi wanda ake magani da shi)
A large edible toad - A turance tana nufin bududdugi.
Misali; Matasan na gasa bududdugi a dandali.
HAU; Bududdugi (Tana nufin ƙaton kwaɗo wanda ake iya ci)
A less favoured wife - A turance tana nufin bora.
Misali; Lami bora ce a gidan Alhaji Mato.
HAU; Bora (Tana nufin matar da ba ta da cikakken gata a gurin mijinta)
A moment ago - A turance tana nufin ɗazu.
Misali; Ɗazu na dawo daga gidan bikin.
HAU; Ɗazu (Tana nufin lokacin da be daɗe da wucewa ba)
Kishiyarsa; Yanzu
A parasitic plant which grows on trees - A turance tana nufin kauci.
Misali; Ana amfani da kauci wajen magungunan cututtuka da dama.
HAU; Kauci (Tana nufin wani tsiro da yake fitowa a jikin bishiya, kuma yana fitowa ne sakamakon sauka da tsuntsaye ke yi daga wata bishiyar zuwa wata)
A person who has no Fulani ancestry - A turance tana nufin kaɗo.
Misali; Fulani ba sa son 'ya'yansu su auri kaɗo.
HAU; Kaɗo (Tana nufin wanda ba bafulatani ba)
A traditional title - A turance tana nufin galadima.
Misali; An naɗa malam Sani galadima jiya da safe.
HAU; Galadima (Tana nufin muƙamin sarauta)
A traditional title - A turance tana nufin kaigama.
Misali; An naɗa shi sarautar kaigama yau da safe.
HAU; Kaigama (Tana nufin ɗaya daga cikin sarautun gargajiya)
A tree whose bark is used as medicine - A turance tana nufin kargo.
Misali; Garin sassaƙen kargo na maganin ciwon haƙori, ciwon kunne da ciwon ciki.
HAU; Kargo (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'ikan bishiya mai matuƙar amfani wajen yin magunguna daban-daban)