Tag: Sihiri

  • Alamomin Da Ake Gane Sihiri

    Alamomin Da Ake Gane Sihiri

    Ana gane sihiri daga alamomi kamar haka:

    • Yawan ɓacin rai ba tare da an maka laifi ba
    • Kasala a lokacin da ka yunƙura za ka yi wani abu mai muhimmanci a gareka ka ji zuciyarka ba ta son abin
    • Yawan ƙunci a ranka
    • Lalacewar al’amura ka ga duk abinda ka sako ka yi mai amfani a gareka ka ga ya ƙi yiwuwa.
    • Sannan za ka ji kamar kai kaɗai aka tsana, kamar kowa ba ya sonka
    • Namiji ya  ji ya tsani iyalinsa haka in mace ce taji ta tsani mijinta. Ko ya shiga ɗakin iyalinsa ya ji ba ya iya mu’amalantar ta da komai. Ana samun haka yana kasancewa da mai mace ɗaya ko biyu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Zirga-Zirga Tsakanin Bokaye Da Masu Duba Don Neman Duniya danna nan. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Shin Menene Sihiri?

    Shin Menene Sihiri?

    Sihiri wani abu ne yanzu wanda ya yawaita cikin al-umma. Kasuwar bokaye ta buɗe, mutane da yawansu suka manta da lahirar su, suka ɗauki duniya ta fiye musu.

    Akan yi sihiri a raba miji da mata, a hana mace aure, a raba mutum da inda aka haife shi a yi masa kurciya; ko a haukatar da mutum. Kuma wannan abu ya zama ruwan dare a yanzu shi yasa fatan mu Allah ya kare mu.

    Ba wani mutum da zai ce ya fi ƙarfin a yi masa sihiri ya kama shi. Wanda ya fi kowa daraja a duniya, fiyayyen halitta Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam); sai ga shi bayahude Labib ya yi masa sihiri kuma ya kama shi. Dan haka kai wanene ni wanene da za mu ce mun fi ƙarfin a yi mana siihiri ya kama mu.

    Fatan mu ubangiji ya ba mu kariya sannan ka zama a zuciyarka ba ka nufin kowa da sharri; sannan kuma kai ma be kamata ka zuba idanu ka zauna a cutar da kai ba. Sai ka roƙi Allah sannan kuma ka bi duk matakan da za ka iya domin samun kariya daga siihiri.

    Ga kaɗan daga cikin shawarwarin da muka ba da bisa koyarwar addinin musulunci don karya sihiri da kuma ba da kariya daga wani don kada ya sameka ko zuri’arka.

    Domin karanta cikakken bayani akan Alamomin Da Ake Gane Sihiri danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin ko ya Halatta A Je Wajen Boka Ko Ɗan tsubbu Domin Sihirce Kishiya? danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su

    Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su

    Nau’ikan Sihiri

    a. Akwai kurciya

    b. Dan baka

    c. Sihirul firaƙ

    d. Sihirul muhabba

    e. Sihirul jini

    f. Sihirul tasrif

    g. Sihirul sariƙ

    Wannan su ne nau’i kaɗan daga cikin nau’ikan sihiri. Kowanne kuma da yadda ake yin sa. Ana yin sihiri mace ta saukar wa da ‘yar uwarta jini, ta rinƙa yin jini a duk lokacin da mijinta ke ɗakinta. Ana yin sihiri uba ya ji ya tsani ‘ya’yan wata sai na ɗaya. A na ma mutum sihiri ya ga duk abinda ya samu ya ruguje, ka ga kana samu amma kuma abun yana rushewa. Kuma ana iya yin sihiri a hana budurwa aure. Sannan ana iya yin sihiri mace ta rinƙa warin jaɓa, saurayi ya zo wajenta ya ji tana wari.

    Ana yi wa yaro sihiri dan a lalata rayuwarsa, ya zama ɓarawo, ɗan iska ko kuma ɗan shaye-shaye. Koma dai wane irin sihiri ne. Allah bai taɓa yin ciwo ba sai da maganinsa.

    Akwai matakai da ake bi domin a karya sihiri. Wani sihirin za a iya yi da an karya shi sai ya dawo, wani kuma da an karya shi yake tafiya. Sakamakon rashin kariya ne da tun farko ba a yi ba shi yasa da an karya zai iya dawowa.

    Da yawan waɗanda sihiri ke jikinsu ba su cika yadda da cewa sihirin ne ba. Gane sihiri aka yi maka, harka nemi maganin karya shi da na kariya shi ma arziki ne. Ga matakan da ya kamata ka ɗauka wajen maganin kariya yadda duk wani sihiri ba zai kamaka ba da kai da iyalanka, haka tsafin mai tsafi ba zai kamaka ba. Ko da mutum yana magana yana fitar da wuta a bakinsa saboda sihiri, to da yardar Allah ka fi ƙarfinsa. Sai dai a ganka ana faman duka amma ka kasa faɗuwa, ka zama shagwan mada. A kan yi amfani da ayoyi guda 33 a cikin Al-Ƙur’ani domin neman kariya daga sihiri.

    Ga ayoyin kamar haka;

    Za ka karanta su ne bayan fatiha Suratul baƙarah aya ta 1-5 Ayatul kursiyyu aya ta 255 Amanar rasul zuwa ƙarshen surar Suratul A’araf aya ta 54-56

    Sannan ka karanta;

    “ƙulid’ullaha awid’ur rahman, ayyam ma tad’u falahul asma’ul husna, wala tajhar bi salatika wala tukhafit biha wabtagi baina zalika sabila”

    Har zuwa ƙarshen suratul Isra’i

    Da kuma suratus safat aya ta 1-11 Da suratur rahman aya ta 33-35

    Sannan ka karanta;

    “lau anzalna hazal ƙur’ani ala jabalin lara’aitahu khashi’an mutasaddi’an min khashyatillah, wa tilka amthalu nadribuha linnasi la’allahum yata fakkarun”

    Zuwa ƙarshen suratul hashri

    Da surar jinn aya ta 3-9 Sannan suratul buruj aya ta 20-22

    Waɗannan ayoyin akan samu ruwan rijiya ko na zam-zam ko ruwan sama a karanta su kowacce ƙafa bakwai a tofa a cikin ruwan, a sa za’afaran ko na mai, ko na gari, ko kuma na ciyawa. Sai a rinƙa ɗiba kaɗan ana sha da safe da kuma in za a kwanta. Za kuma a iya karanta su a tofa a cikin man zaitun da man habba da man kwa-kwa ko na riɗi, a rinƙa shafawa a jiki. Mutum zai iya shafawa da iyalansa gaba ɗaya. Muddin kai da iyalanka za ku rinƙa shafa wannan addu’ar, ba wani tsafin mai tsafi ko sihirin mai sihiri da zai yi tasiri a jikinka insha Allah. Sannan wannan addu’ar ka karanta ta a gidanka kullum da safe, Ubangiji zai ba iyalanka da gidanka kariya daga dukkan sharrin mutum da aljan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Kariya Daga Hassada, Maita, Da Sharrin Aljanu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Maganin Damuwa danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu