Tag: Maganin Ciwon Zuciya

  • Ciwon Zuciya Tsantsa (Heart Failure)

    Ciwon Zuciya Tsantsa (Heart Failure)

    Matukar kana jin ire iren wadannan matsaloli ko alamomi a tare dakai yakamata ka dauki mataki dan kare kanka daga fadawa ciwon zuciya.Ciwon zuciya shine rashin aikin zuciya kacokan 

    Ga Alamomin Da Mutum Zai Fahimci Ko Yanada Alamun Ciwon Zuciya Heart Failure (Signs And Symptoms)

    • Karancin nunfashi, mutum yarikajin nunfashi na masa wahala musamman idan mutum ya kwanta.
    • Akwai kuma gajiya, rashin karfin jiki ko dibgewar jiki.
    • Kunburin kafafu wanda ake kira (edema) shine idan ka latsa wajen za aga yayi rami sai a hankali zai ciko wannan babbar alamace ta ciwon zuciya.
    • Saurin bugawar zuciya idan aka taba allon zuciya ko kirji aji tana bugawa da sauri
    • Rashin tabuka kome, ya zama mutum ya kasa aikin daya sabayi a baya, gashi yanaso amma baya iyawa.
    • Akwai yawan tari wanda bayada majina wani lokaci ko kuma majinar ta rika zuwa da kauri abunda ya banbanta ta data mura.

    Domin karanta bayani akan Hawan Jini (Hypertension) Danna nan

  • Ciwon Zuciya

    Ciwon Zuciya

    Ciwon Zuciya: Na nufin gazawar zuciyar wajen aika jini ga sassan jiki kamar yadda sassan jikin ke buƙata,ciwon zuciya kan iya samo asali daga hawan jinin da ba a bashi kulawar da ta kamata ba.

    Abubuwan Dake Saka Mutum Ya Kamu Da Wannan Matsalar 
    • Kibar data wuce kima
    • Hawan jini
    • Shan giya
    • Gadon ciwonzuciya
    • Cin abinci marar tsafta
    Alamomin Da Zakaji Bayan Ka Kamu Da Ciwon

    Numfashin Dake Bayar Da Sauti

    • Saurin gajiya
    • Daukewar jin yunwa
    • Kumburin fuska da kafafu 
    • Wahalar shakar numfashi yayin kwanciyar rufe da ciki
    • Faduwar gaba ko saurin bugawar zuciya

    Numfashi Sama-Sama

    • Kake jin kan ka tamkar ba nauyi
    • Rashin jurewa motsa jiki
    • Tari; matsakaici ko mai tsanani

    Domin gujewa kamuwa da wannan ciwo sai mutum ya guji wadancen abubuwan dana lissafa a  sama wadanda ke haddasa ciwon sannan da zarar mutum yaji yanajin wadannan alamomin saiya hanzarta zuwa asibiti domin yaga likita

    Domin karanta bayani akan abubuwan dake haddasawa mace ganin ruwa clear ko ruwan nono na zuba daga nonuwanta ko saurin inzali (premature ejaculation)

    Domin karanta Ƙarancin Bacci (Sleep Deprivation) Danna nan