Tag: Kura

  • Tatsuniyar Kura Da Kurege (Na Huɗu)

    Tatsuniyar Kura Da Kurege (Na Huɗu)

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Kurege yana farauta a daji sai ya ga mushen Kurciya, sai ya ɗauka ya ajiye a kan itace. Ya ci gaba da tafiya sai kuma ya ga mushen Giwa, ya matsa kusa, ya dubi mushen da kyau, ya yi dariya. Daga nan sai ya kai wa Kura ziyara.

    Ya same ta tana saka zana sai yace: “Ki bari in kwanta a kan zanar nan taki.” Sai Kura ta ce: “To, kwanta mana.” Da Kurege ya kwanta sai ya lumshe idanunsa. Jim kaɗan kuma ya buɗe; sai ya ce da Kura: “Na yi mafarki wai mun je yawo da ke sai muka sami kan Kurciya mai kyau.”

    Kura na jin haka sai ta ce: “Kai-kai, ai gara ka sake kwanciya ko ka ƙara yi mana mafarki mai daɗi fiye da wannan.” Kurege ya rufe ido, ya buɗe sai ya ce: “Kai na sake yin mafarki wai kin sami mushen Giwa ke kaɗai.” Kura na jin haka sai ta ce da Kurege: “To mu tafi mu bi sawu.”

    Da ya ji sai ya ce: “Yanzu dare ya yi, sai dai can idan gari ya kusa wayewa.”Bayan zakara ya yi cara sai Kura ta sake cewa da Kurege su tafi, shi ko yace ta bari sai da hantsi. Kura ta kasa haƙura, sai ta hura wuta a kan ɗakinta wai hantsi kenan. Amma Kurege sai ya gane, ya ce da ita: “Ai wannan wuta ce kika hura a kan ɗakinki.”

    Daga ƙarshe dai da gari ya waye hantsi ya ɗaga, sai suka kama hanyar bin sawun mafarki. Suna cikin tafiya sai Kurege ya tura Kura wajen kan Kurciya. Da ta gani ta kirawo shi suka raba. Suna cikin tafiya sai Kurege ya tura ta wajen mushen Giwa. Da ta gani sai ta je ta yi kashi domin ta kasayar da abin da ke cikinta, domin ta sami damar cin naman mushen Giwa sosai, tun da ga nama kamar ba iyaka.

    Kurege da Kura suka shiga gyara nama. Suna cikin wannan aiki kenan sai ga ‘ya’yan Giwa sun bi sawun uwarsu. Sai tsoro ya kama Kurege da Kura. Sai Kurege ya ce: “Zan shiga cikinta in buya.” Sai Kura ta ce: “Kai yaro ne, ni babba ce zan shiga ciki.” Da Kura ta dage sai ta shiga cikin Giwa, shi sai ya shiga mafitsarar mushen Giwar.

    Da ‘ya’yan Giwa suka je kan mushen uwarsu, sai suka fitar da mafitsarar suka yar da Kurege a ciki. Da Kurege ya fita daga cikin mafitsarar, sai ya ga wata ƙarama daga cikin ‘ya’yan Giwar tana yankan ciyawa sai yace: “Wayyo, wa ye ya zuba mini ruwa?” Sai ‘ya’yan suka ce: “Ayya sannu ba mu san kana nan ba.”

    Sai ya ce: “A a, me ya sami kakata?” Sai baki ɗayansu suka ce: “Ba mu sani ba.” Sai Kurege ya ce: “Ku kawo jar dawa in zuba a ruwa in yi muku duba.” Da suka ba shi jar dawa sai ya ce: “Abin da ya kashe kakar nan tawa yana cikinta. Abin da za ku yi sai ku ɗauko sanduna ku yi ta dukan cikin.” Sai ko ‘ya’yan Giwa suka yi kamar yadda Kurege ya faɗa.

    Da duka ya ishi Kura sai ta ce: “Ba ni kaɗai ba ce, ni da Kurege ne.” Kurege ya ce: “Kada ku saurari maganarta, ku bugi wajen gefen bakinta.” Haka suka yi ta jibgar Kura, ta fito daga cikin Giwa jina-jina, ta gudu ta tsira da ƙyar. Sai ‘ya’yan Giwa suka ɗauki sauran mushen uwarsu suka kai gida domin su binne. Sai Kurege ya roki su ba shi kan kakarsa dominwai yabinne a gidansa. Sai suka yarda suka ba shi.

    Niyyarsa yana so ya dafa ne. Da zuwansa gida sai ya sa a tukunya aka hura wuta, aka sa tukunya akan murhu, kuma ya ce wa ‘yarsa: “In wuta ta mutu sai ki zo ki faɗa mini cewa ciyawa ta kare a gaban doki.” ‘Yar Kurege ta ce: “To baba, na ji.” Shi kuwa Kurege ya sa kai ya koma wurin ‘ya’yan Giwa zaman makoki.

    Da wuta ta cinye icen, sai ‘yar ta je gidan Giwa inda ubanta ke zaman makoki tace masa: “Baba ciyawa ta kare a gaban doki.” Kurege na jin haka ya ɗauki hannu, kuma ya tashi ya bi ‘yarsa suka tafi gida. Ya tarar naman kan Giwa bai gama dahuwa ba, sai ya ƙara ice, ya koma gidan makoki. Bayan wani dan lokaci da kan Giwa ya gama ɓararraka, sai yarinyar ta koma gidan Giwa inda ake zaman makoki ta ce masa: “Baba ai kan kaka kamar ya nuna.”

    Da ‘ya’yan Giwa suka ji haka, sai suka ce: “Ashe ba binne kan ka yi ba, dafawa kake yi? To sai a kama shi a kashe nan take.” Da ya ji haka sai ya falle da gudu tal-tal-tal ana bin sa, sai ya tarar da wani Kurege yana saƙa. Sai Kurege mai saƙa ya ce da Kurege mai gudu: “Me ya koro ka?” Sai Kurege mai gudu ya ce da Kurege mai saka: “Ai Sarki ne ke son wutsiyar Kurege dubu, sai mu gudu.”

    Da jin haka sai Kurege mai saƙa ya falle da gudu shi kuwa Kurege mai laifi
    ya yi zamansa ya kama saƙa. Da ‘ya’yan Giwa da masu taya su bin sawun Kurege mai laifi suka ga wancan Kurege yana gudu, sai suka bi shi, har suka kama shi, suka kashe. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Zafin nema ba ya kawo samu.
    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Dabara ta fi ƙarfi.

    Karanta Tatsuniyar ‘Yar Sarkin Da Ta Saci Ɗinya

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Uku)

    Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Uku)

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Kurege ya je gidan Kura ya ce su tafi farautar kayan daɗi a jeji. Kura ta amince. Suka shirya suka kama hanyar daji. Da suka isa bakin rafi sai Kura ta ce, to su rabu a nan. Ta ce tunda shi Kurege ƙarami ne ya bi cikin ciyawa, ita kuma Kura da yake babba ce, za ta bi kan hanya.

    Da fari Kurege ya ƙi yarda, amma daga baya ya haƙura, ya bi cikin ciyawa yana tafiya har ya kai ga gidan zuma, ya tarar ƙudan Zuma suna ciki. Sai ya saurare su ya ji duk sanda za su fita sukan ce: “Buɗe bus,” sai ƙofar gidan ta buɗe, su fita. Idan sun dawo sai su ce: “Rufe kif,” sai kuma ƙofar ta rufe.

    Da ya gane yadda suke yi, sai ya laɓe har ƙudan Zuma suka fita sarai. Da ya ga haka sai ya matsa kusa yace: “Buɗe bus,” sai ƙofa ta buɗe. Sai Kurege ya shiga ya kwashi zuma ya sha, ya cika jakarsa da ita, ya fito, ya dubi ƙofa ya ce: “Rufe kif,” sai ƙofa ta rufe, ya kama hanya ya dawo inda suka yi alkawari za su haɗu da Kura.

    Ita kuma Kura da ta kama hanyarta, ta rinƙa tafiya ba ta ga komai ba, ga shi ta fara jin yunwa. Can dai ta hango zawayi a malale a gindin bishiya, ta je ta kama shan zawo har ta ƙoshi. Daga nan ta ɗebi sauran zawayin nan ta zuba a jakarta, ta kama hanyar inda suka yi alƙawari za su haɗu da Kurege.

    Da ta iso sai ta tarar ashe Kurege ya riga ta dawowa. Kurege ya dubi Kura, ya ce: “Kura ga shi kin ciko jakarki da kayan daɗi, sai ki ɗan ɗebo mini abin da kika samo.” Da Kura ta ji haka sai ta ƙi, ta ce ina nasa? Sai ya ce to zai ɗan ɗebo mata, ita ma ta ɗebo masa nata, amma idan na Kurege ba daɗi, zai biya ta nata.

    Kurege ya yarda. Da Kura ta buɗe jaka sai Kurege ya fara jin warin kashi, ya dubi Kura ya ce mata ya fasa shan abin da ta zo da shi. Da ta ji haka, sai ta ce to shi ke nan, amma ya ɗan ba ta nasa. Kurege ya buɗe jakarsa ya ɗeba mata, ya ba ta. Da ta ji zaƙi sai ta jefar da jakarta ta kuma ce sai Kurege ya nuna mata inda ya samo wannan zumar.

    Kurege ya ce to su tafi ya nuna mata. Suka kama hanya, har suka je gidan Zuma, ya gaya mata yadda za ta buɗe ƙofar gidan Zuma. Nan take Kura ta je ta buɗe gidan zuma, ta fara shan zuma har ta ƙoshi, ta cika jakarta. Amma kuma sai ta manta yadda za ta buɗe ta fita, sai ta rinƙa cewa: “Rufe kif.”

    Ta dai kasa fita har Ƙudan Zuma suka dawo daga cin furanni, suka faɗa Kura da harbi, duk jikinta ya kumbura. Kurege ya gudu ya bar ta, daga baya ta koma gida duk fuskarta a kumbure. A gida aka tambaye ta me ya same ta, sai ta ce: “Ai na yi yaƙi ne da wasu namun daji, amma duk na kashe su sai dai jikina ya kumbura.”

    Da ta je gidan Kurege sai ya buya, ya ce: “A gaya mata ba na gida.” Kura ta ce: “Idan ya dawo a gaya masa in bakinsa ya yi masa ƙaiƙayi, to ya daka da dutse kafin mu haɗu,” sai ta yi tafiyarta. Da ba don Gizo ba da na yi muku ƙarya. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Natsuwa maganin kuskure.
    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Cin Kasuwar Sama

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can cikin wani ƙungurmin daji akwai wata Zomanya mai ciki, wadda gidanta yake kusa da na wata Kura, ita ma mai juna biyu. Suna zaman lafiya da junansu irin na maƙwabta. Wata rana sai Zomanyar nan ta je wurin Kura ta ce mata: “Kin ga ni da ke mun kusa haihuwa, ya kamata mu nemi wurin da za mu rinƙa  ɓoye ‘ya’yanmu.

    “Sai Kura tace: “E, gaskiya ne, to amma bari mu tona rami babba domin mu saka ‘ya’yanmu a ciki.” Da suka tona rami sai suka zauna tare, har lokacin haihuwarsu ya yi. Da suka haihu, sai suka tara ‘ya’yansu a rami ɗaya, kuma suka yi alƙawari cewa Kura za ta rinƙa samo musu abinci, ita kuma Zomanya za ta rinƙa renon ‘ya’yansu.

    Suka zauna, in Kura ta tafi neman abinci ta dawo, sai ta miƙa wa Zomanya ta ci, kuma ta raba wa ‘ya’yansu. Kullum haka. Amma ita kuwa Zomanya, in an kawo mata abinci sai ta ba ‘ya’yanta su ci, in sun ƙoshi sai ta cinye sauran, ta hana ‘ya’yan Kura. Kullum haka, kuma in Kura ta zo ta ce za ta duba lafiyar ‘ya’yanta sai Zomanya ta ce ai sun ci abinci sun ƙoshi, suna barci.

    Haka suka yi ta yi, har dai wata rana Kura ta ce sai ta ga ‘ya’yanta. Da ta leƙa ramin ta jawo ‘ya’yanta sai ta ga duk sun rame. Sai ta tambayi ‘ya’yanta abin da ya same su, suka rame haka. Sai ‘ya’yan suka ce ai ba a ba su abinci, in an kawo abinci sai Zomanya ta hana su, ta bai wa ‘ya’yanta, su kuwa sai ta sa su yi barcin dole kullum.

    Da jin haka sai ran Kura ya ɓaci, ta yi kuka, ta yi gumani da ƙaraji mai tsanani, ta ce tun da Zomanya ta ci amanarta, to ita da ‘ya’yanta za su cinye Zomanya da ‘ya’yanta gaba ɗaya. Ko da Zomanya ta ji abin da Kura ta faɗa, sai ta rasa abin da za ta yi, idanunta suka raina fata.

    Tsoro ya kama ta. Sai ta dubi Kura ta ce: “To shi ke nan, tunda kin ce ni da ‘ya’yana mun zama nama, to ki yi haƙuri mu fito daga rami tukunna.” Zomanya ta shiga rami ta gaya wa ‘ya’yanta idan ta fita Kura ta bi ta, to su fita da gudu su yi nasu wuri. Da Kura ta sake magana, sai Zomanya ta haɗa manyan kunnuwanta biyu, ta ɗan miƙo su waje ta ce da Kura: “Don Allah ki riƙe mini takalmana kafin in fito.

    “Jin haka sai ya sa ran Kura ya ɓaci, ita a tsummaninta yaya za a yi kamar Zomanya ta ce ta riƙe mata takalmanta, bayan ta zama nama a wurinta. Sai ta kama kunnuwan Zomanya da ƙarfi ta finciko su ta jefar, wai ita a nufinta takalma ne. Sai kunnuwa suka sulluɓe, Zomanya da ‘ya’yanta suka ranta a na kare.

    Kamar wasa, Kura ta kasa kama ko ɗaya daga cikinsu. Da ba domin Gizo ba da na shara muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    •  Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.
    • Ƙarshen maci amana jin kunya.
    • Kowa ya ci zomo, ya ci gudu

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu