Tag: Fish – Cakes

  • Yadda ake Fish – Cakes

    Yadda ake Fish – Cakes

    KAYAN HAƊI 

    • Farin kifi 8 (dafaffe) 
    • Dankali 8 (dafaffe) 
    • Cokali 1 na kayan ƙ amshi. 
    • Cokali 1 na ruwan lemon tsami 
    • Ƙwai guda 1 
    • Butter cokali 1 
    • Tafarnuwa 1 
    • Abin ɗanɗano/ attaruhu da albasa

    Domin karanta bayani akan Yadda Ake Rice Cocktail Bites Cikin Sauki Danna nan

    Yadda za a haɗa

    A ɗan daka dankali sama-sama sannan a sa kifi, a zare ƙayar, a daka tafarnuwa da kayan ƙamshi a haɗa da sauran gaba ɗaya da attaruhu da albasa duk a haɗa a cakuɗa su gaba ɗaya. 

    Daga nan sai a sa ɗanɗano, Sai a cuccura su gabaki ɗaya kamar ƙwallo, a ɗan barbaɗa fulawa a tsoma a ruwan kwai sannan a soya a ruwan mai mai zafi.

    Domin karanta cikekken littafin Girke Girke  Danna nan