Tag: Fassarar Huɗuba

  • Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya 1st August 2025

    Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya 1st August 2025

    Huɗubar 07/02/1447H 01/08/2025M

    Mai huɗuba: Sheikh Dr. Yasir Ibn Rashid Addausari

    Mai fassara: Malam Salisu Alhaji Abdullahi

    Huɗuba ta farko:
    Dukkan yabo tabbata ga Allah, Wanda Ya koyar da alƙalami. Ya koyar da mutum abin da bai sani ba. Muna gode Masa bisa ni’imominSa masu bibiyar juna, da baiwarwakinSa waɗanda ba a iya ƙirga su ko a ƙididdige su. Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya, Ya kewaye dukkan komai da iliminSa, kuma Ya sanya iyaka ga kowane abu.

    Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, mafi alherin wanda ya bi tafarkin shiriya, kuma ya gargaɗi al’umma game da bin hanyoyin halaka.
    Tsira da amincin Ubangijina su tabbata a gare shi, da Alayensa da Sahabbansa ma’abota hankula, da Tabi’ai da waɗanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
    Bayan haka, ku ji tsoron Allah matuƙar tsoronSa, kuma ku hararo kulawarSa gare ku a sarari da yayin ganawa, kuma kada rayuwar duniya ta ruɗe ku.

    Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: (To, amma duk wanda ya yi ɗagawa () Kuma ya fifita rayuwar duniya () To lallai wutar Jahimu ita ce makoma () Kuma duk wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaban Ubangijinsa, kuma ya hana zuciya bin abin da take so () To lallai Aljanna ita ce makoma).

    Ya ku mutane:
    A zamanin nan namu, bil’adama na fuskantar cigaba na ban mamaki ta fuskar rayuwa, da bunƙasa ta musamman a fagage na fasaha da na’urori masu ƙwaƙwalwa, da kafafen sadarwa na dijital, da su ne sadarwa ta sauƙaƙa, kuma nesa ta zo kusa, kuma aka taƙaita lokuta, kuma aka aiwatar da ayyuka, aka kuma inganta hidindimu, kuma aka sauƙaƙa isa ga ilimi ta kafafen zamani, don haka, sai fasahar zamani ta zama wani ɓangare da ba zai iya rabuwa da rayuwarmu ba.

    Kuma idan al’ummu suna yin gasa a fagen fasaha, to lallai ƙasarmu mai albarka ta bambanta da hangen nesanta, kuma ta yi fice a matakan da ta ɗauka, sai ta zama jagora a wannan fanni, tana ribatar fannin fasaha kuma tana amfani da ita wurin hidimtawa al’umma da ɗan’adam, har ta zama abin kwaikwayo da ake yabawa kuma ake koyi da ita a cikin wani yanayi mai ban sha’awa da ke tabbatar da matsayinta a mataki na duniya a fannonin fasahohin zamani masu zurfi.

    Kuma haƙiƙa ƙasarmu ta tabbatar da cewa cigaba ba ya cin karo da ɗabi’u na ƙwarai, kuma ba ya saɓa wa al’adu, bari-dai, yana gina su ne kuma yana dogaro da su, sai ƙasar ta daukaka ba tare da ta manta da tushenta ba, kuma ta cigaba ba tare da ta yi watsi da tabbatattun al’adunta ba.

    Madalla da wannan a matsayin wata ni’ima daga Ubangiji, kuma kyauta daga Allah, wadda take wajabta yabo da godiya, don haka, dukkan yabo ya tabbata ga Allah da Ya hore mana waɗannan hanyoyi, kuma Ya buɗe mana kofofin alheri da sauƙi, kuma Ya datar da jagororimmu shiryayyu zuwa ga amfani da su da kuma inganta su.

    Ya ku bayin Allah
    Kuma idan har wannan ni’ima na daga cikin manyan ni’imomi, kuma na daga alamomin samun rinjaye a wannan zamani, to lallai ita ni’ima idan aka sanya ta a inda bai dace ba, sai ta koma azaba da bala’i.

    Kuma a yayin da fasahar zamani take rasa alƙiblarta, kuma aka rasa wayewar addini tattare da masu amfani da ita, to a wannan lokaci sai na’urori su koma tarko, hanyoyin kuma su koma ababen da suke zamarwa, daga nan ne wata cuta da aka jarrabi wasu mutane da ita ta bayyana, duk da bambancin shekarunsu da wayewarsu da jinsinsu, wannan kuwa ita ce cutar ɗamfaruwar zuciya da kafafen sadarwa na zamani, da nutsewa a cikin duniyar yanar gizo da ba ta da iyaka, har ma a wajen wasu wayoyi suka sauya daga kasancewarsu hanyoyin sada zumunci zuwa hanyoyin kaɗaici da yanke alaƙa.

    Sai ka ga mutum cikin jama’a tamkar gangar jiki ne da babu zuciya da hankali a tare da shi; yana kai-komo tsakanin kafafen sadarwa, yana shiga manhajoji sai shafukan yanar gizo su riƙa fizgar sa, kuma yana kallon bidiyoyi masu yawa, bai ma san abin da yake nema ba, kuma bai samu wani abu mai amfani ba.

    Wannan wata fitina ce mai hallakarwa, mutum yana rayuwa a cikinta cikin ruɗani ba tare da wasu manufofi ba; kamar ƙaramin kwale-kwale ne a tsakiyar teku ba tare da na’urar gane hanya ko abin tuƙa shi ba, kuma kamar matafiya ne wanda bai isa inda zai je ba kuma ga shi ya halakar da abar hawansa. Tir da shekaru da ke wucewa kamar gajimare, kuma suke ƙarewa ba tare da wani guzuri don ranar hisabi ba.

    An karɓo daga Ibn Abbas Allah ya ƙara musu yarda ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Akwai wasu ni’imomi guda biyu da ake yi wa yawancin mutane kamunga a cikinsu, su ne lafiya da lokaci). Bukhari ne ya rawaito shi.
    Ibnul-Ƙayyim Allah Ya masa rahama ya ce: “ɓata lokaci ya fi tsanani fiye da mutuwa; domin mutuwa tana raba ka ne da duniya, amma ɓata lokaci yana raba ka ne da Allah da kuma rabauta a lahira”

    Ya ku Musulmi:
    Lallai zuciya idan ba a shagaltar da ita da ayyukan ɗa’a ba, to sai ta shagaltu da saɓo, musamman ma a wannan zamanin na kafafen sadarwa na zamani, da yawan bibiyar hotuna da labaran yau da kullum, da ƙawata shafuka, sai ka ga mutum ya nutse cikin ruɗanin da ba shi da ƙarshe, da burace-burace waɗanda ba sa ƙarewa, kuma abin da ya fi wannan muni shi ne wanda yake rayuwarsa cikin bibiyar rayuwar wasu kuma yake ɓata lokutansa, kuma yake sa ido a rayuwar mutane amma yake manta tasa rayuwar.

    Kuma haƙiƙa lallai gargaɗi ya zo daga shari’a game da irin wannan shagaltuwa abar zargi, kuma ɗabi’a mai guba, wadda ke lalata wa mutum addininsa, kuma ta ɓata masa lokacinsa. An karɓo daga Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Yana daga cikin alamomin kyawun Musuluncin mutum, barin abin da bai shafe shi ba” Tirmizi ne ya rawaito shi.

    Kuma Abubakar Allah ya ƙara masa yarda ya ce: “Lallai wasu mutane sun sadaukar da rayuwarsu ga wasunsu, kuma sun manta da kawunansu, saboda haka, ina hana ku ku zamto kamar su”.

    Kuma ya kamata a sani, ya ku bayin Allah, cewa: Lallai kafafen sada zumunta na zamani a mafi yawan lokuta sun zama matattarar rayuwa ta ƙarya, kuma wajen gasa marar amfani, sai cutar hassada da ƙiyayya ta shiga zukatan wasu, kuma fushi da ƙin juna ya yi naso a zukatansu, sai godiya da yabo ga Allah bisa nani’imominSa da baiwarwakinSa su yi ƙaranci.

    Kuma daga cikin sharrori da masifu akwai shafukan ƙarya na bogi da ke fesa gubarsu cikin al’umma, kuma suke yaɗa fitintinu da ƙarairayi, suna ƙirƙirar maganganu da jita-jita, kuma suna fatawowi na ƙarya da sunan malunta, a cikin wasu shirye-shirye da aka ɗau nauyinsu, da kuma ɓatanci da ake yi da gangan, waɗanda ba sa la’akari da addini ko kyakkyawar ɗabi’a.

    Abin mamaki baya ƙarewa game da wanda ke bibiyar irin waɗannan shafuka ba tare da tantancewa ba, yana gaggauta yaɗa abin da suka wallafa ba tare da jinkiri ba, kuma ba tare da komawa ga majiyoyin hukuma da amintattun tashoshi ba.
    Allah Maɗaukaki Ya ce:

    (Ya ku waɗanda kuka yi imani! Idan wani fasiki ya zo muku da wani labari, to ku yi bincike, don kada ku cuci mutane cikin rashin sani, sai ku wayi gari kuna masu nadama game da abin da kuka aikata)

    Ya ku mutane,
    Kuma akwai wata fitina da ke lalata zukata a lokutan kaɗaici, lokacin da mutum ya ke keɓancewa da wayarsa a wuraren da babu kowa, sai ya keta alfarmar addini, yana kallon haramtattun abubuwa, yana raina umarnin Allah, ba ya damuwa da abin da Allah Ya hana, yana mai manta irin cututtuka da annoba da irin waɗannan abubuwan kallo ke jawowa, da keta mutunci, da ɓata shekaru da lokuta, da kuma salwantar da kyawawan ayyuka.

    An karɓo daga Sauban Allah Ya ƙara masa yarda, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Lallai ina sane da wasu mutane daga cikin al’ummata, za su zo a ranar alkiyama da kyawawan ayyuka masu girma kamar manyan duwatsun garin tihama farare, amma sai Allah Ya mayar da su ƙura abar sheƙewa)

    Sauban ya ce: Ya Manzon Allah, ka siffanta mana su, ka fito mana da su fili mana, saboda kada ya zama muna cikinsu alhali ba mu sani ba, sai ya ce: (Lallai su ‘yan’uwanku ne kuma daga cikin danginku, kuma suna ibada a wani sashe na dare kamar yadda kuke yi, sai dai su wasu irin mutane ne waɗanda idan suka keɓe da dokokin Allah sai su keta su) Ibn Majah ne ya rawaito shi.

    Ya ku bayin Allah, Allah Ya mana albarka cikin Alƙur’ani mai girma, kuma Ya amfanar da mu abin da ke cikinsa na ayoyi da ambato mai hikima, ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah gare mu, don haka ku nemi gafaraSa, lallai Shi Mai yawan gafara ne da jinƙai.

    Huɗuba Ta Biyu

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya shiryar da mu zuwa ga hanyar samun rabo, kuma Ya nusantar da mu zuwa ga hanyar tsira, kuma Ya saukar da haske da rahama a cikin littafinSa, kuma Ya sanya shiriya da hikima a cikin sunnar AnnabinSa, kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba shi abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, tsira da aminci da albarkar Allah su tabbata a gare shi, da Alayensa da Sahabbansa da wanda ya bi tafarkinsa zuwa ranar ƙarshe.

    Bayan haka, Ya ku ‘yan’uwa Muminai!
    Lallai daga cikin mafiya girman ni’imomin Allah akwai cewa mutum ya faɗaku game da tasgaronsa kafin ƙurewar lokaci, kuma ya lura da zuciyarsa kafin rufi ya mamaye ta, sau dayawa muna buƙatuwa ga maganin wannan alaƙa mai cutarwar a wannan duniya ta dijital da fasaha, hakan zai kasance ne ta hanyar ɗaga kafa, wanda da shi ne za mu daƙile guguwar amfani da waɗannan na’urori, ba wai don mu ƙaurace wa rayuwa ba, bari dai, sai don mu sabunta daidaito game da tasgaro da aka samu a rayuwarmu.

    Ibnul Jauziy ya ce: Ban taɓa ganin abin da ya fi amfani ga zuciya ba, fiye da ƙauracewar da mutum zai gano aibobinsa kuma ya riƙa nazari cikin makomar al’amuransa).

    Ya ku bayin Allah!
    Lallai addininmu addini ne na tsaka-tsaki da daidaito, don haka, ku ware wa ibada lokaci, haka rai ma a ba shi nasa kason, kuma iyalai ma a ba su rabonsu, haƙiƙa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gaskata maganar Salman ga Abu Darda’i Allah Ya ƙara musu yarda cewa: (Lallai Ubangijinka Yana da hakki a kanka, kuma kai kanka kana da hakki a kanka, kuma iyalanka suna da hakki a kanka, don haka ka ba wa duk wani ma’abocin hakki hakkinsa) Bukhari ne ya rawaito shi.

    Kuma ku sani Allah Ya muku rahama cewa: Lallai fasaha ni’ima ce mai girma idan aka fuskantar da ita zuwa ga alheri kuma aka dabaibaye ta da dabaibayin shari’a da hikima, don haka ita ba tsagwaron sharri ba ce, kuma ba abar ƙyama ba ce a asalinta, bari dai, ita kamar takobi ne mai kaifi biyu, saboda haka ka zamto wanda yake amfani ba wanda ake amfani da shi ba, kuma na’urarka ta kasance hadima ba shugaba ba, kuma gada zuwa ga ɗa’a ba ramin da zai kai ka zuwa ga saɓo ba, kuma ta kasance tsani na samun ilimi da fahimta ba filin wasa na son zuciya da jahilci ba.

    Saboda haka ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah, kuma ku yi riƙo da sabbuban tsira, kuma ku riƙa tunawa koda yaushe cewa lallai za a tsayar da ku a gaban Ubangijinku, kuma za a tambaye ku game da gaɓɓanku, haƙiƙa Allah Mai girma da ɗaukaka Ya ce: (Lallai ji da gani da kuma tunani, duk waɗannan sun zama abin tambaya ne game da su).

    Don haka, ku ribaci shekarunku kuma ku mori lokutanku, domin duk wanda yaƙininsa ya gaskata, to zai yi da gaske kuma zai yi ƙoƙari, kuma duk wanda burinsa ya taƙaita, to zai yi guziri da tanadi, ya zo cikin Sahihu Muslim daga Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Ka yi kwaɗayi kan abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah kada ka yi ƙasa a gwiwa).

    Ya ku bayin Allah,
    Wannan kenan,
    Kuma ku yi salati da sallama ga wanda aka aiko shi da hikima da kuma shiriya, mafi alheri cikin halittu kuma mafi darajar wanda ya taka ƙasa, kamar yadda Ubangijinku Mai girma da ɗaukaka Ya umurce ku da hakan cewa: (Lallai Allah da Mala’ikunSa suna yi wa Annabi salati, ya ku waɗanda kuka yi imani, ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa).

    Ya Allah Ka yi salati ga Annabi Muhammad Manzo amintacce, da Alayen Annabi Muhammad, kamar yadda Ka yi salati ga Annabi Ibrahim da Alayen Annabi Ibrahim cikin talikai, lallai Kai Abin yabo ne Mai girma, kuma Ka yi albarka ga Annabi Muhammad da Alayen Annabi Muhammad kamar yadda Ka yi albarka ga Annabi Ibrahim da Alayen Annabi Ibrahim cikin talikai lallai Kai Abin yabo ne Mai girma.

    Ya Allah Ka yarda da Halifofi huɗu shiryayyu, jagorori masu shiryarwa, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, ya Allah Ka yarda da Sahabbai baki-ɗaya, da Tabi’ai da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako, Ka haɗa da mu cikin baiwarKa da karamcinka da kyautatawarKa ya Mafi karamcin masu karamci.
    Ya Allah Ka ɗaukaka Musulunci da Musulmi, Ka kare shingen addini, Ka sanya wannan ƙasa ta kasance mai aminci da lumana da yalwa, tare da sauran ƙasashen Musulmi ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah muna roƙon Ka dace da gamonkatar ga shugabanmu kuma majiɓincin al’amarinmu hadimin Masallatai biyu masu alfarma da magajinsa amintacce, kuma Ka saka musu da mafi alherin sakamako game da ƙasa da mutane da Musulunci da Musulmi. Ya Allah Ka taimaki jami’an tsaronmu da sojojinmu a kan iyakoki, Ka kare su da kariyarKa, Ka jiɓince su da kulawarKa ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah Ka yaye damuwar waɗanda suke cikin damuwa, Ka kwaranye baƙin cikin masu baƙin ciki, Ka biya bashin waɗanda ake bi bashi, Ka warkar da marasa lafiyarmu da na sauran Musulmi. Ya Allah Ka jiƙan mamatanmu da na sauran Musulmi, Ka taimaki masu rauna daga cikin Musulmi a kowane wuri, da kuma ƙasar Falasɗinu, ya Allah Ka ba su waraka daga dukkan damuwa, da mafita daga dukkan ƙunci, da kuɓuta daga dukkan bala’i, ya Allah Ka warkar da masu rauninsu, Ka tsare jinanensu, Ka tabbatar da zukatansu, ya Allah Ka kare Masallacin Ƙudus, Ka sanya shi ya zamto mai ɗaukaka da buwaya har zuwa ranar Alƙiyama.

    Ya ku bayin Allah
    Lallai Allah Yana umurni da yin adalci da kyautatawa da kuma bai wa makusanta taimako, kuma Yana hana alfasha da mummunan aiki da zalunci, Yana gargaɗin ku don ku wa’azantu, don haka ku ambaci Allah Maɗaukaki mai girma, Shi ma Zai ambace ku, kuma ambaton Allah shi ne abin da ya fi girma, kuma Allah yana sane da abin da kuke aikatawa.

    Don karanta Yadda Falalar Karanta Ayatul Kursiyyi Ya Ke danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya daga Masallaci mai Alfarma 7th March 2025

    Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya daga Masallaci mai Alfarma 7th March 2025

    1. Mai Huɗuba: Sheikh Dr Abdullahi Bin Awwad Aljuhani

    Mai Fassara: Dr Usman Muhammad Ahmad

    Shugaban Shashi: Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

    Huɗuba Ta Farko

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Mai yawan baiwa, Mai yalwar falala da kyautatawa, Ya wajabta azumin watan Ramadana ga bayinSa Muminai. Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, Majiɓincin masu taƙawa da bayinSa nagartattu, Ya karrama al’ummar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah masu yawa su tabbata a gare shi da watan Ramadana.

    Kuma ina shaidawa lallai Shugabanmu kuma Annabinmu Muhammadu BawanSa ne kuma ManzonSa, Mafi alherin wanda ya yi Salla da azumi, kuma ya yi ɗawafi a ɗakin Allah, daɗin tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Sahabbansa, taurarin shiriya kuma fitulu a cikin duhun ɓata.

    Bayan haka:

    Ina muku wasici da kiyaye dokokin Allah Maɗaukakin Sarki, da Masa biyayya a kowane waje da lokaci, kuma ku sani cewa ɗan ƙanƙanin aiki da yawa yake a wajen Allah idan ya haɗu da tsoron Allah Maɗaukakin Sarki, mai yawansa kuma ɗan kaɗan ne idan bai haɗu da tsoron Allah ba, kuma ku yi riƙo da rukunen Addini da rassan Imani, saboda ba za ku tsira ko ku rabauta a cikin rayuwarku da mutuwarku ba sai da jin tsoron Allah Maɗaukakin Sarki da Imani da Shi.

    Kuma ku yi Amfani da damar da kuke da ita a cikin wannan rayuwa kafin ta kuɓuce muku, sannan ku yi rigegeniya izuwa ga ayyukan ɗa’a, saboda ku fa kuna cikin mafi ɗaukakan lokutansu ne. Shi mutum a wannan rayuwa ta duniya ba za a ba shi rayuwa da ba ta ƙarewa ba, kuma ba zai wanzu ba, bari dai, shi samamme ne daga babu, kuma mutuwa ita ce ƙarshensa, kuma lallai lokuta da suke gittawa ga mutum a wannan rayuwar duniya kamar ƙiftawar ido suke, ƙiftawa bayan ƙiftawa, haka mutum zai ta rayuwa har zuwa lokacin da zai isa zuwa ƙarshen rayuwarsa, kuma wannan lamari ne da kowane ɗaya daga cikinmu yake ji a jikinsa.

    Kuma a kodayaushe mu riƙa tuna ‘yan uwanmu da suka kasance tare da mu a shekarar bara, suna jiran watan Ramadana watan alheri da albarka, amma sai dai ajalinsu ya cimmu su, kuma ayyukansu sun yanke, sai suka samu kansu a cikin wasu ramuka na ƙasa da babu komi tare da su a cikinsa face ayyukansu, kuma ba su bar wa kawunansu komi a bayansu ba face wata sadaka mai gudana, ko wani ilimi da ake amfanuwa da shi, ko wani ɗa nagari da yake musu addu’a, kuma mu masu tafiya ne izuwa ga wajen da suka tafi.

    Kamar haka ne kuma zamani ya juyo, kuma watan Ramadana ya dawo a wannan shekara, ya dawo bayan mun yi mantuwa mai yawa, bayan mun kutsa muna masu ninƙaya a cikin al’amuran duniyarmu ninƙaya mai zurfi, to, watan Ramadana ya dawo, kuma muma an ƙaddara mana dawowa tare da shi don mu shaida kwanakinsa masu haske kuma mu raya dararensa masu ƙyalli.

    Ya ku Musulmi!

    Lallai yana daga cikin mafiya girman ni’imomin Allah Maɗaukakin Sarki a kan bayinSa Muminai, ni’ima da Ya yi musu a cikin waɗannan kwanaki na riskar wani lokaci cikin lokutan alhairai, wanda shi ne watan Ramadan, ma’abocin rahama da albarkatu, watan da masu azumi suke farin ciki a cikinsa, kuma masu aiki suke samun riba a wajen Allah, watan da ake ruɓanya ladan farillai a cikinsa sama da ladan farillai a waninsa, watan da nafilolinsa kamar farillai suke a wani wata da ba shi ba, watan kyauta da sadaka, watan da ake yafe kurakurai a cikinsa, kuma ake kankare zunubai, Allah ya wajabta mana azumtar sa, shi kuma Manzon Allah tsira da amincin Alah su tabbata a gare shi ya sunnanta mana tsayuwa a dararensa.

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana albishir wa Sahabbansa yana cewa: (Watan Ramadana ya zo muku, watan albarka, Allah Yana saukar da rahama a cikinsa, kuma Yana yafe laifuka, Yana amsa addu’a, kuma Allah Yana alfahari da ku ga Mala’ikunSa, don haka ku bayyana wa Allah alheri daga gare ku; saboda taɓaɓɓe shi ne wanda aka haramta masa rahamar Allah a wannan wata). Haisami ya dangana shi ga Ɗabarani a littafin Maj’ma’uzzawa’id.

    Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Idan watan Ramadana ya shigo ana buɗe ƙofofin Aljanna, kuma ana rufe ƙofofin wuta, sannan kuma ana ɗaure shaiɗanu). Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

    Haƙiƙa yana daga cikin shiriyar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda shi ne mafi cikar shiriya, Yawaita mabanbantan ibadu, haƙiƙa ya kasance ya fi kowa yawaita kyauta a cikin mutane, kuma yafi yawaita kyauta a watan Ramadana, yana yawan sadaka a cikinsa, da kyautatawa, da karatun Alƙur’ani, da zikiri, da i’itikafi, kuma ya kwaɗaitar a kan yin Umara a watan Ramadana.

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce wa wata mata cikin Mutanen Madina: (Me ya hana ki yin aikin Hajji tare da mu?), sai ta ce: “Mun kasance muna da wani raƙumi mai bayin ruwa, sai baban wane da ɗansa- wato mijinta da ɗanta- sai ya bar wani raƙumin muna bayi da shi”, sai ya ce: (To, yin Umara a watan Ramadana kamar aikin Hajji ne tare da ni). Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

    Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana keɓance watan Ramadana da wasu ibadu da ba ya keɓance sauran watanni da su, don haka ku gode wa Allah a bisa ni’imar riskarsa, kuma ku gode Masa ta hanyar ƙara himma da ƙoƙari da raya lokutansa da ayyukan ɗa’a mabanbanta, kuma ku fuskance shi ta hanyar kiyaye shi daga kurakurai da laifuka, Allah Ya muku rahama.

    Waɗannan lokuta ne masu falala, ina masu amfana da su? Waɗannan lokuta ne na kasuwanci mai ba da riba, to, ina masu nema?

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: (Dukkan ayyukan ɗan Adam nasa ne, Sai dai azumi, domin shi Nawa ne, kuma Ni ne zan ba da sakamakonsa, Azumi garkuwa ne, idan ya zama ɗayanku na azumi a wani yini, to, kada ya yi yasasshen zance, kuma kada ya yi hayaniya, idan wani ya zage shi ko ya nemi yin faɗa da shi, to, ya ce: Ni ina azumi. Ina rantsuwa da Wanda ran Muhammadu ke hannunSa, warin bakin mai azumi ya fi ƙamshi a wajen Allah fiye da ƙamshin almiski. Mai azumi yana da farin ciki guda biyu da zai yi, idan ya sha ruwa zai yi farin ciki, haka kuma idan ya haɗu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da azuminsa).

    Allah Ya taimake ni tare da ku a kan azumtar sa da tsayuwa a dararensa muna masu Imani da fatan samun lada, kuma Ya gafarta mana kurakurai gaba ɗaya, Ya suturce mana dukkan laifuka, kuma Ya mana yafiya a ranar tambaya da hisabi.

    A’uzu billahi minash-shaiɗanir-rajim. Bismillahir-Rahmanir- Rahim: (Ya ku waɗanda kuka yi Imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta wa waɗanda suka shuɗe gabaninku don ku samu taƙawa).

    (Waɗansu kwanaki ne ƙididdigaggu. To duk wanda ya kasance marar lafiya a cikinku ko yake halin tafiya, to, (idan ya sha azumi) sai ya rama a waɗansu kwanakin na daban. Kuma waɗanda za su yi azumi da wahala su ba da fansa ta ciyar da miskini; to, duk wanda ya ƙara (a kan abincin miskini), to hakan alheri ne gare shi, amma ku yi azumin shi ne ya fi muku alheri, in har kun kasance kun sani).

    Domin Karanta Shakku a Cikin Sallah danna nan

    (Watan Ramadana shi ne wanda aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane kuma ayoyi ne bayyanannu na shiriya, kuma mai rarrabewa. Don haka, duk wanda ya riski wannan wata daga cikinku, to, ya azumce shi, kuma wanda ya kasance marar lafiya ko yake halin wata tafiya, to, (idan ya sha azumi) sai ya rama a wasu kwanakin na daban. Allah yana nufin sauƙi a gare ku, Kuma baya nufin tsanani a gare ku, don ku cika adadin (Kwanakin Ramadana), kuma domin ku girmama Allah bisa ga shiryar da ku da Ya yi, don ku yi godiya).

    Allah Ya albarkace mu da Alkur’ani, kuma Ya amfanar da mu da abin da yake cikinsa na bayani. Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma gare ni tare da ku da dukkan Musulmi daga dukkan zunubi, don haka, ku nemi gafararSa, lallai Shi ne Mai yawan gafara, Mai jinƙai.

    Huɗuba Ta Biyu:

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Wanda Ya lulluɓe zukatan bayinSa da ni’imominSa, kuma Ya raya zukatansu da hasken Addini da hukunce-hukuncensa, kuma Ya musu wasici da riƙo da abin da Ya shar’anta musu daga hikimarSa da hukunce-hukuncenSa.

    Ina shaidawa lallai babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya a zatinSa da siffofinSa da aikinSa. Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, Ya aiko shi ga dukkan mutane don Ya rinjayar da shi a kan dukkan addinai. Tsira da aminci su tabbata a gare shi da Alayensa da Sahabbansa masu riƙo da igiyarsa.

    Bayan haka:

    Ina yi mana wasiyya da jin tsoron Allah, da yin gaggawa wajen neman gafarar Allah da kuma neman Aljanna wadda faɗinta yake daidai da sammai da ƙasa, wadda aka tanade ta ga masu taƙawa.

    Kuma ku sani cewa watanmu mai albarka, watan falala da alheri, kuma lokacin ayyukan ibada da kyawawan ayyuka, wasu ranaku sun shuɗe daga cikinsa, kuma kwanakinsa suna ci gaba da tafiya, kuma nan ba da daɗewa ba za su ƙare. Marabauci a cikinsa shi ne wanda ya yi tunani cikin lamarinsa, ya yi takatsan-tsan, kuma ya yi amfani da wannan damar kafin ta wuce, kuma ya ribaci falalar Ubangijinsa Ma’abocin kyauta da karamci da kyautatawa.

    Saboda haka, ku yawaita karatun Alƙur’ani, da ciyar da abinci, da sadaka ga talakawa da marayu, kuma ku kiyaye gaɓɓanku daga aikata laifuka da zunubai a cikinsa. Kuma ku yawaita salati da sallama ga Shugaban halittu kuma cikakken haske. ((Lallai Allah da Mala’ikunSa suna yi wa Annabi salati. Ya ku waɗanda kuka yi Imani! Ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa)).

    Ya Allah Ka yi salati da salama ga Shugaban dukkan halittu, Shugabanmu kuma Annabinmu Muhammadu, da Alayensa nagartattu tsarkaka, da Sahabbansa masu haske da albarka, amintattu a kan da’awarsa, kuma komondojin rundunarsa, waɗanda duk wanda ya roƙa musu rahama, kuma ya yi musu addu’a, sannan babu ƙiyayyarsu a cikin zuciyarsa, to lallai shi ne wanda Allah Maɗaukaki ya nufa da faɗinSa:

    (Waɗanda suka zo bayansu suna cewa: “Ya Ubangijinmu Ka gafarta mana mu da ‘yan’uwanmu waɗanda suka riga mu yin Imani, kuma kada ka sanya wata ƙullata a zukatanmu game da waɗanda suka yi Imani. Ya Ubangijinmu! Lallai Kai Mai tausayawa ne, Mai jinƙai).

    Da kuma waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar Alƙiyama. Ka yarda da mu tare da su, ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah, ya Mai kawar da damuwa, Mai yaye baƙin ciki, Mai karɓar addu’ar waɗanda ke cikin matsanancin hali, Mai Rahama Mai jinƙai a duniya da lahira, Kana bayar da su ga wanda Ka so, kuma Kana hanawa ga wanda Ka so, Ka yi mana rahama wacce za ta wadatar da mu daga neman rahamar waninKa, ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah muna neman tsarinKa daga talauci da rashi da ƙasƙanci, kuma muna neman tsarinKa kada a zalunce mu ko mu yi zalunci. Ya Allah! Ka wadatar da mu da halal daga barin haram, kuma Ka wadatar da mu da falalarKa daga falalar waninKa, ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah, Ya Wanda zunubin masu zunubi ba ya cutar da Shi, kuma biyayyar masu biyayya ba ta amfanar da Shi, Ka yi mana rahama, Ka yi falala ga waɗanda suka miƙa hannayensu gare Ka suna masu ƙanƙan da kai, suna neman Ka ‘yanta su daga wuta ma’abociya tsanani da muni.

    Ya Allah muna roƙon Ka Ka sanya mu daga cikin waɗanda za Ka ‘yanta daga wuta a cikin wannan wata mai albarka, kuma daga cikin masu tsira daga gidan halaka gidan wuta, daga cikin waɗanda za su dawwama a gidan tabbata Aljanna. Lallai Kai Mai rahama ne, Mai yawan gafara, ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah lallai Muna roƙon Ka a cikin wannan wata mai albarka, muna kamun ƙafa da fuskarKa mai girma, da LittafinKa mai hikima, kada Ka bar mana wani zunubi a wannan lokaci face Ka gafarta mana, kuma kada Ka bar mana wani aibi face Ka suturce shi, ko wata damuwa face Ka kawar da ita, ko wata cuta face Ka warkar da ita, ko wata matsala face Ka yaye ta, ko wani Imani face Ka tabbatar da shi, ko wata zuciya face Ka yalwata ta, ko wani ɓatacce face Ka shiryar da shi, ko wani marar lafiya face Ka warkar da shi, ko wani mamaci face Ka yi masa rahama, ko wani da ake tambaya cikin ƙabari face Ka datar da shi, ko wani da ke tsoron azabarKa face Ka amintar da shi.

    Ya Allah, Ka gafarta mana abin da muka riga muka aikata da abin da zamu aikata, da abin da Ka ƙididdige na zunubammu mu kuma muka manta, da abin da Ka sani amma muka jahilta.

    Ya Allah, kada Ka bar mana buri face Ka cika mana shi, ko wata buƙata face Ka sauƙaƙa mana ita, ko wani alheri face Ka ba mu shi, ko wani sharri face Ka nisantar da mu daga gare shi, ya Mafi alherin Wanda bawa ya dogara da Shi kuma ya yi fatan samun alheri daga gare Shi, Ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah, Ka amintar da mu a ƙasashenmu, Ka shiryar da shugabanninmu da masu jagorancinmu, Ka ƙarfafi Hadimin Masallatai biyu masu alfarma Sarki Salman bin Abdulaziz da Magajinsa amintacce Muhammad bin Salman da ɗaukaka da nasara bayyananniya.

    Ya Allah, Ka kiyaye su cikin cikakken lafiya da kariya, Ka saka musu da mafificin alheri game da hidimar Masallatai biyu masu alfarma da wurare masu daraja ga Musulunci da Musulmi.

    Ya Allah, Ka datar da dukkan shugabannin Musulmi kuma ka shiryar da su zuwa ga abin da yake alheri ne ga Addini da ƙasashensu. Ya Allah, Ka kare sojojinmu, Ka kare iyakokinmu da sansanoninmu, Ka kare jami’an tsaronmu, ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah, muna neman gafara daga gare Ka, lallai Kai ne Mai gafara, Ka saukar mana da ruwan sama mai albarka. Ya Allah, Ka saukar mana da ruwa ya Allah, Ka saukar mana da ruwa ya Allah, Ka saukar mana da ruwa. Ya Allah, mu halittu ne daga cikin halittunKa, kada Ka hana mu falalarKa saboda zunubanmu.

    (Tsarki ya tabbata ga Ubangijininka Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa. Aminci ya tabbata ga Manzanni, kuma godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai).

    Danna nan don karanta Falalar Salati Ga Annabi SAW

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Fassarar Huɗubar Juma’a daga Masallaci mai Alfarma 7th February 2025

    Fassarar Huɗubar Juma’a daga Masallaci mai Alfarma 7th February 2025

    Mai Huɗuba: Sheikh Dr. Abdullah Awwad

    Mai Fassara: Dr Usman Muhammad Ahmad

    Shugaban Shashi: Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

    Huɗubar Masallaci Mai Alfarma: Sheikh Dr. Abdullah Awwad 12/06/1446H

    HUƊUBA TA FARKO

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna gode Masa, muna neman taimakonSa da gafararSa, kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunammu da munanan ayyukammu, duk wanda Allah Ya shiryar, to, babu mai ɓatar da shi, kuma duk wanda Ya batar, to babu mai shiryar da shi.

    Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa.

    (Ya ku waɗanda kuka ka yi Imani, ku ji tsoron Allah matuƙar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kusa Musulmi)

    (Ya ku mutane, ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicce ku daga rai guda ɗaya, kuma Ya halicci matarsa daga shi, kuma ya yaɗa maza da mata masu yawa daga gare su, kuma ku ji tsoron Allah Wanda kuke yi wa juna magiya da Shi, kuma ku kiyaye yanke zumunci, lallai Allah Mai kula da ku ne)

    (Ya ku waɗanda kuka yi Imani, ku ji tsoron Allah kuma ku faɗi magana wacce take daidai, Zai kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubbanku, kuma duk wanda ya yi ɗa’a ga Allah da ManzonSa, to haƙiƙa ya rabauta rabauta mai girma)

    Bayan haka:

    Lallai mafi gaskiyar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma mafi sharrin lamura su ne ƙirƙirarru, kuma kowane ƙirƙirarren abu bidi’a ne, kuma kowace bidi’a ɓata ce.

    Bayan haka:

    Ya ku mutane! Lallai Allah Wanda hikimarSa ta ɗaukaka, Ya halicce ku ne domin ku bauta Masa, kuma Ya kallafa muku ayyukan da za ku iya, don haka, ku aikata su. Ku ji tsoron Allah ta hanyar bin umarninsa, da nisantar abin da ya hana da manyan zunubai, kuma ku yi la’akari da abin da ke cikin Alƙur’ani mai girma na ababen lura.

    Haƙiƙa Allah ya saukar da shi a gare ku don ku bi shi, domin lallai yana daga cikin mafi girman tanadi na samun tsira, saboda abin da yake ƙunshe da shi na farillai da mustahabbai da halacci da haramci da wa’azozi da jan kunne, to me ya sa zukata ba sa bin umarninsa, kuma ba sa barin abin da ya hana kuma ya tsawatar, kuma ba sa jin tsoron wanda ya san bayyane da boyayye cikin ayyukan bawa, da sirrikansa da kuma zahirinsa!

    Haƙiƙa gafala ta yi musu katutu, kuma sha’awace-sha’awacen zukata sun kautar da su daga lura da ababen suka saɓa musu, sai su ka ji daɗin ɗanɗanon ɓarnarsu, kuma suka jahilci ɗacin sakamako da za a musu a lokacin mutuwarsu, don haka, sai suka doge a kan saɓonsu, ba su ji tsoron yini da za a damƙe su ta ƙafafunsu da makwarkwarɗarsu ba.

    Ranar da za a ninka azaba ga wanda ya bar salla kuma ya tozarta ta, wanda ya yi sakaci game da lamarin zakka kuma ya ƙi ba da ita, wanda ya keta alfarmar watan Ramadana ya sha azumi a cikinsa, wanda ya jinkirta faralin Hajji alhalin yana da ikon yi kuma ba tare da wani uzuri ba.

    Ranar da za a shayar da mashayin giya da ruwan ɗiwa, a kwankwaɗa masa abin da zai ɗanɗani kaito da kuɗarsa da shi daga ruwan mugunyar ‘yan wuta. Ranar da za a sako harasan wuta ga mazinata da fajirai, kuma a dake su da bulalunta ta gabansu da bayansu.

    Maciyin riba kuma ya ci daga bishiyar zaƙƙum, lallai zina da cin riba ba su taɓa bayyana a cikin wasu mutane ba face sai sun sauko wa kansu da azabar Allah, muna neman tsarin Allah daga fushinsa da azabarsa, kuma azzalumai za su wanzu a cikin iska mai tsananin zafi da kuma tafasasshen ruwa, da kuma inuwa ta turnuƙun hayaƙi.

    Ku saurara! Lallai duk wanda ya shagala da kansa, to, ba zai samu lokacin aibata waninsa ba, kuma duk wanda gazawarsa ta dame shi, to, idanuwansa za su makance daga ganin gazawar waninsa da abin da yake aikatawa, don haka, ku kame harsunanku daga keta mutuncin mutane- Allah ya muku rahama- saboda lallai Allah Yana kusa da harshen duk wani mai magana, kuma duk wanda ya keta mutuncin ɗan’uwansa kuma ya cutar da shi da magana ko da aiki, to, Allah Shi ne Abokin husumarsa.

    Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: ((Waɗanda suke cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da sun yi laifi ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage da kuma zunubi bayyananne)).

    Babban malami Ibnu Usaimin Allah Ya masa rahama ya ce: “Wato suna jifansu da abin da ba su aikata ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage, wato ƙarya. Ƙage kuma, shi ne ka ambaci ɗan’uwanka da abin da bai tare da shi; don haka ne ma lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi tambaya game da yi da wani, sai ya ce: “Shi ne ka ambaci ɗan’uwanka da abin da yake ƙi”. Ya ce: Ya Manzon Allah! Idan ɗan’uwana yana tare da abin da nake faɗi fa? Ya ce: “Idan yana tare da abin da kake faɗi, to haƙiƙa ka ci namansa, idan kuma ba ya ɗauke da shi, to, haƙiƙa ka masa ƙage”. Muslim ne ya rawaito.

    Sannan Allah Ya masa rahama ya cigaba da cewa: Kuma cutar da Mumini yana kasancewa da magana da kuma aiki, kuma hanyoyinsa na da yawa, lallai waɗanda suke cutar da muminai ba tare da sun yi laifin komai ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage wa kawunansu, kuma shi ne ƙarya, da kuma laifi bayyananne, shi ne uƙuba mai girma, Allah Ya amintar da mu”. A nan maganarsa ta ƙare, Allah Maɗaukakin Sarki Ya masa rahama kuma Ya saka masa da alheri bisa hidimarsa ga Musulunci da Musulmi.

    Ya Ubangijinmu, Ka sanya harsunanmu su kasance masu tsarki, zukatanmu su kasance masu ƙaunar muminai. Ya Ubangijinmu, Kada Ka sanya ƙiyayyar waɗanda suka yi imani a cikin zukatanmu. Ya Ubangijinmu, lallai Kai Mai tausayawa ne, Mai jinƙai.

    Ya Allah Ka tsare mu daga son zuciya, da kuma bin zuciya mai yawan umarni da mummuna, sannan Ka tsare mu daga shaiɗan la’ananne. Ku ji tsoron Allah, ya ku bayin Allah! Kuma ku yi gaggawar yin amfani da damar da aka ba ku matuƙar tana nan. Ku ci gaba da ingantattun ayyukanku muddin ana karɓar su, kuma ku kakkaɓe kawunanku daga aikata laifi matuƙar igiyar rayuwa bata katse ba.

    Kuma ka rage buri, ya kai wanda ya ruɗu, domin rayuwa gajeriya ce. Ka tsarkake aikinka ga Allah domin Mai duba aikin Mai gani ne, kuma ka bar kusakuranka, domin lissafin mai tsauri ne. Kuma ka gyara laifukanka ta hanyar tuba, domin makoma ta yi maka daɗi.

    Imam Ahmad -Allah Ya yi masa rahama, da Imamul Bukhari Allah Ya yi masa rahama a cikin “Al-Adabul-Mufrad”, da kuma Albaihaƙi da isnadi mai kyau, sun rawaito daga Abdullahi bin Amr Allah ya yarda da su: cewa Annabi tsira da amincina Allah su tabbata a gare shi ya ce:

    (Ku yi jinƙai, za a jiƙanku, ku yi gafara, za a gafarta muku. Kaicon waɗanda suke zama kamar masakin magana. Bone ya tabbata ga masu dogewa da yin abin da suka sani cewa mummuna ne). Ma’anar “Masakin magana”: su ne waɗanda suke sauraron magana amma ba sa fahimtar ta, kuma ba sa aiki da ita.

    A’uzubillahi minash shaiɗanir rajim, bismillahir Rahmanir Rahim: (Sai ka yi bushara ga bayina () Su ne waɗanda suke sauraron magana kuma su bi mafi kyawun ta, Waɗannan ne waɗanda Allah ya shiryar, kuma waɗannan su ne ma’abota hankula).

    Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah gare mu da kuma dukkan Musulmi, don haka, ku nemi gafaranSa, lallai Shi Mai yawan gafara ne kuma Mai jinƙai.

    HUƊUBA TA BIYU

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai ɗorewa tare da wanzuwarSa. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo da ba ya ƙarewa sai idan Ya nufa. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo na dindindin, ba abin da zai samu wanda ya faɗe shi sai yardarSa. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo dauwamame a kowane ƙiftawar ido da numfashin abu mai rai.

    Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa da waɗanda suka bi shiriyarsa kuma suka yi kira irin kiransa.

    Bayan haka:

    Ku ji tsoron Allah ya ku Musulmi don ku rabauta, ku fargar da kawunanku daga gafala, kuma ku bi hanyar tsira, idan ba ku aikata haka ba kuka tasaya, to fa ku sani cewa shi ajali tafiya yake da ku, kyawawan ranaku na wucewa, ita mutuwa kuma tana farke a farfajiyarku, kuna nufin samun duniya Shi kuma Allah Yana nufin Lahira.

    Ya ku bayin Allah!

    Ku yawaita salati da sallama ga mafakar mutane a babbar matsaya ranar Alƙiyama, Annabinmu kuma mai cetonmu Muhammadu tsira da amincin Allah mai yawa su tabbata a gare shi da Alayensa.

    Ya Allah ka ƙara yarda da Halifofi shiryayyu da sauran Sahabbai gaba ɗaya, da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Ya Allah Ka amfanar da mu da son su, kuma Ka tashe mu cikin tawagarsu, kuma kada Ka karkatar da mu daga bin tafarkinsu da hanyarsu ya Mafi karamcin masu karamci. Ya Allah! Ka ƙarfafa Musulunci da Musulmi, Ka ɗaukaka Kalmar gaskiya da Addini da falalarka.

    Ya Allah! Ka ƙarfafa Shugabanmu kuma Majiɓincin lamuranmu da gaskiya da yin daidai da dace, Ka yi riƙo da hannunshi ga ayyukan nagarta da taƙawa, Ka azurta shi da mashawarta nagari, Ka ɗaukaka AddininKa da kalmarKa da shi, Ka sanya shi ya zama mai taimako ne ga Musulunci da Musulmi, kuma Ka haɗa kan Musulmi da shi a kan gaskiya da shiriya ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah! Ka datar da shi da Yarimansa da ‘yanuwansa da mataimakansa zuwa gaskiya da shiriya da kuma duk abin da yake akwai gyara ga al’umma da ƙasa a cikinsa, Ka saka musu da alheri saboda kulawarsu da Masallatai biyu masu alfarma da daraja, da kuma duk abin da suke gabatarwa saboda cigaban Musulunci da Musulmi.

    Ya Allah! Ka datar da masu jagorancin Musulmi ga yin aiki da Littafinka da Sunnar Annabainka Muhammadu – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- Ka sanya su su zama rahama ga bayinKa Muminai, Ka haɗa kansu akan gaskiya ya Ubangijin talikai, Ka kuma datar da duk jagororin Musulmi ga duk abin da yake gyara ne ga Ƙasa da mutanen.

    Ya Allah! Ka saki labulan suturtawarka akan ƙasarmu da kuma dukkan ƙasashen Musulmi. Ya Allah! Muna kamun ƙafa da yardarKa kada Ka yi fushi da mu, kuma muna kamun ƙafa da amincinKa kada Ka yi mana uƙuba, kuma muna nema tsarinka daga azabarKa, ba mu iya kaiwa matuƙa wurin yaɓonKa kamar yadda Ka yabi kanKa.

    Ya Allah! kada ka yi mana azaba da munanan ayyukanmu, kuma kada Ka kama mu da abin da wawayen cikinmu suka aikata, Ka isar mana duk wani abin da ya dame mu, kuma Ka kasance Mai ƙarfafawa da ba da nasara a gare mu.

    Ya Allah! Lallai mu muna roƙon Ka farin ciki da zai lulluɓe zukatanmu da ‘yantuwar Masallacin Ƙudus daga hannu Yahudawa ‘yanƙwace, Ya Allah Ka jefe su da kibiyarKa da ba ta kure, Ka saukar musu da uƙubarKa mai tsanani, ya Majiɓincin masu rauni, ya Ma’boci ƙarfi mai tsanani! Ya Mai gudanar da giragizai! Ya Mai rusa rundunonin maƙiya! Ka saukar wa ‘yanta’adda azaba mafi tsanani, Ka sanya su abin ɗaukar izina ga masu hankali.

    Ya Allah! Muna roƙon Ka farin ciki saboda samun nasarar Musulmi a kan abokan gabansu azzalumai. Ya Allah! Lallai mu muna roƙon gafararKa, saboda lallai Kai Ka kasance Mai yawan gafara ne, don haka Ka saukar mana da ruwan sama mamako, ya Allah! Ka saukar mana da ruwan sama, ya Allah! Ka saukar mana da ruwan sama, ya Allah! Lallai mu wata halitta ce cikin halittunKa, don haka kada Ka hana mu falalarKa saboda zunubanmu.

    Ya Allah! Ka karɓa daga gare mu lallai Kai Mai ji ne kuma Masani, kuma Ka karɓi tubarmu lallai Kai Mai yawan karɓar tuba ne Mai tsausayi. Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa, aminci ya tabbata ga Mazanni, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

    Danna nan don karanta Addu’ar Shiga Masallaci

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Fassarar Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 17 Rajab 1446 AH 17 January 2025

    Fassarar Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 17 Rajab 1446 AH 17 January 2025

    Mai Huɗuba:
    Sheikh Dr Abdurrahman Al Sudais

    Mai Fassara:
    Dr Usman Azzuhri

    Shugaban Shashi
    Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

    TAKEN HUƊUBA: GWALA-GWALEN KALMOMI GAME DA KARIYA DA GARKUWA
    17 RAJAB, 1446H

    Huɗuba Ta farko:
    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna gode Masa, muna neman taimakonSa da gafararSa, muna tsarkake Shi tare da gode Masa; Ya ƙaddara al’amura kuma Ya zartar da su, kuma Ya haramta ɓarna da abin da ya yi kama da ita.

    Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, Ma’abocin girma, kuma duk wanda ya zama ma’abocin godiya da gode Maka, to, haƙiƙa ya haɗa ababen yabawa. Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, irin yabo da ba ya ƙididdiguwa ga maƙididdigi, shin akwai mai iya ƙididdige tsakwankwani da tsirrai da yashi da ruwa mai mamako.

    Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, shaidawa da take kare jikkuna daga tawaya da ke lulluɓe su. Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu Annabi Muhammadu shi ne mafi alherin halittu kuma mafi tsarkakarsu, Allah Ya yi daɗin salati da sallama da albarka a gare shi, da alayensa da sahabbansa, zaɓaɓɓun halittu kuma mafiya matsayinsu, waɗanda suka kai maƙura a matakan kariya da garkuwa, da Tabi’ai da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa Ranar sakamako.

    Bayan haka:
    Ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah, ku ji tsoronSa a sarari da ɓoye, duk wanda ya lazimci tsoron Allah, to, haƙiƙa ya amsa wa mai kira zuwa ga Allah, ya kuma yi tsauri ga ababe masu ɓatarwa kuma ya gagare su, kuma zuciyarsa da ruhinsa sun tsarkaka.
    Tsoron Allah shi ne rabautar mutum a kodayaushe, kuma da shi ake ƙetare wahalhalu masu girma.

    ((Ya ku waɗanda ku ka yi imani, ku ji tsoron Allah kuma ku faɗi magana wacca take daidai () Zai gyara muku ayyukanku, kuma Zai gafarta muku zunubanku, kuma duk wanda ya yi wa Allah da ManzonSa biyayya, to, haƙiƙa ya rabauta rabauta mai girma)).

    Ya ku taron muminai:
    A cikin wannan zamani da ke cike da masifu da ƙalubale, da ɗimuwa da koke-koke, yaro na fatan ya girma, tsoho na burin ina ma ya koma yaro, mara aikin yi yana fafutukar neman aiki, ga ma’abocin aikin yi kuma ya ƙosa da aikin nasa, ma’abocin dukiya na cikin gajiya, shi ma matalauci na cikin gajiyar.

    A cikin wata al’umma da ayyukan sihiri da tsaface-tsafacen shaiɗan ke yaɗuwa, da cututtukan kambun baka da annobar zukata, da abin da ke samun musulmi daga haka na damuwa da jinya, ko tawaya na rayuka da dukiyoyi, da kuma abubawa da Allah tsarki ya tabbata a gare Shi Yake ƙaddarawa na jarrabawa ga ɗaiɗaikun mutane da al’ummomi.

    Kuma ita jarrabawa tsani ce na samun darajojin kamala ga wasu mutane, ga wasu kuma, kaffara ce daga munanan ayyuka, amma shi lamarin musulmi alheri ne gaba ɗayansa, idan bala’i da ƙunci suka sauko masa ((Kuma zai iya yiwuwa ku ƙi wani abu alhalin shi alheri ne a gare ku, kuma zai iya yiwuwa ku so wani abu alhalin shi sharri ne a gare ku. Kuma Allah Shi yake da sani, ku ba ku sani ba)).

    Ya ku masu Imani!
    Tunatarwa game da maudu’in kariya da garkuwa na daga cikin mafi mahimmancin abin da mutane suke buƙata, musamman ma a wannan zamani da cututtuka masu yawa suke game rayuka kuma suke kutsawa cikinsu, suke fuskantar su da matsaloli kuma suke ratsa su, na farfaɗiya da shafan aljanu da tsafi da kambun baka, da ƙullata da hassada masu kai wa ga mutuwa.

    Haƙiƙa ayoyin Alƙur’ani sun haskaka da manyan hujjoji, Hadisan Annabi da mafi kyawun bayani, da shaida na gani da ido cewa su ne magani da waraka daga kowace gagararriyar cuta, Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: ((Ka ce shi (Alƙur’ani) ga waɗanda suka yi imani shiriya ne da waraka)).

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ku bijiro mun da ruƙiyyoyinku, babu laifi a ruƙiyya matuƙar ba shirka ba ce). Muslim ne ya rawaito.
    Sau da yawa za ka ga mara lafiya da yake dab da halaka da mutuwa, wanda manyan asibitoci da ƙwararrun masana da likitoci su ka gagara magance masa cuta, sai ya nemi waraka ta hanyar ruƙiyya ta Shari’a, sai Allah Ya tabbatar masa da lafiya da waraka.

    Imamu Ibnul-ƙayyim Allah Ya masa rahama ya ce: “Alƙur’ani shi ne waraka cikakkiya daga dukkan cututtuka na zuciya da na jiki, idan mara lafiya ya kyautata yin magani da shi, ta yaya ma daman cututtuka za su iya turje wa maganar Ubangijin ƙasa da sama, maganar da da za ta sauka a kan duwatsu da ta rududduge su, ko a ƙasa da ta keta ta”. Allahu Akbar.. Madalla da wannan yaƙini tabbatacce.

    Lalle tofi saboda guba ko kambun baka, idan ya kasance da tsantsan ayoyin Alƙur’ani ko sunnar Annabi ne, to wannan yana daga shiriyar Annabi da Shari’arsa, kuma wannan babu saɓani cewa Sunna ne.

    Ya ku al’ummar Musulmi!
    Kariya da garkuwa hanya ne da ake bi don nisantar cuta da jinya da rashin lafiya, don haka ya ku bayin Allah ina horon ku da kare kanku da ‘ya’yanku da gidaddajinku da wuridodi na Shari’a, da zikirai na safiya da maraice, da zikiran shiga gida da fita, da na ci da sha, da na bacci da farkawa, da wasunsu cikin zikirai da suka tabbata daga Shugaban halittu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, saboda su ne garkuwa mai kariya da izinin Allah, tare da tawakkali mai ƙarfi ga Allah Majiɓinci Mai gani da ji, da mai da lamari ga gudanarwarSa mai tsari da kyawu, kuma yaƙini da Allah shi ne mafi girman ƙudurori, kuma shi ya fi haske a cikin duhun ɗimuwa: ((Yanzu Allah bai ishi bawanSa ba?).

    Na yarda da Ubangijina, kuma na mayar da lamurana gare Shi, kuma Ya isa Ya kasance Mai taimako na. Kada ka yanke tsammani saboda masifun zamani, lallai yaƙini na da Allah shi ne makarina. Bukhari ya rawaito a cikin Sahihinsa daga Hadisin Ibn Abbas Allah Ya ƙara masa yarda cewa: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yi wa Hasan da Husaini addu’ar neman tsari yana cewa: (Lalle mahaifinku yana yi wa Isma’il da Ishaƙ addu’a da wannan addu’ar ta neman tsari: ‘A’uzu bi kalimatillahi at-tammati min kulli shaiaɗanin wahammatin wa min kulli ‘ainin lammah).

    Kuma ya zo a cikin Sahihu Muslim, daga Hadisin Abu Umama Al-Bahili Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: (Ku karanta Suratul Baqara, domin lallai karanta ta albarka ne, kuma barinta hasara ne, kuma matsafa ba a datar da su ga koyonta).

    Imam Ahmad ya rawaito a cikin Musnad ɗinsa daga Abu Huraira Allah Ya ƙara masa yarda cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Kada ku sanya gidajenku su zama kaburbura, domin shaiɗan yana guje wa gidan da ake karanta Suratul Baqara a cikinsa), musamman ma ayatul Kursiyyi da ayoyin ƙarshen surar, da Ƙulhuwallahu da Falaƙi da Nasi kamar yadda hakan ya kasance shiriyar Manzonku.

    Ya ku taron Musulmi,
    Saboda rashin kulawa daga yawancin musulmi wajen neman kariya ga kansu, da ‘ya’yansu, da gidajensu, tare da raunin imani da aƙida ga wanda shaiɗan ya shafa da wasiwasi ko wasu abubuwa masu kama da haka, ko wanda aka shafa da kambun baka ko hassada, wasu daga cikinsu suna tunkarar sihirce-sihirce da tsubbace-tsubbace da tatsuniyoyi, da tsafi da damfara da aikata laifuka, suna faɗawa hannun wasu daga cikin masu raya yin ruƙiyya, ko waɗanda suke raya warware sihiri da makamantansa.

    Sai ka ga mai ruƙiyya yana rubutun da ba a ganewa kuma yana yin laya, wani kuma yana magana mara ma’ana, wani kuma yana tabbatar da cewa cutar kambun baka ce, kuma wanda ya yi kambun bakan a cikin dangi yake, wani kuma ba ya rabuwa da yin duka mai cutarwa, kuma mafi yawan waɗannan masu ikirari suna ɓoye haƙiƙanin lamarinsu ta hanyar bayyana siffofin mutane masu hankali da taƙawa, amma su ba komai ba ne illa mayaudara waɗanda suke cin dukiyoyin mutane, suna neman dukiya ta hanyar aikata rashin gaskiya, kuma ana iya bijiro da shi da wasu siffofi don yaudarar talakawa, musamman ma ta hanyar amfani da tashoshin talabijin da shafukan yanar gizo da kafafen sada zumunta, har ma da wasu manhajoji.

    Ya ku bayin Allah!
    Sannan shi kariya da garkuwa ba ya buƙatar wahala ko tsananta wa kai, ko faɗawa cikin tarkon maƙaryata, bari da, shi amintuwa ne daga waɗannan gaba ɗaya, mutum zai iya yi shi da kanshi, haka tare da iyalanshi da ‘ya’yanshi. Kuma yana taimakawa wajen kiyaye ɗaiɗaikun mutane da al’ummomi, da kishi wajen ba da kariya ga daɗaɗɗar aƙida, da ƙayatattar Shari’a.

    A’uzu billahi minash-shaiɗanir-rajim: ((Kuma daga Alƙur’ani muna saukar da abin da yake shi waraka ne da kuma rahama ga Muminai; ba kuma zai ƙari azzalumai da komai ba sai taɓewa)). Allah Ya albarkace mu da Alƙur’ani da Sunna, Ya kuma amfane mu Ya ɗaukaka mu da abin da ke cikinsu na ayoyi bayyanannu da hikima.

    Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina nema mana gafarar Allah Mai girma da sauran Musulmi daga kowane kuskure da zunubi, don haka ku nemi gafararSa kuma ku tuba zuwa gare Shi, Lallai Ubangijina Mai gafara ne Mai jin ƙai.

    Huɗuba ta biyu:

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah bisa ni’momi da Ya yi, tsarki ya tabbata a gare Shi Ya yi wa bayinSa baiwa mai yawa. Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya.

    Kuma ina shaidawa lallai Annabinmu Muhammadu shi ne abin koyi ga masu tsoron Allah, tsira da aminci da albarkar Allah su tabbata a gare shi, da Alayensa masu tsarki zaɓaɓɓu, da Sahabbansa masu biyayya da tsoron Allah, da Tabi’ai da waɗanda suka bi tafarkinsu har zuwa Ranar Alƙiyama. Bayan haka:

    Ya ku bayin Allah!
    Ku ji tsoron Allah ta hanyar bin umurninSa, da kuma guje wa haninSa da jan-kunnenSa, saboda Shi Allah Maɗaukakin Sarki Yana tsinkayar al’amarin da yake ɓoye ko bayyane, da abin da ke ɗarsuwa a zukata da abin da suke ɓoyewa.

    Ya ku taron Muminai!
    Jarabawowi da masifu da tashe-tashen hankula da fitintinu da damuwowi da bala’o’i, da ke samun al’umma ba su ɓuya a gare ku ba, waɗanda suka jawo mata rashin jin daɗi matuƙa. Saboda haka, lallai daga cikin mafi mahimmancin nau’ukan kariya a wannan mawuyacin hali shi ne: Kare hankulan matasa ta fuskar tunani da kuma aƙida.

    Wannan nauyi kuwa ya rataya ne akan malamai da masu wa’azi da iyaye da malaman tarbiya da saita tunani, da kafafen yaɗa labarai da fitattun marubuta. Don haka ya wajaba a kansu gaba ɗaya su ba da gudumawa wajen kare matasa ta ɓangaren tunani da kuma aƙida, da kuma kwaɗaitar da su ga komawa wajen malaman al’umma masana, da kuma yin gargaɗi dangane da fatawowi waɗanda suke bauɗaɗɗu da masu ingiza mutane da kuma masu dilmiyarwa.

    Da kuma faɗakar da su game da ƙalubalen da ke fuskantar su, a wannan zamani da fitintinu na son zuciya da shakku suka yawaita, tashe-tashen hankula suka shiga tsakanin ma’aurata da iyalai da al’umma. Da kuma yin riƙo da hannayensu daga aukawa cikin ramukan gurɓatattaun tunani, tare da wayar da kai ta hanyar bayyana shirin maƙiya da daƙile hanyarsu ta cimma munanan muradansu.

    Allah Ya kiyaye matasanmu da al’ummarmu daga dukkan sharri da munanan abubuwa, Ya kare mana tsaronmu da zaman lafiyanmu da aƙidarmu da shuwagabanninmu, Lallai Ubangijina Makusanci ne kuma Mai amsa addu’a. Ku saurara! Allah Ya yi muku rahama- Ku yi salati da sallama ga shugaban Manzanni da Annabawa, jagoran masu tsoron Allah kuma tsarkaka, kamar yadda Ubangijin talikai Ya Umarce ku da hakan inda Yake cewa:

    (Lallai Allah da mala’ikunSa suna yi wa Annabi salati. Ya ku waɗanda kuka yi imani, ku yi masa salati da kuma sallama mai yawa). Kuma ya zo a cikin ingantaccen hadisi: “Duk wanda ya yi min salati ɗaya, Allah Zai yi masa salati goma.”

    Lallai yin salati ga Annabi babbar riba ce…duk wanda ya same ta, to, ya samu matsayi kuma ya mallake shi. Ku ribaci wannan dama ku riƙa yin salati ga Annabi, kuna masu cewa: Allah Ya yi masa daɗin tsira da aminci, har abada. Ya Allah Ka yi salati da sallama ga Annabinmu Muhammad da Iyalansa masu tsarki da tsarkaka, da Sahabbansa masu haske da ɗaukaka, da Halifofinsa shiryayyu Abubakar da Umar da Usman, da Ali da dukkan sauran Sahabbai gaba ɗaya, da Tabi’ai da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa Ranar sakamako.

    Allah Ka haɗa mu tare da su cikin falalarKa da kyautarKa da karamcinKa, ya Mafi karamcin masu karamci. Muna neman kariyar Ma’abocin mulki da iko, mun yi riƙo da Ma’abocin buyawa da ƙarfi, mun dogara da Mai rai wanda ba ya mutuwa.

    Muna neman kariya da cikakkun kalmomin Allah waɗanda nagari ko fajiri ba su iya ƙetare su daga dukkan wani shaiɗani da dabba mai guba, muna neman kariya da cikakkun kalmomin Allah daga sharrin abin da Ya halitta da wanda Ya ƙaga da wanda Ya samar, da sharrin abin da yake sauka daga sama da sharrin abun da yake fitowa daga ƙasa da ma sharrin kowacce dabba wanda Kai ne Kake riƙe da ita, lallai Ubangijina a kan tafarki madaidaici Yake.

    Ya Allah Ka ɗaukaka Musulunci da Musulmai, Ka kare shingen addini, Ka sanya wannan ƙasa ta zama mai aminci da kwanciyar hankali, da yalwa da wadata, tare da sauran ƙasashen Musulmai. Ya Allah, Ka amintar da mu a ƙasashenmu, ka datar da shuwagabanninmu da jagororinmu, Ka ƙarfafi Shugabanmu kuma Jagoranmu da gaskiya da dace.

    Ya Allah ka datar da Shugabanmu Hadimin Masallatai biyu masu alfarma da Mataimakinsa ga abin da yake ɗaukaka ne ga Musulunci da kuma gyara ga Musulmi, da kuma abin da yake alheri da shiriya ga mutane da ƙasa. Ya Allah ka datar da ɗaukacin jagororin Musulmi.

    Ya Allah, Ka taimaki jami’an tsaronmu da masu dako a iyakokinmu. Ya Allah duk wanda yake nufatarmu da Musulunci da Musulmi da wani sharri, Ka sa ya shagala da kansa, Ka mayar da mugun nufinsa a kansa, Ka sanya dabararsa ta zama hallakarsa, Ya Maji roƙo.
    Ya Allah, Ka haɗa kan al’umma akan Alƙur’ani da Sunna, ya Ma’abocin kyauta da falala da baiwa.

    Ya Allah ba a iya karya rundunarKa, ba a saɓa alƙawarinKa. Ya Allah Ka taimaki ‘yan’uwanmu a Falasɗinu, ya Allah Ka tarwatsa maƙiyansu Ka wargaza taronsu, Ka sanya su su zama izina ga masu lura. Ya Allah, Ka tsara wa wannan al’umma lamari na shiriya, wanda zai ɗaukaka ma’abota biyayya da imani, kuma ya shiryar da masu bijirewa da yin zunubi.

    Ya Allah, muna da ‘yan’uwa waɗanda ɗari da talauci suka shafe su, ya Allah, ya Mai biyan buƙatu, ya Mai kawar da talauci, ya Mai agaza wa wanda ya ke cikin ƙunci, Ka saukar musu daga ɗumin jinƙanKa, Ka wadatar da su da falalarKa da albarkatunKa, ya Maji roƙo, ya Mafi jinƙan masu jinƙai. Ya Allah, Ka ba mu alheri a duniya Ka ba mu alheri a Lahira, Ka tsare mu daga azabar wuta.

    Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa, aminci ya tabbata ga Manzanni, godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai.

    Danna nan don karantasahihin sirrin iza ja’a

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu