Tag: Zubar Jini

  • Yadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa

    Yadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa

    Mahaifar Mace wato “Uterus” a sanda ta ɗauki ciki babu wani guri a jikin halittar ɗan adam da jini ke kai-komo ba tare da ƙaƙƙautawa ba irin wannan gun…. Saboda ƙoƙarin jiki don ganin ya samarwa da abinda ke cikin iska, jini, abinci da kyakkyawan yanayi. Guri ne da ake kira “No go Area” in dai da sunan wargi ne, saboda ko ya hatsari ya faru ana iya shiga uku.

    A duk minti ɗaya na agogo wato sekons 60 sai jini adadin Milimeter 800 zuwa dubu (1liter) ya shiga mahaifa ya fita. Wato dai kwatankwacin ledar pure Water 3 zuwa 4 na jini a duk minti. Shi ko jini baki ɗaya a jikin mutum an yi ƙiyasin ba ya wuce lita 5. Ka ga kenan a minti biyar kacal duk adadin jinin da ke jikin mutum ke shiga ya fita daga cikin Mahaifa. 

    Toh wannan ne yasa ko ya mace ta haihu jini ya ɓalle minti 4 zuwa 5 kacal ta mutu ta gama. Abun ba ya buƙatar ɗaukar lokaci, domin kafin a ankara an yi ta an ƙare. Shi yasa zubar jini bayan haihuwa da ake kira post partum hemorrhage ke kashe mata a karkara da birane ba ji ba gani, domin ko kuna raye a inda manyan asibitoci suke jinkiri kaɗan na abin hawa, ko shawarwarin ya za ai, ko cinkoso a hanya na iya kawo mutuwa ɓagatatan. 

    Toh yanzu Mace masu ciki sun saka kansu cikin wata musiba ta shan wani ruwa da suke wa laƙabi da “RUWAN NAƘUDA” ko a sakaya a riƙa faɗin “RUWAN ADDU’A”. Da ake karɓarwa mata a ba su su sha da sunan naƙuda ta zo musu a gurguje su haihu nan da nan abinda muke kira “PRECIPITATE LABOR.” 

    To alal haƙiƙa ku sani wannan ba wani ruwa ba ne illa ruwan musiba, ruwan guba, ruwan ta-da zaune tsaye, wallahi, wallahi, wallahi duk macen da ke marmarin tafiya lahira a dalilin haihuwa, ko take da burin ta sha da ƙyar tare da ja wa mijinta da iyayen ta asarar manyan kuɗaɗe ba tare da shiri ba, ko take da burin daga haihuwa ɗaya kar ta kuma har abada…

    Toh ta je a ba ta wannan ruwan ta riƙa sha, tunda Allah ya ba ku hankali don ku yi tunani amma sam kun mai da ƙwaƙwalenku tamkar tsumma. Kowanne tarkace yanzu kawowa ake mata su kuma su ɗiba babu lissafi. Shi wancan ruwan wasu muggan sinadarai ake sa mishi masu aiki irin na “Okzitosin” da nan da nan ke sa mahaifa ta fara harbawa tana jijjiga domin juye abinda ke cikinta, tana fisga tana talewa ƙarshe musibar da ake shiga FASHEWAR MAHAIFA yake haddasa wa inda nan da nan Mace kan fita hayyacinta, ta nufi lahira.

    Amma masu ba da irin wannan ruwan wasu ma iyayen yaran ne ke kawo musu. Sun kashe ‘ya’yansu ba tare da sun san su ne suka kashe su ba, sai dai a ce ta haihu amma jini ya ɓalle Allah ya yi mata rasuwa. Karya ne ku kuka kashe ta, kuma akwai shari’a gaban Allah. Kun ba ta abinda ba ku da ilimi kansa, kun ƙi kuma saurarar masana ku ji jan hankalin da suke game da irin wannan muggan al’adun.

    A ƙalla na sami mata uku da suka mutu a wannan tsakanin dalilin shan wannan ruwan naƙudar. Sannan na sami mutum 2 tsakanin nan ‘ƴar shekara 17 da ƴar 21 wanda suka sami fashewar mahaifa, duk da ba su mutu ba sun sha da ƙyar to amma dai hakan na nufin ba su ba kuma ɗaukar ciki ballantana su haihu a duniya, in mahaifa ta fashe ba batu ne a ɗinke ta ba, ta riga ta yi condemn.

    Kuma abin takaici duk jariran nasu sun mutu tun a ciki, shikenan in ba mazajen ƙwarai ba ne shin wa zai zauna da macen da ba zata iya haihuwa ba a irin wannan rikitaccen zamanin namu? Sabuwar amaryar shekara ɗaya a ce ka gane ba ita ba kuma haihuwa dole sai kai shirin kuma sabon aure in kana son haihuwa. 

    Toh wannan ba shi ba ne ma ƙarshen damuwar, ba su ba kuma iya riƙe fitsari, yanzu rayuwarsu za ta dauwama ne da robar fitsari a jika, hanyar kashi ta ɓulle ta dubura ta haɗe da farji. Tsabar wauta da rashin hankali, yarinyar da ko haihuwar fari ba ta yi ba amma da zarar ta sami juna biyu shikenan anta mata aiken abubuwa iri-iri ana ta sha, wannan maganin zaƙi, wannan maganin ciwon mara da dai sauran su.

    Ya kamata idon ya buɗe ku gane me duniya take ciki, kar ki laminci ganganci da rayuwarki. Lallai mu hankalta. Babban abin damuwar har ‘yan boko ko matan da kake ganin suna da ilimi su ma sukan auka cikin irin wannan ɗebe-ɗeben, a haka na sami mace me Masters amma ta je wai an ba ta maganin fibroid a Islamic CHEMIST. An ce idan ta sha zai narke, ƙarshe ga shi fibroid bai narke ba dukkan mararta ta zazzage.

    Dole aka cire mahaifar aka zubar, sannan ba ita ba kuma haihuwa, sannan mafitsararta “Bladder” ta fashe ba za ta gyaru ba, fitsari yanzu ta cikin farjinta yake fita, haka zalik kashi ma wani na fita ta duburarta wani kuma na biyo ta cikin farjinta duk. Yanzu me ya fi wannan tashin hankali, kin je kin kashe kuɗi kin illata kanki a banza da wofi.

    Hakance dai ke faruwa a fannin breast cancer, mace na fama da ciwon nono amma taita biye-biyen masu magunguna a loko suna karɓe mata kuɗi, ba za ta je asibiti ba sai abu ya gama lalacewa nono ya fara wari, in cancer ta gama yaɗuwa inda sai de mutuwa kurum. Don haka Lallai Yan Uwa Mata ku yi hattara, lafiya ta wuce wasa wallahi in kunne ya ji……

    Karanta Yadda Hawan Jini Yake (HYPERTENSION)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Zubar Jini A Cikin Wata Uku Na Farkon Samun Juna Biyu (FIRST TRIMESTER HAEMORRHAGE)

    Zubar Jini A Cikin Wata Uku Na Farkon Samun Juna Biyu (FIRST TRIMESTER HAEMORRHAGE)

    Idan mace tana da juna biyu, takan sami sauye-sauyen zubar sinadarai (hormones) a cikin jikinta. Wannan zai iya sanya mata zubar jini. Mai yiwuwa ne ta riƙa ganin ɗigon jini ba mai yawa ba a pant ɗinta. Irin wannan jinin bai cika zama matsala ba. Amma idan ya yi yawa sosai, to, ya kamata ta tafi asibiti domin ta ga likita.

    Abubuwan da suke haifar da zubar jini a first trimester sun haɗa da:

    1. Implantation, wato lokacin da ƙyanƙyasasshen ƙwai na haihuwa yake ƙoƙarin maƙalewa a jikin mahaifa.

    2. Cervical polyp, wato zazzagowar mahaifa

    3. Jima’i ko kuma sanya wani abu a cikin farji wanda zai iya haifar da samun rauni ko kujewa a jikin fatar farji

    4. Miscarriage, wato lalacewar ciki

    5. multiple babies, wato juna biyu mai ɗauke da ‘ya’ya fiye da ɗaya

    6. Ectopic pregnancy, wato juna biyun da yake zama a bayan mahaifa maimakon cikin mahaifa

    7. Molar pregnancy, wato cikin karya ba na gaskiya ba

    8. Subchorionic hemorrhage, wato zubar jinin da yake faruwa idan mabiyiya ta rabu da jikin mahaifa

    9. Infection, wato kamuwa da wasu ƙwayoyin cututtuka.

    SANNAN ZUBAR JINI A CIKIN WATA UKU NA BIYU KO KUMA UKUN ZANGO NA ƘARSHEN SAMUN JUNA BIYU (SECOND AND THIRD TRIMESTER HAEMORRHAGE)

    Zubar jini a lokacin da ciki ya shiga second trimester ko third trimester ya fi zama hatsari ga mai juna biyu, domin yana nuna cewa akwai wata babbar matsala da juna biyunta. Abubuwan da suke haddasa shi sun haɗa da:

    1. Cervix problems, wato matsalolin da suka shafi mahaifa kamar kumburi, tsiro, ko samuwar ruwan ciwo a cikin mahaifa.

    2. Placental abruption, wato rabuwar cibiyar jariri daga jikin mahaifa ko kuma rabuwarta daga jikin mabiyiya, da sauransu.

    ZUBAR JINI BAYAN HAIHUWA (POSTPARTUM HAEMORRHAGE)

    Wannan yana nufin zubar jini daga farjin mace bayan ta haihu. Hakan ba zai zama a cikin matsala ba sai idan ya kasance ya yi yawa, kamar a ce tana jiƙa pads guda biyu ko kuma fiye da biyu a cikin awa ɗaya. Abubuwan da suke haddasa shi su ne:

    1. Samuwar ƙari (tear) a farjin mace a lokacin haihuwa ko kuma samuwar rauni a jikin mahaifarta

    2. Fashewar wasu daga cikin jijiyoyin da suke kai jini zuwa cikin mahaifa

    3. Samuwar ƙwayoyin cuta a cikin mahaifa, da sauransu.

    Idan mace ta fuskanci zubar jini a ɗaya daga cikin lokutan da na faɗa a sama, to, ya kamata ta tafi asibiti ne domin a bincika a gane abinda ya haifar mata da matsalar. Daga nan za a ɗauki matakin da ya dace da irin matsalar da take da ita.

    A kowane lokaci ana shawartar mata masu juna biyu da su fara zuwa awo da wuri, kuma su guji shan magani idan ba likita ya ba su ba, domin a can ne za a buɗewa mace file wanda za a riƙa rubuta tarihin matsalarki, aune-aunen da aka yi mata, magungunan da aka ba ta, da kuma nasarori ko akasin haka da aka samu. Kun ga kenan idan maganin ya haddasa wata matsala, to, za a shawo kanta a cikin sauƙi.

    Don karanta Duhun Matse-Matsi [DARKNESS OF INNER THIGH] danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tsayar Da Zubar Jini  (Agajin Gaggawa)

    Tsayar Da Zubar Jini (Agajin Gaggawa)

    A duk lokacin da aka samu wani hatsari har ta kai da rauni dake  zubar jini, mutanen dake kusa da wurin akwai abinda ya kamata suyi kafin ko a hanyar kai su asibiti, idan mai karatu ka/ki na wurin da hadari ya faru ga abinda ya kamata ka/ki yi.

    Ka Kare Kanka.

    Idan a tsakiyar titi ne, sai a matsar da mara lafiyar gefen titi sannan asa ganye a matsayin alamar  hatsari, don kare kai daga wasu motocin dake wucewa.

    • Ayi amfani da tsumma/kyalle  mai tsafta a ninka shi sannan a sa a danne akan inda jini ke zuba (kamar yadda na nuna a hoton dake sama) 
    • A daga bagaren dake zubar jinin sama 
    •  Idan jini yaci gaba da fita da karfi, a wannan yanayin ne ake daure wurin saboda gudun kar a rasa ran mutum ta hanyar zubewar jinin jikin sa.
    • Na karshe, sai a miki mara lafiya zuwa asibiti mafi kusa.
    Jan Hankali 

    A matakin farko na tsayar da jini ba a daure wurin, saboda hakan na dakatar da jini zuwa kasa da inda aka daure, wanda idan ya dauki lokaci yakan iya kawo mutuwar wannan bangaren sai dai a yanke daga baya.

    A gajin gaggawa ana yin sa ne don cetar rai ko takaita nakasar da mara lafiya zai iya samu, yana da matukar amfani kowa ya iya.

     Sai lokaci na gaba, zan kara zuwa muku da wasu agajin gaggawa akan wani abun.

    Domin karanta bayani akan Family Planning Injection (Noristerat) (Norist) Danna nan