Tag: Wasan Ƙunshi

  • Sakamakon Bincike A Kan Wasan Ƙunshi

    Sakamakon Bincike A Kan Wasan Ƙunshi

    Wannan bincike wanda aka gudanar, an yi amfani da hira da ziyar gani da ido da shiga cikin masu aiwatar da wasan inda ya binciko wasu bayanai masu matuƙar muhimmanci wajen gudumowar da suka bayar game da adana da bunƙasa tarihi da al’adun gargajiya na Hausawa musamman na Arewacin Nijeriya.

    Sakamakon binciken takardar ta gano cewa, wasan ƙunshi wasa ne da yake ƙara haɗa kan matasa musamman samari da ‘yan mata na kusa da na nesa, wanda hakan yana samar da soyayya ta ƙullu har a samu zamantakewar aure a tsakani.

    Sannan takardar ta gano cewa, wasa ne da ake aiwatarwa sau ɗaya a shekara, wannan ya haifar da son kowa lokacin ya zo domin aiwatar da shi tare da kashe kwarkwatar idanunsa.

    Haka kuma, takardar ta gano ce har zuwa wannan lokaci ana aiwatar da shi, duk kasancewar akwai tasirin zamani kamar karatun addini musamman zuwa makaranta allo da islamiya sannan kuma da makarantar boko, wanda waɗannan suna taimaka wajen dusashewar wasan ba kamar yadda ake gudanar da shi a baya ba.

    Sannan takardar ta nazarci yadda wasan yake ƙara ƙulla zumunta da son juna Samar da zumunci a tsakanin al’umma da ƙara danƙon zumunta a tsakanin al’umma da ilimantar da jama’a kan zamantakewa da raya al’adun Hausawa na gargajiya da bunƙasa tattalin arziƙin a tsakanin al’umma.

    Takarda ta gano masu aiwatar da wasan sukan yaɗa tare da watsa wasan kai tsaye ta amfani da hanyoyi isar da saƙo na zamani ciki da wajen ƙasar nan. Wanda yin hakan ya taimaka gaya wajen sanin wasan da kuma masu bibiyarsa. Haka waɗanda ba su sami damar halarta ba bisa wasu dalilai su ma ba a bar su a baya ba.

    Daga ƙarshe binciken ya gano cewa, wasa ne na gargajiya da ake aiwatar da shi tsawon lokaci mai nisan domin babu wanda zai ce ga lokacin da aka fara shi, sai dai a bisa hasashe.

    Kammalawa

    A cikin wannan takarda da aka aiwatar, an yi taƙaitaccen bayanin game da ma’anar wasa da kuma wasannin gargajiya a ƙasar Gaya, sai kuma aka yi bayani a kan wasan ƙunshi da yadda ake aiwatar da shi da masu gudanar da wasan da rana haɗi da lokacin da ake gudanar da shi a ƙasar Gaya, da ke Jihar Kano.

    Har wayau, takardar ta fito wasu hanyoyi da ake bi wajen sanarwa da sadarwa haɗi da shirye-shirye gudanar da tanade-tanade wasan, an kuma yi bayanin masu aiwatar da shi, da kuma bayanin yadda ake gudanar da wasan a jiya. Haka kuma ta fito tare da bayani yadda ake aiwatar da wasan a yau tare da kawo yadda zamani ya yi tasiri a cikinsa. Kazalika takarda ta fito da muhimmmanci wasan yake ɗauke da shi, wasa ne da ya ke bunƙasa zumunci da tattalin arziƙi da kuma adana tarihi.

    Manazarta

    Alhassan, H. da Wasu, (1982). Zaman Hausawa. Bugu na Biyu. Zaria: Institute of Education, Ahmadu Bello University.

    Bunza, A.M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria Limited.

    Bunza, D.B. (2016) “Taubashi Bahaushe: Wani Mashigi Na tantance Asalinsa Da Zuriyarsa”. Kaduna: A Cikin The Hausa People, Language And History Past, and Present and Future. Department of Nigerian Languages and Linguistics. Faculty of Arts, Kaduna State University. Garkuwa Publishing Ltd.

    Ɗangambo, A. (2008) Rabe-Raben Adabin Hausa. Kano: (Sabon Tsari) Amana Publishers Ltd, No. 1166 Sabon Gari Market.

    Ibrahim, M.S. (1982). “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa.” Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Gaya, M.A. (2018). “Keɓaɓɓun Wasannin Hausawa na Gargajiya a Ƙasar Gaya.” Kundin Digiri na Biyu, Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

    Magaji, A. (2002). “Wasu Al’adun Hausawa Yanaye-Yanayensu a Ƙasar Katsina.” Kundin Digiri Na Uku, Kano: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Sa’id, B. da Wasu (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Zaria: Ahmadu Bello University Press.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga maƙala mai taken Nazarin Wasan Ƙunshi Jiya Da Yau A Ƙasar Gaya wadda Magaji Ahmad Gaya Ph.D Sashen koyar da Hausa Jami’ar Northwest, Kano ya wallafa.

    Emai: magaya@nwu.edu.ng

    08066009039

    Danna nan don karanta Wasan Ƙunshi A Yau

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda ake Gudanar da Wasan Ƙunshi

    Yadda ake Gudanar da Wasan Ƙunshi

    Da zarar watan azumin ya kama, watan (Ramadan), ‘yan mata su ne masu ko suke gudanar da wannan wasa a ƙarƙashin tallafin ‘yan uwa da abokan arziƙi na danginsu da ma na dangin surukai, har ma da abokan ‘ya’yansu, da samarinsu da abokan samarin, da duk waɗanda suka sani suna da alaƙa da su.

    Wannan alaƙa ta ‘yan uwantaka ko kuma ta zaman tare, a ɓangaren cinikayya ko kuma a zaman unguwa ɗaya, mutun ya kan bayar da tallafinsa na gudanar da wannan wasa da zarar watan ya kama na azumi daga dangi na kusa da na nesa.

    Yadda ake karɓar wannan tallafi shi ne yarinya za ta yi wanka ta ɗaura atamfa kyakkyawa kamar ranar Sallah, a wannan lokaci tana bin gidajen danginta, tana zuwa gaishe su, inda za ta faɗa musu ta zo karɓar hatsin ƙunshi. Nan take idan wurin da za a yi wasa da dariya ne, sannan a ɗebo abin da ya samu a ba ta.

    Waɗansu sukan bayar da gero, ko dawa ko maiwa ko shinkafa ko kaza ko zakara ko ɗan shila. Waɗansu na bayar da zabi waɗansu ƙwai waɗansu kuma sukan bayar da kuɗi da dai sauran abubuwan da mutum yake da halin da zai iya bayarwa. Idan ta haɗa waɗannan kayayyaki ta kammala karɓar tuwon ƙunshi na wannan shekara ke nan.

    Abu na gaba, za ta tafi ta ɗauki ‘yar ƙunshi. Ita ‘yar ƙunshi yarinya ce ‘yar ƙarama za ta samu ko ‘yar yayarta ko ‘yar ƙanwarta ko kuma ‘yar uwar ɗakinta, ko kuma ‘yar abokiyar wasanta, ko kuma wata daga cikin dangi. Wannan yarinya ita ce ‘yar ƙunshinta, sai ta sanar da mahaifan yarinya, yarinyar wacce ba ta wuce shekara shida zuwa shekara tara ba (6-9).

    Daga wannan lokaci su ma iyayen yarinya ta same su, domin kuwa su ma za su haɗa kayan abinci su ba uwar ɗakin ‘yarsu, daga wannan lokaci wannan yarinya da aka ɗauko wato (‘yar ƙunshi), shi ke nan duk wata ɗawainiyarta, ta koma kan uwar ɗakinta, (wato wannan budurwa).

    Wankanta da shanta da cinta, waɗansu ma idan suna da hali har ma tufafinta duk sun koma kan uwar ɗakinta. Wannan nauyi ya ɗoru har lokacin da za a yi auren wannan budurwa. Wannan yarinya ita ce za ta zama ‘yar zaman ɗaki kafin kwana arba’in (40).

    Za a saka tabarma ta kaba (turarriya) a yi mata ado mai kyau. Wannan tabarma za a ba wa ‘yar ƙunshi a ce mata ga tabarmarmu ta cin tuwon ƙunshi, saboda haka, wannan yarinya ita ce mai alhakin kula da ita, bayan an kammala waɗannan shirye-shirye. Ga waɗanda suke da hali suna yin sababbin ɗinkuna, waɗanda kuma ba su sami halin hakan ba, sukan sanya tufafinsu kyawawa.

    Ita wannan yarinyar za a yi mata ƙunshi tare da uwar ɗakinta kafin lokaci ya rage kwana ɗaya ko biyu. A ranar da ake azumi na ashirin da shida (26), a wannan rana kowace budurwa komai girmanta, ba za ta yi azumi ba, saboda rana ce ta wannan wasa na ƙunshi.

    Dangane da waɗancan kayayyakin abinci da kuɗaɗe waɗanda aka samu daga dangi da abokan arzuƙa. A ranar ashirin da shida (26) har zuwa ashirin da takwas ana girke-girke, na alfarma a duk gidan da budurwa take, idan an gama dafa abinci, su yara ƙanana-ƙanana suna shiga gida-gida suna cewa a ba su tuwon ƙunshi, kowanne da kwanonsa, za a karɓa a zuba musu.

    Da rana ta yi, za a tafi wani gida da aka ware ko dai gidan wata Amarya a unguwar ko kuma gidan wata mata wadda ta yi fice a wannan unguwa, inda ‘yanmatan suke wasanninsu tare hirarsu a gidan, sai su ce bana a gidan wance za a ci tuwon ƙunshi.

    Idan an kammala dafa abinci kowacce ‘yar ƙunshi da aka ɗauko za a ɗora mata wannan tabarma a saka ta a tafi wancan gida da aka ambata a can za a ci tuwon ƙunshi. Kowacce budurwa a nan gidan za ta ɗauko abincinta ta ci. Kuma kowacce zata zo da sabuwar tabarma da aka saƙa ta musamman.

    A wancan lokaci yara maza suna zagawa wurin waɗanda suka sani, suna cewa a ba su tuwon ƙunshi, kowanne da kwanonsa. A ɓangaren yarinyar ‘yar ƙunshi a ranar babu abin da za ta yi sai zama da kuma cin abinci wadda take so. Sannan a hannu guda kuma, ita wannan matar gida, ‘yanmata za su zuba abinci a kwano a kai mata.

    Haka abubuwan za su ta tafiya tare da kai wa-da-komowa wasu zau tafi dandali wasu kuma bayan gari ya danganta inda suka ga dama har bayan sallar la’asar ana guje-guje da tsalle-tsalle da wasannin gargajiya iri-iri da gata da waƙoƙi da sauran wasanni har zuwa almuru ko kuma faɗuwar rana, sai kuma a dawo wannan gida, kowacce ta rage kuma ta ajiye abincinta haɗi da tabarma ta za a ɗauko sauran abincin a ƙarashe shi, daga nan an gama cin tuwon ƙunshi na ranar farko.

    A rana ta biyu (2) wato ranar ashirin da bakwai (27) da kuma ranar ashirin da takwas (28), duk waɗannan wasannin iri ɗaya ne, sai kawai hidimar wata rana tana fin ta wata rana, a nan ake samun bambanci. To idan an yi wannan abinci na ranar ashirin da takwas ga wata (28), wato ranaku uku (3) ke nan ana gudanar da wannan wasa, to shi ke nan an kammala cin tuwon wasan ƙunshi.

    Ita kuma ‘yar ƙunshi za a yi mata saye-saye daga gidan su uwar ɗakinta (wadda ta ɗauko ta), sannan ta ɗauke ta mayar da ita wurin iyayenta, shi ke nan wannan ‘yar ƙunshi ta yi uwar ɗaki, shi ke nan duk shekara ta zama ita ce ‘yar ƙunshinta ba wacce za ta ɗauki wannan yarinya sai ita.

    Yayin da wannan budurwa ta kawo munzalin ayi mata aure, ita mahaifiyar ‘yar ƙunshi sai ta taka rawar gani a al’amarin auren, idan an yi auren ‘yar ƙunshin da ita za a tafi gidan mijin, sannan a canza mata suna ta koma ‘yar burganci”, ma’ana mai yi wa amarya aikace-aikacen gida, da ayyukan da amaryar nan za ta yi. Wannan ‘yar burganci ita ce mai yi mata hidima kamar share-share da wanke-wanke da duk wani aiki da amarya za ta yi. A nan gidan take kwana take tashi, har kwana arba’in.

    Game da azumin da ba a yi ba wato suka sha ya tafi shi ke nan, sannan kuma sauran azumi guda biyu (2) ko ɗaya (1) ba kowace budurwa rama shi ba ko kuma take ƙara yinsa ba, da yawa ba sa ramawa, wasu kuma sukan ƙara har zuwa ashirin da tara ko talatin (30) ya danganta da yadda aka yi a wannan shekarar, ashirin da tara (29) ko talatin (30).

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga maƙala mai taken Nazarin Wasan Ƙunshi Jiya Da Yau A Ƙasar Gaya wadda Magaji Ahmad Gaya Ph.D Sashen koyar da Hausa Jami’ar Northwest, Kano ya wallafa.

    Emai: magaya@nwu.edu.ng

    0806600903

    Danna nan don karanta Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe

    Edita@rumasau-kallamu

  • Menene Wasan Ƙunshi?

    Menene Wasan Ƙunshi?

    Wasan ƙunshi, yana daga cikin nau’o’in wasannin gargajiya wanda samari da ‘yan mata suke aiwatarwa shekara-shekara. Sannan yana ɗaya daga cikin wasanni na al’ada da ake aiwatar a watan cika ciki.

    Mafi tsufa daga cikin mutanen da aka gana da su sun bayyana cewa wannan wasan haka suka tashi suka ga ana gudanar da shi ba za su iya tabatar da lokacin da aka fara shi ba. Sun bayyana mana sunayen iyaye da kakanninsu da suka yi wannan wasa irin su: Uba maiwake da Hamza Kashi da Tokare da sauransu. (Hira da Shehu Maroɗo).

    Wasan ƙunshi wasa ne na Hausawa na gargajiya a ƙasar Gaya ya nuna al’ada ce daɗaɗɗiya “wasa ne da ake gudanar da shi domin nuna farin ciki musamman a cikin watan azumi.”(Hira da Ɗahiru Roka). “Wasa ne na gargajiya wanda ake haɗuwa samari da ‘yan mata da yara wajen nuna farin ciki da sanya nishaɗi.” (Hira da Rabi’u).

    Don haka,a taƙaice wasan ƙunshi wasa ne wadda ake gudanar da shi a tsakanin ‘yan mata da samari domin sanya nishaɗi tare da motsa jiki bisa tsarin gargajiya.

    Ranar Wasan Ƙunshi

    Babu wata rana da ake sanyawa domin a tsayar da lokaci ko wuri wajen aiwatar da wasan. Wannan ya samo tun asali tun farko farko samar da wasan, saboda haka kowa ya san watan da kuma ranar aiwatar da shi.

    Amma a wannan lokaci ko kuma a yanzu saboda tasirin zamani ana yin la’akari da ranakun da ba a yin aikin gwamnati, misalin Asabar ko Lahadi, domin ranaku ne da ba a zuwa makarantun boko, suna yin haka, saboda wasu daga cikin ‘yan matan da ake shirya wasan tare da su, suna a makarantun kwana.

    Hanyoyin Sanarwa da Sadarwa

    Kafin samun kafofin sadarwa na zamani da kuma hanyoyin isar da saƙo na karta kwana, babu wata hanya da ake amfani da ita wajen sanar da wasan sai ta hanyar gargajiya, ita ce wannan ya faɗawa wannan da dai sauran hanyoyin isar da saƙo na gargajiya.

    Amma a sakamakon juyawar zamani ana amfani da waɗancan kafafen yaɗa labarai da kuma wayoyin tafi da gidanka wajen faɗakar da al’umma, musamman samari da ‘yan mata.

    Masu Aiwatar da Wasan Ƙunshi

    Bisa al’ada yawancin wasannin gargajiya a ƙasar Hausawa, ya fi ta’alaƙa ga samari da ‘yan mata musamman wajen aiwatar da shi, domin su ne matasa manyan gobe. Haka abin yake a wasan ƙunshi, masu aiwatar da wannan wasa su ne samari da ‘yan mata sai kuma ƙananan yara waɗanda suke taimakawa wajen gudanar da shi, duk da kasancewar iyaye mata ba abar su a baya ba, domin suna bayar da gagarumar gudummawa tare da ruwa da tsaki wajen aiwatar da wasan.

    Lokacin Gudanar da Wasan Ƙunshi

    Wasan ƙunshi, wasa ne da ake gudanarwa shekara-shekara, ana gudanar da shi a cikin watan azumi (Ramadan). Watau ana fara wa daga ranar ashirin da shida (26) ga watan, zuwa ashirin da takwas (28) ga wannan wata, wato kwanaki uku (3) ake yi ana gudanar da shi

    Tanade-Tanaden Wasan

    Iyaye mata sukan tanadi wasu abubuwa waɗanda za su taimakawa ‘ya’yansu wajen alkinta kafin lokacin aiwatar da wasan, a wasu lokutan akan tanadi kayayyakin amfanin gona da aka samu daga roro ko kale ko ja-gindi ko tsinka da sauransu, wacce yarinyar ta samo domin adanawa sai lokacin ya zo, wadda da irin wannan ne ake sayarwa domin a yi mata sabon ɗinki da takalmi da a warwaro da sauran kayan ƙawa.

    Haka nan, Budurwa takan kai ziyar gidajen ‘yan uwa da abokan arzuƙa, da sauran dangi, bayan sun gaisa akan ba ta wasu abubuwa da suka haɗa da; sabulai da turare da kayayyakin abinci kamar hatsi da wake da gyaɗa da sauran nau’o’in kayan amfanin gona. Wasu kuma sukan bayar da kuɗi, dukkaninsu suna daga cikin tanade-tanaden gudanar da wasan ƙunshi.

    Sannan samari da ‘yammata sukan tanadi kuɗaɗe, idan ranar wasan ta kusanto sukan je kasuwa su sayo kayayyakin da suke da buƙata. ‘Yammata ne suke ɗaukar nauyin saye-sayen kayayyakin da ake da buƙata, domin samarinsu da iyayensu na samar masu da kuɗaɗen, domin su sami damar sayen kayayyakin da suke buƙata.

    Amma a yau abubuwa wasu sun sauya saboda sauyin zamani inda samarin da ‘yanmatan su ne suke tanadar waɗannan abubuwa da kansu da suka haɗa da; kayayyakin ciye-ciye wadda suka haɗar da; biredi da cincin da biskin da doya da kwai da arnaki da biri-biri. Sai kuma kayayyakin shaye-shaye, waɗanda suka haɗa da; kyayyakin tsotse-tsotse, misalin; alawar madara, da sauran alawoyi, iri daban-daban.

    Ana amfani da kayayyakin shaye-shaye na zamani, irin su lemukan roba da bobo da yagot da lemon kwalaba kamar fanta da kokakola da diyu da kuma lemukan gwangwani kamar maltina da fefsi da lakasera da mirinda da sifirayit, da lemukan kwali, misalin fayif alayif da kuma ruwa iri daban-daban.

    Daga cikin samari da ‘yan mata masu aiwatar da wannan wasa akan samu wasu daga cikinsu sukan ɗinka sababbin tufafi domin yin amfani da su, a lokacin wasan. Amma yin ɗunkuna ba wajibi ba ne. Saboda haka, ana samun wasu daga cikin samari da ‘yan mata waɗanda ba su yi sabon ɗinki ba a lokacin wasan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga maƙala mai taken Nazarin Wasan Ƙunshi Jiya Da Yau A Ƙasar Gaya wadda Magaji Ahmad Gaya Ph.D Sashen koyar da Hausa Jami’ar Northwest, Kano ya wallafa.

    Emai: magaya@nwu.edu.ng 08066009039

    Karanta Waiwaye A Kan Al’adun Gargajiya

    Edita@rumasau-kallamu