Tag: burger

  • Yadda Ake Boga (Burger)

    Yadda Ake Boga (Burger)

    Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girken mu na WikiHausa. A yau za mu koyi yadda ake burger.

    Abubuwan da ake buƙata:

    1.Fulawa
    2.Yeast
    3.Kwai
    4.Bota
    5.Dankalin Turawa
    6.Salad
    7.Ketchup
    8.Salad cream
    9.Nama
    10.Albasa
    11.Maggi
    12.Kayan ɗanɗano da kayan ƙamshi
    13.Tumatir

    Yadda ake haɗawa:

    • A hada fulawa da gishiri da yis, ki kwaɓa su da ruwan ɗumi,
    • Sai a kai shi  ƙarƙashin rana ya yi kamar minti ashirin,
    • Sannan a shafa wa gwangwanin gashin bota a jikinsa, sai a saka kwaɓin fulawar a ciki.
    • A gasa a abin gashi, ya gasu har dai bayan ya yi brown, a cire a raba shi biyu.
    • A dafa nama tare da albasa da maggi, a daka shi, sannan a soya shi sama-sama,
    • Za a yanka dankalin Turawa ƙanana, sai a dafa shi tare da ƙwai, a yanka ƙwan, amman a tsaitsaye,
    • Sai a ɗauko wannan biredin da aka gasa, a shafe shi da salad cream da ketchup, a ɗauko salad a sa a ɓari ɗaya na jiki, amma kar a yanka salad ɗin.
    • Sai a zuba nama, ƙwai, dankali da yankakken tumatir da albasa a kan salad ɗin nan, sai ki rufe da ɗaya ɓangaren.
    • Idan ana so, ana iya ƙara gasa shi sama-sama ko a ci a haka.