Tag: al’adar bahaushe

  • ASALIN KALMAR HAUSA DA MA’ANARTA

    ASALIN KALMAR HAUSA DA MA’ANARTA

     Akwai maganganu da yawa dangane da asalin kalmar Hausa, inda suka bayyana a matsayin ra’ayinsu. Daga cikin maganganun akwai:

    Nil Skinner (1968) cewa ya yi, “Asalin kalmar Hausa, an samo ta daga Songhai. A ganinsa, akwai daɗaɗɗiyar dangantaka tsakanin Hausawa da su mutanen Songhai, har ta kai Hausawa suna aron kalmomin Songhai. Domin a nasa binciken cewa ya yi, kalmar Hausa an samo ta ne daga ‘Assa’ sunan da suke kiran mutanen da suke Gabas da su, su kuma Hausawa suka aro suka laƙaba wa kansu.

    Malam Aminu Kano kuwa, ya bayyana cewa an samo kalmar Hausa daga kalmar Habasha, wai don a cewar sa, asalin Hausawa mutanen Habasha ne, kuma a maimakon a rinƙa cewa Habasha ɗin, sai ake cewa Hausa. (Adamu, M.T. 1997:19).

    A nasa tsinkayen, Mr. C.R. Niben (1971) cewa ya yi, an samo asalin kalmar Hausa ne daga Buzaye, domin kuwa haka suke kiran mutanen dake zaune a Arewacin Kogin Kwara, wato Hausa. (Adamu, M.T. 1997: 19).

    Shi kuwa mai Martaba Sarkin Ningi; Alhaji Haruna Wakati, cewa ya yi, an samo kalmar Hausa ce daga labarin zuwan Bayajidda garin Daura, a lokacin, da ya isa da daddare ya sauka a gidan wata tsohuwa ‘Ayyana’ ko kuma ‘Wayre’, inda ya buƙaci ruwan sha a wurinta, da cewar ba ta da ruwa ya tambaye ta, ina zai samu? Ita kuma ta sanar da shi babu inda zai samu sai ya je rijiya, kuma matsalar ba a ɗiban ruwa sai mako-mako ake zuwa a ɗebo ruwan; saboda wata macijiya mai suna sarki.

    Daga nan, sai ya buƙaci ta ba shi guga, ta nuna mai inda rijiyar take, ya je ya zura guga ya fara debo ruwan, sai wannan macijiyar ta biyo igiyar gugar, shi kuma ya sa takobi ya sare kanta. Inda labari ya bazu a gari har Sarauniya Daurama ta samu labarin abin da yake faruwa, ta sa a nemo wanda ya kashe macijiyar don a yi masa kyautar bajintar da ya yi.

    Ana ta neman wanda ya kashe amma ba a same shi ba. Sai aka tambayi tsohuwa, wanda ya kashe ta ba a same shi ba. Sai ta ce musu “Ai ya hau”. Hau-sa maimakon ta ce ya hau doki tunda ita ba ta taɓa ganin doki ba. To wai wannan ‘Ya hau-sa’ ne aka haɗe kalmomin ne suka koma ‘Hausa’.

    Haka kuma a wata fadar an ce, da can Larabawa da suka zo harkar cinikayya Arewa zuwa Kurmi, lokacin da suka zo, suka ga kalmomi da ɗabi’u irin nasu, sai suka ce waɗannan mutane sun so su yi kama da mu, amma sun ɗan karkace. To shi ne idan za su zo, sai su ce: “Za mu Hawasa”, wato za su garin karkatattu. (T/Wazirchi, 2009:14).

    Masu ra’ayin Harshe suna ganin cewa kalmar Hausa a wurin su ‘Bahaushe’ ma’anar ta “harshe”, domin idan ka yi magana da wani harshe daban, Bahaushe yakan ce ” Ya ji ana wata Hausa”, wato a nan Hausa sunan harshe ne, ba na ƙabila ba, kuma al’ummomin da suka taru suke magana da wannan harshe su ne Hausawa. (T/Wazirchi, 2009: 16).

    A taƙaice dai, Kalmar Hausa tana nufin harshe, tana kuma nufin mutanen da suke magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa, kamar yadda kuma take nufin ƙasar da su waɗannan al’umma ta Hausa suke zaune. Saboda haka ne ake kiran harshen da cewa “Harshen Hausa” a kuma ce “Bahaushen Mutum” sannan a cewa mazauninsu “Kasar Hausa”.

    SIFFOFIN BAHAUSHE DA HALAYENSA

    Bahaushen mutum baƙi ne, amma ba baƙiƙƙirin ba, irin waɗanda Turawa ke kiran su Negroid, domin su bakinsu wankan tarwaɗa ne.

    Bahaushe ba shi da dogon gashin kai irin na mutanen Songhai, amma ƙirar jikinsa da kamanninsa daidai yake da na al’ummar Aryaniyawa (Aryan), waɗanda da suke zaune a tsakanin kasashen Turai da Asiya, kafin su yi hijira su watsu wurare daban-daban a duniya.

    Game da halayensa kuwa, halaye ne na nagarta, waɗanda ya shahara da su, kuma yana ɗaya daga cikin shahararrun ƙabilun da ake girmamawa a Afirka. Waɗannan halaye na Bahaushe, su suka ɗaga shi, har ya yi fice aka san shi a duniya ta da, da ta yanzu, fiye da sauran ƙabilun baƙar fata a Afirka ta Yamma. (Kantoma, 2011:16-17).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hausawa da al’adunsu ko kuma a karanta asalin ƙasar Hausa danna koren rubutu nan

  • AL’ADAR BAHAUSHE

    AL’ADAR BAHAUSHE

    Abin kunya ne budurwa ta je gidan su saurayinta a ƙasar Hausa

    Da a al’adar Bahaushe, ba yadda za a yi budurwa ta bi saurayi gidan su ko ta je wajensa, saboda kunya da kamun kai irin na Bahaushe.

    Amma yanzu don rashin kamun kai da rashin sanin ƙimar kai, sai ta karaɗe dangin su kaf kafin a yi auren.

    Don haka, ba mai mararin ganin ta, yayin da aka yi auren, don duk sun gama ganinta, don haka ba za ta yi irin farin jinin da amarya ke yi ba.

    kuma yanzu iyaye mata su ke ba wa ‘ya’yansu lasisin yin haka, domin su ma irin waɗannan iyayen akwai alamun rashin kamun kai a tare da su.

    Shi ma kuma saurayin sai ya yi ta kwasarta, yana yawo da ita, wai shi ga mai budurwa.

    Hakan ne yake jawo shi ɗin ma, karan kansa saurayin ba zai damu da ita ba, bayan an yi auren.

    Shi ne bayan auren lokaci kaɗan, sai a ga an fara samun matsaloli, ta yau daban ta gobe daban, tunda dama mahaifiyarta ba ta ba ta tarbiyya mai kyau ba.

    A ƙarshe ya kamata mu koma kan al’adar mu ta asali, iyaye su nuna wa ‘ya’yansu cewa ba burgewa ba ce bin saurayi zuwa wani waje, ko da kuwa gidansu ne, ta haka ne za mu kare ‘ya’yanmu daga faɗawa cikin rayuwa mara kyau da gurɓatattun halaye.

    Domin karanta tarihin Hausawa da al’adunsu danna nan