-
-21%
Sauro Halittar Allah Mai Ban Al’ajabi
0Lallai ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lallai shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta
-
Shugabanci A Musulunci
1Hassada wani mummunan ciwo ne da yakan kama zukatun masu raunin imani da jayayya da ikon Allah. A duniyar nan babu wahalalle irin mahassadi. Saboda shi kullum baƙin ciki yake ga baiwar da Allah yake yi ga bayinsa, in ta son ranshi ne a ƙwace a ba shi, ko a fasa kowa ya rasa.
-
-38%
SUTURA DA KWALLIYAR MATA
0Mafi yawan mutane a wannan zamani, sun afu da sha’anin ado da kwalliya, musamman mata waɗanda a kullum ake ƙirƙiro musu da kayan ado da sanyawa iri-iri, har ta kai wasu kayan kwalliyar na iya kawo tangarɗa ga lafiya da tattalin arziƙi da sauran su.
-
-38%
TSUMAGIYA
0Ina gabatar wa al’umma wannan littafi ne, a matsayin gyara-kayanka, don haska mana wasu miyagun ayyuka da wasu daga cikinmu suke cusa kansu a cikinsu, ko sa bari don a samu sauyi nagari a nan gaba. A ƙarshe, ina fatan Allah Ta’ala ya albarkaci wannan littafi da mai shi da sauran al’ummar musulmi gaba ɗaya. Amin.
-
-17%
Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka
0Baiwa ta naƙaltar harshe da iya samarwa da sarrafa kalmomi a tsari da ɗabi’ar al’umma
hanya ce wadda take ba da dama a shirya waƙoƙi kuma a rera wa jama’a. -
Wanene Bahaushe?
0Littafi ne da ya ƙunshi tarihin Bahaushe tun asali, da yanayin yanda yake gudanar da rayuwarsa da zamantakewarsa kafin zuwan addini da kuma bayan zuwan addini.
-
-38%
ZATON WUTA A MAƘERA
2Muna nan tsaye cirko-cirko da rana tsaka cikin jiran tsammani, idandunanmu bubbuɗe. Rana na ƙara zafi amma busawar iska da tsananin ɗoki ya sa ba mu ƙosa da tsaiwa cikin garjin ranar ba. Shitu ya haɗiye yawun da ke bakinsa a lokacin da ya ga ma’aikaciyar jinya ta tunkaro mu tana neman mai gidan Saratu.
-
-38%
ZOBEN ALƘAWARI
0Wasu shekaru masu yawa a can baya da suka shuɗe.
Matsanancin gudu take ci iya ƙarfinta ko waiwayen baya ba ta yi, dafe da turtsetsen cikinta kamar an kifa ƙwarya, da ya hana ta samun damar yin gudun sosai.